← Book details Insaaf Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 53

Sashe 11

Insaaf Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Kullum de haka ake masa, za'a kawo masa farmaki amma maganar de itace guda daya za'ayi bincike za'ayi bincike amma daga baya kuma saide aji Shiru, ahaka case din zai mutu
Daddy ma da yaji Shiru yasan bazai sake samun wata amsar ba, Dan haka ya sake kallonsa yace "Toya kukai dasu?"
Yanzun ma kamar bayason maganar yace "Sunce zasu tsaurara" (
Mamy ta dafe kanta da hannunta (
Tace "me zasu tsaurara?

Kayi Bayani mana"
Kansa yadago ya kalleta yace "bincike"
Kafin mamy tasake bashi amsa anty Lubna tayi sallama tashigo cikin d'akin tace "Mamy angama hada dinner"
Tace "to Lubna gamunan futowa"
Daddy ya dauki waya Yana Kira daga nan yayi compound
Ahankali yadago kansa yace "mamy gameda yarinyar nan"
Mamy tazuba masa ido tana kallansa, tanaso taga yanzu zai Bude baki yayi mata Bayani ne kokuwa Shima Bayanin bazai Bude baki yayi ba
Cikin rashin damuwa tace "inajin ka"
Saida yayi kalar tausayi da fuskar sa sannan cikin shagwaba yace "Mamy batada kowa"
daganan kuma Sai yayi Shiru
Mamy ta jinjina wannan qarfin hali na Asim a cikin ranta, kallansa tayi cikin ranta tace zanyi ma ganinka, amma afili saitace "Allah sarki, to madallah"
Cikin sauri ya kalleta, ganin ta dakatar da maganar tasu daga nan, yayi Shiru Shima Yana jira yaji ko akwai abinda zatace amma Sai yaji Shiru (
Ya kalleta yace "mamy inaso ta zauna tare damu kafin Allah yakawo iyayenta"
Murmushi tasaki ganin yabude bakinsa yayi mata magana, tace "Asim, kaga kadena saka damuwa aranka, Sai kwanan ka yaqare zaka mutu, kuma Insha Allah maqiyanka bazasu ga bayanka ba, kadena saka wannan damuwar aranka har tasa kakasa sakewa damu muyi wasa da dariya kamar da, haba Asim Yaya kake so nayi ne?Kuma ni inde wannan yarinyar ce babu damuwa, Allah yabamu Zaman lafiya "
Murmushin sa mai mutuqar tsada yayi mata, dimple dinsa suka futo sosai, yace" to mamy insha Allah zanyi yanda kikace "
Sumar kansa ta shafa badan ta yarda da maganar tasaba tace" to Asim, Allah yayima albarka "
Daga nan suka fita falo domin cin abincin dare
Gaba dayansu family dinne a dinning suna cin lafiyayyen abincin da Lubna da Amrah suka hada, Daddy, mamy, Asim, Amjad, Lubna, Amrah, baby widad, dakuma Amina.

Anty Lubna Sai yatsina fuska take, tana watsawa Amina wani Dan iskan kallo
Shikuma Amjad Sai wani kallo yake mata cike da birgewa
Daddy yagoge bakinsa da tissue ya kalli mamy "hajiya, baquwa mukayi ne?

Dazu mun gaisa amma ban tambaya naji wacece ba"
Shiru wajan yayi, kowa Yana jira yaji amsar da mamy zata bashi, kallonsa tayi tace "Alhaji ai Asim ne yazo tare da'ita, zata zauna damu nadan wani lokaci"
"kinsan da cewa banason wannan kwashe-kwashen ko?"
Gaban Amina yafadi, jin furucin daddy, dama tasan hakan zai Iya faruwa shiyasa tun farko tace masa yakai ta gidan marayu, itama dama tunda ta ganshi taji itama bai kwanta mata Arai ba, da alama bashida kirki, amma kuma gashi dansa yanada kirki sosai
Asim ya ajiye spoon din hannunsa yazubawa daddy ido amma baice komai ba, Anty Lubna kuwa wani irin dadi ne ya mamaye mata zuciya, harta Kasa boye hakan a ranta, saida tafuto fili tace "hakane kam Daddy, idan batada galihu ne akaita gidan marayu mana"
Daddy yace "Nima abinda nagani kenan"
Tsananin bacin rai kam ya baiyana afuskar Asim, cikin tsawa yace "Lubna!!!"
Kowa saida hantar cikinsa ta motsa musamman Amina, lokaci daya taji tsoron sa ya kamata, jikinta har rawa yake, Ahankali tamiqe cikin rawar murya tace "naqoshi" daga nan tayi d'akin Amrah
Mamy tace "haba Alhaji, bansanka da wannan halinba, asalima da temakon naqasa dakai nasan ka"
Cikin bacin rai Yatashi yayi dakinsa, saboda me daddy da Lubna zasu Fadi wannan maganar agaban wannan qanqanuwar yarinyar?

Ko basusan hakan zai Iya haddasa mata damuwa ba?

Daga nan kuma tunani yayi mata yawa tazo tasamu matsala tun tana qaramar ta (
Haushi ya kama anty Lubna ganin Shima Asim din yatafi daki, hakan yana nufin ransa ne yabaci kenan har yabar abincin saboda waccan yarinyar ta tashi, gabanta ne yafadi, innalillahi...

