Sashe 17
Insaaf Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Niban rungume taba"
"to koma de menene banason naqara jin hakan, kadena biyewa shirman Lubna"
Wata irin Ajiyar zuciya yasaki a6oye, sannan yayi hamdala a ransa da mamy Bata ganoshi ba, kansa aqasa yace "insha Allah mamy"
Tace "Allah yayi maka albarka, tashi katafi"
Babu musu ya tashi yafuto daga d'akin, mamy tabishi da kallo, itade tasan Asim baya mata qarya, amma wannan Sosa qeyar da yayi alamu ne na rashin gaskiya, kuma tunda take da Asim baitaba kawo mata yarinya yace yanaso ba, ita kanta Lubna tasan cewa bayaso amma ahaka ya aureta, to kode son Minal din yake?
Tayaya zata yarda cewa bai rungume taba?
Bayan kulle d'akin sukayi? (
Kuma sunaji Ana nocking sukaqi budewa, idan ba rungume ta yayi ba to nasiha yake mata?
Ajiyar zuciya tasaki tana fatan ace Bahaka bane, Dan batasan tashin hankalin da Lubna zata shiga ba Akan haka, kuma kowa Sai hankalin sa ya tashi Akan haukan kishinta
Amjad ne ya shigo d'akin, Yana zuwa yafada jikinta, cikin shagwaba yace "mamy I miss you sosai wallahi"
Kansa ta shafa tace "Anya kuwa Amjad wannan aikin naka baka saka shiririta acikinsa?
Daga zuwa wajan aiki yan Kwanaki harka dawo gida?"
Cikin shagwaba yace "uhm...
Allah mamy ni bazan iya irinna Yaya ba, bazan iya wata daya batare dana ganki ba"
Taji Dadin furucinsa sosai, tace "Allah yayi muku albarka autana, Allah yaraya minku"
Sake shigewa jikinta yayi yace "Amin, mamy wata magana zamuyi"
Dagoshi tayi daga jikinta, sannan tayi masa kallon fahimta tace "inajin ka, wacce irin magana?"
Kallanta yayi yace " mamy dama zan fada miki ne, inason Minal, inason in aureta idan kun amince Keda Yaya"
Murmushin manya mamy tayi, cikin ranta taji dadi sosai, ko banza Amjad yakawo musu maslaha Akan rikicin Lubna da Asim, tace "to Allah ya tabbatar mana da Alkhairi, zan sameshi muyi maganar dashi insha Allah"
Cikin murna Amjad yace "yes...shiyasa nake sonki mamy na, Allah yabar mana ke" yakama hannunta yayi kissing hannun, sannan yafuto daga d'akin cikin murna
*** ****** ***
Zaune suke a d'akin su washe Gari, itada Amrah
Amrah ta kalleta taga tayi Shiru tana tunani, ta matsa kusa da'ita tace "Minal, in baki wata shawara mana"
Kallonta tayi tace "menene Anty Amrah?"
Amrah takama hannunta tariqe tace "Bari kiji in fada Maki, Kinga idan zaki sake acikin gidannan ki dinga harkokin ki toki sake, wallahi idan kika tsaya Anty Lubna tana marinki, bakya ramawa, rainaki zatayi, kisaki jikinka, kema gidanku ne, ki dinga daukan wanka kina kwalliya, kisaki ranki, kiyi walwala, kiyi Fara'ah da dariya kamar kowa, babu wanda yataba ganin dariyarki a gidan nan Minal, kullum fuska babu Fara'ah kamar fuskar Yaya Asim "(
Murmushi tayi mai ciwo, tatuno asalinta, ba tasan wacece itaba,ba tasan iyayenta taba, waya sani ma ko shegiya ce shiyasa aka wullarta, idanunta yayi raurau kamar zatayi kuka tace"wacce irin walwala Anty Amrah,banda kowa, bansan tushenaba, bansan ta Yaya aka haifeni ba, ina Naga wani Damar da zanyi kwalliya?Kuma ni ban'iya Bama "
Amrah tasake matsowa tace" Minal, kowa baya wuce qaddarar sa, ni kinsan tawa kaddarar ne?
