← Book details Insaaf Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 53

Sashe 3

Insaaf Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kiyi mana Bayani mana"
Numfashinta Yana Sama Sama kadan, tace "Yaya Ammar wallahi aljanine, aljani nagani a Rafi"
Gaba dayansu su ukun suka hada baki suka ce " Aljani Amina!!"
Babanta ta kalla tace "Eh wallahi baba, zan Debi ruwa kenan naganshi, nikam shikkenan nayi gamo" ta qarasa maganar tana Dora hannun ta a kanta (
Babanta ne ya kalli yayanta yace "Ammar muje mugani, wata qila akwai abinda yake faruwa"
Cikin sauri tariqo baban "Baba karkuje, wallahi idan kukaje kuma zai Bude muku ido, karkuje baba"
Murmushin manya kawai yayi, suka nufi hanyar fita shida Ammar, Inna ma dake tsaye tace "a a Malam, ai muma bamuga ta zama ba, ya za'ai yarinya tace taga aljani kutafi kubarmu mu biyu agida, idan wani shegen ne yayi mata ture fa" (
Baba yace "kumafa hakane larai, to kutashi mu tafi, idan magana tafi karfin mu Sai a fadawa mai Gari yakira masu ruqiyya ayi mata"
Inna ta yafa mayafi tabisu, itama datayi tsuru agefe cikin sauri ta tashi takama hannun Inna tariqe gam, a haka suka tafi, a hanya duk wanda yaga Amina dauke kansa yake, idan yarane kuwa saide kawai kaga sun kwasa aguje sun gudu, Abin Yana mutuqar damunta, saide tashin hankalin data gani a Rafi yafi tsaya mata Arai
Suna qarasawa kuwa tasake riqe hannun Inna,sukaja suka tsaya daga nesa, amma duk da haka saida ta buya a bayan Inna, Ahankali Ahankli take Dan leqo kanta
Baba da Yaya Ammar kuwa cikin sauri suka qarasa,Yana Nan agefen ruwan a kwance kamar yanda ta ganshi itama, baba yace "subhanallah, duba duba Ammar, ai kamar mutum nake gani"
Ammar yace "Wallahi mutum ne baba"
Bismillah sukayi sannan suka janyo shi waje,hannunsa kuwa jini ne yake zirarowa mai kauri, baba ya kalli su Amina da suke can gefe, "Larai mutum nefa, wannan yarinya da shashanci take" ya qarasa maganar Yana Kallan Amina
Inna tace "Auto, Bari mu qaraso" (
Wajan suka qarasa, Amina ta zuba masa ido tana Kallan tsantsar kyan da Allah yayiwa wannan bawan Allah, Yana kwance kamar babu rai ajikinsa, amma jakar laptop dinsa tana nan ajikinsa, gashin idonsa dogaye Zara-Zara,ga wani irin saje da yayi wa fuskar sa mutuqar kyau, bashida gemu saide saje daya qara masa kyau sosai, Inna ma data ganshi saida ta tsorata, cikin ranta kuwa cewa take wannan kyan nasa ai yayi yawa
Baba yace "Ammar inaga daukansa zamuyi, mukai shi gidan maigari, duk abinda ya yanke shine daidai"
Girgiza kansa yayi "haba baba, wanne irin maigari awannan halin da yake ciki, mukai shi asbiti kawai, idan muka dawo dashi Sai akai shi gidan maigarin muji ta bakinsa"
Baba yace "to muje asbitin"
kamashi sukai suka dagashi, baba yacire jakar laptop din yayarta anan, ya cacimeshi yariqo hannun, aikuwa jini nan yafara Bata hannun baba, shikuma Yaya Ammar yariqo qafafun, wucewa sukai dashi gefen titi suna tare Mota, suma su Inna sukabi bayan su, harsun tare Mota suna qoqarin sakashi Amina tajuya, ta kalli jakar da baba yacire ajikin wannan bawan Allah yayar, ta kallesu sun sakashi aciki suma suna kokarin shiga, da gudu tajuya taje ta dauko jakar ta ratayata a hannun ta, Inna kam ko lura da abinda Amina tayi batayi ba, sannan sukai sallama dasu baba, su suka dau hanyar komawa gida itada Inna, su kuma su baba suka wuce Asbiti
