← Book details Insaaf Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 53

Sashe 7

Insaaf Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Wallahi yau kam hakuri na yaqare"
Tana fadar haka tamiqe tadauki bahon wanka ta cikata da ruwa tanufi cikin d'akin dasu Amina suke, tana zuwa batayi wata-wataba ta sheqawa Amina wannan ruwan (
) cikin masifa tace "tashi shegiya!, annamimiya, munafukar Allah"
Jin saukar ruwa ajikin ta shi yayi Sanadin farkawarta cikin razana, tana goge fuskarta data Gama jiqewa
Inna tayi mata wani irin kallon tsana, tace "kin kashemin dana Amina, burinki yacika, ashe dama maganar da mutane suke gaskiya ne, yau na gaskata maganar su, wallahi tallahi bazan taba yafe mikiba Amina, Allah Sai yayi mana sakayya"
Baba ne yace "larai kiyi hakuri mubi komai a sannu Dan Allah"
Inna Bata saurari baba ba, takamo hannun Amina data qame waje daya, tayi tsakar gida da'ita, Amina ta daga kai tana kallon mutane yanda sukai dandazo Akan katanga dakuma kofar gidansu, Inna Bata damu da mutanan da suke kallanta ba ta hankad'ata waje, sannan Takoma ciki tadauko mata bakkon kayan ta tabiyota da'ita
Babane yafuto da sauri yariqe jakar, Inna tana Jan jaka baba yanaja, haka suka futo kofar gida, adede lokacin maigari yaqaraso shida tawagarsa
Cikin tsananin fishi yace "Malam Buba dakai da larai, da wannan annobar ku tattara yanaku yanaku kubar min garina, Dan Naga alama d'aya bayan d'aya nema take saitaga bayan yan Garin nan"
"Annobah"
Kalmar ta daki dodon kunnan Asim daya dawo domin tambayarsu ko sunga laptop dinsa a lokacin da suka tsinceshi a ruwa, yamaida kallansa ga Amina datake zaune aqasa inda Inna ta wullar da'ita, kayan jikin ta duk ajiqe harkana iya hango shacin brezia d'in jikinta, da sauri yadauke Idonsa daga wajan, yamaida kallansa ga mutane yanda suka taru akofar gidan danqam kamar Ana kallon wani babban Abu
Inna da baba da basu lura da dawowar Asim ba, suka fara Bawa maigari hakuri, Inna tasake cewa "kayi hakuri Yalla6ai, karufa mana asiri ayiwa d'ana sutura, karka rabamu da mahaifarmu"
Maigari yadubi fadawan dayazo dasu yace "kushiga cikin gidannan kufuto musu da kayansu, shikuma Yaron ayi masa sutura, Ana gamawa azo ahada dasu da kayansu a kore su subarmin gidana"
Baba yace "innalillahi wa Inna ilaihirraji'un,wannan masifa dame tayi kama?"
Inna kuwa tana jin abinda maigari yace tajefawa Amina jakar kayanta, cikin kuka tace "Allah ya'isa tsakanin mu dake Amina, kinji dad'i ankoremu daga mahaifarmu, tokema kije babumu babu ke"
Al'amarin ya d'aurewa Asim kai, ba yarsu bace ne?

Meyasa suke jifanta da wannan kalaman?

Yajuya ya kalli Amina yaga ta sunkuyar da kanta tana kuka kamar ranta zai fita, sosai ta bashi tausayi,yatsani kukan mace arayuwarsa,ko babu komai yarinyar nan ta dalilinta yazo wannan qauyen, awannan yanayin kam bazai yi Shiru yanaji Yana gani ayi mata irin wannan tozarcin ba, Ahankali ya kutsa kansa ta cikin mutanan dasukaiwa wajan dandazo yaqaraso wajansu Inna, nanfa kallo yakoma Sama, domin kuwa gaba d'aya 'yan wajan kallansa sukeyi, tambayar kansu suke shikuma wannan meya kawo shi nan?

Isyaku yayan lubabatu kuwa Yana ganin Asim yagane shine wanda akasa kudi Ana nemansa,saida yaqara kallonsa sosai har wani karkatar dakai yake Yana yiwa Asim kallon qurulla domin ya tantance shid'inne dayaga photonsa atv ta gidansu koba shi bane? (
cikin sauri yabar wajan ya garzaya folice station domin sanar da 'yan sanda,bazaiyi sakaci wannan kudi ya wuceshi ba (
Cikin damuwa Asim yadubi baba yace "haba Baba, wannan yarinyar ba 'yarku bace?

Meyasa kuke jifanta da wannan kalaman?"
Baba yayi Shiru Yana kuka yakasa Bawa Asim amsa, inna ma cikin kuka tace "Amina ba 'yarmu bace, bamu San taba, bamu San tushenta ba, bamusan sunan taba, muma tsintarta mukai muka riqeta tsakani da Allah kamar yarmu ta cikin mu, munyi mata Rana mun rufa mata asiri ashe Bahaka bane a ranta, Gatanan azaune aurenta biyar duk mazajen data aura mutuwa suke, jiya jiya muka rufa mata asiri muka aura mata d'anmu, Toshima yau mun wayi Gari takashe shi, takashe Ammar, Ammar shine d'anmu na cikinmu, Amina ba 'yarmu bace " (
Gaban Amina yayi wata irin fad'uwa, cikin sauri tad'ago kanta ta kalli Inna, Inna ta kalli qwayar idonta tace"qwarai kuwa abinda kikaji shine gaskiya, kije can kinemi Iyayen ki, babu ni babu ke Amina tunda kikamin Sanadin rabani da d'ana "
Asim kuwa qamewa yayi atsaye, aure biyar? gakuma Ammar Aure shidafa kenan, wannan qanqanuwar yarinyar?

