Sashe 36
Insaaf Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ajiyar zuciya ya sauke ya kalli Mamy
"zantafi office mamy, saina dawo"
"inason magana dakai"
Dawowa yayi ya zauna, ta kalleshi da kyau, tanaso ta tambayeshi menene damuwar sa? dawa yake waya haka Sai kashe murya yake kamar yasamu budurwar sa, duk da tasan ba lalle ne yabata amsa ba, ya kamata ace taji da wadda yake wannan maganar, kartaje haqilon banza kawai take akansa
tace "dawa kake waya ne?"
Kai tsaye yace "Mami Minal ce..."
Murmushi tayi tace "lafiya dai ko?"
"gashinan de"
"meyake faruwa to?"
"mamy tunda sukai tafiyar nan Bata ta6a nemana ba, sannan memakon ta sauka anan shine tabisu Takoma can gidan, nakirata ina mata maganar Bata kirana, shine tacemin tayi missed din Amrah" yaqarasa maganar Yana hade rai
Mamy tayi Shiru tana Kallan tsantsan karfin hali dakuma rashin gaskiya irin na Asim, da kunnanta taji yana cewa Amrah tana son magana da ita, amma yanzu Wai qiri-qiri yake cewa yayi mata magana Bata kiransa
Kallansa tasake tace "Asim"
"na'am mamy"
Tace " kafita daga cikin Idona na rufe Asim,kafadamin kana son wannan yarinyar kokuma baka sonta?"
Cikin sauri ya kalleta yace "Mamy daga maganar kiran waya meya kawo zancen soyaiya kuma?"
Mamy tace "ikon Allah,toka sauwaqe mata, ina amfanin zama da mutumin da baya qaunarka?"
"to mamy waye yace Bana qaunarta?, itace Bata sona, Nima shiyasa ban nuna mata ba"
"waye yafadama Insaaf Bata qaunarka?"
"mamy Muhsin ne yacemin ranar dasuka hadu a hanya yadauke ta suka tafi gidansa ita da kanta take roqonsa yakai ta court Araba auren mu"
"Subhanallah..., to Amma kasan yarinya ce, sannan may be da rashin kulawar da kuke Bawa juna shiyasa tafadi haka, Asim baka kula ta, itama Bata kulaka, tayaya zaku Fahimci juna?"
"Nima bansan ina sonta ba, saida Muhsin ya fadamin, daga baya sainayi tunani Naga hakanne, sannan mamy akwai abinda nake tsoro, duk mazajen da Minal ta aura mutuwa suke mamy, inajin yanzu saura ni, saboda banajin zan iya rayuwa batare da'itaba Mamy"
Mamy tayi murmushin jin dadi, lalle fa a kace soyaiya mai sauya Bawa, Wai yanzu Asim ne yazauna yake fada mata yanda yake son wata yarinya, inda Ishraqa taji wannan maganar ai Zaman unguwar saiya gagareshi, Dan tasamu abinyi kenan
Tace "Asim maganar mutuwa kowa kaga yamutu, kwanan sa ne yaqare, Amma dama kasan tataba yin aure amma baka fada mana ba Asim?"
Kansa aqasa yace "Aurenta shida mamy, nine ba bakwai, kuma dukansu mutuwa suke, shine dalilin dayasa mutanan da suka raineta suka gujeta, ni kuma nataho da'ita"
"innalillah...., Asim aure shida fa kace?
To menene yake damunta?
Menene Sanadin mutuwar tasu?, aini nayi tunanin befi aure biyu ba kake nufi"
"A a shida ne, sannan Nima banyi mata wannan tambayar ba, saboda kartaga kamar cin fuska nake mata"
"tabdi, lalle akwai abinda yake faruwa, a 'yan qananun shekaru irin nata tayi wannan auren kuma ace duk suna mutuwa Asim akwai alamar tambaya, amma katashi kaje zanyi magana da Ishraqa, idan ma Addu'ah za'a mata da roqon Allah duk Sai ayi, amma kadena tsoro kaji?
"
ta qarasa maganar cikin sigar lallashi
Kansa ya d'aga mata sannan yace"to Mamy yaushe zata dawo?"
