← Book details Insaaf Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 53

Sashe 2

Insaaf Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

INSAAF LTD (OIL&GAS SERVICES)
anyiwa wajan kwalliya sosai yanda ya kamata,mutane sun taru danqam awajan, su kadai ake jiran zuwansu, cikin sauri daya daga cikin Escort dinsa yabude musu bayan motar suka futo shida qaninsa
P.A dinsa Auwal ne yamatso da sauri yafara yimasa Bayani "Yallabai wannan sune takardun dazaka saka hannu bayan angama taro, sannan akwai wasu baqi da suke buqatar ganinka, akwai maganar kwangila data kawosu wajanka, dangane da wajan wannan taron kuma babu matsala, angama komai kamar yanda kabada umarni"
Adede lokacin da PA yagama Bayani, adede lokacin suka qarasa ciki, ahankali yace "Okey"
Bayan yagama jin Bayanin nasa
Bayan anbude taro da Addu'ah kuma anyi Bayani sosai Akan wannan company, Sai aka Bawa mamallakin company dama yayi nasa jawabin, bedauki wani lokaci mai tsawo Yana Bayani ba, ya damqa amanar kula, dakuma riqe wannan company a hannun qaninsa, kuma dan'uwansa, ma'ana yabashi dama ya tsaya a matsayin shugaba na wannan company
A take wajan ya dauki qaran tafi, kowa farin-ciki dauke Akan fuskar sa, mutane dayawa kuwa suna mamakin irin yanda yake qaunar wannan qanin nasa
Lokaci daya hawayen farin-ciki suka zubo masa, yadaga kansa ya kalli yayan nasa, Ahankali yace "Yaya..."
Cikin sauri yayan nasa ya dakatar dashi ta hanyar daga masa hannu, saida yagama ganawa daduk mutanan da PA dinsa yayi masa Bayani, sannan sukai shirin tafiya gida, kwata kwata zuwansu, dagama taron bedauki wani lokaci maai tsawo ba, mutane sunci sunsha sunyi hani'an, amma shi oga kwata kwata ko ruwan wajan baishaba
Daga nan basu tsaya yin komai ba, aka Bude masa Mota suka shiga, Yana zama wayarsa tafara qara, be dauka ba, saida yabari ta katse dakanta, sannan ya kirata, yanaji andauka daga daya bangaren yace "ISHRAQA"
Saida tayi murmushi sannan tace "dama kiranka nayi inji Yaya taro, dafatan komai lafiya"
Ahankali kamar mai koyon magana yace "koh?"
Dariya tayi, tace "Naga alama har yanzu fishi kake dani saboda naqi zuwa,akwai abinda yasa banzo ba"
"yayi" shine kawai abinda yace
Dan daga muryarta tayi cikin fishi tace "Wai kai Sai wani binka nake Ina baka hakuri Sai kace wani sarki Sai amsamin kake kamar bakaso d'an rainin hankali kawai, ni Sai anjima" tana fadar haka takashe wayarta
Murmushin dabai shirya yi bane ya qwace masa, har dimple dinsa ya futo sosai, cikin ransa yace "yar rainin wayo kawai" sannan ya ajiye wayar agefensa yabude computer Yana Moving wasu documents zuwa wata folder
Qanin nasa yayi sakare Yana kallansa, zai Iya cewa tunda Garin Allah ya waye babu wanda yaga murmushi afuskar yayan nasa, amma saboda Ishraqa tayi magana dashi har tayi Sanadin sakashi murmushi, shikam baisan shaquwar datake tsakanin suba, abinda yasa ni shine Ishraqa abokiyar shawarar yayan nasa ce, kuma baya boye mata komai, haka itama yasan sirrikanta dadama a matsayin su na Class Mate kawai
Ajiyar zuciya yayi, yadubi yayan nasa "Yaya Naga Alama kana cikin farin ciki saboda Anty Ishraqa takiraka, kude kuna son junanku, inama ace Nima nasamu qawa wadda zamuyi qawance da'ita haka kamar ku"
Juyowa yayi ya kalli qanin nasa, tsantsar Kallan yarinta da shirme yake masa, in banda shirme mezaisa yace suna son juna da matar datake da aure akanta, batare da yayi magana ba, ya maida Hankalinsa kan computer
Haushi ya kama qanin nasa, Dan haka Shima yayi Shiru kawai
Bayan wasu mintuna ya dago kansa tare da rufe laptop din,yasaka ta a cikin jaka sannan yarufe jakar, Ahankali yafara magana "Nagama Dora kowanne documents dawasu takardu daya danganci filaye,gidaje, gonaki, da takardun duka sauran companies na INSAAF dama sauran kadarori Akan laptop dinnan"
in banda qanin nasa Yana kusa dashi da bazai jishi ba, cikin sauri ya kalli yayan nasa "Amma Yaya kana ganin babu kuskure kuwa Akan hakan?"
Shima Kallan qanin nasa yayi cikin mamaki batare da yayi magana ba, wanne irin kuskure yake magana Akan Andora takardun komai Akan computer?

