← Book details Insaaf Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 53

Sashe 18

Insaaf Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hakan kamar tonon Asirin yarinyar ne
Dakinsa yashige, yaga Lubna da Amrah suna ciki, brief case dinsa kawai ya ajiye yafuto, Amrah tana masa sannu da zuwa ya amsa batare daya Kalle taba, daga nan yafi ce daga gidan, bai zarce ko'ina ba Sai wajan babban abokin sa Muhsin Wanda Shima acikin unguwar yake, a compound din gidan Muhsin ya tsaya Yana zagaye wajan cikin tashin hankali bayan yakira shi awaya
Muhsin yafuto daga gidansa yace "abokina mu qarasa ciki mana"
"no Muhsin nanma ya'isa"
Kallansa yayi da mamaki yace "amma lafiya kuwa?"
"lafiya, amma ba qalau ba" (
Muhsin yace "tooo, to bari nasa a kawo mana abin Zama, amma ya zakazo gidana kuma mu tsaya atsaye"
"ai maganar danazo da'ita Muhsin Bata zama bace" (
"ikon Allah" cewar Muhsin, sannan ya sake cewa "to inajin ka, meyake faruwa?"
"ina yarinyar nan dana baka labari nazo da'ita?"
Muhsin yace "eh nagane, koba Amina ba?"
Girgiza kansa yayi yace "no, call her Minal"
Mamaki ya kama Muhsin, yace "tonaji, meyake faruwa ne?"
"Muhsin komai ma yafaru, Amjad ne yake son aurenta"
"to menene a ciki?

Ai wannan abun murna ne"
"awajan ka kenan, Muhsin yarinyar nanfa duk wanda ya aureta mutuwa yake, maganar gaskiya ina tsoron Amjad ya aureta Shima yamutu, aurenta shida, duk mazan basa wuce sati daya sun mutu, tayaya zan Bari ya aureta?

Idan kuma Shima yamutu fa?"
Muhsin ya kalleshi sosai, bayan tashin hankalin daya hango a fuskarsa harda tsananin kishi ma, kafadarsa ya dafa yace "to menene aciki?

Asim kowa fa yamutu kwanansa ne yaqare, idan Amjad bai aureta ba Kaine zaka aure ta?"
Cikin sauri yace "wa? ni?

Wannan qanqanuwar yarinyar?to tamin me?"
Muhsin yayi dariya yace "tamaka abinda zaisaka kuka da ihu wallahi, d'an renin wayo, to idan ba kishi kakeba menene nashiga damuwa haka?"
Cikin zafi yafara yiwa Muhsin magana "saboda inason dan'uwana, kuma bazan Bari inaji ina gani yaje yamutu ba, tayaya zanyi kishi Akan hakan, kawai banaso Amjad yamutu ne, kuma ni Bana kishinta"
Muhsin yayi murmushi yace "to shikkenan, muyi musu Addu'ah kawai, shi ne mafita"
Kallan Muhsin yayi, wato har abinma ya tabbata kenan daza'aje ga yin Addu'ah?
kasa cewa komai yayi, daga qarshe ma saiyace "Sai anjima Muhsin"
Muhsin yayi murmushi yace "to saimun hadu"
Shima yajuya cikin gida cike da mamakin abokin nasan, haqiqa Asim Yana kishin yarinyar nan, gaskiya zaiso ace yaga wannan yarinya kosau daya ne, yaga yarinyar da tayi nasarar sace zuciyar abokin nasa, dukda da alamu shi Asim din baisan cewa yafara kamuwa ba
Yana futowa daga gidan ya tsaya a waje, shida yazo wajan Muhsin ko zaisamu wata shawarar wadda zaisa afasa wannan auren, shine zaice masa ayi musu Addu'ah?

To yanzu Yaya zaiyi?

Kode wajan Ishraqa zaije?

