← Book details Insaaf Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 53

Sashe 51

Insaaf Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kowa kika gani da haka yasa ba Amrah, kicire tsoron sa aranki, inba hakaba ramewa zaki dinga yi, kiyi hakuri kinji, kuma ki dinga shiga ruwan dumi kina zama"
Hawaye ta share tace "to Anty"
Ishraqa ta kamo hannunta suka futo, murya qasa qasa tayiwa mamy sallama sannan suka tafi
Tsawon wata biyu kenan suka dauka suna gudanar da rayuwar su cikin farin ciki, yanzu kam Amrah harta saba da Amjad, tasaki jikinta tana zaune lafiya dashi, Insaaf yanzu ta Dan rage yawan kwadayi tana rainon cikinta itada Asim batada wata damuwar komai, gasu Inna atare da'ita, ga iyayenta gakuma mamy da mijinta, haka rayuwar su taci gaba da Juyawa cikeda farin-ciki babu abinda ya sauya har watan haihuwar ta ya kama, gaba daya kafafunta sun kumbura, idan tazauna daqyar take tashi, tana Hawa Asim tausayi sosai, ga yarinta, shiyasa koda yaushe yake zaune agefenta koda akwai abinda take buqata, Ishraqa tanaso idan Insaaf ta haihu tadan sake gyara ta tunda haihuwa ce har yan biyu, shiyasa tacewa mamy ko zata Bata Insaaf bayan ta haihu tayi wanka saita dawo dakinta, babu musu mamy ta amince, saboda tasan tsakanin ya da uwa dole akwai wasu abubuwan daya kamata ace sun shirya, kuma koba haka Bama yawanci a al'adance a nayi
Asim nede yaji babu dadi duk da ba Nisa zatayi dashi ba ga-gida ga-gida, kwanan ta biyu da tafiya amma Sai yaji kamar tayi shekara Bata tare dashi, yau da wuri ya shirya ko break fast beyi ba yayi wa mamy sallama, ta kalleshi tace "bazakayi break fast bane?"
"ina sauri mamy, zanje office ne akwai abinda zanyi"
"to Allah yadawo dakai lafiya"
Amsawa yayi sannan yafice daga gidan, suna futowa daga gida ya kalli direbansa yace "muje gidan Ishraqa"
Babu musu direban yajuya, suka qarasa gidan, Ishraqa tana break afalo taga Asim yashigo, mamaki ya kamata yaushe Rabon ta dataga Asim a gidanta, Sai yau Sanadin Insaaf
Tace "Asim sannu da zuwa"
Zama yayi Akan kujera yace "yawwa Maman Insaaf, yagida yame jiki?"
Bread ta karya tanaci tace "Insaaf, inajin tana dakinta, uwar raki, komai raki, duk kagama sangartata, haihuwa cede a gaban ku"
Kallon ta yayi yaga tana magana hankalinta kwance, bread ma takeci amma tabar masa mata adaki yace "yanzu tayi break fast ne?"
"nakai mata abincin ta, inajin taci, Kai zataci ma, waya fada mata Yara biyu wasa ne, cikin ma kadai zaisa ta jin yunwa"
Ajiyar zuciya yayi ya tashi yashige d'akin Insaaf, Ishraqa ta kalleshi tace kukuka sani
Yana shiga d'akin yaganta azaune da uban ciki, wanka tayi tana shiryawa, tana ganinsa tace "Sannu da zuwa Yaya"
"Sannu baby, ina missing dinki da yawa" ya qarasa maganar Yana shafa cikinta
Rigarta ta daga sata saka, ya taimaka mata tasaka amma Sai taqi saukowa qasa, cikin shagwaba tace "Yaya kagani fa, Allah duk kayana sunmin kadan" tana qarasa maganar hawaye ya silalo daga idonta
Lokaci daya ya rikice "kiyi hakuri baby, sorry sorry, ai kin kusa haihuwa insha Allah tunda edd dinki yacika, yi hakuri kinji" yajanyota jikinsa ya rungume ta sosai, itama jin qamshin turaren sa yasa ta gyara kwanciyar ta a qirjinsa tare da lumshe idonta
Amnah El yaqoub
[3/7, 4:05 PM] El~Yaqoub: INSAAF
Writing by:Amnah El yaqoub
57&58
Like my page on Facebook
https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493
*Dedicated to:*
Fati Ahmad(fatyn yalleman)
Anty mama
Hafnah El Yaqoub
Hudancy luv
Fatyn Kaihaf
*Special gift to:*
Its Sadeek
Fauziya s madaki
Unique Jamaal
Prince Abba bakarya
Ayusher Abdallah
Alhusna Mrs Idris
Maman Musa
Hannunsa yadora abayanta Yana shafawa, sun dauki lokaci ahaka sannan yatashi yaduba mata doguwar riga acikin kayanta, yasaka mata
Ishraqa ta jisu Shiru babu wanda yafuto acikinsu, afili tace "ku kuka sani" daga nan tatashi tayi dakinta
Shikuma Asim abincin ta na break yaja yafara Bata, Shima ba abincin yaci ba, Danhaka yayi zamansa Yana Bata Shima yanaci, saida yaga taqoshi sannan yatashi zai tafi office, tace "Yaya idan katashi zaka biyo tanan?"
