← Book details Insaaf Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 53

Sashe 27

Insaaf Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Rabuwa tayi dashi ta dauki wayarta takira Amrah tace taturo mata Minal da Amjad
Amjad ne yafara shigowa, Yana ganin Asim yakoma kusa dashi yazauna,tana shigowa d'akin ta gansu shida Amjad duk sun mamiqe ajikin mamy kamar wasu yan yaye, musanman Asim ma yawani rirriqeta kamar zata gudu ta barshi
Ahankali tazauna aqasa tace "mamy gani"
Mamy tace "Minal yanzu Asim yake fadamin wata magana, menene gaskiyar al'amari ne?"
Gabanta yafara faduwa, yau kam taga ta kanta, Ahankali tace "hakane Mamy, kafin muzo nan wani malami yayi mana aure ni dashi"
Amjad najin haka yazaro Idonsa waje
Cikin sauri yace "Aure kuma?

Keda Yaya Asim din?"
Cikin sauri ta daga kanta sannan tace "Amma...

Ni banaso, nafison na zauna haka, banason nasake yin wani auren"
Amjad yace "subhanallah...

Minal meyasa zakice haka?

Innalillah..., meyasa baki fada mana tunda wuri ba?

Da yanzu alhaki Yana kaina" yajuya ya kalli Asim yace "Yaya Dan Allah kayi hakuri"
Fuskarsa cike da bacin rai ya tashi daga jikin mamy ya kama kunnansa yariqe "meyasa zaka ban hakuri?

Kaine baka sanar da'ita shirin dakake yi ba, shiyasa, but Duk abinda kakeso inde baifi karfina ba zan mallaka mashi Amjad,saboda haka zan saketa ka aureta"
Cikin sauri Amjad ya manta da zafin da kunnansa yake masa, ya kalli Asim "A a Yaya, na hakura wallahi, Nima nabarma ita"
Asim ya Girgiza kansa yace "banason musu"
Mamy tace "ya'isa haka dan Allah, Minal tashi kije idan alhaji yazo zanyi masa Bayanin komai"
Tashi tayi, su kai ido hudu da Asim cikin sauri yadauke Idonsa daga kanta, idan tunanin ta yazama gaskiya saitaga kamar tsoron ta yake ji
Tana fita, Shima Amjad ya kalli mamy "Zanje nahuta mamy, kaina yanamin ciwo"
Mamy tace "to saida safe" daga nan bai sake magana ba yafuto daga d'akin, jiyake kansa kamar zai rabe gida biyu, mamy kuwa kawai de tace masa saida safen ne, amma dole zata bishi dakinsa taga halin dayake ciki, bazata iya barin autan ta cikin wani hali ba
Yana zuwa tsakiyar falon nasu yadora hannunsa aka,
jiyake kamar yafashe da ihu, hanyar dakinsa yanufa, Sai kuma yajuyo ya nufi d'akin Amrah, budewa yayi yashiga, Sai kuma ya tuna dazu sunyi fada
Saiya dawo baya, yarufe musu d'akin, Amrah tana kwance Akan gado ta hango shi, tayi tunanin zai shigo Sai kuma taga yakoma,Ahankali tatashi tabi bayansa
Tana zuwa dakinsa ta hango shi acan qarshan gado yana kuka, cikin sauri ta qarasa wajansa tazauna kusa dashi tace "nashiga uku Amjad meyasameka kake kuka?"
Yana ganinta kusa dashi yafada jikinta Yana kuka wiwi kamar mace, mamaki ya kama Amrah, ta kalli yanda yafado jikinta abinda bai taba yiba tunda suka tashi gida daya, janye shi tafara yi daga jikinta tace "Amjad, kayi magana mana menene?"
Cikin kuka yace "Narasa ta Anty Amrah, Narasa Minal, ashe anyi musu aure itada Yaya Asim"
"ohhh, saboda kaji Minal tana auren Yaya Asim shiyasa kadawo kacemin Anty Amrah kenan ko..."
Girgiza kansa yayi dake jikinta, cikin shagwaba yace "Niki daina yimin wasa"
Wani irin abu taji a jikinta, tafara kokarin janye jikinta, amma Amjad saiya dora kansa Akan cin yarta, ya Zagayo da hannunsa ta baya yariqe cikekken hips dinta
Lokaci daya taji wani yarrrr!