Nayi soyaiya da Al'amin, munshaqu da juna, kowa Yana farin-ciki da hakan, saida nagabatar dashi awajan Daddy da Mamy suma suka ce yayi, bashida matsala, Rana daya yazo wajena Yana kuka yacemin anyi masa mata agida, auren dole za'ayi masa, nashiga cikin damuwa,Yana kuka ina kuka, alokacin yace muyi alqawari bazamu taba rabuwa da juna ba, komin Daren dadewa injirashi zaizo muyi aure,lokacin ina shekara a shirin da biyar,Minal shekara daya tawuce, biyu ta wuce, Shiru babu labarin Al'amin, ni kuma abin baqin cikin shine yanda na yarda dashi, duk abinda yafadamin ina yarda dashi, saida abin ya ishi Yaya Asim yaje neman Al'amin da kansa, domin yaji meyake faruwa ne, lokacin dayaje bai samu Al'amin ba, amma yahadu dawani maqocinsu, anan aka sanar dashi cewa Al'amin ba auren dole aka masa ba, kawai yaudara ta yake, yarinyar daya aura ma yar unguwar suce,kuma kowa yasan Al'amin Yana son yarinyar, a ranar da Yaya Asim yazaunar dani yayimin fada na hakura da Al'amin, kwana nayi banyi bacci ba, Minal niban taba zaluntar kowa ba, ina zaune da kowa lafiya, amma ga abinda wanda nayarda dashi yayi min, har gobe idan nayi sallah ina roqon Allah, idan nice na zalunceshi, Allah yasa ka masa, idan shine ya zalunceni Allah yasa ka min, Minal shekaru na talatin yanzu babu aure, Abin Yana damuna sosai, amma babu yanda zanyi da qaddarar ubangiji, gashi ina walwala ta, ina harkokina kamar kowa, duk abinda yasamu Bawa yamiqa lamuransa ga Allah Minal, da wannan tunanin da kike da Addu'ah kika Dage da'ita, zaifi, amma Dan Allah ki saki ranki mu dinga abinda mukeso a gidan nan, ni tunda naganki sainaji kamar nasami 'yar'uwa, tunda dukansu yan'uwan nawa maza ne, ba kamar mace ba"
Minal tasaki Ajiyar zuciya ta kalli Amrah tace" yanzu Anty Amrah kedin har kinyi shekara talatin?
Naga jikinki bai nuna hakan ba"
Amrah tayi murmushi tace "inda nasake godewa ubangiji na kenan, yanzu babu wanda zai ganni nida Amjad yace nagirmeshi"
Zaro ido Amina tayi tace "waida gaske kinfi Yaya Amjad?, dama shiyasa yake cemiki Anty Amrah?"
Murmushi Amrah tayi tace "na fishi Minal, shekara daya nabashi, inde Kasa Allah acikin lamuranka ai zai taimakeka Minal, kema kisaki jikinki, kiyi gayu, ki daina yin Shiru, kuma inde kwalliya ce Karki damu zan koya miki"
Cikin mamaki tace "gaskiya hakane Anty Amrah, insha Allah Nima zan kamanta kamar yanda kika bani shawara, kuma dama Yaya Asim yace zai tayani duba iyayena"
Amrah ta kama ha6arta tana kallon Minal tace "Wai yaushe har kuke haduwa ne kuke fira ke dashi?, nifa mamaki nake, ganinake kamar ba Yaya Asim dinmu ba, Anya kuwa Minal babu wata aqasa?"
Rabonta da shagwaba harta manta, amma yau saita tsinci kanta dayin shagwabar, tace "Allah Anty Amrah babu komai"
Amrah tace "ai shikkenan, idan tayi tsami maji" (
Daga nan tafuto daga d'akin tana tunani a ranta, Amjad dinne zai samu kokuma Yaya Asim?
*** ****** ***
Dawowarsa kenan daga wajan aiki, fuskarsa babu wata Fara'ah kamar kullum, Yana sanye cikin suit da tayi masa kyau sosai, Kai tsaye d'akin Mamy yawuce, Yana zuwa ya ganta tana sakawa d'akin nata turaren wuta, brief case dinsa ya ajiye Akan gadon, sannan yacire jacket dinsa, itama ya wullata kan gadon, sannan yafada gadon Shima ya kwanta, tare da fadin,"Wash! sannu mamy" sannan ya lumshe Idonsa, inda ace zai samu maiyi masa tausa yanzu daya so hakan
Murmushi tayi tace "kaje wajan matarka ne?"
