Sashe 20
Insaaf Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ahankali tafara takawa zuwa gare ta, Ishraqa tazuba mata ido, haka itama Amina idonta cikin na Ishqara, ganin da gaske kamar wajan ta zatazo kawai saita Girgiza kanta tawuce cikin gida
Cikin sauri Amina ta miqa hannunta tanaso takira sunan ta amma kuma saide tuni tashige cikin gida, jitayi wani irin baqin ciki ya kamata, ta d'ade tana son ganin matar gashi yau Allah ya had'asu amma kuma batayi mata magana ba, dama hakane, Saikaga Allah yadora ma kaunar mutum aranka, amma shi awajan sa ba Bahaka bane, wata zuciyar tace da'ita, meyasa zakiyi mata magana?inake ina wannan matar?
Gwalgwalan da suke hannunta kad'ai ya'isa kasan cewa ba qaramar mace bace, girgiza kanta tayi, afili ta furta "bazai iyu ba"
Daganan tanufi get din gidan, Sai alokacin maigadi yabudewa El Hameed get, kafin yarufe tuni Amina ta fad'a cikin gidan (
Amrah tayi sauri ta kwashi ledojin kayansu tabawa maigadinsu itama tabiyo bayan Amina cikin sauri
Tun kafin El Hameed yafuto daga Mota Amina ta qwalawa Ishraqa Kira
"ANTY ISHRAQA"
Cak ta tsaya awajan datake batare data juyo ba, me kuma wannan yarinyar take nema awajan ta?
Kawai daga haduwa saita shigo mata gida? da waye ma yafada mata sunan ta?
Shareta tayi, taci gaba da tafiyar ta batare data juyo ba bare Amina tayi tunanin samun kyakkyawan kallo
Ganin zata shige ta qyaleta ne yasa ta daga muryarta tace "MAMAN INSAAF !!"
Cikin sauri Ishraqa ta juyo, saboda an kirata da sunan datake mutuqar so, d'an sauran kukan data riqe ya qwace mata, Ahankali hawaye ya silalo daga idonta
Amina tana ganin tajuyo ta qarasa wajan ta da sauri, duk da gabanta Yana faduwa bataji tsoron taba, kawai saita bar faduwar gaban nata a matsayin kwarjini da matar tayi mata, dakuma rashin sabo
Kallon idonta tayi cikin in-ina tafara magana "dama..
Nace...
Dan Allah...
Ko zaki iya rungume ni?"
Amrah tashigo gidan, tana ganin Amina awajan Ishraqa tace "yau Naga takaina"
Tadaga murya takirata "Minal !!"
Amina tana jinta ta qyaleta
El Hameed yana daga gefe Yana kallon ikon Allah, yasan Ishraqa ba zatayi abinda yarinyar tafada ba, musanman yanzu datake cikin bacin rai tsaf zata huce akan yarinyar, amma abinda yaqara bashi mamaki harya Kasa boyewa shine ganin Ishraqa ta meqawa yarinyar hannu
Amina na ganin haka tafada jikinta ta rungume ta sosai, itama Ishraqa jin yarinyar a jikinta saitaji wata irin nutsuwa tana shigar ta, hawaye ya sakko daga idonta, Ahankali tasaka hannu ta rungume Amina, lokaci daya Amina ta lumshe idonta, tana sauke wata irin Ajiyar zuciya
Pls kuyi hakuri da wannan ba yawa
Sharhi please
Amnah El~Yaqoub
[2/11, 10:41 PM] El~Yaqoub: INSAAF
writing by:Amnah El~
19&20
Like my page on Facebook
https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493
Tsawon minti uku suka dauka a haka, El Hameed dai yayi Shiru Yana kallansu, ita kanta Ishraqa bazata ce ga dalilin dayasa ta rungume yarinyar ba, Amrah ta qaraso ta janyeta daga jikin Ishraqa, tace "Anty Ishraqa Dan Allah kiyi hakuri"
Ko sake kallon fuskar Amina batayi ba, cikin sanyin jiki ta dagawa Amrah kai, hannun Amina cikin na Amrah suka futo daga gidan, Amma Sai waigowa take tana Kallan Ishraqa, wani dadi yana qaruwa acikin zuciyar ta
El Hameed ya qaraso wajanta Yana mamakin yanda fuskarta tasaki kamar ba'ita ce take kuka ba,yayi Ajiyar zuciya Yana kallon get din nasu bayan fitarsu Amrah "yanzu fa inda ace Insaaf tana nan zata iya kaiwa kamar wannan yarinyar"
Hararar wasa tayi masa "Habibiy yaushe zan iya haifar kamar wannan?, kaduba kaga yarinya budurwa kace zan haifi kamarta?"
