← Book details Insaaf Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 53

Sashe 26

Insaaf Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Inason raina, saboda haka dan Allah katashi katafi Nina gode da wannan ziyarar "
Muhsin yayi murmushi yace"to Allah de yatsare gaba Asim, danna baya kam yariga ya faru"
Daga nan yafi ce daga falon, shikuma yaja computer sa yanaci gaba da aikinsa
*** ****** ***
Ganin shirin da ake yi a gidan, yasa Asim Kiran Amina falonsa
Taje tazauna a qasan kafet din d'akin,tana kallonsa, cikin ranta tace shide kullum aiki, inama inada dama wallahi dasai na qwace, mutum kullum babu hutu, daga aiki Sai aiki
Hankalinsa Yana kan computer daya sake Yana wani aiki, yace mata "akwai maganar danake so muyi"
Tace "to Yaya"
"kishirya anjima akwai inda zamu fita"
Tasake cewa "to Allah yakaimu, zan shirya"
Jinjina kansa yayi, wannan Karon ma be kalleta ba Yana aikinsa yace "medame kike shiryawa, me kike buqata wanda za'a siyo miki?"
Dago kanta tayi ta kalleshi, kamar bada ita yake magana ba, Hankalinsa Yana kan laptop din gabansa, tace "Yaya shirin me kuma?"
Kai tsaye yace "na aurenku mana, Keda Amjad"
Dam!

Dam!!

Gabanta yayi wata irin faduwa, cikin sauri tace "Aure kuma?

Wanne irin aure Yaya?ni bamuyi maganar dashi ba, be fadamin ba" ta qarasa maganar cikin rikici, kana ganinta zaka san cewa a rikice take
Batare daya Kalleta ba yace "yanzu kinsani"
Idanun tane sukai rau rau, ta kalleshi "nifa inada aure"
Computer gabansa ya ture, yajuyo yazubawa manyan Idonta wani kallo, shide yasan cewa a gabansa aka koreta, kuma da bakin ta tace kafin Ammar yarasu yasaketa, idan ma bai saketa ba to ai yariga yarasu, yaushe tayi wani auren?

Tanaso tace masa tasake auren wani mutumin na bakwai kenan ko me?

Kode batasan girma da darajar aure ba ne shiyasa zata fara wasa dashi?

Sake kallon qwayar idonta yayi yace "yaushe kikai auren?

Waye mijin naki?"
Gabanta ne yafara faduwa, cikin alamun tsoro ta dago kanta ta kalleshi sannan tace "Gaka"
Group d'inda basa sharhi insha Allah nadena yimusu posting
Masoyan littafin INSAAF nagode
Comments
Sharhi
Amnah El~Yaqoub
[2/17, 12:07 AM] El~Yaqoub: INSAAF
Writing by:Amnah El~Yaqoub
27&28
Like my page on Facebook
https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493
Akwai abubuwa dayawa wanda ya kamata ace na rubuta saboda aso Widad, amma haka na ciresu saboda karma yarinyar tashiga ran mutane dayawa, saina rubuta page daya biyu amma ko sako yarinyar banyi aciki ba, ashe gudun Gara nayi
, duk da haka ban tsira ba, ya kamata fa ace muna tunawa da mutuwa, bazai iyu a rubuta littafi haka babu wani wanda zai ta6a ran mai karatu ba, kenan ma soyaiya kadai zamu rubuta
, mutuwa tana kan kowa, wanda basuji Dadin mutuwar Widad ba suyi hakuri please
Ina masoyan Daddy?

Toku matso kusa
__________
Gabansa ne yayi wata irin faduwa, yanayin fuskarsa ya sauya, yayi quri da ido Yana kallonta cike da mamaki, yace "what?

Kinsan me kike fada kuwa?"
Ahankali tadago idonta tana kallonsa, amma takasa ce masa komai, dama tasan cewa hakan zata iya faruwa koma fiyeda haka, daqyar ta'iya daga masa kanta, muryarta na rawa tace "E...eh wallahi, Allah da gaske nake"
Gaskiyar daya hango Akan fuskar yarinyar ne yasa yagane gaskiya take fada masa, but tayaya?, yaushe hakan tafaru?

Shida yake gudun Amjad ya aureta ashe shine rikicin yake kansa?Ahankali Ahankali yafara maimaita kalmar innalillahi wa Inna ilaihirraji'un....

Cikin ransa
To inhakane menene ma amfanin daga Hankalinsa Akan neman computer?

