← Book details Insaaf Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 53

Sashe 35

Insaaf Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Duk yanda nake dashi betaba fadamin labarinki ba tun kafin nasan ke 'yata ce, Insaaf Ada kenan ma dabaisan akwai wata alaqa a tsakanin muba, tayaya kike tunanin yanzu zai fadamin wannan matsalar?

Asim mutum ne Insaaf, abun so awajan kowa, bazan taba yarda kirabu da Asim ba, Insaaf tun kafin na haifeki nake tare da Asim, tun kafin yasan ke wacece yake kula da dukiyar ki, idan kika rabu dashi kwata kwata ni baki kyauta minba, zan samu babanki nayi masa magana gobe, amma kidena cewa kinaso yasakeki kinji, Allah bayason haka "
Ahankali ta daga mata kai, sannan tace"to Anty"
"yauwa karbi maganin ki Kisha, ki kwanta kihuta"
Babu musu ta karba ta shanye Sannan ta kwanta, Ishraqa taja mata Bargo sannan takashe mata wutar d'akin tatafi d'akin El Hameed itama ta kwanta
Qasa qasa yake jin kukan ta Yana ratso cikin kunnansa
Ahankali ya karanta Addu'ar tashi daga bacci, ya kalleta yace "Habibty lafiya kuwa?"
"Habiby nayi magana da Insaaf ne yanzu"
"magana kuma?

Dama baki Barta ta kwanta tahuta ba?"
"A a Habiby, maganar tanada muhimnci sosai, Insaaf tana tare da matsala Habiby, tacemin tanaso Asim ya saketa"
Yanajin haka ya tashi zaune da sauri "saki kuma?

Meyake faruwa to?"
"Habiby Insaaf fa aurenta shida kafin Asim...." tsaf ta zayyana masa komai kamar yanda Minal ta sanar da'ita
"innalillahi...yanzu Ina Insaaf din take?"
"ta kwanta, tana dakinta"
"wanne irin tana dakinta Ishraqa, tayaya yarinya zata fada miki wannan maganar kitaso ki Barta cikin damuwa?"
"to ai Naga dare yayi, kuma daga tafiya me nisa muke, kaima bansan dagama hankali"
Dan qaramin tsaki yaja yace "Kinga, tashi muje dan Allah, to Ishraqa kodaga bangon duniya muke ya dace mubar ta cikin damuwa ne?

Muje idan na tabbatar tayi bacci saimu dawo"
Daga masa kai tayi, sannan suka nufi d'akin Minal, suna zuwa ya kunna wutar d'akin, harta fara bacci Alokacin, wutar dasuka kunna ne yasa tatashi, zama Sukai Akan gadon, El Hameed ya shafa dogon gashin ta yace "bakya tare da damuwa Insaaf?"
Cikin mamaki tace "Abba damuwa kuma?"
"mamanki tayi min Bayani yanzu, kiyi hakuri karkisa damuwa aranki harta ta6a lafiyarki"
Murmushi tayi tace "babu komai, ai harna fara bacci ma"
"to Allah ya yi miki albarka yata, kwanta kiyi baccinki"
Komawa tayi ta kwanta, ya sunkuya yadora ba kinsa a kanta yayi kissing sannan yaja mata bargon
Fira suka fara yi shida Ishraqa kadan kadan, basusan yaushe bacci ya dauke suba, haka suka kwana duka su ukun a dakinta
*** ****** ***
Zaune yake a falon su, yayi kyau sosai cikin shigar sa ta kullum wato suit, breakfast yagama amma yana zaune afalon baitafi wajan aiki ba, mamy tana gefensa da Carbi a hannun ta,idan bai manta ba rabonsa da Insaaf tun kafin sutafi Sudan, ta nemeshi awaya ma ya gagara, wajan contact din kan wayar sa yashiga yafara duba numbers din ciki, saida yagama gani sannan ya yatsina fuskarsa, Sai yanzu yatuna batada waya , ya kamata ace yakira ta ya nuna mata kuskuren ta Akan rashin kiranshi, to Amma kuma ta'ina zai kirata?

Ishraqa zai Kira ko El Hameed?

Amrah ce tafuto daga d'akin su kai tsaye wajansa ta nufa ta zauna aqasansa ta gaida shi
A taqaice ya amsa mata,zuciyarsa ce ta bashi shawara yanemo number Ishraqa.

Number yakamo yayi dialling saiya katse, yasake yi a Karo na biyu nanma ya katse
Wayar ya ajiye agefe, to yanzu idan ya Kira Ishraqa ma meze cemata?

Wata zuciyar ce tace dashi kakirata, kasan Yara da San wasa da waya, yanzu haka wayar tana hannun Minal din tana yin game da'ita
Haka yasake dialling number, tana shiga kuwa aka daga, muryar Ishraqa yaji tace "Salamu Alaikum Asim katashi lafiya?"
Wayar ya kalla, cikin sauri ya kashe, anata bangaren tace "kode network ne?, Bari nasake Kira"
Tana Kira yad'auka yace "Sorry akwai number dazan Kira ne sainayi mistek"
Tace "to shikkenan, jiya mun sauka da daddare, ko zaka shigo ne kafin kawuce office?"
"no, akwai ayyukan da zanyi"
Mamy dake gefe ta daga kai ta kalleshi, Yana cewa akwai ayyukan da zaiyi amma kuma Yana zaune bashida alamar tafiya office dinma, tarasa meyake jira?

