← Book details Insaaf Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 53

Sashe 40

Insaaf Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"
" bansani ba "qit yakashe wayar sa, yajuya zai Bawa Amjad wayar Sai yaga fuskar Amjad agefe da alamu ma dariya yake masa, daure fuska yayi yace" kai miye haka?"
Amjad ya nutsu, Ahankali yace"sorry Yaya"
"kiramin likita, yazo ya sallame ni gida zamu tafi"
Bayan yakira likitan ko awa daya basu qara ba suka bar asbitin, suna tafiya a hanya Amjad ya kalleshi yace "Yaya, dama inaso zamuyi wata magana"
Asim yayi tunanin maganar ta shafi jinyar tasa, saiya sake dauke kansa yace "ina jinka"
"Akan Anty Amrah ne"
Sai alokacin ya kalleshi yace "meyake faruwa?"
"Yaya wallahi I love her so much...."
Asim ya d'aga girarsa guda daya Yana kallon Amjad, Shima Amjad din daya kalleshi saiya sake samun qwarin gwiwar Ci gaba da magana "Yaya inajin tsoron tane, bansan Yaya zata kalli al'amarin ba, amma nide gaskiya ina sonta"
Asim yace "babu damuwa, Bari muje gidan"
Cikin sanyin jiki yace "to Yaya"
Suna qarasawa gida maigadi da suke zaune a bakin gate suna Dan taba hira, suka taso da gudu suna masa sannu, cikin kwanciyar hankali ya amsa musu sannan suka shige ciki, Kai tsaye d'akin mamy sukaje
Mamy na ganinsu tace "Daga ina kuke?"
Asim ya shafa sumar kansa, Amjad na ganin haka yayi sauri yace "daga unguwa mamy"
Ta kalli Asim daga Sama har qasa tace "kuma unguwa da jallabiya?"
Murmushi sukai gaba dayansu, sannan suka nemi waje suka zauna, tace "kode akwai wani abu ne?"
Asim yace "mamy Autanki ne yasamu matar aure"
Lokaci daya farin ciki ya kama mamy tace "Alhamdulillahi, Allah abun godia, wacece?"
Kai tsaye Asim yace "Amrah"
Fuskar mamy saita tashi daga yanayin farin-ciki zuwa yanayin mamaki tace "wakace?"
Asim kuwa yasake cewa "Amrah, Amrah de taki ta gidan nan"
Mamy tasaki Ajiyar zuciya tace "tooo.....

Ikon Allah, to Asim da'ace wanine yafadamin wannan maganar bazan yarda ba, amma dayake Kaine da kanka, yanzu na yarda, yanzu kai Asim da hankalinka da komai shine Amjad zai sakoka agaba kazo kanamin wannan maganar?

Asim harka manta da yaqin da sukeyi?

Saboda masifar Amjad da Amrah tafi qarfin fad'a saide muce yaqi, wataran gidansu kamawa zaiyi da wuta, Dan haka bada niba "
Asim yayi murmushi, Amjad kuwa yanayin fuskar sane ya sauya zuwa shagwaba, yace" mamy Allah nide nadena, dama ai komai ma duk laifin tane, saita dinga cemin yaro "
"to Kaine kullum saika dinga nuna mata kai Yaron ne, komai shagwaba, komai shagwa6a badole tacema Yaro ba" cewar Asim
Mamy tasaki baki tana kallonsu tace "Okey dama Kaine kake zigashi kenan, to Yana Dan autana idan beyi shagwaba ba qarfe kakeso yakoma dagawa kamar kai?"
Asim yace "to yaci gaba mamy, wataran idan yaje zance wajan wata ya kama yimata wannan shagwa6ar wallahi saita kifa masa mari"
Mamy tace "naji, yayi abarsa, lokaci be, wataran ai bazai yiba"
Kallanta yayi Shima cikin shagwa6ar de yace "A a mamy nikam nadena"
Tace "Okey kunyatani zakayi kenan?