Kansa ya Sosa yace "A a baby, ba lalle ba, Kar mamanki tace ina damunki"
"babu abinda zata fada wallahi, nide ka shigo Dan Allah, inaso naganka"
"angama baby, idan na tashi zanzo kiganni saina wuce gida"
Kokarin tashi take tace masa "muje na rakaka"
"a a a a baby, kinyi nauyi dayawa ai, kiyi zamanki ki huta"
Zama tayi tace "Allah yadawo min dakai lafiya"
Murmushi yasaki, yaji Dadin Addu'ar Tata, saida ya sunkuya yayi kissing lips dinta, sannan ya amsa da Amin, yafice daga d'akin, yayi tunanin zaiga Ishraqa afalo Sai yaga Bata nan, bai nemeta ba Shima yafice daga nan suka wuce office
*** ****** ***
Bayan sati biyu
Tana jikinsa a kwance Sai zance yake mata murya qasa-qasa, riqon ta yake Akan ta shirya tabi shi sutafi
Tace "yanzu Amjad idan nabika kuma su mamy fa"
"yanzu tare kike dasu?

Idan naje Yola ma bazan Dade ba zan dawo tunda na barki anan, amma idan kika shirya muka tafi nasan bnda wata damuwa, kina tare dani"
"toka bari idan naji sauqi saimu tafi, yanzun banajina normal kamar da"
Kallanta yayi Dasauri yace "kede kifadamin kode qwallo na tashiga raga"
Kukan shagwaba tafara masa tana masa wani irin dukan soyaiya a qirjinsa, murmushi yayi yana qara godewa Allah Wai shine Amrah tasake dashi haka har dasu shagwaba
Kanta ya shafa yace "Anty Amrah kifadamin gaskiya bahaka bane?"
Cikin shagwaba tace "to ba gashi kasani yanzu ba"
Wata irin runguma yayi mata Yana fadin "Alhamdulillahi, Nima na kusa zama Daddy Anty na zata Haifa mun Baby"
Tanajinsa tayi Shiru, ita kunya takeji ace Wai cikin Amjad ne a jikinta, yanda ta botsare afarko harda cewa bazata dawo gidansa ba, gashi yanzu tadawo anjita shiruuuu harda tsarabar Baby, shi kuwa Amjad wayar sa yad'auka yakira mamy, amma Bata kusa Bata dauka ba, saiya tura mata text yafada mata, yakira Asim Shima yafada masa, bayan sunyi sallama Asim ya Girgiza kansa, Amjad kenan, wayaga Amjad da Baby
*** ****** ***
Yau tunda tatashi take jin jikinta babu dadi,ga wani irin ruwa datake zubarwa, ko awa daya Bata qaraba cikinta yafara ciwo, Ishraqa na ganin haka, suka wuce asbiti cikin sauri, saida likitoci suka karbeta sannan tasamu takira mamy da Asim ta sanar dasu, Hankalinsa atashe sukazo Asbitin, tunda safe take labour har azahar, Asim yarufe fuskarsa da hannayensa Yana Addu'ah Allah yasauketa lafiya
Sai bayan sallar la'asar sannan suka jiyo kukan baby, gaba daya su ukun atare suka miqe tsaye, wannan ya kalli wannan, wannan ya kalli wannan, mamy ta daga hannunta Sama tace "Alhamdulillahi...."
