← Book details Insaaf Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 53

Sashe 24

Insaaf Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Saina kasheki yanzu yanzun nan, tunda kika kashe min 'yata "
Gaba daya Sai waje ya kaure da kuka, mamy tana kuka tana dukan hannun Asim yacika Lubna amma Asim ya kama wuyanta yariqe, daga mamy har Amrah babu wanda ya Fahimci komai, ita Lubna tana cewa Asim ya kashe mata yarinya, Shima Yana cewa Lubna ta kashe masa yarinya, Daqyar da taimakon likitocin asbitin aka qwaci Lubna daga hannun Asim, idanunsa yayi jajir, amma baiyi hawaye ko daya ba, tarin wahala Lubna take saki, numfashinta Sai Sama yake, cikin kuka mamy tace "haba Asim....,da hankalinka da komai, so kake ka kashet....."
Kafin ta qarasa yatareta, "mamy ku dauke ta daga gabana nadena ganinta, babu ni babu ita, taje na saketa"
To jama'ah, karkuji ni Shiru zan Dan huta insha Allah, tunda muka fara bamu hutaba
Insaaf tana gaisuwa gareku
Wanne irin sirri Lubna take tsoron atona mata?
masu maganar yaakamata Ishraqa ta hadu da yarta, da masu cewa ya kamata ta bashi laptop dinsa duk najiku, babu yanda za'ai an rubuta labari a banje shi adawo da gaba baya, idan kukai hakuri zamuzo wannan ga6ar insha Allah, nagode
Amnah El~Yaqoub
[2/15, 10:19 PM] El~Yaqoub: INSAAF
Writing by:Amnah El yaqoub
Like my page on Facebook
https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493
25&26
Cikin kuka mamy tace "Asim.... saki Asim?"
Cikeda 6acin rai yace "Mamy na tsaneta, ta cutar da rayuwata, kuma Sai taga abinda zai biyo baya"
Wannan furucin nasa da yayi na sakine yasa su Amina da Amrah cigaba dakuka, ita kanta Lubna kalmar sakin daya fada tasata acikin wani tashin hankalin, jitayi numfashinta Yana Sama-Sama, tasa hannunta aqirjinta, likitocin dasuka qwace ta ne suka fara kokarin temaka mata.

Adede lokacin tashigo asbitin hankalinta atashe,yauma kamar kullum laffaya ce a jikinta, tana zuwa ta nufi wajan mamy datake kuka sosai, shikuma Asim kansa Yana qasa yamaqi kallon kowa.

"mamy meyake faruwa?

Megadi ya shiga gidana yacemin kun kawo Widad Asbiti, meya sameta?"
Kafin mamy tabata amsa yadago kansa yana mata nuni da Lubna "Gatanan...ki tambayeta"
Juyawa tayi wajan Lubna wadda gaba daya Bata haiyacinta, likitocin dasuka riqeta ne suka maidata wani daki, tajuya ta kalli Amrah da Amina, suma taga suna tsaye suna kuka, tasake kallon mamy itama kukan take, cikin tashin hankali tace "Dan Allah Ku fadamin, meyake faruwa ne?

''
Mamy ce ta share hawayen idonta tace"Ishraqa Widad tarasu yanzu "
" innalillahi wa Inna ilaihirraji'un....

"
Shine abinda Ishraqa tafada tazauna awajan jagwab, hawaye ne yafara ambaliya Akan kuncinta, ta kalli Asim da kansa yake qasa"meyasame ta?