Nan take ya yarda da shawarar zuciyarsa, Yana zuwa gidan Ishraqa maigadi ya rissina ya gaidashi kasancewar ba boyaiye bane, har falon nata ya shiga, yazauna Akan kujera
Gidan yatsaru sosai, an narka masa dukiya kamar baza'a mutu ba
'yar aikinta tazo da sauri ta kawo masa abin motsa baki, baima kalli abinda ta ajiye masa ba, yace "ina Antynki?"
Saida ta rissina sannan tace "tana ciki Yallabai, Bari a kirata"
Daga mata kai yayi, tare da jingina da kujerar yarufe Idonsa
Dawowa tayi tace "Yallabai tace kashiga"
Bude Idonsa yayi, sannan ya tashi ya nufi d'akin dayaga tashiga, wanda Bana Ishraqa bane, shi kansa duk zuwan dayake gidan, bai taba shiga cikin dakinba
Yana shiga d'akin yaga wasu hadaddun photuna na yarinya dabata wuce shekara biyu ba, chocolate beauty ce yarinyar, babu ta inda take kama da Ishraqa, ga wani gado na Yara agefe harda matakalar da zata kaika saman gadon, banda uban kayan wasa dayake zube acikin d'akin, Ishraqa Yagani tana ta faman mopping din d'akin (
Ahankali yazauna tare da dafe Kansa (
Tanaganin haka, tasan cewa ba kalau ba, tadawo gefensa ta zauna tace "Asim lafiya kuwa?, waye yamutu?" (
"lafiya Ishraqa, ke kinji ki da wata magana, kawai kuma daga ganin yanayin mutum Sai maganar mutuwa? banjin Dadin jikina ne"
Tace "sannu, amma ka fadawa Lubna ne?"
Kansa ya Girgiza yace "ba tasan ma nataho nan ba"
Tausayin sa ya kama Ishraqa, kullum inde Yana cikin damuwa tarasa meyasa Lubna Bata kwantar masa da hankali, tace "a a Asim, kafadamin mana, menene yake faruwa?"
Ahankali yadago kansa yace "akwai yarinyar danazo da'ita rannan, saboda ita ne"
Ajiyar zuciya TASAKI tace "menene damuwar?"
"kawai de Akan maganar aure ne, Amjad yanason auren ta, ni kuma banso"
Tace "tokai sonta Kakeyi ne?"
Baqin ciki ya kama Asim, Wai meyasa kowa yake masa Kallan yanason Minal ne?

Fisabilillah me wannan yarinyar zata iya Masa?

Yarinya kullum kuka, tayaya zata iya tarairayarsa?

Memakon ta bashi kulawa ma ai saide yaqare a rainonta (
Danhaka yayi Shiru baice da Ishraqa komai ba, yaga alama itama bazasu daidai ta ba, yadaga kansa ya kalli d'akin, dakuma uwar dukiyar da aka narkawa d'akin, yace "me kike yi anan d'akin?

D'akin waye?"
Jikinta ne yayi sanyi kalau, tayi Shiru takasa ce masa komai, Shima yasake kallanta yace "gaba daya kin maida d'akin kamar d'akin rainon Yara, ko 'yarki ce aciki ai Sai haka"
Kallansa tayi, wannan Karon hawaye ne suka zubo mata, yajuya ya kalleta yace "subhanallah...

Meyafaru Ishraqa?"
Hawayen idonta ta share tace " d'akin tane"
Cikin sauri yace "Wai wa?"
Kai tsaye tace "INSAAF"
mamaki ya kamashi sosai, yace "Ishraqa Wai wacece insaaf ne?

Menene hadinki da'ita?tsawon shekarun nan ya kamata ace nasan ko wacece"
Hawaye ne yasake zubo mata, Ahankali ta kalleshi fuska cike da hawaye tace " 'yatace Asim"
Cikin sauri ya kalleta yace"what?"
Girgiza masa kai tayi alamun hakane, sannan tasa hannu ta share Hawayen idonta tace" 'ya tace da qaddara tarabani da'ita tun tana shekara biyu a duniya, kayi hakuri Asim, bantaba boyema komai nawaba Sai wannan, Asim inada 'ya Nima, wadda muke qaunarta kamar hauka nida EL HAMEED, ita kadai muka Haifa alokacin danayi shekara daya da auren sa, kuma har yanzu bansake haihuwa ba, wayasani. ma ko banda Rabon ganinta harna koma ga mahalicccina, amma ina fatan ace duk inda insaaf take ta kasance mai taimakon naqasa da'ita, mutane su sota, tayi farin jini awajan kowa, tun lokacin da muka dawo Lagos muka ware mata wannan d'akin, muka zuba mata komai acikinsa, har yau gani nake kamar zata dawo gareni, shiyasa kullum babu ranar fashi sainazo nagyara mata dakinta "
Asim yayi Shiru kamar ruwa ya cinye shi, shida yazo da matsala gashi ya tadda wadda ta take tasa (
Sai da aka jima caaan, sannan yace" yanzu Ishraqa kinada yarinya amma kikasa sanar dani?

