← Book details Insaaf Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 53

Sashe 52

Insaaf Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dan Allah kidena wannan maganar, ku kadai zan kalla naji dadi, tunda Allah yahore mana abinda zamuci musha, muyi musu tarbiya ai Alhamdulillahi "
Cikin sanyin jiki tace" to Yaya,Allah yaraya mana su"
"yauwa wife, kokefa" ya qarasa maganar Yana Jan hancinta, atare suka sanya dariya
Ranar suna Yara sukaci sunan El Hameed dakuma Abban Asim, El Hameed ne da kansa ya hada walimar da aka gabatar da gidansa ta sunan yan biyu, Yara sunga gata kamar ba'a taba haihuwa a familyn ba
Haka kawai El Hameed zaisa a dauko masa yaran yasa su agaba Yana karatun jarida, haka kawai Allah yadora masa qaunar jikokin nasa a ransa
Ishraqa ta Dage Sai gyara yarta take, tana kula da abincin datake Ci, dakuma na yaran, kasancewar Ana qara musu da madara sai sukai qiba bulbul dasu gwanin sha'awa
Watarana Asim yazo gidan yaga yanda ake dura musu madara, Kota ido babu haka yafuto qiri qiri yace a daina basu, su dinga shan nono, saboda zaisa qwaqwalwarsu ta Bude, Ishraqa tace ai madarar tana taimaka wa yaran, saboda nonon baya isarsu sosai
Amma haka Asim ya qeqasa qasa yace shifa abasu nono
Ita kuwa Ishraqa duk lokacin da yaran suke hannunta haka take dura musu madara
Idan suna hannun Insaaf din kuma Sai Insaaf din ta dinga basu nono
Zaune suke afalo itada Ishraqa, tana Bawa yaran nono Sai tsaki take ja, Ishraqa ta kalleta tace "Keda waye?"
"Anty yaran nan ne mana, basa qoshi wallahi, ko fitsari sukai yanzu zakiji sun fara kukan yunwa"
"ki dauko madara kibasu, tunda suna shan madarar Aida sauqi"
Cikin wani irin Salo tace "to Anty ai Yaya yace bayason Ana basu madara"
Ishraqa ta riqe ha6arta tace "to Laila majnun, ai jiki magayi, shi yayan daya Fadi haka a qirjinsa suke shan nonon?"
Insaaf takasa Bata amsa tayi Shiru, Yaron ta ajiye ta dauki dayan tafara bashi, Ishraqa tace "nikam bari naje daki, idan kingama basu nonon kikawo minsu ki huta"
Tana shiga daki Insaaf tacire Yaron tafara matsar qwalla
Adede lokacin yashigo falon Shima, cikin sauri yace "subhanallah baby lafiya?"
Kuka tafashe dashi tace "Yaya basa qoshi, Allah ni nono na zafi yake min"
Rikicewa yayi lokaci daya yace "Sannu, sannu baby, Kinga tashi muje daki ki kwanta ki huta, idan kin huta saiki basu, barsu haka yanzun"
Yaron ta dauka guda daya, Shima ya dauki guda dayan suka shige dakinta
Saida tahuta kamar yanda yafada, sannan ta qarasa Bawa yaran nonon, kamar dole Sai sannu yake mata tana runtse ido
Suna gama Sha ya daukesu duka su biyun yace "ina Antynki?"
Kamar zatayi kuka tace "tana dakinta"
Kallanta yayi cikeda tausaya wa yace "sorry, ina zuwa, Bari nakai mata su"
Dakin Ishraqa yatura yashiga, tana zaune tana linkewa yaran kayansu, Sai ganin Asim tayi yashigo tace "har sun Gama shan nonon kenan"
"sunga ma, dama aiki zan tayata, shine tace nakawo su wajanki"
Ishraqa tace "eh nace ta kawo min su, kwantar dasu kawai"
Babu musu ya kwantar da yaran yafice daga d'akin
Yana komawa d'akin ya Janyota jikinsa yadora ta Akan cinyar sa, cikin rada yafara lallashin ta "baby suna damunki ko?