Shida yakusa mutuwa bai saniba?

Yana yiwa Amjad kallon gawa ashe shine gawar,
Yana yiwa Amjad kallon zai auri bazawara ashe shine yake auren ta bai saniba
Hannunsa yasa ka cikin sumar kansa, yakasa furta komai, yanzu shikkenan Shima bin Widad zaiyi?

Kallonsa tayi, taga yakasa magana, Ahankali cikin nutsuwa tafara magana "tun muna qauyensu Malam mai Allo, shine wanda ya daura mana aure, lokacin bakajin dadi, yafadamin washe Gari zai sanar da kai amma Allah bai nufa ba washe Garin yarasu, idan baka yarda ba zan nunama sadakin daya bani yace shine sadakin aure na, matarsa ma sheda ce, tasan komai, tasan da auren, amma ni banason in qara yin wani aure a rayuwata, Bana fatan ace haqqin mutune yadinga taruwa akaina, Bana fatan ace tasanadina wani ya sake mutuwa, nasan cewa wata qila da haqqin rayukan mutanan da suka mutu ta Sanadina ne yasa har yanzu ban samu iyayena ba, Dan Allah karku min aure Akan aure, inaso ka sauwaqe min, ni bazan sake aure ba har abada....

"tana qarasa maganar hawaye ya silalo daga cikin idanuwanta, ahankli tatashi tafice daga falon, tanaso ta tambayeshi karfe nawa zasu fita?

Amma babu Damar hakan Dan taga fuskarsa tayi wani iri kamar zaiyi kuka
*** ****** ***
Tunda ya zauna a falon yake sakin tsaki shi kadai, ga waya a hannunsa Yana danne danne, Amrah ta kalleshi "Amjad lafiya kuwa?"
Saida yayi Dan qaramin tsaki sannan yace "nida wani Gaye ne muke tafka fada a Facebook, Sai batamin rai yake, shine Nima nace masa inda zan ganshi Sai an qwace shi a hannu na"
Amrah batasaan lokacin data saki wata irin dariya ba, tace "Kaine zaka daki mutum har a qwace shi a hannunka?"
Shima dariyar yayi "ke duk kurin banza nefa nakeyi, Kinga mutane Sai hakuri suke bani, jisuke wani babba ne, Nima kuma Sai da naduba profile pic dinsa naganshi wani gabjeje, tayaya da hankalina zan yarda nahada hanya dashi?

Hauka nake?

Saide in bashi hakurima ince ya kamata mubar fadannan haka "
Me Amrah zatayi inba dariya ba, sosai takecin dariya sannan tace
"yawwa Amjad, Nika tunamin ma,kaga pic din wannan gayen, last month nahadu dashi"
Wayar datake bashi ya karba, ya kalli gayen sosai, babu qarya ya'iya dressing daga ganinsa Dan wanka ne, yace "A'ina kuka hadu?"
"Facebook"
"to inde Yana sonki da gaske yafuto mana"
Murmushi tayi "Yana sona gaskiya, kuma Nima Ina ganinsa Naga Yamin, amma nace yaushe zaizo, saiyace min Wai bayaso yazo gida da farko, yafuso mufara haduwa awani wajan, Sai kuma yasa time yazo gida"
Amjad ya Girgiza kansa Yana kallon Amrah cike da mamaki "yanzu Amrah idan ance miki yarinya kihau mutum da bala'i, tayaya zaki Ci gaba da kula shi, bayan daga jin wannan furucin nasa kinsan mayaudari ne, kirabu Dashi kawai, ba mijin aure bane, idan mutum yanason aurenki da kansa zai fara miki maganar aure, idan beyi miki ba dazaran kince yafuto zai futo, saboda shirme kin tsaya kina kula wannan gaulan, Karki sake kula shi nafada miki "
Amrah tasaki baki da hanci tana kallon Amjad yanda yadage Yana mata fada saikace wani Yaya Asim, cikin masifa tace"to Daddy"
Kallanta yayi shi ma cikin fishi yace"Daddy kuma?

Namiki kama da Daddy ne?"
" to waye zaiyi abinda kayi inba Daddy ba?, kawai daga nunama pic din mutum saika hau yin fada kamar kasamu wata qanwar ka kokuma sa'ar ka?,harda kallon qwayar Idona kana cemin yarinya, ban girmeka ba?