Batada lafiya ne?"
Sai alokacin yad'ago kansa, idanunsa sunyi jajir, har gara ace yayi kuka zaifi wannan tsananin bacin ran dayake ciki
Yace"lafiyarta kalau Ishraqa, ni tayi niyyar kwashewa ba widad ba, dama nafada miki ai "
Ishraqa tasake fashewa da kuka tana fadin" hasbinallahu wa ni'imal wakeel "
Mamy ta kallesu cikin sauri, akwai wata aqasa kenan, da alama dama can shida Ishraqa sun san da wata maganar
Doctor ne ya shigo yace" zasu iya zuwa police station suyi report daga nan saisu dauki yarinyar, tashi yayi cikin qarfin hali yace "Bama buqatar hakan doctor, already munsan wanda ya aikata hakan, Bari mu dauke ta muje gida kawai"
Doctor ya jinjina kansa sannan sukai cikin d'akin da yarinyar take
Bayan shigar su d'akin Sai kowa yayi kanta, Gatanan a kwance kamar zaka kirata ta tashi
Abubuwa da dama suka dinga dawo wa Amina a ranta
tatuna ranar da ta dauke mata mayafi, da ranar datake cewa tanaso su dinga wasa tare,wani irin abu ya tare mata maqoshi, Sai kuka take, Amrah kuwa kawai kallon gawar yarinyar take, Wai widad ce ta mutu
Ishraqa kuka kamar 'yarta ce tarasu, bakomai ne yafado mata a ranta ba Sai 'yarta, inama ace itama zataga koda gawar 'yarta ne? dataji dadi a ranta, kuma hankalinta zaifi kwanciya, tasan Insaaf ta riga ta mutu, amma yanzu batasan ma ina take ba
Ahankali ya tsugunna ya shafa fuskar yarinyar, (Daddy yauni a wajanka zan zauna muyi wasa)
Yatuna maganar yarinyar ta qarshe, Sai alokacin yaji qwalla tacika Idonsa, yasa hannu zai share Yana kokarin maida kukan, mamy ta dubeshi "kayi kuka Asim..., Kar hakan yajama matsala please kayi kuka ko yaya ne..."
Girgiza kansa yayi "a a mamy, Allah yaji qanta, Allah yayi mata rahma yasa mai cetonmu ce"
Gaba dayansu suka amsa da amin, bai qara cewa komai ba, daga haka yadauke ta suka tafi gida
Tunda a kayiwa Widad sutura aka kaita makwancinta gidan yayi Shiru, Daddy da Amjad dakuma wasu daga cikin dangin Lubna duk sunzo, saide har yanzu duk wanda yazo idan ya tambayi ina take, aka fada masa tana asbiti Tofa idan yatafi baya dawowa
Ishraqa kuwa tana gefen mamy tsoron duniya ya shigeta
Kawai tuna lokacin da Asim yaje mata da maganar take, gaskiya mutum ba'a bakin komai yake ba, haka kuma mutum ba abin yarda bane, to Amma Yaya akai ita wannan yarinyar tasan da wannan maganar?

Mamy kuwa tana amsar gaisuwa ba tayiwa Asim maganar Lubna ba, kuma batayi wa Ishraqa magana Akan maganar dataji sunayi itada Asim ba
Gaba daya hankalinta Yana wajan Asim din, tunda yamma daya shige dakinsa bataga yafuto ba, gaisuwar ma su Daddy ne da Amjad suke karba a compound, gashi beci komai ba, haqiqa yau taga amfanin Lubna, ko yaya inde mutum yanada mata yafi ace bashida ita, tasan dayana da wata matar dole zata sashi yaci abinci,zata jashi a jiki ta rungume shi ta lallasheshi,ta Fahimci halin dayake ciki, to Amma menene yake faruwa atsakanin Asim da Lubna?

Ita Lubna tace ya kashe mata yarinya, meyasa zai Barta taci abinci?Hakan yana nufin itadashi sunsan akwai guba acikin abincin kenan kome?

Toshima kuma Yana cewa takashe masa yarinya, dole zata nemi qarin Bayani awajan Asim, Amrah ta kalla tace "tashi kikaiwa yayanki abinci"
Amrah tatashi zata kitchen din, jiri ya debeta, tazauna cikin sauri, sauran jama'ar falon suka hau yimata sannu
Ta kalli Amina tace "jeki kai masa Minal"
Ahankali tatashi daga gefen Ishraqa
Dan dama tunda ta ganta a falon saida tasan yanda tayi ta mamuqa tashiga tazauna agefenta, wani ma tsaf zaice tare sukazo gidan
Kitchen din tashiga tahada masa komai kamar yanda taga sunayi, sannan ta nufi dakinsa
Afalonsa ta ganshi, Yana kwance Akan doguwar kujera ya lumshe Idonsa, ga TV nan tana yi Yana sauraron karatun alqur'ani
Ahankali ta tsugunna, tazuba masa abincin d'an kad'an, batayi karanbanin zubawa da yawa ba, tasan cewa Kota zuba dayawama ba lalle ya'iya ciba
Kallonsa tayi, tarasa tayaya zatayi masa magana,ba tasan Yaya zatayi ba, amma tabbas shidin abin tausayi ne, ba tasan hanyar da matarsa takebi wajan kwantar masa da hankali ba, wata zuciyar tace, ya kamata ki bashi kulawa, akwai auren sa a kanki, haqqinsa ne ki kula dashi, ki saurareshi, ki lallasheshi koda hakan shine abinda zaki masa na qarshe a rayuwarki, matsawa tayi gab da inda kansa yake ahankali tace "Yaya..."
Yana jinta, amma bai Bude Idonsa ba, da farko ma yayi tunanin Amrah ce, kansa ne yake masa mugun ciwo, bayason damuwa ko kadan
Ita kuma dataji yayi Shiru, tayi tunanin ko Yasamu bacci ne, tannunta tadora Akan goshinsa taji da zafi sosai, cikin sauri ta dauke tace "subhanallah..."
Ahankali yabude Idonsa yazubesu a kanta, kallonsa tayi damuwa ta baiyana Akan fuskarta qarara "bakada lafiya ne? tashi Kaci abinci saina kawoma magani, tashi Yaya"
Beyi niyyar cin abincin ba, saboda jin cikin sa yake duk acunkushe, amma ganin yanda duk ta rikice, shine yasa ya tashi ahankali yazauna, abincin ta dauko tadawo gefensa tazauna Akan kujerar itama, kusancin nasu yayi kusanci har tana jin yanda jikinsa yake gogar nata
Spoon din ta dauko, tadebo abincin takai bakinsa, cike da yarinta tace "haa, Bude bakin Kaci abinci"
Mamaki ya kama Asim, yanda ta Dage zata bashi abincin saikace irin mamansa d'innan kokuma wata babbar mace, wannan yarinyar haqiqa Amjad zai samu kulawa sosai idan sukai aure, shida yake ganin Lubna tana kulawa dashi ashe wasan Yara take....

