← Book details Insaaf Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 53

Sashe 38

Insaaf Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kidena jin tsoron sa, kiyi masa duk abinda ki kasan zaki samu Lada, ga qananun kayan ki nan, jiya nasiyo miki su, dakuma sauran kayaiyakin ki"
Kayan tajanyo tafara dubawa, kaya ne qananu masu nuna surar jikin mutum tace "Anty wannan kayan ai sunyi qananu dayawa kuma....."
"to 'yar qauye, Karki saka, ki ajiyesu adaki, wannan wayar dayake yawan danne danne aciki,daya hadu da wata inta liqe masa shikkenan, idan kika masa magana saide kiji Yana cewa ya ina lissafi kina dawo dani baya?"
"a a wallahi....Allah idan ya kula wata sainayi fishi dashi"
Ishraqa ta kalleta, tana ihu batason Asim amma kuma Sai kishin sa take, to bazata qara magana ba, tsakanin mata da miji Sai Allah, tunda tace fishi ba tasan me zatayi masa ba, su suka sani
Tashi tayi tace "to nikam natafi gidana, amma Dan Allah inga sauyi daga yau Insaaf"
"to Anty, muje narakaki"
"a a, yi zamanki, nagode Sai anjima"
Daga nan tafita daga d'akin tajawa Minal kofar
Dawowa tayi tazauna tafara tunani, to yanzu ta ina zata fara?

Yanzu Anty data kawo mata wannan kayan tayaya zata sakasu a gidannan ta zauna dasu?

Ajiyar zuciya tayi, tatashi taduba cikin kayanta ta dauko wani dogon hijabi, ta ajiye agefe, kayan nata tafara dubawa duk qananu ne, yanzu wannan kayan zata saka kuma ta zauna Yaya Yaganta ahaka?

Anya?

Mayardasu tayi ta ajiye sannan tafara gyara d'akin, tashiga toilet nanma ta gyara shi
Tafuto tasaka turaren wuta ko'ina ya dauki qamshi, sannan tashiga tayi wanka, ta shirya cikin riga da sket, kayan sunyi mata kyau sosai, tafuto falo tazuba abinci taci
Dakin Amrah Takoma, suna fira, Amrah ta karbi wayarta taga duk babu wasu abubuwan na amfani aciki, tace "Minal yanaga ko Dan whtaspp dinnan bakya yi?"
"to dawa zanyi Anty Amrah?

Nida ba qawaye ba?

Kece kuma gakinan agida ina ganinki"
"kamarya ni?

Mijin naki fa?kawo kiga na Bude miki, zan turawa qawaye na number ki suyi adding dinki a group na matan aure,zaki sake sanin wasu abubuwan"
"to Anty Amrah gashi''
Amrah ta karba tabude mata, number Yaya Asim taduba taga tasa Yaya, ta kalleta tace" lalle ma, harda wani Yaya, ina laifin ma kisa masa wani sunan, haba Minal kamar ba 'yar zamani ba?

"
" to ai Gara ni inada number tasa, may be ma shi bashida tawa "
" to baki ki rashi ba tayaya zai samu number ki?

Kinga gashinan online karbi kitura masa txt kice kina missing dinsa yadawo gida da wuri "
Dariya tayi tace"tab, Yaya Asim din?

Kawai saboda nace ina missing dinsa saiya bar aikinsa yataho wajena?

Shida yakeda jarabar aikin nan"
"kina mamaki kenan?

Minal yayafa Yana sonki, amma ki gwada kigani"
Wayar ta karba tatura masa sallama, sannan tafara typing "Yaya ya aiki, yaushe zaka dawo..."
Amrah ta kalli wayar tace "goge wannan, ba gwada shi zakiyi ba?