Suna zuwa gida kuwa tawuce dakinta da wannan jaka, zama tayi har zata Bude taga menene aciki Sai kuma tafasa, haka tazauna tazubawa jakar ido cikin ranta tana so taga menene aciki, Ahankali tasa dogayen yatsun hannun ta tabude jakar, computer ce ta baiyana mai launin brown, ruwa yagama cikata harta gaji da cika, rubutun sunan INSAAF dake jikin computer tashafa ahankali, daga nan ko budeta batayi ba bare tayi tunanin shanyata arana, tamaidata cikin jakar tarufe, sannan tabude bakkon kayan ta tasakata acan qasa, qarqashin kayanta (
Sukuwa su baba kai tsaye suka ce driver yakaisu Mubi General Hospital, sunje anyi musu duk abinda ya kamata amma basu ta'bashi ba, Kai tsaye daga nan suka turasu Adamawa State Specialist Hospital anan aka fara bashi temakon gaggawa,daqyar suka yarda Akan zasu fara yimasa aikin saboda basuzo da kudi ba, saida baba yayi musu alwaqarin cewa Gobe gobe za'a kawo musu kudin
Daga nan aka shiga dashi Dakin tiyata har sukai nasarar cire masa harsashin, baba Yana zaune a waje shida Ammar, kawai tunanin yan shanunsa qwaya biyu yake yi, wanda yake kiwonsu saboda ranar Bikin Amina, yanzu dole saide yasiyar guda daya yanaji yanagani (
Hakan ce kuwa ta kasance, washe Gari Ammar yakoma gida yayiwa Inna Bayani, aka saida saniya guda daya yakoma asbiti da kudin, bayan sungama biyan kudin aka basu wani Rasit dakuma magungunan da'ake buqata, baba yazubawa wannan takardar Rasit din ido yayi Shiru Yana kallanta, kawai hoton saniyarsa yake gani ajikin takardar (
Haka suka siyo magungunan ma, saide kuma fatan Allah yasa marar lafiya ya farfado lafiya
Labarinsu :
Gidan Malam buba kenan, cikakken bafulatanine da yake zaune aqauyen Mubi, Yayansu biyu shida matarsa larai, akwai Ammar da suke riqewa awajan su, shi Dan ruqo ne, Ammar shine kamar babba a gidan, Sai kuma yarsu Amina daga ita kuma babu qari, Amina yarinya ce qarama sosai, kwata kwata shekarunta goma Sha takwas , amma Allah yayi mata jiki dakuma sura irinta manya, kasancewar aqauye suke ba kowane zai gane hakan ba, Tanada qirji manya,hips dinta yan daidai misali, Ba qaramar kyakkyawa bace, chocolate Beauty ce sosai, kalar fatarta kamar ta Sudanese, tanada manyan idanuwa, gashinta dogo ne sosai, danma baya samun gyara
Auren Amina biyar awannan qauyen nasu,duk wanda ta aura adarensu na farko yake mutuwa, muddin angon ta yazo karbar haqqinsa Tofa saide wani bashi ba, adaren zai mutu,aurenta nafarko auren soyaiyane da saurayinta datake mutuqar so Haruna d'an kande, d'an kande Yana bala'in son Amina, kamar yanda aka sani kowanne ango Yana murna ankawo masa amarya haaka ce ta kasance awajan d'an kande, duk da amaryar tana noqewa haka d'an kande yanemi haqqinsa, amma tun kafin yakaiga neman hanyar sa yaaji maqoshinsa yariqe, numfashinsa yafara yin Sama kamar me asma, awannan dare d'an kande yarasu, al'amarin yataba Amina sosai, saida aka hada da malamai masuyi mata roqon Allah
Aurenta na biyu ta auri wani abokin Haruna, aminin d'an kande ne sosai, shikuma be mutu adaren auren su ba, Sai washe Gari, Yana tsaka da wasa da amarya yaji yawun bakinsa Yana tsinkewa, daga nan wani irin kumfa yake futo masa, kafin safiya Shima Allah yayi masa cikawa
Daga nan Amina tafara Bawa kowa tausayi aqauyen, wasu suce kwanan su ne yaqare, wasu kuma sabanin haka
Aurenta na ukuma hakace ta kasance Bata sauya zaniba
Tofa daga nan aka fara gudun Amina, wasu har agabanta suke mata habaici cewa ita matsafiya ce, duk Iyayen dasuka San Amina tana qawance da yarsu saisu datse wannan alaqar, Abin Yana damun su Inna sosai, daga nan baba yafara karbo mata rubutu awajan liman tanasha