"Habibty koda yaushe maida Insaaf baya kike, karfa ki manta last month mukayi mata birthday party na 18 years, saboda haka yarinya de ta girma, ke kuma kin zama tsohuwa" ya qarasa maganar cikin sigar tsokana
Ahankali tad'an daki qirjinsa sannan tad'ora kanta akai, murmushi yayi yasa hannu Yana shafa gadon bayan ta
*** ****** ***
Da daddare gaba dayansu zaune suke afalo, Widad tana cinyar Mamy, Asim yana daga can gefe azaune Yana kallonsu, waya ce a hannunsa Yana dannawa, amma hankalinsa yanakan su, Amrah da Amina suna zaune aqasa kowa Hankalinsa Yana kan kallo, Amrah tana Bawa mamy labarin inda sukaje d'azu dasuka fita kasuwa, saida tayi maganar kasuwa sannan ya tuna da maganar gyaran gashin dayace ayi mata, kallon gashin nata yayi yaga Sai sheqi yake, yakai dubansa zuwaga rigar jikinta, idanunsa sukai arba da nashanunta wanda rigar tabasu haqqinsu na futowa sosai, fuskarta de babu kwalliya, amma tayi kyau sosai, kayan ya karbi jikinta
Widad ta tashi daga cinyar mamy tadawo wajan Amina takama dogon gashinta, tace "laaa kema Ana saka miki gashi irin wanda ake Sawa momy na?"
Mamy tayi dariya tace "Widad Bari mana, kidena ja mata gashi, wannan ba irin na momynki bane"
Sake dago kansa yayi yaga yanda widad take wasa da gashin, Sai hakan yabashi sha'awa yakasa dauke Idonsa akansu, Yana qaunar gashi arayuwarsa, shiyasa ma da Lubna take saka attachment beta6a Hana ta ba
Amrah tace "Ai mamy awajan saloon dinma bakiga yanda ake kallonta ba, saikace gashin Anty Ishraqa"
Mamy tace "eh maman Insaaf ma irinsa ne da'ita, ko anyi mata kitson baya iyuwa, shiyasa kullum take hanyar wajan masu saloon"
Amina tana jinsu batace komai ba saide Dan qaramin murmushi da tayi kawai
Amjad ne ya shigo d'akin bakinsa dauke da sallama, yayi kyau sosai acikin qananun kaya,wasu takardu yabawa Asim sannan yayi wajan mamy yazauna akusa da'ita tare da d'ora kansa Akan kafadarta yace "Mamy nadawo"
Kansa tashafa tace "Sannu Autana, kunyi waya da Daddynku kuwa?"
"eh nakira shi dazu, mun gaisa, yacemin ma yakusa dawowa, mamy Wai kinyi masa maganar sa ranar ne?"