Amina tayi saqare da cokali a hannu, gabanta ne yafara luguden faduwa saboda wata shawara da zuciyarta tabata, Anya kuwa zata iya?

Sai kuma wata zuciyar tace to ai mijin ki ne, ba haramun bane, kwarjinin da yayi mata ne yasa hannunta yad'an fara rawa kadan, Ahankali takai dayan hannunta kan lallausan lips dinsa, tabude masa bakin nasa,saita ji laushi saikace bakin Yara, jin hannunta Akan lips dinsa yasa ya lumshe Idonsa babu Shiri
Saida yaji tana kokarin saka masa spoon din abakinsa ne sannan yabude Idonsa, beyi musu ba kuwa ya qarasa Bude mata bakin tafara bashi abincin, cikin zuciyarsa Yana tunanin dole zai dauki kyakkyawan mataki Akan Minal, yanda take masa d'innan wata Rana Sai Asamu matsala, duk tabi ta maidashi wani Dan jariri cikin mintunan dabasu fi goma ba, zata iya yiyuwa anata bangaren tana ganin hakan ba komai bane, zata iya yiwa kowa, but anasa bangaren akwai matsala gaskiya
Ko cokali biyar beyi ba, yaji wani irin amai yataso masa, kafin yayi yunqurin tashi harya fara yi ajikin hijabinta, duk ya 6ata mata gaban hijab din, lokaci daya ta rude, tafara jera masa sannu, sannan tatashi taja hannunsa tarakashi toilet ya wanke bakinsa, hijabin jikinta tacire, tasake kamoshi suka dawo falon, Akan kujerar ta zaunar dashi tana masa sannu
Kansa kawai ya d'aga mata, Idonsa a lumshe, tace "Bari naje nakawo ma magani awajan mamy"
Cikin sauri yariqe hannunta, dayan hannun nasa Yana dafe da goshinsa yace "karkije, ciwon Kaine kawai, zai daina anjima"
Dawowa tayi tazauna tasaka hannunta duka biyun ta janye nasa hannun daga kan goshinsa tace "to sannu, Allah yasawaqe"
Baisan lokacin da yaji hawaye sun zubo daga idanunsa ba, tunda widad ta mutu har suka kaita makwancinta beyi kukaba Sai yanzu
Amina ta rikice ganin hawaye a'idon babban mutum kamar wannan, tarasa Yaya zatayi masa, duk saita daburce, itama kukan taji Yana kokarin zuwa mata, Bata yi kokarin Hana kanta ba tabar hawayen suka fara sintiri a kumatunta, cikin kuka tace "Dan Allah kayi hakuri kaji...."
Lokaci daya ya fuzgota jikinsa yasaki wani irin kuka, sosai yake kuka kamar mace, baqin ciki sa daya me yayiwa Lubna?

Yanzu badon Allah yakawo Minal gidan ba kenan da yanzu shine yamutu, meyasa takeson kashe shi?

Dama tanada wata manufa ne akansa?

Cikin sheshshekar kuka yace "thank you Minal.....
Chapter 24 · 0% Book details