Ai Yana ganin kamar hakan shine zaifi sauqi
Kafin qanin nasa ya sake magana aka yiwa motar tasu wani irin duka, arazane suka d'ago kansu suka kalli gabansu, cikin sauri driver yataka birki, hakan dayayi shiya basu Damar dukan motar ta ko'ina, gaba daya sun faffasa glass dinta
dak! dak!! gaban qanin nasa yafara faduwa,musanman dayaga gabza gabzan qartin dasuka zagaye motar tasu, lokaci daya tsoro yakamashi ya kama murdaddan dantsan hannun yayan nasa yariqe (
Jikinsa Sai rawa yake, shikuma gogan ko kadan babu alamar tsoro a ransa, bare kagani Akan fuskarsa, shi dama yasan dole za'a rina, tunda yaga babu motocin gabansu da bayan su yasan cewa dole ansake shirya masa wata maqarqashiyar kamar yanda aka saba
Jakar laptop dinsa ya dauka cikin sauri ya ratayata ajikin sa, sannan yabude kofar motar zai fita
Qanin nasa ya sake qanqame hannunsa, tuni hawaye sun samu matsugunni Akan fuskarsa (
Cikin kuka yafara girgiza kansa "Yaya ASIM.... karka fita, Allah zasu kasheka,Dan Allah Yaya karka fita suyima wani abu"
Batare dayace komai ba ya qwace hannunsa yafice daga motar, suna ganin futowar sa kuwa suka hau kansa da duka,babu ji babu gani,Shima yafara ramawa, driver Yana ganin yanda suke fada Shima yafuto da sauri domin temakon ubangidansa amma kafin yaqaraso daya daga cikin su yasa bindiga ya harbeshi acikinsa, nan take yace ga garinku nan (
Wani irin karfi ne yazo masa, har yayi nasarar qwace makamin daya daga cikin su yafara yimusu wani irin mahaukacin duka dashi
Shikuwa qanin nasa dake Mota qamewa yayi azaune, tunda yake baitaba ganin harbi a zahiri ba Sai yanzu, wani irin danshi yaji a Wandonsa, wanda ya tabbatar ko tantama babu fitsari ne (
Yajuya ya kalli yayan sa yaga yanda yake fada kamar a filin Wrestling, gaba daya Jikinsa ya dauki mazari, daya daga cikin yaran ganin Yana dukansu kuma idan sukai wasa tsaf zai musu illah, Dan haka nan take babu Bata lokaci yazaro bindigar sa yaseta shi, ji kake taaaas ya harbeshi akafardarsa
Wata irin gigitacciyar qara qanin nasa yasa, dakarfi yace "Yaya!!!"
Shikuwa Asim cak ya tsaya, lokaci daya ganinsa yafara daukewa,ya tabbatar da cewa mutanan da suke neman rayuwar sa yau sunci galaba akansa, Ahankali labbansa suka furta "Amjad"
Sannan yadaga hannunsa daqyar yayiwa qanin nasa daya Kira da suna Amjad alama yagudu, dif idanuwansa suka dauke, yazube Akan gwiwar sa, sannan yafadi awajan
Idanun Ammar sunyi jajir saboda kuka, Akan idonsa yayansa yafadi, yasan cewa yanzu kuma saura shi, cikin sauri yabude motar yafuto, bai tsaya awajanba ya kama gudu, baisan ma inda yake dosa ba
Suna ganinsa Yana gudun tsira, amma abin mamakin babu wanda yayi masa komai, asalima Dena kallansa sukai, ganin Asim a kwance kamar matattace yasa suka kwashe da wata irin dariya, su kayi kama-kama suka mai dashi cikin motar, hannunsa banda jini babu abinda yake zuba
Babban cikin su yakira waya yace "oga mungama aikinmu, yariga ya sheqa saide labarinsa"
Daga daya bangaren akai magana, sannan Yaron ya sake cewa "angama oga" daga nan yakashe wayar
Babban tafkin ruwan dake tsallaken titin wajan nan suka tura motar, babu tunanin komai suka tura motar da Asim din yake ciki cikin wannan ruwa
Suma suka hau motarsu suka tafi a dari da sittin, wajan yarage daga fassasun glass din motar, Sai jinin Asim daya zuba, dakuma gawar driver dake kwance male-male a cikin jini
Shikuwa Amjad Yana cikin gudu kwata kwata baya Kallan gabansa, saiji yayi wata Mota tayi Sama dashi, nan take yafadi awajan sumanme
*** ***** ***
Hawayen Idonta ta share Akaro na ba a dadi, mutuqar gajiya ta gaji da wannan diban ruwan, gashi yayanta baya nan, idan ta zauna ma babu abinda zatayi, Gara ta debo musu ruwan ko hakan zaisa ta ragewa kanta dinbin damuwar datake damunta
Tana qarasawa Rafin ta tsugunna da niyyar debo ruwan saitaga yayi ja, tasa hannu tana kawar dashi taga abu yaqi qarewa, tana juyawa hannun ta na dama taci Karo dashi, gabanta ne yayi mummunar faduwa, cikin sauri ta miqe tsaye ta callara wata irin qara wadda tasa cikin dajin amsawa, amma Shiru kakeji daga ita Sai kukan tsuntsaye, jikinta ne yadau ki rawa kakar-kakar, tafara ja da baya tana girgiza kanta, ganin cikakken mutum a kwance fari tass dashi tamkar bazaka masa hausa ya amsa ba, baya baya takeyi tana cewa "Ba mutum bane, wallahi aljanine" awajan tabar tulun ta kwasa aguje tayi gida, kasancewar tanada yalwar dukiyar fulani,Sai gudun datake yasa suma suke rawa
Baram!