Hannunta tadora Akan hannunsa dayake kan qugunta tace "kai cikani, saikace kasamu mamy duk ka riqeni, kayi hakuri mana to, Kai saika dinga kuka saikace mace"
Hannunsa yadauke daga kan hips dinta ya share hawayen, cike da shagwaba yace "Toba ke ce kikaqi lallashi naba"
Gaban Amrah yafadi, tambayar kanta tafara yi, Anya kuwa kalau Amjad yake, menene hakan yake mata?

Cikin sauri tamiqe tsaye har Yana dago kansa Yana kallonta cikin mamaki, jitayi yanayin ta Yana sauyawa, wacce irin masifa ce wannan tarasa Akan wanda zataji feeling Sai qaninta?

"Anty Amrah tafiya zakiyi?" yadoko mata tambaya
Tace "Amjad banson shirman banza, nabaka hakuri kaqi hakura Sai rirriqeni kake kamar kasamu wata sa'arka, kuka kakeso na zauna na tayaka?"
Shima cikin fishi yace "to Kar Allah yasa ki tsaya din, kitafi mana, kifi ruwa gudu"
Mamy ce tashigo d'akin tace "kai innalillah...

Wai yaushe zakuyi hankali ne?

Amrah da girman ki ban hanaki kula Amjad ba?

Miye ya shigo dake dakinsa?"
Baqin ciki ya kama Amjad, Wai da girman ta, to ba dole ma ta raina shi ba, tayaya za'ai mamy ta dinga fadar haka agabanta?

Haushi yasa ya maida kansa cikin fillo yaqi kallon mamyn
Amrah kuwa fuska babu walwala tafice daga d'akin, kullum mamy saita dinga cewa itace babba ta qyale Amjad, koda yaushe ita ce me daukar laifi, wallahi yasake yimata rashin kunya qararsa zata kai wajan Yaya Asim
Washe Gari suna zaune afalo bayan Break,Amrah tana danna wayarta, Amina kuwa kallo take, mamy na karanta Hisnul Muslim
Futowa yayi cikin qananun kaya, riga da Wandon jeans, amma rigar yadora mata jacket asama, kayan sunyi masa kyau sosai kasancewar ba sakawa yake ba, daga suit Sai manyan Kaya, sune kawai kayan sakawarsa
Qamshin turaren dayasa yacika falon nasu
Babu wanda bai daga kai ya kalleshi ba, idanun sane yahadu da nata, cikin sauri ya janye Idonsa daga cikin nata
Mamy tana lura dashi, Amina kuwa shaf tama manta da maganar auren da tayi masa jiya, saboda abin be dameta ba, ba auren ne agabanta ba, Bata fatan ace wani mutum yasake mutuwa adalilinta, haka babu abinda takeji a ranta game dashi, tasan de tana hashi girmansa a matsayin sa na babban mutum,
tsoron data hango acikin qwayar Idonsa jiya, yauma shita gani
Sai abin ma yabata dariya, Ahankali tayi murmushi ta dauke kanta daga kallonsa
Amrah ta rissina tace "good morning Yaya"
Daga mata kai yayi kawai, yanemi waje yazauna, already sun gaisa da mamy tun bayan asuba, amma duk da haka saida ya dubeta yace "mamy Barka da safiya"
Kallansa tayi taga yanda yake wani dauke kansa, tarasa gane wanne irin karfin hali Asim yake dashi, kanason yarinya amma bazaka nunaba, koda yake may be tunanin ta ne yazama gaskiya, Shima ba lalle yasan yanason Minal dinba
Ataqaice tace masa
"yauuwa"
Tamaida dubanta ga Amina tace "Minal, tashi ki kawo wa Asim break fast dinsa"
Cikin sauri ya kalleta, Minal kuma, Wai meyasa mamy take masa hakane?

Bayan da itace take kawo masa da kanta, haka yayi Shiru yasake dauke kansa
Ahankali tatashi ta dubeshi tace "Yaya ina kwana?"
Batare daya dago kansa ya kalleta ba yace "lafiya"
Dan tabe bakin ta tayi tawuce kitchen din tana magana a ranta, idan auren ne bayaso ai komai yazo cikin sauqi, tunda itama bataso kawai saiya saketa
Kawo masa abincin tayi ta ajiye, ko zuba masa batayi ba Takoma wajan zamanta tazauna, ransa yaqara baci, Tome yarinyar nan take nufi?