Daga dayan bangaren Ishraqa tace "Ok, Allah yakiyaye hanya"
Shima yace "Amin" sannan yakashe wayar
Ishraqa tayi Murmushi, kode Asim yana neman Insaaf ne?

Ikon Allah, aure me Hana wani abun,aure mesa ayi wani abun, jidai yanda Asim yake magana da'ita kamar ba Ishraqa tasa ba, kamar ba aminiyarsa Ishraqa ba, Ahankali tatashi tashiga d'akin Insaaf, tana zaune da breakfast agabanta, El
Hameed Yana karanta mata Jarida, zama tayi ta kalleta tace "idan kingama break din kishirya muje kizabi wayar da kikeso, yanzu mijin ki yanason magana dake, kikirashi"
Ta ajiye mata wayar agefenta
El-Hameed yace "saide kuje Keda ita, ni akwai inda zani, nayi waya da wani malami Akan issue dinta, zanje musan abinda ya kamata ayi"
Tace "to zamuje insha Allah"
Kallan Minal yayi yace "Insaaf idan kingama wayar, ki same mu adaki"
Ahankali tace "to Abba"
Suna fita takirashi, yayi mamakin ganin kiran Ishraqa bayan sunyi sallama ita dashi, dauka yayi tare da sallama, itama anata bangaren ta amsa masa, tace "Yaya ina kwana"
Wata irin Ajiyar zuciya yasauke, har ita kanta Minal din taji shi, Kallan gefen mamy yayi, ya kalli Amrah data zauna agabansa, lokaci daya ya tsinci kansa da qaramar murya
Cikin qasa-qasa da murya yace "bakya kira kiji lafiyar mutane ko?"
Cikin shagwaba tace "to Yaya ni banda waya fa..."
Yasalam!

Yafurta hakan a ransa
"Alright, kishirya Amjad yakaiki saiki za6i wadda ta miki, Amrah tanason magana Dake"
"Yaya Anty tace zasu siyamin, ka cewa Anty Amrah ina missing dinta"
Idanunsa ya runtse
Iya Amrah take missing, Ahankali yace "Bye" qit yakashe wayar
Mamaki ya kamata, Ana magana rimi-rimi kuma Sai abun yaqare a haka?

Tashi tayi ta nufi wajan Iyayen nata, anan suka fara nuna mata kayaiyakin ta, da wasu daga cikin kadarorinta,da kayanta tana qarama, Abin saiya dinga Bata mamaki yanda suka iya Adana kayan har zuwa wannan lokacin, anan El Hameed yabar su, yafice zuwa wajan Malamin da sukai magana
*** ****** ***
Amjad ne yafuto daga dakinsa, kana ganin fuskarsa zaka tabbatar Yana cikin damuwa, bayan ya gaisa da Mamy yazauna kusa da Asim, yace "Yaya ina kwana"
Kallansa yayi yace "lafiya, yaushe zaka tafi Adamawa ne?"
"inata shiri Yaya, zan koma insha Allah, Bana Jina yanda ya kamata ne shiyasa"
Asim ya jinjina kansa, yasan cewa damuwar Amjad Bata wuce Akan Daddy bane.

Amjad ya kalli Amrah yace "Anty Amrah ina kwana"
Tanaji tayi banza dashi, yayi Dan qaramin murmushi yace "bazaki amsa ba?"
Nanma batace masa komai ba tayi Shiru, Asim ya kalleta, yaga alama kamar Amjad Yana son Amrah, amma ba zaice komai ba tunda Shima Amjad din be furta ba, inda hakan ta kasance kuwa zaifi kowa farin-ciki, ko banza Amjad dinsa zai zama cikakken namiji, yadena wannan shagwa6ar,yanda yakejin Amjad a ransa zai Iya bashi kowanne irin goyon baya Akan hakan, ajiyar zuciya yayi yace "ba dake yake magana bane?"
Kallan Asim din tayi tace "naji shi Yaya, kafada masa ni yafita harkata, kowa yayi abinda ya shafeshi"
Asim ya dafe kansa da hannunsa yace "meyake damun kune?

Ku qananun Yara ne?

Koda yaushe bakuda aiki daga fada Sai fada?"
Mamy dake gefe ta kalli yaran nata "doke-doke zaka ce Asim,Abin ai yafi qarfin fada, ninariga na zare hannu na daga Al'amarin su, saide Kai in zaka iya"
Amjad ya shafa sumar kansa yayi murmushi, ya tashi yace "Bari in dauko wayata akwai inda zani, Anty Amrah ko zakije?"
Yaqarasa maganar Yana kallonta
Kanta ta girgiza tace "A a"
Daga nanma tatashi tashige dakinsu, tunani take a ranta tayaya ma zata bishi?

Agidama ya matse ta yayi kissing dinta idan tabishi waje tasan mezai faru?

Shima murmushi yayi kawai yawuce dakinsa, Asim yabishi da kallon mamaki, baiyi tunanin Amjad zai share Amrah ba,yayi tunanin zai biyeta suyi cacar baki ne kamar yanda suka saba, amma abin mamakin saiyaga murmushi ma yayi, kode tunanin sane yake shirin tabbata?
Chapter 35 · 0% Book details