Sashe 22
Insaaf Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Idan matarsa tazo ta gansu kuma tahau dukanta, Ahankali tace "a a Yaya, nanma yayi"
"ki tashi nace"
Cikin sauri ta tashi tazauna a'inda ya nuna matan, Ahankali yajuyo Yana fuskantar ta,yanda yajuyo yake kallonta saika dauka wasu shahararrun masoyane, yanaso yayi mata maganar Amjad, ya kamata a matsayin sa na wanda yakawo ta gidan ace sun tattauna Akan maganar, ko yaya ne abata haqqinta, idan ta amince da auren shikkenan, idan Bata amince ba Sai tayi karatu, amma Yana fatan ace bazata amince ba, saboda a halin datake ciki yanzu karatu shine gatan ta, zai so ace tayi karatu me Nisa domin ta in ganta rayuwarta har zuwa lokacin da iyayenta zasu baiyana idan Allah yayi suna Raye
Ajiyar zuciya yayi "inaso zamuyi magana ne..."
Gabanta ne yake faduwa, ganinsa agabanta sosai yayi mata kwarjini,gashi yajuyo Yana fuskantar ta, Ahankali ta daga masa kanta
Yace "Akan maganar Amjad ne, kina ganin kamar...babu wata damuwa ne zaki iya..."
Amina tadago kanta ta kalleshi, meyasa yaqi yayi mata maganar kai tsaye?
Meyasa yake wata irin hanya-hanya kamar bayason yin maganar?
Da alamu duk abinda zai fada mata me wahalar fada ne awajan sa
Dan haka ta katse shi tace"Yaya, Nima akwai maganar danakeso muyi "
Shiru yayi Yana kallonta, kode itama ta ganene bayason yimata maganar shiyasa zatayi abinda zai fishsheta?
To bari yaji dame tazo kuma, yace "inajin ki"
"dama.... am dama fa....
Kwanaki ne..."
Daga nan tayi Shiru takasa qarasawa, tunani take a ranta tayaya zai karbi abun? ta wacce hanya zata fahimtar dashi abinda matarsa take qulla masa?
Anya kuwa zai yarda?
Karfa yace sharri take yiwa matarsa...
Dago kanta tayi ta kalleshi, taga yazuba mata ido Yana kallonta, gaba daya ya tatt
ara Hankalinsa waje daya yabata, daga kansa yayi, alamun yanajinta taci gaba, Ahankali tafara wasa da yatsun hannunta tace "Yaya, kwanaki naji Anty Lubna tana waya... wai, wai zata saka maka magani acikin abinci, idan Kaci zaka mutu...."
Gabansa ne yayi wata irin faduwa, lokaci daya yanayin sa ya sauya, idanunsa suka furfuto, ya sake kallonta yace "Lubna kuma?
Kinsan abinda kike fada kuwa?"
Cikin ranta tace dama nasani, nasan bazai taba yarda ba,to wannan na kwanakin bayan ma kenan yaqi yarda inaga tafada masa abinda taji jiya?
gabanta yaci gaba da faduwa, idanunta ya raina fata, Ahankali tace "Eh Yaya, kuma tasaka maganin a abincin, shine nazubar dashi, alokacin sau biyu tana marina"
Lokaci daya yatafi duniyar tunani, ya tuna lokacin daya shigo gidan yaga tana marinta saboda tazubar da abinci, Anya kuwa yarinyar nan da gaske take?
Tayaya Lubna zatayi masa haka?
Ita da kanta ta nuna tana sonsa aka hadasu aure to tayaya zataso yamutu?
To idan tanaso yamutu su kuma wanda suke son ganin bayansa waye yake turosu?
Ahankali yakamo hannayenta duka biyun yariqe, ya hada idonsu waje daya, gabansa Sai faduwa yake, mamaki tattare saman fuskarsa yace "fadamin....,ki fadamin komai"
Lokaci daya tsoro ya kamata, ganin irin yanayin dayake ciki,to idan yaji harda computer sa take nema Yaya zaiyi?