"no, ban shiga ba, sonake nafara ganinki mamy"
Tace "naji, to ai kaganni, kaje kaga matarka, Kaci abinci saika kwanta acan kahuta, cinyata Bata hutaba, gadona ma bazaku barshi yahuta ba Asim"
Murmushi yayi yabude Idonsa batare da yayi magana ba
Turo kofar d'akin tayi ta shigo bakinta dauke da sallama, jin zazzakar muryar ta ne yasa yakai Idonsa ahankali ya kalli kofar
Idonsu ne yahadu dana juna,Yana daga kwancan yazuba mata ido, Idonsa ne yasauka Akan qirjinta, yatuno lokacin data rungume shi, yaji wani irin laushi, cikin sauri ta dauke idonta itama, tana tuno ranar data fada jikinsa ta rungumeshi, da yanda ya sake matseta a jikinsa Yana sakin Ajiyar zuciya , shi kuwa Kasa dauke Idonsa yayi a kanta, yanajin wani irin yanayi na shigarsa
Gaba daya saita diririce tarasa mema zatace, amma data tuno shawarar Anty Amrah, saita ji qwarin gwiwa yazo mata
Wani irin murmushi tasaki tace "mamy sannu da aiki"
Sake Bude Idonsa yayi ya kalleta da tsananin mamaki, dama yarinyar nan tana murmushi?
Mamy kuwa kallonta tayi tace "sannu Minal, yau kece adakin nawa?"
Gabanta ne yafara faduwa ganin yanda yazuba mata ido Yana aikin kallonta, tace "eh mamy, dama nazo neman Anty Amrah ne"
"Amrah Bata nan inaga tana wajan Lubna, kije d'akin Lubna may be suna tare" (
Cikin ladabi tace "to mamy kawo na qarasa miki aikin"
Mamy tayi murmushi tace "a a Minal, jeki hutawarki, Aina gama ma"
Tace "to mamy afuto lafiya"
Sannan ta kalleshi, cikin sauri yadauke kansa, itama cikin ranta tace bayan nakama din, amma afili saitace "Yaya ina wuni"
"lafiya"
Abinda yafada kenan ya lumshe Idonsa, can qasan ransa yanajin Dadin yanda tafara sakin jikinta da 'yan gidan, laptop dinsace tafado masa, lokaci daya yanayin sa ya sauya
Tashi yayi, yafara daukan jacket dinsa zai fita, mamy ta dubeshi tace "Asim qaninka fa yabani saqo wajanka"
Kallanta yayi sannan yadawo kan gadon ya zauna yace "to mamy"
Itama zama tayi sannan tace "yace afada maka yanason auren Minal, ni kuma na amince masa"
Wata irin faduwar gaba ce ta ziyarci Asim, harya Kasa 6oye hakan saida yadora hannunsa Akan qirjinsa, mamy tana ganin yanayin sa mamaki ya kamata, Anya kalau Asim yake kuwa?
Hannunta ta Dora Akan kafadarsa tace "lafiya kuwa?"
Kansa ya jinjina yace "lafiya mamy"
Bakomai ne yasa gabansa faduwa ba Sai tinawa da yayi yanda mazajen da Amina ta aura suke mutuwa, aure shida kowa Yana mutuwa, hakan yana nufin Shima Amjad kenan idan ya aureta mutuwa zaiyi?
Anya kuwa zai yarda da wannan maganar?
To ai kuma mamy zata tambayeshi menene dalilinsa naqin yarda?
Mamy ta kalleshi da kyau tace "kayi Shiru Asim, ko baka amince bane?"
Fuskarsa babu yabo babu fallasa yace "a a mamy, Allah ya tabbatar da Alkhairi"
Daga nan ya tashi ya dauki kayansa yafita daga d'akin cikin tashin hankali, da kallo mamy ta bishi, taga gaba daya yanayin sa ya sauya, Anya kuwa Asim bayason Minal?
Meyasa yanayin sa ya sauya lokaci daya haka?
Yana futowa daga d'akin yafara furta kalmar innalillahi wa Inna ilaihirraji'un, tayaya zai Iya futowa fili ya fadawa mamy cewa Amina duk mazajen data aura mutuwa suke?