Sashe 14
Insaaf Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Asim hadaddan Gaye ne, ya'iya daukar wanka me daukar hankali, halinsa nede Sai ahankali kawai, miskilancin sa yayi yawa, kuma haka yasamo asali ne daga lokacin da yasan yanada maqiya daga gefe, koda yaushe idan yazauna yayi Shiru baida aiki Sai tunanin waye yake son ganin bayansa?, kalar fatar jikinsa fari ne sosai, bashida gemu saide saje daya zagaye bakinsa dashi wanda yaqara qawata fuskarsa, wani lokacin ko magana yake haka zakaga dimple dinsa suna futowa, bare kuma idan yayi murmushi anan ne zaka san daure fuskar dayake ba yayi masa kyau ko kadan
Shekarunsa 38, amma idan ka ganshi bazakace yanada wannan shekarun ba, saboda abinci dayake ci mai kyau da wajan zama mai kyau, uwa uba yawan motsa jiki dayake, wanda yazame masa dabi'a har hakan yasa hannunsa jikinsa ya murde musanman hannunsa, amma kallo daya zaka masa kasan cewa gwarzo ne kuma jarumin namiji, haka kuma dole ajinjinawa matar datake iya daukan larurarsa wato Lubna
Bayan yayi aure yadade bai samu haihuwa ba, Sai kwanan nan Allah yabashi yarinya mace, ya saka mata suna Hussaina wato sunan mamy, suke kiranta da Widad, kwata kwata yarinyar shekarar ta uku da rabi
Haka Amjad Shima fari ne sosai, idan ka ganshi shida Asim Sai kace iyayensu daya, saboda kwata kwata Amrah ita Bata iyo farin su ba, tanada Dan duhun fuska kadan, Sukuwa duk farare ne har mamy
Shekarunta 30 shikuma Amjad 29
Mace ce ita maison ado, dakuma son girma, batason raini, shiyasa tasu ba tazo daya itada Amjad ba, tun suna Yara har yanzu idan suka fara fada itadashi saika dauka qananun Yara ne, musanman idan suka fita unguwa wani yace ita qanwar sace, anan za'a dinga fada, wannan shekara dayan data bashi ganinta take kamar ta bashi shekara dari
Da kudin INSAAF dayake wajan Asim yasake Bude wani reshen kamfanin nasu a Yola, shine ya yanke shawarar zai Dora Amjad akai, wannan dalilin ne yasa suka shirya sukaje Yola domin Bude wannan company, kuma daga wannan ranar yasan cewa har yanzu akwai sauran masu bibiyar sa domin kashe shi, dama yadade Yana nazarin dauke duk wasu takardu dayasan banashi bane na INSAAF ne, domin ya dorasu Akan laptop, kuma yayi nasarar hakan, daga qarshe kuma ya nemi computar yarasa,(
Hajiya Amina ta dauke mana kuma Naga alama batada niyyar bamu
Back to story
To masu son jin labarin Asim, gashinan, yanzu kunji alaqar sa da Ishraqa, qawarsa ce, class mate dinsa, aminiyar sa
Comments pls
El~Yaqoub
[2/8, 10:21 PM] El~Yaqoub: INSAAF
Writing By:Amnah El~Yaqoub
13&14
Like my page on Facebook
https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493/
Har Asim yafuto daga wanka Lubna tana kuka, kallanta yayi yadauke kansa, gaban mirror ya qarasa Yana shafa mayuka masu Dadin qamshi a jikinsa, fatar nan Sai shining take, murdaddan jikinsa ya baiyana, faffadan qirjinsa ya sake futowa sosai, itama dataga tayi kukan tayi,amma ko kula ta baiyiba Sai tayi qwafa tafice daga d'akin
Bin bayan ta yayi da kallo, yaje yarufe kofar d'akin sannan yacire towel din yajefa shi kan gado (
yarasa meyasa Lubna ta raina shi, kokuma saboda tana ganin baya daukar mataki a kanta ne oho.