Amina da Amrah da Asim duk suna jinsu, kowa yasan Akan abinda suke magana, amma ita ko kadan ba tasan a kanta ake maganar saka ranar ba
Mamy tace "nayi masa magana, yace abari yadawo tukunna, amma nasan babu wata matsala zai amince, saboda haka kawai kufara shirye shirye kaida yayanku"
Lokaci daya yaji wani irin farin ciki ya lullu6eshi, Wai shine zai auri Minal, shide Allah yadora masa qaunar yarinyar acikin ransa, kallonsa yakai gareta yaga hankalinta Yana kan kallo, haka yadinga jifanta dawani irin kallon soyaiya mai tsayawa a zuciya
Asim ya kallesu shida mamy, ya sake kallon Amjad yaga yanata farin-ciki Sai wani kallo yake mata, girgiza kansa yayi cike da taqaici,maganar zuci yafara, Sai wani rawar jiki yake saboda zai auri bazawara, besan tayi aure harsau shida bane shiyasa yake wannan yarintar, uwa uba ma da yaji cewa duk mazan data aura mutuwa suke dabai fara wannan rawar kafar ba,
yasan cewa yarinta ce kawai take damun Amjad, shi kam yanason ransa, bazai iya auren mutuwarsa ba, to yarinyar datayi aure shida ma ai ba qaramin namiji ne zai Iya Mata ba, tunda tashiga hannun maza Kala-Kala
Tsintar maganar mamy yayi tana cewa Amjad "kunyi maganar kaida itane, babu wata matsala daga nata bangaren?"
Asim yaqurawa Amjad ido yanaso yaji amsar dazai bayar,Minal d'in ta amince kokuwa
Amjad ya shafa kansa cike da kunya yace "bamuyi magana ba mamy, amma nide a nawa 6angaren babu wata matsala, ko a Yaya take zan'iya auren ta"
Asim yanajin haka ya tashi yabar falon, ya nufi nasa falon, cikin ransa Yana cewa ai shikkenan tunda yaga zai Iya karbar mutuwar
Wannan ai babu amfanin ma afad'a masa mutuwa ake kokuma bazawara ce, idan sukai auren shida kansa saiya tabbatar waya aura
Mamy tabishi da kallo cike da mamaki, me hakan yake nufi?
Amrah kuwa bayansa tabi da kallo tana dariya qasa-qasa
Mamy ta kalleta tace "Amrah kawowa Amjad abinci"
Saida tad'anyi jimm sannan ta nufi kitchen tana gunguni, saikace wani Babba mamy zata sata ta tashi, bayan itace ya kamata ace ta aikeshi, tana cikin tafiya taji muryarsa yace "AMRAH"
Cikin mamaki ta juyo ta kalleshi, Rabon dataji Amjad yakirata kai tsaye harta manta, zata iya cewa tun suna Yara, cikin masifa tajuyo tana kallonsa, shikuwa wani irin murmushi yasaki Yana shafa sumar kansa sannna yace "ki zuba min d'an kadan"
Abincin ta kawo masa ta dangwarar a gabansa ko zuba masa batayi ba, tawuce dakinsu
Yana zuwa dakinsa abokin sa Muhsin yakira shi, dauka yayi tare da lumshe Idonsa yace "ina jinka"
Daga d'aya bangaren Muhsin yace "Abokina munyi magana da principal din wannan makarantar , yace zata fara zuwa ranar Monday"
Dasauri yabude Idonsa yace "Monday...
Jibi kenan fa"
Muhsin yace "akwai damuwa ne?"
"no, da'inaso nayi mata lesson ne kona one week ne kafin tafara zuwa, to bansamu lokaci ba"
"tokai da ina kaga lokaci? da Amjad Kasa ma Aida tuni sunyi Nisa"
"Amjad kuma?"
"to menene dan Amjad din yakoya mata?ko kana kishi ne?"
"A a....
Allah yasawaqe"
Muhsin yayi murmushi yace "Amin, Nima Ina hanya ganinan zuwa gidan naka, ya kamata kayi mata karatun de kafin Monday din ko Yaya ne, Saikaga qoqarinta, kaga daga nan Sai kasan abinda zaka yanke"
"da sonake kawai tazana jarabawan ssce, saina nema mata Admission tatafi University, madecine nakeso tayi, tunda yarinya ce qarama saitai tayin karatun, nasan karatun nata bazai wuce 6 years ba"
Muhsin yanajin wannan qarfin hali na Asim yayi daria, kaiba auren yarinya zakayi ba amma Kaine da tsara mata yanda kakeso, afili yace "kaga gashinan naqaraso gidan, Bari nashigo"
Katse wayar yayi, yakira Amrah, tana dauka yace "turomin yarinyar nan, tataho da littafi da biro"
"yarinya kuma Yaya...?