To ai shikkenan, inde nice na haifi Amrah, nabaka ita Amjad, amma da sharadi daya, idan ta amince, kaje ka sameta duk yanda kukai inde ta amince din, Toni banida damuwa"
Yanajin haka yasaki wani irin ihun murna ya rungume Asim, sannan yace "Angama mamy" yafice da gudu daga d'akin
Asim yabishi da kallo ya nuna shi da hannu yace "kingani ai, Kinga irinta ko?"
Mamy tayi dariya tace "kai jama'ah, Dan Allah Asim kabarmin yaronnan ya wataya, haba"
Kansa ya shafa yace "to shikkenan mamy, Allah ya tabbatar da Alkhairi"
Murmushi tayi tace "Amin"
Daga nan yafuto daga d'akin nata
Falon nasu yashigo hannunsa dauke da ledoji niqi-niqi, Kai tsaye d'akin ta yashiga, tana karatun novel Sai ganinsa tayi yashigo d'akin nata,ledojin ya ajiye mata agabanta, sannan ya zauna Akan gadon Yana fuskantar ta, tafin kafarta ya kalla, Ahankali yakai hannunsa ya shafa, 6ata fuska tayi tace "miye hakan kuma?"
Wani irin kallo yazuba mata mai karya garkuwar jikin yanmata, sannan yace "naganta ne fes kamar yanda kike komai naki fes fes"
Idanuwanta tajuya
tace "too yau kuma da salon da kazo kenan"
Murmushi yayi yace "A a, tana birgeni ne, ko zaki shirya muje ayi miki qunshi, zaiyi miki kyau wallahi tunda bakyayi sosai, Kinga yatsun kafarki ma idan aka miki wani irin kyau suke" ya qarasa maganar Yana dora hannunsa Akan yatsun kafarta
Tsaki taja ta qwace qafarta tace "Amjad, menene yakawo ka?

Banason wannan kwane kwanen dakake"
"nikuwa Anty Amrah menene zai kawoni wajanki banda zumunci?

Kinga kaza ce nasiyo miki da ice-cream, nasan zakiji da dinsu" ya qarasa maganar yana turo mata ledar gabanta
Cikin sauri tafara Bude ledar tace "Allah Amjad?

Allah sarki dan'uwa Rabin jiki, kace yau bazanci abincin gidannan ba"
Yace "koh?"
Tace "eh mana"
"idan kina so ai kullum zan dinga siyomiki nikam"
Kallansa tayi tace "Amjad Anya kuwa Kaine?"
"nine mana, mekika gani?"
"kawai gani nayi kamar bakai ba"
"toki daina wannan tunanin, kinsan kuwa yanda nake bala'in qaunarki?"
Naman kazar ta dauka takai bakinta tace "Allah sarki Amjad, toka sa hannu mana muci"
"saide...

Ki bani....

A baki.. na..."
Ya qarasa maganar a rarrabe
Harararsa tayi tace "karkaci"
Cikin shagwaba yace "uhm..

Allah kibani, toba nine nasiyo ba"
Kallan sa tayi tace "nace gashinan Kaci, ka tsaya kanamin wani fi'ili, toka zauna kajira Dan Allah"
Tana gama fada masa haka tasaki Jan kazar gabanta tanaci hankali kwance, kallonta yayi, ya yi qasa sa murya yace "Anty Amrah"
"ina jinka Amjad"
"zaki iya auren qaninki?"
Wani irin murmushi tayi tace "abin dariya wallahi, Wai Yaro ya tsinci haqori, to Amjad kaida kanka mafa cewa kayi qanina, to ta Yaya zan iya auren sa?

In rasa wazan aura Sai qanina?

To ai bari kaji, ko Kaine dakayi tsawon qafa harka Fini tsawo, bazan iya auren kaba, saboda auren yarannan yan Ashirin da biyar da shida duk shirme ne, dayawa daga cikin su mafa ba'a gama musu tsawa ba, tayaya zasu tsawatar dani?