tsaf ya shirya a tsinake cikin manyan Kaya, riga da Wando na farin yadi, Ana iya hango farar Singlet din jikinsa, bazai taba iyuwa ka kalleshi ka dauke kanka ba, Sai zuba qamshi yake, yafuto fuskar nan tasa amurtuke, Lubna tana zaune afalo tana danna waya, qamshinsa dataji ne yasa ta daga kai ta kalleshi, Kasa dauke idonta tayi akansa, ita kanta tasan cewa tayi sa'ar miji, amma har yanzu yakasa ganewa cewa saboda kishin sa take wani abun
Maimakon tatashi ta bashi abincin saita dauke kanta, Shima bai nemeta ba yaci abincin sa yawuce d'akin mamy,alokacin mamy tagama yin sallah kenan itama futowa zatayi, Yana ganin haka Shima saiya biyota suka dawo falon
Lubna tana ganinsu tatashi tashige dakinta, mamy tana ganin yanayin fuskarta tasan cewa akwai damuwa, saboda Lubna Bata iya boye bacin ranta ba
Akan kujera ta zauna Shima Asim dayake binta kamar jela ya kwanta Akan kujerar sannan yayi fillo da cinyar mamy ya lumshe Idonsa baice da'ita komai ba
Mamy tayi murmushi, tana shafa sumar kansa datake sheqi, inde wajan kwanciya akan cinyar ta ne taga alama da Amjad da Asim dakuma 'yar Asim din sune zasu qarasa mata 'yar cinyar Tata (
Shi Asim saide kawai yayi fillo da cinyar Tata ya lumshe ido yayi shiru, har Gara Amjad surutu zaiyi ta mata, ta wannan Fannin kam Amrah ta qwace girman, domin kuwa duk cikin su itace Bata wannan son jikin
Ajiyar zuciya tayi tace "meya hadaka da matarka Asim?"
Idanunsa a lumshe yace "babu komai mamy"
Mamy najin haka tayi Shiru, tsakanin mata da miji Sai Allah, kartaje Garin tambaye tambaye ta tambayowa kanta abinda yafi qarfin kunnanta
Dayaji tayi Shiru batace komai ba saiya bude Idonsa yace "Mamy inason Minal Takoma School"
Tace "eh kayi tunani mai kyau, kafin muga abinda hali zaiyi Itama nasan karatun nata yayi Nisa, yarinyar nan tana bani tausayi Asim"
"abinda takasa ganewa kenan" ya Fadi hakan a baiyane, shi yayi tunanin a zuciyarsa yafadi maganar Yana nufin Lubna takasa gane Amina abar tausayi ce, ashe afili yafada
Mamy tace "wacece takasa gane hakan?"
Kansa ya Sosa yace "ahh babu komai mamy"
Jinjina kanta tayi batare da tayi magana ba, ta riga tagano bakin zaren, tasan da Lubna yake, kowa yasan kishin Lubna Akan Asim, kuma yanzu ma tasan Akan kishin ne suka samu wannan Dan sabanin, duk da yaqi fada mata ko menene ya hadasu
Amina tafuto daga d'akin su zata kawo masa handkerchief dinsa tayi tozali dashi a kwance Akan cinyar mamy,taqame awajan cikin tsananin mamaki, yanzu wannan qaton ne mamy tabari ya kwanta Akan cin yarta?
Kuma itama Sai shafa kansa take yawani lumshe Idonsa Sai kace d'an jariri, Ahankali tajuya Takoma cikin daki batare da sun ganta ba
*** ***** ***
Kamar kullum yauma sassafe tabi ta Corridor tahau saman beni tana Kallan gidan wannan matar da Anty Amrah takirata da Ishraqa, ba tasan dalili ba tun lokacin data ganta taji tanason sake Sakata a'idonta, matar tana birgeta, gata yar gayu,komai nata abin birgewa, bataqi ace ta zauna tanata kallonta ba
Yau sosai take fuskantar gidan ma, ko tsoron su gantabataji, har wani karkata kanta take tana hango lungu da saqo na gidan (
Zagaya wajan tafara yi,tana miqa wuya saikace wanda a kace mata Ishraqan tana zaune ne a compound
"ke kam Narasa meyasa kika liqewa wajan nan Minal"
Juyawa tayi ta kalli anty Amrah tayi murmushi tace "Anty Amrah inason nasake ganin wannan matar dakikamin Bayanin tane ranan nan"
Cikin mamaki Amrah tace "wacce mata kenan?"
