← Book details Insaaf Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 53

Sashe 29

Insaaf Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Kiyi mana Bayani mana, mamy ko Amjad ne ya6ata miki ranki?, Dan Allah kiyi hakuri, mamy Karki hukuntashi shi kadai, kiyi mana tare, Amjad Yaro ne zai iyayin kuskure"
Cikin kuka tace "kanaso ka nunamin abinda yake daidai ne Asim?, toka ta6ashi kagani, wallahi Sai ranka ya6aci"
Su Ishraqa da El Hameed ne suka shigo cikin d'akin nata, ganin yanda take kuka tana hada kaya ne yasa duk Sai mamaki ya kamasu
Asim yace "innalillahi wa Inna ilaihirraji'un"
Yakoma bakin gadon yazauna, Amjad kuwa kawai kallon mamy yake, har yanzu gani yake kamar ba mamyn sa ba, mai sonsa mai qaunarsa, wadda take fifita soyaiyar sa Akan ta 'ya'yanta
El-Hameed yace "Hajiya meyake faruwa ne?

Duk hankalin mu ya tashi, kiyi hakuri kiyi mana Bayani"
Ishraqa ma tace "Mamy meyake faruwa Dan Allah?"
Kafin tabasu amsa Amrah tashigo d'akin hannunta janye da jakar kayanta, cikin sanyin jiki ta kalli mamy tace "mamy nad'auko kayan"
Ishraqa tace "kayan me kuma?

Ina zaku da kaya?"
Asim yad'ago kansa yace "Nima abinda tafada min kenan, inje inhado kayana zamubar gida"
Sai lokacin Amina tashigo d'akin itama, hannunta dauke da kayanta, amma Bata dauki masu yawa ba, dan batasan abinda yake faruwa ba, kawai de Anty Amrah tace mata tahad'o kayanta
Dan haka kala uku ta dauka kawai, Sai kuma kayanta da Inna tabata wanda suka tsinceta dashi, doguwar riga dakuma zoben gold dinta
Gani tayi mamy tana kuka, Asim azaune agefen gado ya dafe kansa
Tunani tafara, dama ba dazu yace mata yayi tafiya ba?

Fasawa yayi kenan?
ta kalli Amjad shikuma Yana tsaye agefe kamar me laifi, gakuma El-Hameed mijin Anty Ishraqa atsaye, dakuma ita kanta Ishraqan ta harde hannunta a qirjinta.
gabanta ne yafara faduwa sakamakon ganin matar, ba tasan meyasa ba duk lokacin dataga Anty Ishraqa gabanta yake faduwa,saitaja ta tsaya a bakin kofar d'akin Bata qarasa shigowa ba
Cikin 6acin rai Ishraqa ta kalli Asim "ku zakubar gida kokuma yarinya ce zata bar gida?

Ai mamy banga amfanin barinku gida da wannan yarinyar ba, domin kuwa duk inda kukaje tana tare daku, kun kashe maciji ne Baku sare kansa ba, idan lokacin mutuwar Widad anyi dace tafadi gaskiya yanzun kuna tunanin ba'ita ce silar kukan mamy ba?"
Asim yadago kansa ya kalleta yace "Ishraqa miye haka ne?"
Cikin fishi tace "wanne irin miye haka?

Ita Minal din ina iyayenta suke da zata barsu tazo nan tana haddasa muku damuwa acikin gida?"
Daddy ne yashigo d'akin ko kula da Amina datake kofar d'akin beyi ba,Idonsa yariga yarufe, kawai so yake yaganta ya koreta tabar gidan domin flan dinsa yatafi daidai yanda ya tsara.
ya kalli Ishraqa yace "abinda nace kenan Ishraqa, tafice tabar min gidana, taje ta nemo waliyin daya daura mata aure itada Asim, saina yarda da wannan maganar, idan bata kawo waliyin ba kuwa ni babu ruwana, babu auren d'ana a kanta"
Baqin ciki ya kama mamy, ta juyo tana kallonsa wani irin hawayen taqaici Yana zubo mata, wata irin tsanarsa tana qaruwa acikin ranta
Hawaye masu d'umi suka zubowa Amina, tasa hannu ta share, idonta Akan Ishraqa, haqiqa Sai yau tasake tabbatar da cewa ba kowa zaka so yasoka ba, yanda take jinta a ranta, Bata cancanci hakaba, yanda Allah yadora mata soyaiyar ta be kamata tayi mata irin wannan cin mutuncin ba, Bata taba jin ta tsani ganin iyayenta ba Sai yau, meyasa zasu wofintar da'ita har Ana yimata cin mutunci Akan abinda tasan cewa gaskiya ne, saboda dukiyar Asim zata dorawa kanta auren qarya ne?