"
" Asim banason tuna labarin ne, da gani har El Hameed babu wanda bashida hawan jini saboda rashin insaaf "(
Cikin damuwa ya kalleta yace" to yanzu tana ina?

Yaya akai kuka rabu?

"
" labarin yanada tsawo Asim, amma zan samu lokacin saina fadama abinda yayi silar rabani da yarinya ta, dakuma yanda akai ta mallaki dukiya mai tarin yawa "
Tana kaiwa nan, wani Hawayen yazubo mata, kallanta yayi cikin tausayi, a ransa yace
"like Minal, abu kadan kuka" (
Yace "kiyi hakuri Ishraqa, amma why not kije ki dauki widad, na baki ita"
Murmushi tayi tace "kuma mamanta fa?

Lubna bazata bani 'yarta ba, Dade nice inda ace insaaf tana nan da saina baka ita ka aureta, harka samu kulawa sosai irinta larabawa"
Cikin sauri Asim ya katseta "haba haba Dan Allah Ishraqa, menene hakan?

Kuma kirasa da wadda zaki hadani Sai 'yarki? da girmana da komai saina tsaya atsaye yarki ta shiryani, ai kema kinsan bazai iyu ba, in auri 'Yata, tacikina"
Yanda ya daddage Yana fada kaikace auren aka daura masa da yarinyar,harda wani
'yarsa tacikinsa kamar shine ya haifeta, Sai abinma yabata dariya, tace "Asim, Wai me ka daukeni ne?

Bazan haifi yarinya in baka aurentaba?

Wai tukunna ma wata nawa kabani ne?

Sai wani abu kake kamar kai kafi kowa shekaru a duniya, to wallahi Kar insaaf tadawo kazo kanamin qaramar murya ehe" (
masu son Insaaf complete kuyi hakuri babu
masu son complete dinsa zasu siya suma ina basu hakuri a kan haka
masu cewa a dinga turowa sau uku arana suyi hakuri ina zuwa makaranta
masu cewa a dinga yi safe da yamma suma suyi hakuri dasafe ina makaranta da yamma ina aikin gida
Duk soyaiyar wannan novel dince tasaku fadar haka, naji dadi kuma nagode,insha Allah zanyi kokari a dinga turo muku k
ullum
Amnah tana yinku sosai kamar yanda kuke yinta
Sharhi pls
Amnah El~Yaqoub
[2/10, 11:17 PM] El~Yaqoub: INSAAF
Writing by :Amnah El~Yaqoub
17&18
Like my page on Facebook
https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493
Anty Amnah yaushe zaki fara novel, yaushe zaki fara posting INSAAF,saide kiyi typing ki ajiye kinqi kifara posting, ta gashinan nafara magana ta qare
wannan page Din nakane kacokam *Unique* *Jamal*, Allah yabaku sa'ar jarabawa yasa ku gama lafiya
________
kallanta yayi, ya Girgiza kansa yace "wannan shirme ne irin naki Ishraqa, impossible"
ya qarasa maganar Yana yatsina fuska
Tace "to shikkenan, Yaya maganar computer?"
"babu labari, kawai saide Addu'ah"
Murmushi tayi tace "ka kwantar da hankalinka, insha Allah babu abinda zai faru, Sai Alkhairi"
Wani irin kallo yayi mata, wacce irin matace wannan?

Ana fada miki kadarar wadda kika Kira da 'yarki tabata, bayan abubuwa na company dasuke ciki, amma kina murmushi kamar babu abinda yake damunki
Ajiyar zuciya yasaki "Ishraqa, nawuce gida"
"to abinci fa?

Kona zubama katafi dashi?"
"matata tamin girki"
Daria tayi "Dade bansan halin Lubna ba shine zaka fadamin haka, harda wani kare ta, kullum saide taita ihu tana sonsa, amma munqi gani aqasa, Sai anjima to"
Shima ya kalleta yace "eh na ji Sai anjima"
Yana fita taji kanta yawani irin sarawa, tasa hannu ta dafe kanta, lokaci daya jira yafara dibanta tatafi zata fad'i, Allah ne yakawo mijinta El Hameed cikin sauri yataro ta tafada jikinsa, kan gadon ya kwantar da'ita yafara jera mata sannu, sannan yajuya cikin sauri yabude fridge din d'akin, babu komai acikinsa Sai ruwa, saboda ba kowa ne yake zama acikin d'akin ba, ruwan yabata Tasha sannan yasake kwantar da'ita yariqe hannunta"yaya kikeji yanzu? kokuma mutafi asbiti?
Chapter 18 · 0% Book details