Ai kalamai zaki tura masa"
Tace "wahalar banza kawai zansha Anty Amrah"
"bawani wahala gwada, Dan gulma kunason juna kun tsaya Sai wani abu kuke kamar 'ya'yan fari, koda yake ashefa 'yan farinne dagake harshi"
Murmushi tayi tace "yayan ki nefa"
"to ganina yake?, idan a gabansa ne na'isa nayi?, kutura masa Dan Allah, yanzu haka dawasu yake magana kintsaya kina wasa da damarki"
Cikin sauri tace "haba?"
Amrah ta kalli idonta tayi murmushi tace "kitura masa cewa Yaya kewarka tamin yawa tunda katafi dasafe nake tinaninka yaushe zaka dawo naganka?"
Zaro idonta tayi tace "kaiiii Anty Amrah, nida yafita yabar ni inata bacci, wallahi babu ruwana nikam"
Amrah ce ta qwace wayar tatura masa
Alokacin Yana office dinsa kishingide acikin kujera, datar ce abude, amma baya kan whtaspp, text din daya shigo masa da wata number ne yadauki Hankalinsa, ya karanta yasake karanta wa, cikin sauri ya hau kan whatsapp dinsa, tunani yafara waye zai turo masa wannan txt din?

Wata zuciyar ta bashi amsa da Insaaf
Murmushi yasaki har dimple dinsa Yana lotsawa, yasaka hannu yashafi sumar kansa, kode itama tafara sonsa ne?

Wayar yasaka cikin aljihun Wandon sa ya tashi yafara tattara kayan sa zaibar office din
Agogon office din ya kalla yaga shabiyu saura, ya dafe kansa da hannunsa, karfa yarinyar nan ta zautar dashi, daga turo masa txt ya tashi yabita, afili yace "tunda tanason ganina menene amfanin zama na anan?"
Hanyar fita daga office din yanufa saiya tuno da mamy, jinjina kansa yayi yace "Kar mamy tace saboda Insaaf nadawo gida"
Cikin zuciyarsa yace to ai kuma tasan ina son matata
Dawowa yayi yazauna afili yace "bari de ayi sallar azahar saina tafi"
Acan gidansu kuwa daga ita har Amrah dasuka ji Shiru kawai Sai suka haqura, ta kalli Amrah tace "kingani ai"
"Mena gani?

Kin tsaya Kinga bezo bane?"
Tace "to, nikam bari natafi daki akwai kayan dazan qara shiryawa"
"to saikin dawo" cewar Amrah
Harta gama qarasa shirya kayanta, tayi sallar azahar, har biyu da wani abu tana zaune da carbi ahannuta tana ja, Addu'ah tayi tatashi taje tasake wanka, tabade jikinta da turare,taduba kayan da Ishraqa ta kawo mata ta dauki wani riga da sket masu kyau tasaka, siket din saura kadan ya qaraso mata gwiwa, rigar kuma Normal riga ce amma an yanke gaban rigar anyi wani round agabanta, kana ganin komai
Dan kunneta tasaka, sannan ta dauki qaton hijabinta zata saka taji an turo kofar d'akin, mamaki ya kamata, amma saitayi tunanin Amrah ce, ganinsa acikin d'akin ne yasa gabanta yafadi, shaf Tama manta da batun text data tura masa, saita fara tambayar kanta menene yakawo shi gida yanzu?

Shikuwa Asim mutuwar tsaye yayi a bakin kofar, gaba daya yarinyar tagama tafiya da tunanin sa
Hijabin tafara dagawa zata saka amma data tuno yanda Ishraqa tabata shawara saita ajiye shi Akan gadon ta nufeshi tace "sannu da zuwa Yaya"
Hannunsa ya miqa mata, babu Musa tasaka nata hannun, cikin sauri ya fuzgota jikinsa tare da sakin wata irin Ajiyar zuciya, hancinsa ne yake yawo a jikinta, duk wani waje dayaji Yana tashin qamshi a jikinta saida yakai hancinsa wajan, yadawo da hancinsa dede wuyanta yasakar mata wani irin kiss, sannan yace "miss you too Baby...."
Wani iri taji, bayan mamaki daya kamata, kenan dawowarsa tanada nasaba da tetx din dasuka tura masa?kode da gaske Amrah take Yaya Asim Yana sonta?

Bata San dalili ba, haka nan taji wani irin farin-ciki ya kamata, cikin sigar shagwaba tace"yaya wajan mamy fa zanje "
Daukarta yayi cimak, yazauna Akan gado ita kuma yadora ta Akan cinyar sa, kansa yadora a wuyanta yace" wacce Mamy?

Bayan kince kina missing Dina nadawo gida?

"
" Yaya nifa dama....