Kiyi hakuri idan suka sake girma Sai adinga basu madarar, Nima inaso ki huta baby"
Kanta ta daga masa, yakai hancinsa wuyanta yafara kissing, cikin wata irin kasalalliyar murya yace "kin haqura ko?"
Nanma batayi magana ba Sai daga masa kai datayi, murmushi yayi yace "baby ni bakiyi missed Dina Bako?"
hararar wasa tayi masa, sannan ahankli tadora lips dinta Akan kumatunsa tayi kissing, cikin sauri yahade bakin su waje daya
Babu musu ta bashi hadin kai, tun suna numfashi kadan kadan har suka dawo suna fidda numfashi mai sauti, Asim yayi Nisa sosai saboda yayi kewar matarsa ba kadan ba, jikinta yafara shafawa lokaci daya tajiyo ihun kukan yaran nasu
Ahankali taraba jikinsu tace "Yaya yaran can suna kuka, Bari na karbo su nabasu nono"
Da jajayen Idonsa ya kalleta yace "ki dauki wayata kikira Antynki kice mata nace abasu madara"
Mamaki ya kama Insaaf, tace "Yaya madara kuma?

Ba yanzu kagama bani hakuri Akan na dinga basu nono ba?"
"baby ai banyi zaton haka suke da shan nono ba, shiyasa na Fadi haka, gaskiya kina kokari, shikkenan Yara Dan fitina daga nono Sai nono, Toni ina zanje naji sauqin abinda yake damuna kenan?kirata Dan Allah, kifada mata abasu madara"
Insaaf tayi murmushi, taga alama Yaya Asim a hannu yake, kiran Ishraqa tayi awaya, tana dauka tace "Anty Wai yace abasu madara"
Ishraqa ta kwashe da dariya kawai takashe wayar, afili tace "kai ya Allah Asim, Asim kenan,"
Tana kashe wayar suka dora daga inda suka tsaya
*After 4 years*
Yara ne su biyu afalo suna fada harda dambe Akan safa,
Kwata kwata bazaka banbance suba saboda yanda suke tsananin kama da juna, komai nasu iri daya
Hassan mai sunan baban Asim shine ya riqe safar yace "wallahi bazan baka ba, kullum saina nemo safata zaka ce takace"
Hussain mai sunan El Hameed yace "Momy!

Kinga Hassan ya hanani safa ta, Allah zanji wa Yaron nan ciwo"
Insaaf tafuto da gudu taji Ana zancen ciwo, taqara girma da wayewa tazama cikakkiyar mace, jikinta luwai luwai kamar ka latsa jini yafuto, takama hannun Hassan tace "babana, ka bashi safarsa, banason rigima, kasan taka safar tafadi, kabari zan nemo ma wata adaki, ka bashi abarsa"
Maimakon yabata safar saiya wullar da'ita aqasa, tasa hannu tadauka tabawa Hussain safarsa
Takama kunnasa tace "duk lokacin danaji kasake cewa Hassan Yaro, har kayi masa maganar Jim ciwo saina zaneka a gidannan kajini?"
Cikin sauri ya d'aga kansa, tace "oya tell him sorry Hassan"
Kallan Hassan din yayi yace "I'm sorry Hassan"
Sallama akayi afalon,gaba dayansu suka saki murmushi daga ita har yaran nata, Amrah ce tashigo falon hannunta dauke da Baby boy
Ta kalli Hussain tace "Hassan, yabaku tafi school ba har yanzu?"
Hussain yace "good morning Anty"
Insaaf ta kalleshi tace "Hussain Kaine Hassan din?"
Dariya Hassan yayi yace "Anty kinganni fa, shine Hussain ya amsa miki"
Amrah tace "oho, nikam har yanzu Bana gane yaran nan"
Insaaf ta karbi Yaron hannun Amrah tace "taho Yaya Asim Dina, ina kika bar widad kuma?"
"widad tana hannun Amjad, gasu can a compound shida Yaya Asim da mamy"
Insaaf ta su Hassan tace "tome kuke jira, kuje Daddyn ku Yana jiranku, karkuji latti a school"
Yaran suka fita da gudu suna mata bye bye
Amrah ta kalleta tace"ashe kungama final exam dinku jiya?