Mamaki de yaqara kama Mamy, tace "Asim kaida Ishraqa ai kunfi kusa, kaje ka dauko matarka"
Nayau ba yawa, kuyi hakuri please
Amnah El yaqoub
[2/25, 5:48 PM] El~Yaqoub: INSAAF
Writing by:Amnah El yaqoub
39&40
Like my page on Facebook
https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493
Cikin sauri yace "A a mamy, duk yanda kukai babu damuwa, Nina tafi office"
Mamy tayi murmushi tace "to Allah yadawo min dakai lafiya Asim"
*** ****** ***
Acan gidansu Ishraqa kuwa zaune suke afalo su biyu, mai ne a hannun ta tana shafawa Minal a kanta,wayar Ishraqa tayi qara, tana dubawa taga mamy ce, ta dauka suka gaisa cike da kulawa, mamy tace "Ishraqa kin dauke min yata, yaushe zata dawo ne?
Shima dan'uwan naki yanzu yagama mita Wai taqi tadawo, nace masa yazo yayi miki maganar shine yace duk yanda mukai daidai ne"
Dariya tayi tace "Mamy Aida kin turo shi yazo da kansa"
"a a, ai yanzu kin zama dodon Asim tunda yagane komai"
"babu wani dodo mamy, ai anzama daya, wallahi Nima inaso ta tare to jiya Sai muka tattauna Akan matsalarta nida Abbanta, yace zaije wajan wani malami yayi masa Bayanin komai, to shiyasa muka jinkirta, ashe Wai yarinyar nan tana tare da matsala amma daga ita har Asim din sukai Shiru mamy "
Mamy tace"kemade kya fada Ishraqa, ni Sai yanzu yake fadamin, shine nace zan sameki muji ta inda zamu 6ullowa matsalar, to ashe itama tafada muku"
"tafada wallahi, kibashi hakuri, idan Abbanta yadawo zanyi masa magana insha Allah"
"to shikkenan Ishraqa babu damuwa, amma babu wani taro da za'ayi Ishraqa?
Ina nufin na tarewar Tata, tunda Kinga dakuka ganta ma babu wani abu da mukai"
"to aini mamy duk jikina ne yayi sanyi, wannan matsalar Tata tafi komai dagamin hankali wallahi, a barshi kawai, muyi musu Addu'ah"
"toshknn Ishraqa hakanma yayi, Allah ya tabbatar da Alkhairi a gaida yartawa".
Suna gama waya ta kalli Minal tace "Insaaf, tashi kije ki dauko maganin ki Kisha, mijin ki Yana maganar tarewarki"
Bakinta taturo gaba, cikin shagwaba "Anty nifa tsoron sa nakeji,tayaya zamu zauna tare ni dashi, kuma ni gara mu haqura, banaso ya mutu"
"banason shirme Insaaf, cemiki akai shi din sonki yake?
To bari kiji da bakina da nasa anan wajan yafadamin tausayinki yake ba sonki yake ba, rannan daga ke saishi naganku afalo kuna zance, zaki kawomin maganar tsoro?
Kinga tashi ki dauko Kisha,idan baki shaba Yaya zanyi dasu?"
Haka taje ta dauki maganin Tasha, sannan tafuto, anan taga Abbanta harya dawo tare da wani malami, Allah ya Sota ta sanya hijabi babba, cikin nutsuwa ta gaida baqon, sannan ta zauna aqasa, Ishraqa ta futo da ruwa da lemo ahannuta ta ajiye musu, sannan tanemi waje ta zauna
Malamin ya dauki iya ruwa yasha, sannan ya qurawa Amina ido Yana kallanta, dago kanta tayi ta kalleshi, cikin sauri ta maida kanta qasa
Saida ya dauki lokaci yana kallonta sannan yace "ke!"
Batare data kalleshi ba tace "Na'am"
"kinada Aljannu ne?"
Cikin sauri ta kalleshi tana girgiza kanta "Aljannu, a a, ni banida aljannu, banida komai"
Murmushi Malamin yayi yace "shikkenan tashi kije"
Babu musu tatashi tashige dakinta, Malamin ya kalli El-Hameed da Ishraqa yace "Alhaji yarinyar ku tanada aljannu, kallo daya nayi mata nagane hakan, akwai baqaqen aljannu atareda ita, sannan jinnul Ashiq ya aure ta, bazai Bari tayi aure cikin kwanciyar hankali ba"
Hawaye ya zubowa Ishraqa, tasa bayan hannunta ta share, to a'ina Insaaf ta hadu da aljannu kuma?