Tabude kofar gidan su tashige, tana zuwa tsakar gidan tafadi akasa
Babanta da yayanta dasuka dawo daga cin kasuwa atare suka ce "Subhanallahi..."
Amma ko kallansu batayi ba, kokarin tashi take tashige cikin dakinta, Inna ce takamota tariqeta cikin tashin hankali tace "ke Amina, menene?

Keda waye?

Waye yabiyo ki haka?"
Hannunta tadora Akan qirjinta datake numfashi Sama-Sama Sai haki take saboda gudun datasha, takasa basu amsa Sai Hannunta dayake rawa ta daga tana nuna musu hanyar kofar gidan
Wacece Amina?

Meyasa ake gudunta?

Meyasa ake bibiyar rayuwar Asim?

Fan's ya bayan kwana biyu?

Amnah El~Yaqoub
[2/4, 11:22 AM] El~Yaqoub: INSAAF
Writing by :Amnah El~Yaqoub
Like my page on Facebook
https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493
Babane yaje Randa yadebo mata ruwa akofi, ya tsugunna agabanta tare da meqa mata "karbi wannan Kisha"
Dasauri kuwa tashanye ruwan, amma duk da haka tana Haki, saide ba kamar nadaba, duk sun zuba mata ido suna Kallan ta, yayanta ma ya matso kusa yace "meyake faruwa qanwata?
Chapter 2 · 0% Book details