Asim kuwa wata irin qwalla ce tafuto masa, Ahankali yasa hannu ya goge Yana qara yiwa Allah godia a ransa, Insaaf kuwa ba tasan ma meta Haifa ba, tana haihuwar ta suma, saida aka dauki lokaci ta farfado sannan taji wani irin ciwon daya take nada, lokaci daya ta gagace tana kuka da Addu'ah
Daya daga cikin nurse din ce tafuto musu da babyn da aka Haifa, cikin sauri suka qarasa wajanta, Cikin murmushi ta miqawa Asim babyn tace "Yallabai ina tayaka murna ansamu Baby boy, amma madam tana wata naqudar"
Jikinsa a sanyaye yakarbi Yaron, Allah abin godia, gaba daya Yaron kamar Asim ne, babu inda yabar Asim, mamy ta qaraso ta karbe shi daga hannunsa tace "kayi mata Addu'ah Asim, insha Allah zata sauka lafiya"
Sai alokacin yadanji nutsuwa a ransa
Saida ta qara awa uku atsakani, sannan ta haihu, daganan kam baccin wahala ne yadauke ta, ba tasan inda kanta yake ba, wata nurse din tasake futowa da wani babyn a hannunta tace "Tasauka hajiya, ansamu wani na mijin, zamu kaita d'akin hutu zuwa anjima zaku iya ganinta"
Asim baisan lokacin da yaji hawaye yazubo masa ba, Ishraqa ta kalleshi tsananin tausayin sa ya kamata
Yara masha Allah lafiyaiyu dasu masu kama daya Sak babu banbanci, kuka daya yafara, Shima dayan yanaji yafara nasa, gaba daya Sai suka kaure wajan da kuka
Asim ya kallesu ya kalli mamy "mamy kuka sukeyi, ko mamansu suke so?"
Mamy tayi murmushi tace "Suda ko ganinta ma basu yi ba Asim, yunwa ce kawai"
Ishraqa tace "ko abasu dabino da zamzam?

Mun taho dashi"
Asim ya kalleta yace "Abasu mana, zoki basu"
Matsowa tayi ta karbe su daya bayan daya ta basu, yaran take qarewa kallo farare kamar ba hausawa ba, Wai Insaaf dinta ce ta haifesu, Allah ya basu ita ita kadai, gashi yanzu ita yabata biyu alokaci daya, wayarta ta dauko ajaka takira El Hameed dayake wajan aiki tace "to Habiby Insaaf tasauka, kasamu abokai biyu"
Cikin farin ciki yace "kaiiiii Alhamdulillahi, ganinan zuwa, Karki bari adamesu ganinan zuwa"
Wayar takashe tana mamakin wannan soyaiya ta El Hameed Akan jikokinsa, aiko Asim din Sai haka
Mamy takira Amrah da Amjad duk tafada musu, lokaci daya asbitin ya karbi baquncin su
Sai dare sannan Insaaf tafarka, cikinta tafara shafawa taji kwalaf babu komai, Sai wata yunwa datake cinta, likitan ya basu Damar ganinta, aikuwa gaba dayansu suka shiga, yaran farko Yana hannun Amjad, dayan kuma Yana hannun El Hameed
Kawai tana ganinsu ta rufe fuskarta da hannunta, gaba daya saita basu dariya
Yaran suka ajiye mata amma firr Insaaf taqi dago kanta ta kallesu, mamy tace subar d'akin ko zata sake da yaran
Asim kam qin fita yayi daga d'akin, Yana ganin fitar kowa yataho wajan ta cikin sauri ya rungume ta, atare suka saki Ajiyar zuciya, bai iya hakuri ba saida ya lalubo bakinta yadinga kissing, dan kansa yazare bakinsa anata, Sannan yace "I luv you my dear, Allah yayi miki albarka, kingama min komai a rayuwata, kalli yaran da kika Haifa mana, suna kama dani Insaaf, Allah yaraya min ku gaba dayanku, Allah yasa ki sake Haifa min wasu yan biyun"
"Yaya haihuwa da wahala fa, jinayi kamar zan mutu, Bazan sake haihuwa yanzu ba, Gara muyi planning"
"bazaki mutu ba baby, amma Dan Allah kidena maganar planning dinnan, shekara kusan arba'in nake shirin yi Insaaf, amma Kinga Sai yanzu Allah yabani haihuwa, ta Yaya zan dakatar da baiwar da Allah yayi min?
Chapter 51 · 0% Book details