← Book details Insaaf Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 53

Sashe 16

Insaaf Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yana shiga d'akin ya ganta ta kifa kanta Akan gado tana rusgar kuka, tausayi tabashi sosai, shide Yana tausayin yarinyar
Ahankali ya zauna agefen gadon dab da'ita, so yake yabata hakuri, amma yarasa mezai ce mata, shide ba lallashin matarsa yake ba bare ya qware wajan lallashi, komaai saide ayi masa, kamar bakinsa Yana masa nauyi yace "kiyi Shiru"
Dago kanta tayi ta kalleshi, batare da tunanin komai ba tafada kan faffadan qirjinsa ta rungume shi sosai tana cigaba da kuka
Mamaki ya kama shi, yarinyar nan kuwa kalau take?

Meyasa zata rungume shi,sake kallanta yayi yaga yanda ta kwantar da kanta Akan qirjinsa,Kasa rungumeta yayi da hannayensa, kukan datake dakuma yanda yake jin tudun nashanunta Akan qirjinsa shine ya haddasa Masa shiga cikin wani yanayi, gakuma tsikar jikinsa Sai tashi take, Ahankali kamar mai tsoron wani abu yasa ka hannunsa ya rungumeta sosai,Yana bubbuga bayan ta alamar lallashi, ita datake kuka maimakon ace itace take sauke Ajiyar a zuciya Sai abin yazo a bazata, domin kuwa wata irin wawuyar Ajiyar zuciya Asim yake saukewa Ajere (
Lubna tabiyosu cikin d'akin cike da masifa, amma saide me?

A halin data gansu ne yasa tajuya cikin tashin hankali ta Dora hannu aka, tasaki ihun kuka "nashiga uku na,nashiga uku shikkenan ta qwacemin mijina"
Asim yanajin kukanta yajanye jikinsa daga na Amina ahankali, ya tashi yakulle kofar d'akin,(
) sannan yadawo yazauna aqasan gadon, yakamo hannyen Amina datake zaune Akan gado yariqe hannayen nata cikin nasa,yazubawa fuskarta ido Yana kallon yanda gashin idonta suka jiqe, saboda kuka
Ita kuwa Amina Kasa dago kanta ta kalleshi tayi, hawaye Yana silalowa daga idanuwanta zuwa kan kumatunta, gashi babu Damar gogewa ya kama hannayen nata duka biyun yariqesu cikin tattausan hannunsa
Mamy da Amrah ne suka qara so wajan, futowar ta kenan daga wanka Amrah tace mata gidan nasu ba qalau ba tazo tayi musu magana
Lubna tayi wani irin zama a falon tana ihun kuka Minal ta qwace mata miji
Mamy ta qarasa bakin kofar d'akin tafara nocking
Tofa, wata dramar Sai a gidan Asim,
Sharhi pls
Amnah El~Yaqoub
[2/9, 11:07 PM] El~Yaqoub: INSAAF
Writing by:Amnah El yaqoub
Like my page on Facebook
https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493
15&16
Yana jinsu suna nocking amma ko alamun tashi baiyi ba, asalima hannunta dayake cikin nasa yafara murzawa ahankali,shikansa baisan dalilin dayasa yake murza mata hannun ba, amma bazai iya daina wa ba saboda sabon al'amarin dayake shigar sa, Kasa dagowa tayi ta kalleshi, gaba daya yayi mata wani irin kwarjini, shidin babban mutum ne ba qananun Samari ba irinsu Amjad..., muryarsa ya sassauta cikin sigar rad'a yakirata "Minal"
Dago idonta tayi ta kalleshi, idonta har yayi ja, hawaye ya zubo daga cikin idonta guda daya, cikin ransa yace "yasalam..."
Tunda take dashi yau ne Karon farko daya taba Kiran sunan ta, saita ji abun wani iri, saboda bai sababa, saide koda yaushe yace mata "ke", kokuma
Ke zonan, ke tashi mutafi, ke dauko min abu kaza, yanda yake murza hannunta saiya hakan yafara haddasa mata shiga cikin yanayi, Ahankali tace "na'am"
Tashi yayi daga qasan gadon yadawo dab da'ita ya zauna batare daya Raba hannunsa danata ba
Cikin rad'a yasake ambaton sunanta akaro biyu "Minal"
Muryarta na rawa ta amsa masa, hannunta yasaki yasake matsowa dab da'ita har suna jin numfashin juna, hannayensa yasaka yariqe fuskarta dashi, sannan yazuba mata ido Yana kallanta batare dayace komai ba,d'an qaramin lips dinta yake kallo,wanda yake ji kamar yadora nasa akai, Ahankali tadago kanta tazuba masa manyan idonta, idonsu ya sarqe dana juna, wannan Karon Bata janye idonta daga cikin nasaba, haka Shima baice mata komai ba, yade riqe fuskartata da hannunsa Yana kallonta kamar yasamu sabuwar halitta, idonta ne yayi raurau yafara kawo qwalla, Ahankali ya Matso da fuskarsa kusa da Tata kamar mai shirin yimata kiss, cikin rad'a yace "ki.... kiyi... hakuri..."
Kallansa tayi, sauran qwallar datake riqewa suka zubo mata, ba kukan komai takeba saina tausayin sa, Yana tare da mata amma baisan tana masa zagon qasa ba.

