Sashe 12
Insaaf Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Tunda suka zo gidan Bata taba kebewa ita dashi ba, wannan lokacin ne ya kamata ace tayi masa maganar datake damunta, idan tabarshi yatafi batason yaushe zasu sake ke6ewa ita dashi su biyu ba bare tayi masa magana akan sirrin ta daba kowane yasani ba Sai shi
Ahankali ta tashi taqarasa wajan sa, kanta a qasa tana Jan hannunta kamar wanda suke mata ciwo ta nemi waje adede kafarsa ta zauna aqasan kafet din, muryarta ta rawa tace "YAYA"
Zazzaqar muryarta tadaki dodon kunnansa, memakon yabude lumsassun idanuwansa saiya sake lumshe su (
Sosai yaji Dadin yanda takirashi da wannan sunan, zaiso ace ko sau daya ne tasake fada, dago manyan idonta tayi ta kalleshi, muryarta tafara rawa, tasake cewa "Yaya"
Nanma Shiru yayi mata kamar wanda yake bacci, hawayen da suke son zubo mata tana tare su, sune sukai nasarar sauka Akan kumatunta, Ahankali ta yunqura da niyyar tashi tabar masa wajan, yanajin haka yabude Idonsa yazube su Akan ta, karaf idonsa ya sauka Akan hawayen dayake zubo wa daga idonta
Ahankali yabude bakinsa kamar me muryar rad'a yace "zonan"
Hawayen tashare sannan tadawo tazauna aqasan sa
Gyara zamansa yayi sosai yadora hannunsa Akan cinyar sa, ya rankwafo da kansa dede fuskarta,kamar Yana rad'a mata wani abu,inda Allah yakawo Lubna awannan lokaci data gamu da hawan ruwa(
"Why are you crying?, ko maganar Daddy ce tasa kike kuka?" ta tsinkayi maganar sa cikin kunnanta
Girgiza masa kai tayi tace "ba wannan ne yasani kuka ba, kawai ina tunanin rayuwa tane, duniya tana cike da mutane mabanbanta, masu halin qwarai da akasin haka, inda ace Allah bai hadani dakai ba, da bansan hannun wa zan fada ba, nagode sosai" tana fadar haka hawaye suka sake zubo mata, ta Dora kanta Akan kafafunta tana kuka harda sheshsheka
Gabansa ne yafadi,Me wannan yarinyar take shirin yi bayan yayi niyyar taimaka mata? akano tace tanaso yakai ta gidan marayu, kode yanzu ma so take tatafi?
Metakeson fada masa?
"saboda....abin...da Daddy yayi miki ne zaki tafi?" yafadi maganar a rarrabe.
Dago fuskarta me cike da hawaye tayi tace "a a Yaya, babu inda zanje, idan natafi wani wajan wanake dashi bayan kai?
Kawai de inaso ka temaka min kamar yanda Allah ya temakeka, kanemo min iyayena afadin duniyar Nan, inaso naji dalilin dayasa suka rabu dani, meyasa zasu wofintar dani, ina tsoron ace niba yar halak bace, ka temakamin, Dan Allah"
Taqarasa maganar tana hade hannayenta waje daya alamar roqo (
Wata irin siririyar Ajiyar zuciya yasauke yace mata "shikkenan?"
Batace dashi komai ba, ta daga masa kanta
"ok zansa abincika miki"
Cikin muryar kuka tace "nikai da kanka nakeso ka temaka min, inaso nasan asalina"
Yatsani kukan mace, ita kuma yaga alama ta maida kukan kamar ba komai ba,tacika kuka dayawa saikace Ishraqa, cikin sauri ya d'aga mata hannu (
) yace "shikkenan...naji...
Is Okey"
Yadauki farin handkerchief dinsa dayake zuba uban qamshi ya miqa mata Yana mata nuni da idonta
Aikuwa Karaf Akan idon Lubna data futo daga d'akin ta tanaso takirashi taji a'ina ya tsaya bai dawo gida da wuri ba? (
Cak taja ta Tsaya awajan tana kallonsu kamar an dasata
Anya kuwa maganar Amrah gaskiya ne Asim baisan wacece INSAAF ba?
Ishraqa Bata boye masa damuwar ta, Shima haka, idan bai Santa ba menene yasa hatta computer sa take dauke da sunan yarinyar?
To kode akwai wata aqasa ne?
Wannan familyn kuwa Anya babu wani abu aqasa?
Mutane zasu so jin waye Asim, kuma menene takamaimai dalilin dayasa ake bibiyar sa?
To duk kubiyoni
SHARHI FA
Amnah El~Yaqoub
[2/7, 11:38 PM] El~Yaqoub: INSAAF
Writing By:Amnah El~Yaqoub
11&12
Like my page on Facebook
https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493
Masoyana masoyan wannan labari ina godia sosai agareku, inajin Dadin yanda kuke tattaunawa Akan wannan labari tun kafin ma labarin yayi Nisa, ina godia sosai
Amina da Asim kuwa basusan tashigo falonba, handkerchief din ta karba tagoge fuskarta dashi
Baqin ciki kamar ya kashe Lubna, kishin mijinta ya kamata, ta tsani taga wata mace tana ra6ar Asim
Ahankali take takowa harta qaraso inda suke, atsaye ta tsaya qerere ta kalleshi babu batun sannu da zuwa babu komai tace masa "ashe kadawo"
Atare suka daga kai suka kalleta, riga da siket ne ajikin ta na les da yayi mata mutuqar kyau, gashin dokin datasa a kanta anyi mata qananun kalba dashi
Amina ta miqe tabar musu wajan batare data bashi handkerchief dinba, Anty Lubna ta maka mata wata uwar harara tabi bayan ta da wani matsiyacin kallo, Asim yazuba mata ido Yana kallonta cike da mamaki
Amina kuwa harta shige daki tana tunani, tarasa meyasa Anty Lubna Bata sonta, idan Yaya Asim ne anfada mata sonsa take ne?
Ina ruwanta dashi?
Abinda yake damunta ma kadai ya isheta, idan tayi hakuri ma Zamanta a gidan nad'an wani lokaci ne, tana samun iyayenta zata bar musu gidansu, tabar mata mijinta, auren da aka daura musu ma hanyar da zata rabu dashi take nema, tayaya zataso mutumin daya taimaka mata yamutu a Sanadin ta?babu soyaiyar Asim ko kadan a ranta, auren ma tana fatan arabashi tahuta
Ajiyar zuciya Lubna ta sauke ta kalleshi, "inama magana kayi Shiru, nace ashe kadawo"
"nadawo" Shima yabata amsa a taqaice
"Wai Dan Allah My dear menene hadinka da wannan yarinyar?
Tunda kuka dawo ina lura dakai Sai nan-nan kake da'ita, ita 'yar gidan uban waye da zata dinga kuka ka zauna kana lallashinta Sai kace zaka maidata jikinka?" (
Tsananin mamaki ya kama Asim, kamar hoto haka yake kallonta, 'yar gidan uban waye? shita zaga kenan?