El-Hameed yace "Subhanallah, yanzu Malam Yaya za'ayi?"
"akwai magungunan dazan aiko muku dashi , saita dinga amfani dashi, insha Allah komai zai wuce,saboda magungunane masu qarfi, idan akwai abinda ya faru kuma saiku sake sanar dani"
Godia suka sake yi masa, sannan suka rakashi yatafi
Suna dawowa El-Hameed yace " bansan yanda akai tasamu wannan matsalar ba, amma insha Allah komai yazo qarshe"
"abinda nagama tunani kenan Habiby, shiyasa itama tace tanaso tarabu da Asim, Kar Shima yamutu"
"a a maganar rabuwa da Asim ma ai Bata taso ba, idan tarabu dashi tayaya ne zamu gane aljanin yabar ta kobai Barta ba?"
"saida na6ata raina na nuna mata babu ita babu rabuwa da Asim, sannan ne tayi Shiru, kuma mamy tamin waya tanaso Insaaf Takoma Dakin mijinta"
"Allah yaqara kiyaye wa, insha Allah idan tafara amfani da maganin nata, saita koma"
*** ****** ***
Da yamma ya aiko musu da magungunan Kala-Kala, saida suka Bata maganin ne tasan cewa Kallon me aljannu suke mata, haka ta hakura ta karba, amma itade tasan cewa batada komai, sati daya suka dauka suna Kallan yanda take amfani da maganin, itade babu ranar fashi kullum saita Sha, amma duk lokacin da zatayi na hayaqi daqyar take yi, Sai Ishraqa ta tsaya a kanta
Saida tayi kwana goma tana amfani da maganin sannan suka fara shirin maida ta gidansu Asim
Ranar Yana wajan aiki, baisan a ranar za'a dawo da'itaba, Ishraqa kuwa da yamma ta rakata, bayan huduba datayi Mata, saita tagama hure mata kunne Akan kula da Asim sannan tabaro gidan
Dakin Amrah tayi Zaman ta, mamy tashigo d'akin da sallama abakinta, cikin ranta tace masha Allah, saboda yanda taga jikin Minal din Sai wani irin sheqi yake, dama tasan zata samu gyara mai kyau inde sukaje Sudan, bare ma yanda Ishraqa take yar gayu takame El Hameed gaba da baya babu yanda za'ai tabar 'yarta haka, zama tayi agefenta tace "Insaaf yakika zauna ke kadai?
Kikirashi mana"
Sarai tasan inda zancen mamy ya dosa, Sai tayi fuska tace "mamy ina Anty Amrah"
"Amrah taje unguwa, amma nasan kafin magrib zata dawo, kikira Asim yadawo da wuri, shida yake tambaya kinje kin zauna yaushe zaki dawo ai gashi kin dawo Shima saiya dawo"
Murmushi tayi batare datayi magana ba, mamy tace "zaman Aure Sai kinyi hakuri Minal... zomu zauna ne, zomu sa6a
Idan wani abu yashiga tsakanin ku mijin ki ne, kiyi kokari ki zaunar dashi ku sasanta kanku, sannan zan fada miki wani sirrin Asim guda daya, Yana son kulawa, shi mutum ne maison akulashi, ko rai ya6ata miki kikai fishi toki shareshi kidena kula shi anan Hankalinsa zai tashi, da haka Lubna ta samu kansa, amma ina fatan yasamu kulawa awajan ki fiye da wadda yasamu awajan Lubna, Kada kiji kunya ta, Nima kamar mahaifiyar kice"
Ahankali ta daga kanta tace "to mamy insha Allah"
Haka mamy ta zauna suna fira kadan kadan har aka Kira sallar magrib Amrah tadawo sannan mamy tabar d'akin
Amrah ta kalleta tace "Amarya Amarya, gaskiya ne, irin wannan kyau haka kamar an miki wankan inji?"
"kai Anty Amrah, ahakan?"
"Emana, kinganki kuwa?