"
" to naji, karkuma abin naki yawuce gona da iri, ya'isa haka Karki kuskura kisake cewa kin girmeni "
" nafadama angirmeka Amjad kayi abinda zakayi, Dan renin hankali kawai, marar kunya "
" OK haka kikace ko?

To nan gaba Karki sake kawomin shawararki, kije ki qarata da samarin ki masu qaton ciki "
" Nima karka sake kawomin labarin yanmatan ka, itama Minal din dakake shirin aura karka sake kawomin maganar ta daga yau, komai yazo qarshe tsakanina dakai "
Suna wannan fadan nasu Minal tazo tawuce su,gashin idonta duk sun hadu, alamun Tasha kuka, tashige dakinsu tareda rufewa
*** ****** ***
Hannuwansa zube cikin aljihun wandon suit din dake jikinsa, tunda tafita daga d'akin yakasa zaune yakasa tsaye, Sai Zagaya d'akin yake, gaba daya kansa ya kulle yama rasa Yaya zaiyi?

Wazai fara tunkara da wannan maganar?

Anya kuwa Amjad bazai shiga cikin wani hali ba idan yaji wannan maganar?

Wata iska me zafi ya furzar, ya qarasa kusa da computer sa da yayi gefe da'ita tun dazu, wayar sa ya dauka yakira Muhsin "Muhsin akwai matsala"
"matsala kuma Asim?

Meyake faruwa?"
"kazo ka sameni please, ina cikin bala'in tashin hankali Muhsin"
"subhanallah... to gani nan zuwa" cewar Muhsin
Duk'da yakira Muhsin har yanzu yana tsaye yana zagaye qayataccen falon nasa, shaf ya Dade da mantawa da aikin dayake a computer
Muhsin ya shigo falon Hankalinsa atashe "Asim meyake faruwa?

Gabana faduwa yake wallahi tunda Kamin waya"
"Muhsin dangane da yarinyar nan ne" yafadi maganar kamar zai fashe da kuka
Murmushi Muhsin yayi "Alhamdulillahi, tafada ma ne?"
Cikin sauri Asim yaruqo hannunsa, "mekake nufi tafadamin?

Kaima kanada labarin abinda tafada min ne?mekake nufi da tafadamin?"
Muhsin yadafa kafadarsa "nifa ba komai nake nufi ba, ina nufin ta fadama ne tana sonka ne itama?"
"Muhsin kadena maganar wasa, yarinyar nan fa tafadamin akwai aure na a kanta, bansan... bansan Yaya zanyi ba"
Muhsin yace "Alhamdulillahi, Asim kace komai yazo mana cikin sauqi, kawai yanzu muyi kokari mujanyo hankalin yarinyar nan"
Kansa ya dafe da hannunsa
sannan yace "Muhsin fice daga gidannan Dan Allah kafin na Bude Idona"
Muhsin yasaki dariya, babu musu yafi ce
Yanajin fitar Muhsin zuciyarsa tagama yanke masa abinda ya dace, Dan haka cikin sauri ya nufi d'akin mamy.

Turare take fesawa a jikinta, tagama shiryawa kenan zata futo falo, ta ganshi ya shigo d'akin nata, yanayin fuskarsa ta kalla kawai tasan ba kalau ba, zama yayi a gefen gadon yace "mamy akwai damuwa"
Takowa tayi tazauna agefensa, "meyake faruwa?

Ko bakada lafiya ne?"
"lafiyata kalau mamy, munyi magana da Minal ne... shi ne... shine..."
Daga nan yayi Shiru yakasa qarasawa, jansa tayi jikinta, ta sassauta muryarta "Asim, fadamin menene?"
"Mamy munyi magana da'ita, ina tambayarta metake buqata ne lokacin bikinsu, shine tacemin tanada aure"
Cikin sauri mamy tace "aure kuma?

Dama ba budurwa bace?

To Ina mijin nata yake kadauko ta kataho da'ita nan?"
Jikinsa ne yayi sanyi, ya kalli mahaifiyar tasa "cewa tayi nine"
Dasauri mamy tace "Kaine mijinta?

Ina Minal din take?Bari nakirata naji daga bakinta"
Tana fadar haka tafara kokarin tashi, sake riqeta yayi sosai a jikinsa "A a mamy karkije, zan saketa!"
Dasauri ta kalleshi, taga alama kuma yanda yafada din zai Iya sakin nata, to meke faruwa ne?

Dama baya sonta ne amma yake nuna kishi a kanta?

To kode Shima besan yakamu da sonta ba?
Chapter 26 · 0% Book details