"
Insaaf tace" wallahi mungama Anty Amrah, yanzu saura taron graduation da suke hada mana kawai "
" to Allah ya tabbatar da Alkhairi "
"Amin Anty Amrah"
Gidan mamy kenan, inda su Insaaf suke rayuwar su kamar da, har yanzu Allah bai Bata haihuwa ba tun daga kan yan biyu, Amrah kuma ya ranta biyu, babbar itace Hussaina sunan mamy taci, suke kiranta da widad, Sai kuma na biyun namiji, suka saka masa sunan Asim
Rayuwar su tana tafiya cikin Jin dadi da kwanciyar hankali
Washe Gari da daddare mamy tawuce daki ta kwanta daga Insaaf Sai Asim dakuma yan biyu suna zaune afalo suna shan fruit, Hussain yace "Daddy, idan na girma ko sonake nazama soja, na dinga tarewa widad fada a school"
Insaaf da Asim sukasa dariya, Asim yace "A a Hussain, kode yar gida zakuyi ne kaida widad kamar yanda Daddyn widad din yayi?"
Hussain bai gane abinda Asim yake nufi ba, Danhaka kai tsaye yace "eh Daddy"
Insaaf tayi murmushi, shi kam Hassan cewa yayi "momy, nikam likita nakeso nazama, in dinga yiwa Hussain allura"
Gaba dayansu su hudun sukasa dariya, Asim yace "kai, kutashi kuje ku kwanta dare yayi, kuma Karku manta this weekend agidansu Inna zakuyi, Sannan momynku zata tasheku da sassafe ayi muku wanka kuyi ado, zamuje unguwa da mamy, da Maman Insaaf, da Alhaji,(El-Hameed)
da Daddy Amjad, da Anty Amrah, dasu widad, duk zamuje kuga kakanku, gobe zai futo daga wani waje daya tafi "
Hassan yace"yawwa Daddy, dama bamu taba ganin kakanmu ba, kullum kullum saikace yakusa dawowa"
Asim yayi murmushi Yana kallon yaran nasa, kullum Basuda magana saita ina ka kansu yake wanda ya haifi Asim?

Basu Bawa yaran labarin irin halin da daddy yayi musu ba, koda yaushe nunawa yaran suke da Asim da Amjad babansu daya, kuma zai dawo yayi tafiya ne, gashi kwanci tashi babu wuya har daddy yayi shekara biyar dinsa zai futo
Yayi ajiyar zuciya yace "gobe zaku ganshi insha Allah, idan kakanku yahuta saimu bi Daddy Amjad Yola muje mugano matar Malam, wadda mijinta yayiwa mamanku waliyi ranar auren ta"
Insaaf tana Jin haka takai hannu ta mintsineshi batare da yaran sun gansu ba
Cikin sauri ta kallesu tace "Hassan, Hussain, go and sleep"
Saida sukai kissing din iyayen nasu sannan suka tafi d'akin mamy,
dayake acan suke kwana
Asim ya kalli Insaaf yadage mata Gira yace "aji dani madam"
Bakinta taturo gaba tace "haba Yaya ...

Allah kwana biyun nan baka barina nahuta, kullum saika gajiyar dani"
"yes ina zan barki ki huta baby, ai saikin Haifa min wasu yan biyun tukunna" daga nan yadauke ta suka shige dakinsu
Cikin sauri nabisu zan dauko rahoto suka bugomin kofar agoshi na
inajin Asim Yana cewa "haba ya kamata kibarmu haka Amnah, tun ranar danayi hatsari kike bibiyar rayuwar mu, kije kibasu labarin BABBAN YAYA kuma"
Ina miqa Godiya tare da jinjina ga :
HAUSA NOVEL GRP
INSAAF NOVEL FAN'S
INSAAF HAUSA NOVEL
AMNAH EL YAQOUB NOVEL
PRINCE ABDUL HAUSA NOVEL
TASKAR LITTATTAFAN HAUSA
ALHUSNA SWEET NOVEL
ZAFAFAN NOVELS (Alhusna)
Kinada Samari masu yawa?

Kinsan hanyar dazakibi kigane wanda yake qaunarki da gaskiya?
Chapter 52 · 0% Book details