Kuka tafashe dashi, sosai take kuka harda sheshsheka
Ishraqa ta kalli Asim tace "Aure kuma? dama aurenta kake shiyasa kacemin bazaka iya korar taba?"
Asim yayi Shiru bece da'ita komai ba, yarasa meyasa Ishraqa takasa fahimtar Minal a wannan lokacin, yarinyar tanada nagartar daba kowacce mace ce Takeda itaba
Ishraqa kuwa dataga bebata amsa ba saita juya Inda take juyo kukan Minal a bakin kofar daki ta kalleta tace
" Hankalinki ya kwanta, kinzo kin hargitsa musu gida, kina murna ke kin auri Asim?

To bari kiji, akwai yarinyar danayi masa, Karki miqe kafa "
Cikin tsawa mamy tace
"Ishraqa!!!"
Ishraqa tajuya ta kalli mamy, bataso ta dakatar da'itaba, cikin bacin rai tajuya takamo hannun El-Hameed suka futo daga d'akin, saida tazo setin Minal ta kalleta ta wurga mata wata irin harara, sannan ta bangajeta gefe guda, har hakan yayi sanadiyar zubewar kayan dayake hannun Amina
Haushi ne ya kamata, a Karon farko taji bazata qyale wannan Anty Ishraqan ba
Abin yayi yawa, jitake kamar tarama abinda Tama, amma kuma babu hali tunda ta girmeta,kuma Bata tashi da tarbiyar yiwa nagaba da'ita rashin kunya ba,amma duk da haka saida ta d'aga idonta, ta kalleta ido cikin ido ta Rama hararar da tayi mata, sannan ta tsugunna tafara tattara kayanta daya watse, mamaki ya kamata Ishraqa, ita wannan yarinyar zatayiwa harara?

Daga ita har El Hameed binta sukai da kallo, saide Idonsu Yana sauka Akan kayan datake d'ebewa gabansu yayi wata irin fad'uwa
Idon El-Hameed Akan rigar da Amina ta d'auke dakuma Dan qaramin zoben da bazai taba mantawa dashiba, da lokacin daya siyoshi a Sudan
Cikin faduwar gaba yace "la'ilaha illallah, muhammadur
rasulullah...."
(s.a.w)
Sai kuka.

Cikin sauri Ishraqa tafara yiwa Amina wani irin kallo idanunta duk sun furfuto waje, kamar ta6a66iya haka tafara dudduba jikinta, takama kanta tana dube dube har zuwa bayan kunnanta, lokaci daya tafashe da wani irin kuka mai tsuma zuciya
Gaba daya kuma sai kallo yakoma kansu
Mamy, Daddy, Amjad, Asim, Amrah, kowa saiya zuba musu ido suna kallonsu cike da mamaki
Yanzu fa suka gama fadawa yarinyar magana, tomenene kuma yasa su kuka?

Ishraqa takama hannun Amina ta riqe gam, tana kuka nafitar hankali,Allah abin godia, yau Allah ya nuna mata 'yarta, Allah ya baiyana mata Insaaf dinta, gudan jininta
sosai take kuka amma kuma kwata kwata takasa dago kanta ta hada ido da yarinyar
Shikuwa El-Hameed har zuwa wannan lokacin salati kawai yake maimaitawa, me suka aikata?

Me suka aikata wa 'yarsu?

Yanzu dama irin rayuwar da Insaaf take fuskanta kenan?