Sake sassauta Muryarsa yayi yace "kinji..."
Hannunta tasa ta share hawayen tace "babu komai Yaya, na haqura"
Kallanta yasake yi yace "are you serious?"
Jijjiga masa kai tayi kawai.

Mummunan bugon da a kayi wa kofar ne yasa yasaki fuskar Tata ahankali sannan ya tashi ya nufi kofar yabude
Gaba dayansu ne suka Danno kansu cikin d'akin (
Mamy, Amrah, da Anty Lubna wadda fuskarta tayi sha6e-sha6e da hawaye, Kallan Asim tayi dayake tsaye sannan ta kalli mamy cikin kuka tace "gashinan mamy ki tambayeshi, wallahi rungume ta yayi, male-male naganta a qirjinsa" (
Gaban Amina yayi wata irin faduwa, idanunta yayi tsilli-tsilli tana kallon mamy
Shikuwa gogan babu alamun damuwa afuskar sa yara6a ta gefensu yafice daga d'akin
Anty Amrah tafice daga d'akin tana girgiza kanta, tayaya Yaya Asim zai rungume Minal?

Mamy ta kalli Lubna tace "kiyi hakuri Lubna, zanyi magana dashi"
Daga nan taja hannunta suka fice daga d'akin, Anty Lubna tadawo d'akin hannunta dauke da ruwa a cup, miqawa Amina tayi tace "ki karba Kisha Minal"
Babu musu tasa hannu ta karbi cup din tashanye duka ruwan, sannan tasaki Ajiyar zuciya, Anty Amrah tayi qasa da murya ta kalli Amina tace "Minal waida gaske ne yaya ya rungume ki?" (
tafadi maganar cikin sigar son jin gulma
Cikin sauri ta girgiza kanta "a a Anty Amrah, ni be rungume niba"
Murmushi Amrah tayi tasake kallanta da kyau "to kuma nida nake qawar takima boyemin zakiyi?

Dan Allah ya rungume ki?"
Sake girgiza kanta tayi "Anty Amrah bafa haka bane"
"bawani nan, kede kawai kice yau Yaya yarage zafi" (
Amina takalleta tace "Anty Amrah kifahimce ni..."
Katseta Amrah tayi "bawani fahimta yarinya, tome yake fada miki dakuka kulle d'akin?"
Kai tsaye tace "hakuri yabani"
Cikin sauri Amrah tace "Dan Allah da gaske kike?

Yaya Asim ne yabaki hakuri da kansa?"
Cikin mamaki tace "baya bayarwa ne?"
Amrah ta jinjina kanta tace "lalle bansan wacce irin sa'ah gareki ba, nida zai aure ki ma danaji dadi wallahi, Anty Lubna kishin ta yayi yawa wallahi, kuma yawanci masu zafafa kishin nan Allah yafi jarabtar su dayi musu kishiya, domin ya gwada imaninsu"
Tana Gama maganar ta tashi tsaye yace "qanina yakusa dawowa daga Yola, Bari naje bakin gate na taro shi"
Amina ta daga mata kai, Wai qaninta, dama Anty Amrah tanada qanine?