Hankalinta Yana kan gidan batare data kalleta ba kai tsaye tace "ANTY ISHRAQA"
Amrah tayi murmushi tace "tana birgeki kenan"
Itama cikin murna ta juyo tana kallon Amrah, har Hakan yabawa Amrah mamaki ganin ita ba gwanar Fara'ah bace, babu wanda zaice yaga Minal tana dariya tunda sukazo gidan
Cikin farin ciki tace "eh Anty Amrah, tana birgeni sosai, inama ace zata rungume ni aqirjinta ko sau daya ne"
Amrah ta zaro ido tace "ta rungume ki Minal?" (
Hankali kwance tace "eh wallahi"
Amrah ta jinjina kai tace "Eh lalle Minal bakida hankali" (
Daga nan tajuya tayi cikin gida tabarta awajan
Ko kadan bataji haushin maganar da Amrah tafada mata ba, saima cigaba da Kallan gidan datayi, tana jira taga futowar Ishraqa amma Shiru Bata ganta ba, haka tayi ta zama harta gaji da jira tajuyo cikin gidan itama
Tazo wucewa ta saitin window din d'akin Anty Lubna taji tana waya, kuma batayi qasa da muryar taba, Ana iya jiyo abinda take fada
Haka kawai ta tsinci kanta da tsayawa awajan, gabanta ne yayi mummunar faduwa yayinda taji Anty Lubna tana cewa "Zansaka masa maganin a cikin abincin sa, insha Allah wannan Karon zamuyi nasara akansa, Yana can yanata fishi, aini inde Akan wannan shegiyar insaaf dinne zan'iyayin komai, natsaneta tun kafin nasan ko wacece, suma layun duk zan binnesu yau, kuma Insha Allah baza'a samu wata matsala b....
"
Bata gamajin wayar ba jikinta ya dauki rawa, gabanta yaci gaba da faduwa, har wani duhu duhu take gani, Ahankali tajuya zata koma baya, amma inaaaa!
Kafafunta sun gaza daukar ta, dole Sai awajan ta zube, yanda kasan yar bori haka ta Zauna, Sai numfashi take saukewa yayinda idonta yake kan windon d'akin Anty Lubna, kanta tacusa cikin Kafafunta tana furta kalmar "innalillahi wa Inna ilaihirraji'un"
Yaya Asim zata binnewa laya?
Tome zata saka masa a cikin abincin?
Karfa ta kasheshi, wata zuciyar tace toke ina ruwan ki? ba'a haka kikazo kika samesu ba?
Wata zuciyar tasake cewa aikuwa tana kasheshi kanki zata dawo, (
Idan Bata kasheki ba kece mace ta farko da zata sa akoreki daga gidan
Cikin sauri ta tashi tabi ta wata hanyar Takoma falon, ya kamata ace ta taimaka masa, ko banza shine mutum nafarko daya taimaka mata alokacin da mutanan qauyensu suka gujeta, Alokacin da wanda take ganinsu kamar iyayenta suma suka gujeta
Afalon tazauna tayi tagumi hannu bibbiyu, dole zata Sawa Anty Lubna ido taga inda zata binne layun, abinda takasa ganewa shine dama Anty Lubna tana da sa hannu wajan son kashe Yaya Asim?
Kokuma saboda insaaf dinne zatayi haka kamar yanda taji tana fada?
To Wai wacece INSAAF dinne?
Kuma dawa take wannan wayar?
Duk wanda ya ganta awannan lokacin yasan kawai de tana zaune ne, amma kana ganin ta zaka san cewa hankalinta baya jikinta
Anty Amrah tafuto falon itama, ganin Amina yau azaune afalo tana kallo Sai tayi mamaki, tazauna ta dauki wayarta tana danne danne
Widad ce tafuto daga d'akin mamy kai tsaye wajan Amina ta nufa tazauna akusa da'ita tace "Kema kinayin kallo?"
Kafin Amina tabata amsa Anty Amrah Tace "fada mata dai widad, kema dole kiyi tambaya tunda Kinga yau tabamu mamaki ta zauna afalo tana kallo"
Murmushi Tayi takama hannun widad tace "inayin kallo mana Widad"
Zaro ido yarinyar tayi tace "laaaa dama kema kinsan sunana?
Toke ma ya sunan ki?"
Amina ta dauki yarinyar ta dorata Akan cinyar ta tace "Sunana Amina"
Dariya widad tayi tace "to Amina zakizo kina tayani wasa a dakina?