Kafin daya daga cikin su ya tambayesu dalilin kukan su, 'yan sanda suka qaraso
Daddy Yana ganinsu ya nuna musu Amina "Gatanan, ku tafi da'ita, ta auri dana ne saboda taci dukiya, ku kamata inspector kutafi da'ita"
Gaban Ishraqa ne yayi wata irin muguwar faduwa, aure?

Meyake shirin faruwa ne?

Hakan yana nufin Insaaf dinta ce ta auri Asim?karfa ace game dinta da Asim ne yake shirin tabbata
Ashe kuwa za'ayi tashin hankali duk d'an sandan daya kuskura yata6a mata yarinya
Daya daga cikin 'yan sanda mace ta qaraso zata kama hannun Amina tasaka mana ankwa, cikin sauri mamy tace "inspector"
Dan sandan yajuya ya kalleta, tace "ba'ita zaku kamaba, shi zaku kama"
Tofa anan kallo yakoma wajan Mamy, mamaki ya kama kowa, Amina kuwa baqin ciki ne yataru yayi mata yawa, Ishraqa tagama cimata mutunci kuma tazo tawani riqe hannun ta tana kuka,menene yayi saura kuma?

Dama saboda Asim ne tazauna agidan, yanzu gashi Ana cimata mutunci Akan haka,saitaji rayuwar duniyar duk ta isheta, gidan duk yafita a ranta, neman Iyayen nata ma taji a ranta bazata sake yunqurin neman su ba, inda basu rabu da itaba dabata shiga cikin wannan halin ba, ya kamata ace tayi nesa dasu, fizge hannunta tayi taqarasa wajan Dan sandan, cikin kuka tace "nice me laifin, please katafi dani"
Cikin sauri Asim ya kalleta, meyasa koda yaushe takesan sakashi a damuwa ne?

Tayaya zata tafi ta barshi bayan tafada masa shi kadai gareta?

Mamy tace "inspector kukama alhaji kutafi dashi"
Sai alokacin Amjad yasake yimata magana, yace "Mamy!

Daddy nefa"
Daga masa hannu tayi batare data kalleshi ba, kuka ne ya qwace mata tace "Alhaji na zauna dakai tsakani da Allah, nasan cewa ka zaluncemu amma ahakan na aureka, yau alhaji Kaine kake neman rayuwar Asim...?

Alhaji Asim danka ne, wanne irin laifi yayi ma wanda zaisa ka kashe min dana,? wallahi saika fadawa hukuma kaida waye kukesan ganin bayan d'ana "
Gaba daya d'akin ya kaure da kuka, lokaci daya kaan Amjad yasara, mamy Bata lura da kukan datake ba ta kallesu tace"saboda nasamu naqwato muku dukiyar ku dake hannunsa yasa na yarda na Aureshi tare da shawarar qawata, ashe shirme nake, nayi tunanin da Asim ya nemi haqqin mahaifinsa awajansa zai bashi, ashe bai bashiba yahada duk yariqe, na riqe masa Dansa batare da cutar wa ba, Amma shi Yana neman ganin bayan nawa 'Ya'yan "
Sai yanzu ne suka Fahimci inda zancen ta ya dosa
Asim de ya sunkuyar da kansa yama Kasa cewa komai, amma bayan El Hameed babu wand baya kuka acikin d'akin, Ana cikin wannan halin Amina ta silale tabar gidan batare da kowa ya lura ba
Yan sanda suka kama daddy suka futo dashi "kai, ku dakata, wallahi wallahi..... , banida laifi inspector, bani kadai bane, wallahi banida laifi, sharrin shaidan ne kawai "
Haka yake ta fada, amma yan sanda basu lura dashi ba suka tusa qeyarsa suka tafi dashi
Ishraqa takai dubanta zuwa bakin kofa taga Wayam!
babu Amina babu dalilinta
Wata sabuwa, ko yaya Asim zaiji a page Din gaba idan yagane abinda yake gudu ne ya sameshi na auran 'yar qawarsa?
Chapter 29 · 0% Book details