Amrah nafita falo taci Karo da Amjad harma ya shigo gidan, hannunta tabude tatafi da sauri kamar zata rungume shi tace "oyoyo d'an qanina" (
Amjad ya kalleta, ya sake kallonta daga Sama har qasa, yadaga murya yace "Wai ke Anty Amrah meyake damunki ne Dan Allah?,yanzu inda tare muke da wasu haka zaki dizgani, Wai qaninki"
Bacin rai sosai a saman fuskar sa, ya nemi waje yazauna a daya daga cikin kujerun falon
Itama zama tayi tace "Dan rainin hankali, danma kasamu inama oyoyo, waye yazo yayima haka a gidan?"
Cikin fada yace "eh Karki qarayi inde saikin cemin qaninki, harda wani god'ai god'ai dani Saina zauna kina cemin qaninki"
"toba qanin nawa bane?

Nawa kake?

Fina kayi?dakaqi dakaso Anty Amrah dole, kuma nice de gaba dakai, babu yanda zakayi dani"
Cikin bacin rai yace "OK haka kikace?"
Itama cikin dakewa tace "yes"
Yace "OK, to wallahi kinemi abokin shawararki, bade niba, samarin ki kowa kika kwaso saikinzo kin nemi shawara ta, todaga yau ta qare, kinemi yayanki, wanda yafi ki, saiya baki shawara" (
Tace "inde Akan nace qaninane kake wannan ihun, wallahi Amjad bazan daina ba, qilama har goyaka nayi lokacin dakake Yaro, wayasani ma ko harda wanka nama (
Kawai daga zuwan ka kamar wani jarababbe kazo kahau ni da masifa"
Amjad yayi Shiru Yama rasa mezai ce mata (
Da Hankalinsa mamy take musu wanka gaba dayansu, amma saboda tsabar rainin hankali shi zata kalla tace tayiwa wanka, harda cewa kamar jarababbe, kallanta yayi Shima yace "aini kamar jarababben ne, ke kuwa jarabar Cema gaba dayanta" (
Kallansa tayi tace "yayi kyau, ka gwadamin hankali, gobe ma idan zaka dawo zan futo ina rawar jiki, na tarbeka" daga nan tafara yunqurin tashi
Hannunsa yasa ya fuzgota saigata azaune Akan kujera, Kallan mamaki tayi masa, yanzu Amjad ne yake da wannan qarfin har ya fuzgota haka?

Shikuma baima lura da irin kallon datake masa ba, yayi qasa da murya yace "haba Anty Amrah, ai Bama 'yar haka dake, menene kuma rayuwar?"
Cikin fishi tace "to ai Kaine kake neman rainani Amjad, saboda kaga kafara ajiye gemu"
Cikin qasa da murya kamar bashi ba yace "kifadi komai ma baji, inde babu mutane awajan (
ina jama'ar gidan suke ne?"
Ajiyar zuciya tayi tace "kowa Yana d'akin sa, ai yau baram baram akayi in fadama"
Zamansa ya gyara yace "haba? dawa akayi?"
"Yaya Asim da Anty Lubna, Akan Minal ne fadan, saura kadan ya Mari Anty Lubna, aikuwa nabar wajan ban tsaya ba, Anty Lubna Sai ihu take Wai Minal zata qwace mata miji, Wai ta gansu itada Yaya Asim harma ya rungume ta"
Gaban Amjad yafadi yace "waida gaske kike?"
Amrah tace "haka de Anty Lubna tace"
Cikin sauri ya miqe zai tafi d'akin mamy, hannunsa ta ruqo tace "ina zaka?"
"zuwa zanyi wajan mamy, wallahi inason yarinyar nan, tun lokacin dana fara ganin ta" (
Tace "aikuwa karka shiga yanzu, Dan naji maganar Yaya acikin d'akin, kabari sugama magana shida mamy Sai kaje"
Cikin damuwa yakoma kan kujerar ya zauna, yace mata "ina abinci na?"
Nuni tayi masa da dining tace "gashi can a dining, Anty Lubna ce tayi"
Girgiza mata kansa yayi, sannan ya nufi dining din
*** ***** ***
"Asim, kafadamin gaskiya, wacce irin magana naji Lubna ta nayi?

Da gaske ne ka rungume Minal?"
Karon farko daya fara yiwa mahaifiyarsa qarya, koda yaushe baya boye mata komai, kullum cikin fada mata gaskiya yake, qeyarsa ya Sosa sannan yakalleta yace "mamy...runguma kuma?"
Tace "Asim matarka zatama qarya ne?

Baka rungume Minal dinba?"
Shima cikin dakiya yace "to mamy saboda me?
Chapter 16 · 0% Book details