Ahankali tafara kokarin cire hannunta daga nasa, tana tsoron ace wani daga cikin yan gidan ya shigo falon ya gansu a haka, uwa uba Anty Lubna, idan ita tana had'a jikinta danasa tasan cewa akwai aure atsakanin su, amma shifa?
Bai saniba, sannan duk gidan babu wanda ya sani
Yanajin yanda take kokarin janye hannunta daga cikin nasa ya sake ruqo hannun, yaqi Bata Damar qwace hannun, domin ta taqaita maganar tasu Sai tace "Dan Allah Yaya karka sakecin abincin da Anty Lubna zata baka, wannan shine abinda nakeso nafadama, Amma fa Amana" (
Da babu Gara dinga ragewa ko kadaanne
Sharhi
Amnah El~Yaqoub
[2/14, 12:43 AM] El~Yaqoub: INSAAF
Writing by:Amnah El yaqoub
23&24
Like my page on Facebook
https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493
"Amana"
Yamaimaita kalmar a ransa, Ana cikin magana ta hankali tasako masa wata yarinta Wai amana,wannan maganar ake kira da amana, yazuba mata ido Yana kallonta yaga idonta yayi wani tsuru tsuru, tsananin tsoro yataru yayi mata yawa, kamar ace mata kyattt tafita aguje, tsananin tashin hankalin data hango a saman fuskarsa ne yasa tasake tsorata, har tana dana sanin fadar maganar da tayi, hannunta dake cikin nasa ya sake riqewa kamar zai 6allata yace "waye yafada miki?"
Girgiza kanta tafara yi tana kokarin qwace hannunta tun kafin ya karyata, kafin tabude baki tayi magana ya daka mata wata irin tsawa "nace waye yafada miki?!!!"
"Babu kowa Yaya, amma...."
"dakata"
Ya dakatar da'ita ta hanyar daga mata hannu
Sannan yasaki hannun ta dake cikin nasa yace "tashi kibar nan wajan"
Cikin sauri ta tashi tawuce daki, Dan dama atsorace take dashi, tana zuwa daki kuwa taji motsin ruwa a toilet alamar Amrah na wanka, kayanta na qauye tabude, ta dauko laptop din ta nadeta acikin wasu kayan, sannan tasake 6oyeta da kyau
Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un kawai yake maimaitawa acikin ransa, ya saka hannu ya hargitsa sumar kansa kamar sabon kamu, tayaya haka zata faru?
A'ina Yarinyar nan taji wannan maganar?
Anya kuwa da gaske ne?
To tayaya za'a ce Lubna tanason ganin bayansa?
Gaba daya kansa ya kulle, yama rasa wanne irin tunani zaiyi,mutum dayace ta Fado masa, yasan cewa kuma zata kamo masa bakin zaren, Dan haka kai tsaye ya nufi gidan Ishraqa, anan ya sake tadda wani abun mamakin, wannan d'akin daya sameta rannan yauma aciki ya ganta, shide yasan cewa Ishraqa Bata aiki da kanta, saide tasa me aiki tayi mata, saide abinda ya danganci mijinta ne kam Bata wasa dashi, tana kiyaye wannan bangaren, amma Sai gashi yauma yazo ya ganta tana gyaran gado tuquru, zama yayi tare da dafe kansa dayake masa mugun ciwo, yace "Ishraqa akwai matsala"
*** ****** ***
Tunda sukai waya da oga har yau takasa samun sukuni, yanzu tayaya zata zubawa Asim guba, wadda zata karya masa garkuwar jiki?