Shine zai zuba abincin da kansa kenan?

Mamy tana kallonsu ta gefen idonta, tanaso taga Yaya zasu qare
Bude abincin yayi, yayi Dan qaramin tsaki sannan ya kalli Amrah "ke taso kizuba min abinci"
Kafin Amrah tatashi mamy tace "Minal tashi kizuba masa"
Yanzun ma cikin sauri ya kalleta, mamy Sai saka yarinyar nan take tana kulawa dashi ba tasan gawa ake Bawa kulawa ba, shi kam yasan cewa yanzu tasa ta qare
Babu musu tatashi tazuba masa, tazauna kenan Amjad ya shigo falon cikin shirin fita
Kallan Amrah yayi, suka sakarwa juna harara, sannna yazauna kusa da mamy, Amina ta gaida shi ya amsa cikin mutunci
Yace "mamy zanbi Yaya office, yau tare zamuyi aikin"
"Autan mamy kabar naka aikin kadawo nan ka zauna ko?"
"mamy bazan iya missing dinki dayawa ba, amma zan koma insha Allah"
Tace "yawwa Autana, Allah yayi muku albarka, Daddynku fa Yana hanya, around 11 zai qaraso"
"Allah yakaimu mamy, idan mundawo daga office saimu gaisa"
Wayarsa ce tayi qara, yad'auka tare da amsawa
"Yallabai gobe kanada meeting din gaggawa a malesia, ticket dinka yazama ready, zaka iya tafiya yau ko gobe"
Tace "babu damuwa, zan tafi yau din" daga nan yakashe wayar ya miqe tare da kallon Amjad
Amjad ya tashi yafice Yana yiwa mamy sallama
Ta kalli Asim tace "to saika dawo, idan alhaji yazo zanyi masa magana Akan maganar ka data Amina"
"babu damuwa, zanje Malesia yau, zuwa jibi zan dawo insha Allah, kimin Addu'ah"
"Allah yakaika lafiya"
cewar mamy, takalleshi taga babu wani abun daya dauko, ko brief case dinsa ma yau bai dauka ba, idonta ya sauka Akan wayoyinsa guda biyu, ta kalli Amina tace "Minal dauki wayoyinsa ki rakashi compound"
Al'amarin mamy kuma yafara Bawa Asim tsoro, kallanta yayi yadauke kansa, cikin sauri yafice daga falon
Mamy ta sake kallon Amina tace "tashi mana"
Ahankali tatashi ta dauki wayoyin nasa akaron farko, tabi bayansa dasu, Amrah sai dariya take qasa qasa
Tana futowa ta ganshi atsaye a bakin kofar falon, hannunsa ya miqa mata batare dayace komai ba
Babu musu ta saka masa wayoyinsa akai tajuya zata koma ciki
Mamaki yakama Asim, wato idan ya matsu yaje lafiya ko karyaje duk shiya sani,duk da mamy tayi masa Addu'ah ai malamai sunce Addu'ar mata Akan mijinta batada hijabi awajan ubangiji, kawai zata bashi wayoyi ta juya ko Addu'ah babu
Ajiyar zuciya yayi yabi dogon gashin ta da kallo sannan yace " ke baki iya Addu'ah ba ko?"
Cikin sauri ta juyo ta kalleshi "Yaya ai danaga mamy tayi ma, amma kayi hakuri" taqarasa maganar idonta na ciko da qwalla
Cikin ransa yace yarinyar nan tacika shagwaba dayawa, afili yace "kina Jina, zanyi waya da Muhsin yazo yakaiki school, har yanzu ke qaramar yarinya ce, kicire tunanin aure aranki kiyi karatu,kuma banson kula qawaye da Samari kinjini?"
Cikin sauri tace "eh Yaya, Allah yadawo dakai lafiya"
"Amin" abinda yace kenan yajuya zuwa wajan motarsa da Amjad yashige tun dazu
Tunani yafara, ya kamata ace Yana dawowa ya tsaya ya nutsu yanemo Iyayen ta, ko hakan zaisa ta dinga dariya kamar kowa
Sai wajan 11:47 Daddy yadawo, bayan yaci abinci yahuta mamy ta kalleshi tace "Alhaji auren Amjad da Minal fa bazai iyuba"
"inajin ki, saboda me?
Chapter 27 · 0% Book details