Allah yasa de ba sonta yake ba, data shiga ukunta, cikin sauri itama tatashi tabishi dakinsa har tana sassarfa (
Daddy yayi Ajiyar zuciya yace "Naga alama saboda maganar danayi ran Asim yabaci, anyway kifada masa na amince tazauna din, but saboda farin-cikinsa nayi haka, saboda banason abinda zai sashi ya sake shiga damuwa"
Amjad yasaki wani murmushi, mamy tace "to alhaji insha Allah zan fada masa"
*** ***** ***
Tundaga lokacin da Amina taji furucin Daddy akanta, dakuma matar Asim, saiya kasance takasa sakin jikinta dasu, koda yaushe tana waje daya ta ke6e kanta, ko kadan Bata so tayi magana, tafi so kawai ta zauna tayi Shiru ita kadai
Tunani kuwa yace Salamu Alaikum, muddin tayi Shiru Tofa batada aiki Sai tunani, tunanin shine yake zame mata abokin fira
Idan Bata daki, to tana can saman Benin gidan, tana kallon kyawawan gidajan unguwar, kamar yanda tasaba zuwa wajan haka yauma taje ta tsaya, ta rungume hannunta aqirjinta, tunani tafara tayaya zata fara neman iyayenta?

Ta wacce hanya?

Anya kuwa bazata nemi temakon Asim ba?

"lala mafi ayyi mishikila ya hammude, natakallam ba'aden kuntu ma'a zaujaty Al'an"
Larabcin dataji Yana tashi abayanta ne yasa tajuya cikin sauri, gidan dayake kallon gidansu Asim ne taga mata da miji suna shirin shiga Mota, amma mijin Sai waya yake Yana larabci, matar tana sanye cikin Baqar laffaya dataji Adon stone Sai walwali take, ta nad'e jikinta gaba daya, fara ce tass kana ganin ta kaga balarabiya ko tantama babu, sumar kanta tuli guda har kana hango tagaban goshinta, shikuma mijin yanada Dan duhu kadan, matar Sai murmushi take masa, da alama tanajin wayar dayake itama
Lokaci daya taji bala'in qaunar ma'auratan tashiga ranta, sosai ta shagala wajan kallonsu ko kiftawa batayi, harma taso ta manta da wata aba damuwa datake damunta, Akan idonta mijin yabude wa matar tasa Mota tashiga gidan gaba, sannan Shima ya zagaya yashige, maigadi yabude musu get suka futo
Wata irin nannauyar Ajiyar zuciya ta sauke
"kinsan tane kiketa kallonta?" ta tsinci maganar Amrah daga bayan ta
Cikin sauri ta juya tace "Anty Amrah"
Dadi yakama Amrah, saboda tana son mutum ya girmama ta, Bata son raini ko kadan, qarasawa tayi kusa da'ita tace "waike bakya gajiya ne kizo nan ki tsaya kinata tunani ke kadai?, yanzu me kike gani a wancan gidan?"
Girgiza kanta tayi tace "babu komai "
Amrah ta
yi Ajiyar zuciya tace"Sunanta ISHRAQA,amma muna kiranta anty Ishraqa,idan kinaso ki birgeta, toki kirata da maman INSAAF, Nima naji mamy tana kiranta da sunan ne, bansaniba ko sunan 'yarta ne, bansan takamaimai wacce alaqa take da'ita da me sunan ba, amma kuma tunda a kace maman INSAAF aikinga may be 'yarta ce, amma bansani ba gaskiya, saboda babu wanda tafuto fili ta fadawa wacece insaaf din awajan ta, ciki kuwa harda aminin nata wato Yaya Asim, ranar da kukazo kina bacci tazo wajan Yaya Asim,qawarsa ce ta qut da qut,kuma class mate dinsa ce, duk yanda kike tunanin shaquwa tota Anty Ishraqa da Yaya Asim tawuce nan, qawancensu Yana birge kowa,tana fada masa damuwar ta, Shima Yana fada mata tasa, tun suna Yara tare sukai karatu har suka girma kowa yayi aure, daga nan ne suka rabu, tsawon wasu shekaru kuma Allah ya sake hadasu anan Lagos, Minal Anty Ishraqa tataka babbar gudunmawa a cikin family dinmu, kuma har yanzu ma tana kan takawa, labarin yanada tsawo sosai, watarana zaki sani,shikuma dayan mijinta ne EL HAMEED, larabawan Sudan ne,labarin su bazai qareba Minal, kizo mutafi ciki muyi kallo, yafi wannan tunanin" tana fadar haka takama hannunta suka yi ciki
Afalo suka zauna Amrah ta kunna musu kallo sunayi, wayarta ce tayi qara ta amsa sannan tashige dakinsu
Amrah na tafiya tazubawa TV ido tana kallo, ba kallon abinda akeyi din take ba, a a kawai tana tunanin Akan tayaya zata hadu da iyayenta?

A'ina zata gansu?

Harya shigo cikin falon Bata sanda zuwansa ba, yayi mutuqar kyau cikin suit, yariqe jacket din a dayan hannunsa, kallanta yayi batare dayace mata komai ba, yafada cikin kujerar ya lumshe Idonsa, bayason damuwa ko kadan, kuma yaga alama yarinyar nan tana son sakawa kanta damuwa, tun tana yar mitsitsiyarta zata haddasa wa kanta tunani daga nan kuma Sai hawan jini, yanzu me take so tarasa zata zauna ita kadai Afalo tana tunani?

Wata zuciyar tace masa ka tambayeta mana, Girgiza kansa yayi cikin ransa yace "no....

Tayaya zan tambayeta?

Mezance mata?"
Amina tajuya ta kalleshi taga Yana Girgiza kai shi kadai (
Magana tafara yi a ranta to kode bashida lafiya ne?
Chapter 11 · 0% Book details