Laptop din de tayi wannan alqawarin, amma guba kam, Sam Sam bazata iya zuba masa ba, to ai idan tazuba masa ma itace a wahale, hatta wankansa kanta zai dawo, komai itace zata masa, Gara ta haqura kawai, to Amma kuma idan batayi ba mutumin nanfa zai'iya zuwa gida yatona mata asiri awajan Asim, ita kuma Bata fatan Hakan, idan mutanan gidan sukaji abinda ta aikata kafin ta shigo gidan haqiqa kowa saiya tsaneta
Tashi tayi tana Zagaya d'akin, Ahankali tafara magana "gaskiya bazan saka masa ba, nahaqura kawai, idan nasaka masa ma nice a wahale, computer de idan naganta dole zan kwashe komai na basu, kodan wannan shegiyar Insaaf din"
"momy ba kince babu kyau Ana cewa mutum shegiya ba"
Ta tsinci muryar Widad tana doko mata tambaya, cikin sauri ta kalli yarinyar taga tana wasa da babyn roba, batasan ma tashi go dakinba
Ajiyar zuciya tayi tace "mekike yi anan?
Tashi muje muyi lesson"
Widad ta daga mata hannu, babu musu Lubna ta dauke ta, tayi kissing kumatun yarinyar sannan suka fice daga d'akin
*** ****** ***
Ishraqa tayi Ajiyar zuciya bayan tagama sauraron Asim wanda yake mata Bayani idanunsa yayi jajir, tace "Nifa Asim kwata kwata ban yarda da maganar yarinyar nan ba, tayaya Lubna yanda idonta yarufe a kanka, matarda taqi jinin ace wata mace ta rabe ka itace zata kasheka, to inasu Mamy da kowa da kowa na gidan?
Kisan kai aiba qaramin abu bane, kaima daka tsaya ka saurareta kafi 6atamin rai,haka kawai baka Santa ba, bakasan tushen taba, yarinya taga kakawo ta gida, tasamu waje ta wanke, ba dole tayi tunanin rabaka da matarka ba?, ni ranar nan naganta tare da Amrah, inda nasan haka halinta yake dana wanka mata Mari tafice tabarmin gidana, tun tuni kayi gaggawar sallamarta, inma gidan marayu ne kakaita, kokuma kasan inda zaka kaita, inba hakaba kanaji kana gani zata rabaka da danginka "
Dago kansa yayi ya kalleta "gidanki kuma?"
Cikin yatsina fuska Ishraqa tace "Um Wai na rungume ta, bansan meya sanyayamin raina ba harna kulata, nide na fadama, inma baka sallameta ba wallahi da kaina zanzo nafitar da shegiya daga gidan" (
Ajiyar zuciya yayi, wannan furucin na Ishraqa shine yad'an kwantar masa da hankali, kuma saiya sake tuna irin soyaiyar da Lubna take masa, komai yimasa takeyi, tagama shagwaba shi, Ahankali yace
"hakane, nima nafi tunanin shirmanta ne kawai, Amma I am sorry Ishraqa, bazan iya korarta ba, ina tausayin ta"
Wannan kalmar tausayin da yayi ne ya sanyaya mata jiki, lokaci daya 'yarta mafi soyuwa a ranta tafado mata, batasan inda take rayuwa ba, tanacin abinci ko bataci, atiti take ko agida, a mace take ko araye, Sai tayi Shiru kawai batace masa komai ba, amma bacin rai kam yarinyar ta6ata mata rai, Wai Kisan kai
Kallan bedsheet din d'akin yayi yaga ta sauya, yace "mekike yi adakin nan ne?"
Ranta ad'an 6ace tace "Insaaf na gyarawa"
Kallanta yayi cikin mamaki "kinganta ne?"
"a a, kuma Naga Insaaf din kakasa sani?kakasa ganinta a jikina? ni dama Ina gyara mata kullum"
Mamaki yaqara kama Asim, "Ishraqa soyaiyar nan tayi yawa,waiku larabawa meyasa kuka cika son Yara dayawa ne? yanzu kina nufin inda tana nanma kece zaki mata aikin?"
"to menene Asim?
'yartawa qwalli daya jal idan bansota ba wazan so?