"
Wani irin baqin ciki ya kama Amjad, babu maganar da tafi masa ciwo irin yanda tace dayawa daga cikin su ba'a gama musu tsawa ba, Wai me Amrah ta dauki kanta ne?

Ajiyar zuciya yayi, ya kalleta Sai cin namanta take tana gasa masa magana hankalin ta kwance, yace"mudena maganar wasa Amrah, da gaske, inason ki, inaso kibani dama na aure ki "
Wani naman ta dauko zataci, amma jin wannan furucin nasa yasa ta tsaya cak, saita yi wani saroro tana kallonsa, aduniya Amjad bai taba cimata mutunci irin na yauba, wato ya matse ta yayi kissing dinta, shine yanzu zaizo mata da wannan maganar, kawai saita zuba masa ido tana kallonsa, gaba daya mamakin sa yagama kamata, tarasa mema zata masa tahuce, kawai Sai tayi jifa da naman tafashe dawani irin kuka, sosai take kuka, ta kifa kanta Akan cinyar ta, haqiqa yau Amjad ya cuceta, yagama ganin gadon baccinta
Ganin yanda take kuka sosai Sai jikinsa yayi sanyi, ahankli ya tashi tsaye yace "kiyi hakuri idan magana ta ta 6ata miki rai, amma Ban taba tunanin zaki iya gudunaba Amrah, hakan yana nufin karnaji haushi idan wata bare ta nuna Bata sona, tunda kema yar'uwa ta kin qini, but I am sorry, bazan iya Hana zuciyata kaunar ki ba Amrah"
Yana fadar haka yafice daga d'akin
Yau bai fita wajan aiki ba, Yana kwance agado amma computer ce agabansa Yana search, futowa tayi daga toilet, tana sanye cikin riga da wando, kayan sun kamata sosai, amma ba qaramin kyau sukai mata ba, wuce shi tazo tayi ta qarasa gaban mirror takama gashin kanta tana daurewa, da kallo yabita, shaf ya manta akwai abinda yake yi a computer
Wata doguwar riga ta dora sannan ta zura hijab dinta tatada kabbarar sallah
Wani irin farin-ciki ya kama zuciyar Asim, hakan yana nufin tayi wankan tsarki kenan, Yana aikin kallonta harta idar, sannan yace "Baby na zokiga wani abu"
Murmushi tayi tace "to Yaya" ta qaraso wajansa
Cikin sauri yace "Dan cire wannan hijabin please"
Babu musu ta cireshi, tana qaraso wa yajanyota jikinsa, sannan ya tura mata computer gabanta, tana gani tace "Wow, gaskiya akwatunan nan sunyi kyau sosai Yaya"
Lips dinta ya kalla, Ahankali yakai hannunsa yafara shafawa yace "da gaske?"
Bata iya bashi amsa ba, kawai kanta ta daga masa
Murmushi yayi, yamatso da fuskar sa kan Tata fuskar yace "ai naki ne"
Cikin sauri tace "haba?"
Murmushi yayi, yarintar yarinyar tana birgeshi, ya Dage ya nuna mata kayanta amma ahakan sake tabbatar wa takeson yi, shine saita sashi ya rantse
Yace "nakine, sun kusa qaraso wa wajanki insha Allah"
"nagode Yaya"
Kallanta idonta yayi, yayi qasa da murya yace "wannan ne kawai tukwici na?"
Dago manyan idonta tayi ta kalleshi, suna hada ido tayi sauri tayi qasa sa idonta tace "tome kakeso?"
Acikin kunnanta ya rada mata "your lips"
Cikin kunya ta rufe idonta, yayi murmushi yace "shikkenan, bani labarin samarinki"
"ni banda Samari ai, Sai mutum daya, Haruna Dan kande, shine yake sona sosai, kuma yarasu"
"sorry, Allah yaji qansa, amma meyasa zakice shine sonki sosai?
Chapter 40 · 0% Book details