Dama...."
" shiiiii"
ya katse ta
Sannan yace "wato bakya kewata ko?"
Girgiza kanta tayi, tace "ina...yi "
"to nunamin"
Kallansa tayi tace "me?"
"kewata mana, ba gashi kinsa nabar aikina nadawo wajanki ba?"
Shiru tayi, tadago kanta ta kalleshi ma takasa, kwarjini yake mata sosai, gashi Yana tayi mata abubuwa kamar ba Shiba
Tunanin tane ya tsaya cak, samakon jin hannunsa a inda Bata zata ba, budaddiyar rigarta ya qarasa zuge mata zip din rigar, lokaci daya rigar tayi qasa, wata irin kunya ta kamata, cikin sauri tarufe idonta da tafin hannunta, tasake fadawa cikin jikinsa
Murmushi yayi, yadora fuskarsa Akan Tata, yayinda hannunsa yake yawo Akan qirjinta, wani irin yanayi ya tsinci kansa aciki, kwata kwata ya manta da yarinyar dayake rainawa yake tare, al'amarin nasa bai tsaya iya nanba, saida yasamu nasarar hade bakin su waje daya, yanda yake shan bakinta da zafi zafi shine ya tabbatar mata cewa haqiqa yayi kewar matarsa, kokarin janye jikinta tafara, yayi sauri yasake ruqota, yaci gaba da abinda yake, yarasa meyasa take masa noqe-noqe kamar ba tasan komai ba, kunyarta tayi yawa, tayaya kin auri maza kusan shida amma kikasa bada hadin kai lokaci daya?

Kwata kwata tunanin sa ya gushe, baisan Yaya akai ba,shide ya tsincesu Akan gado,lafiyarsa kalau yashigo gidan, amma Sai yaji lokaci daya kansa yasara kamar wanda aka buga masa wani abu, amma bai kawo komai a ransa ba,boobs dinta dake cikin hannunsa ya matsa, cikin wata irin murya yace "Baby nawane ko?"
"uhmm...

Yaya ni Dan Allah kabari"
Zuciyarta daya tafadi wannan maganar, ba tasan shagwa6ar datayi masa sake tunzurashi tayi ba
Murmushi yayi, yayi kissing goshin ta, da idanunsa dake cike da buqata ya kalleta yace "bansan meyasa ba, inaji kaina yanamin wani irin ciwo"
Tace "Yaya ai akwai magani" tafadi haka batare data kalleshi ba
"ai kece maganin"
Murmushi tayi takauda kanta gefe, yace "inaso inyi wanka,ko zaki rakani?"
Idanunta tarufe cike da kunya tace "a a"
Hancinta ya lakace mata, sannan yafara gyara mata rigar Tata, amma yaqi yarufe mata bayan, daqyar ya'iya Raba hannunsa da qirjinta da suke mata wani irin zafi, sannan yashige toilet domin watsa ruwa
Washe Gari cewa yayi bazai je office ba, haka tazauna adakin nasa tana kokarin sakin jikinta dashi, kamar yanda yafada mata batada wajan zama Sai jikinsa hakan ce ta kasance, saide wuni guda yad'auka Yana sake alwala, da yayi sabuwa zata karye, tashiga wanka kenan ya dauki waya yakira Muhsin, bayan sun gaisa Muhsin yace "Ango mijin Amarya, ya aiki?"
"banje office ba yau, ina gida ne"
Dariya Muhsin yayi yace "tab, amma Insaaf tanada sa'ah, gaskiya kana kokarin tausayin yarinyar nan"
Murmushi yayi "Muhsin ai wannan yawuce tausayi, saide so"
"Okey, yanzu kadawo kan hanya kenan?"
"dama na Dade da dawowa"
"Alhamdulillahi, gaskiya naji dadi Asim, Allah kuma yakawo qannan widad da wuri"
"qanne kuma tun yanzu?"
"tome zaka jira?

Ai lokacin abu ayishi"
Dariya yayi yace "kaide bakada dama"
Muhsin yace "gaskiya ne, gobe idan kafuto office akwai wani laqani dazan baka, zakasha mamaki na"
"wanne irin laqani kuma Muhsin?"
"kaida muhadu goben"
"no, bawani gobe Malam, kazo ina gida ka kawo min yanzu, kuma ka fadamin na menene"
"to shikkenan ganina
n zuwa"
Ko 30 mint basu yi ba, yazo gidan,Asim yafuto compound din gidan yace "wanne irin laqani ne zaka Bani?

Kona soyaiya ne?
Chapter 38 · 0% Book details