Ana cikin wannan hali wani babban mutum mai mata uku yace zai aureta,alhaji ilu mai kudin qauye ne, kullum haka zaka ganshi azaune akofar gidansa Yana zare ido shi Ala dole gamai kudin qauye, haka yadage Akan zai auri Amina, inma itace take kashe mazajen auren to shi shine ajalinta,awannan lokacin su baba suna cikin tashin hankali kotakan Amina ba'abiba a kayi aure, ango yazo da kazarsa da daddare, Amina tana zaune adakin ita kadai, Yana zuwa kuwa yazubawa qirjinta ido Yana kallo kamar maye, ko alwala basuyi ba bare sallah ya afka mata, haka ya turmushe yar mutane ko qanqantar shekarunta be dubaba, babu wani wasa haka yafara neman hanya, ita tsoro ma yabata yanda taga duk ya rikice, gaba daya tsoro yahanata sakin jikinta bare yasamu hanyar shiga, haka yadinga neman hanya amma wajan qamas yake babu komai bare alamar danshi, ahakan yacire tausayi zai shiga, itade Amina batasan Yaya a kayi ba Sai hango alhaji ilu tayi a bakin kofa, anyi jifa dashi Yana fitar da numfashi daqyar,Kasa tashi yayi daga wajan saboda gaba daya ma jiyayi besan inda kansa yakeba, daga qarshe ma saiya miqe kafa yaci gaba da kwanciya anan (
Itama Amina da sauri jikinta na rawa ta tashi tazauna tatakure kanta a cikin cinyar ta, awannan Rana yanda taga Rana haka taga dare, washe Gari kuwa daga wannan kwanciya ta barci alhaji ilu ya zarce, ita batasan ma yamutu ba, saida uwargidansa tazo taduba sannan tafasa ihu da kururuwa, yayansa da matansa suna kukan mutuwarsa suna dukan Amina, haka suka Koreta daga gidan jina-jina
Al'amarin yabawa kowa tsoro, tundaga nan manya da Yara idan sukaga Amina kowa gudu yake, kowa ta kansa yake, gudunta suke sosai idan bakayi ban waje
Ana tsaka da wannan hali Dan maigari yadawo daga wajan karatu, Laminu Yaro Dan qwalisa tunda ya qyalla idonsa Akan Amina yace Yagani yanaso, shi bashida wata mata bayan Amina
Maigari yaso yaqi, amma Laminu ya nuna masa cewa duk wanda yamutu dama can kwanansa ne yaqare, bawai Amina ce take kashe su ba, haka a kayi wa Laminu auren gata, kasancewar sa Dan boko saiya raina shekarun Amina, Dan haka bai nemeta ba,Yana ganin kamar tayi qarama, itama dataga haka saita sake dashi, har shaquwa tafara shiga tsakanin su, saida auren su yayi sati daya, Laminu Yana nan ras da ransa, har Gari anfara gulmace gulmace Amina taga kudi shiyasa taqi kashe Laminu, ta ganshi Dan mai Gari gashi Dan boko, Laminu tun Yana daurewa harya Kasa, a kwana na takwas yanemi Amina, Shima a cikin ranar Allah yayi masa rasuwa
Gari ya dauka Amina takashe Laminu, maigari kuwa yanke jiki yayi yafadi, daqyar aka samu yadawo haiyacinsa saboda Yana qaunar Laminu sosai a ransa, tundaga nan yatara mutanan Gari yace yakori Amina daga Garinsa(
Al'amarin yadagawa baba da Inna larai hankali, daqyar suka hadu aka Bawa maigari hakuri, bai hakura ba saida yakafa musu sharadi muddin Amina tayi aure mijin ya sake mutuwa asanadinta,to kawai daga Dakin mijin tafice tabar masa garinsa, basai tabiya ta gidan iyayenta ba
Dahaka su baba suka amince, kowa yaguji Amina, duk wanda ya ganta tsakanin su dauke kai kokuma gudu, saboda wannan abun kowa yaqi ta, babu mai sonta bayan Yaya Ammar, Inna, baba, Sai kuma lubabatu qawarta
Back to story
*** ***** ***
Lagos, Surulere local government
"yanzu ranka yadade so kake kacemin Yaron nawa yamutu?
Chapter 3 · 0% Book details