Tayaya?

Wannan wanne irin tashin hankali take gani?to suwaye Iyayen ta?

Begama tunanin saba yaga Amina ta tashi tazube gwiwoyinta qasa, tahade hannayenta biyu waje daya (
) cikin matsanancin kuka tace "Inna..... baba,Wallahi bani nakasheshi ba, Bana kashe mutane Inna, Yaya yariga yasakeni Inna, Dan girman Allah Karku rabu dani, Inna wanasani aduniyar nan bayan ku?

Karku rabu dani Inna, idan kuka barni ina zanje?

Nayarda kuyimin kowanne irin hukunci amma Karku rabu dani Inna, Ni kune iyayena, kuna sani tunda na tashi, bansan kowa ba bayanku, kuyi hakuri Dan girman Allah kuji qaina Inna....kada laifin danayi muku yasa kuce niba 'yarku bace Inna..." taqarasa maganar cikin sheshshekar kuka
Inna ko kallonta batayi ba, baba kuwa yama Kasa d'ago kansa ya kalleta, larai ta riga tatona musu asiri, ta tonawa yarinya asiri a cikin wannan d'unbin jama'ah, da wanne ido zai kalli Amina?

Inna tajuya cikin kayansu da maigari yasa aka futo musu dashi ta dauko wata baqar Leda tasake jefawa Amina ledar tace "ga tsiyar kinan,dasu muka tsinceki,Allah yahadamu a darussalam"
Cikin bacin rai Asim ya qarasa wajanta tare da miqa mata fari kuma lallausan tafin hannunsa, fuska a d'aure yace "ke tashi mutafi"
Cikin sauri tad'ago jajayen idanunta da suke cike da hawaye ta kalleshi
Sorry fan's, kunji nace sunan labari INSAAF amma kuma inata maganar Amina Amina,
to Masu wayo dakuma fahimta ne kadai zasu gane wacece INSAAF a cikin wannan page din
Amnah El~yaqoub
[2/5, 10:53 PM] El~Yaqoub: INSAAF
Writing by:Amnah El yaqoub
Like my page on Facebook
https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493
Idonsa cikin nata ya d'aga mata kai alamun da gaske yake
Hawaye masu zafi suka sake zubo mata, yayinda jama'ar wajan suka zama 'yan kallo suna ganin wani sabon salon iskanci, namiji Yana meqawa mace hannu a cikin bainar jama'ah (
Kallansa take hawayen idonta sunqi tsayawa, waye shi?

Bata sanshi bafa, tayaya zata bishi tabarsu Inna? idan tabishi tasan irin tashin hankalin da zata haddasa masa agidansu?

Cikin ranta take wannan tambayoyin, ahankli ta girgiza masa kanta alamun bazatabishi ba
Dago Idonsa yayi ahankali, asace yake kallon d'unbin mutanan da suke kallonsu amma yarinyar nan ta kunya tashi agabansu, saboda me zata zauna da mutanan da sukai mata irin wannan cin mutuncin,?

Baiyi wata wataba yasa hannunsa ya fuzgota tare da bakkon kayan nata harma da ledar da Inna ta wullo mata
Mutanan wajan kuwa suna ganin haka suka fara salati (
Hannunta takeson qwacewa amma yahana ta Damar hakan, janta yayi suka fara tafiya, Amma Amina sai kuka take sosai kamar ranta zai fita, juyowa tayi tana kallonsu Inna, cikin matsanancin kuka tace "Inna Karki barni, baba..."
Haka Inna ta dauke kanta, shikuma baba har zuwa wannan lokacin ya Kasa kallon Amina
Akan idon jama'ar wannan Gari, Asim yatafi da Amina babu wanda yahana shi, suna ganin kamar ma yatemakesu ne tunda yarabasu da masifa
Tun suna tafiya tana turjewa har tayi hakuri taci gaba da binsa, cikin bacin rai da tsananin damuwa ta fizge hannunta daga riqon dayayi mata
Cak! ya tsaya yadaina tafiya, juyowa yayi ya kalleta fuskar sa adaure, inbanda rashin hankali da kuma yarinta me zaisa wannan yarinyar tazabi zama a cikin mutanan da basa kaunar ta?

Har sai yayi mata dole Akan rabuwa dasu?

Afuto dakai waje ayima wannan tozarcin amma ahakan kake kuka kana kiransu?

Haushi ya kamashi, jakar bakkon kayanta da d'aya ledar yazubar agabanta sannan yajuya yayi tafiyar sa (
Wani irin zazzafan zazzabi yakeji, ga kansa da yake ciwo, shi mema yasa yadawo ne? da yanzu ba zaiga wannan tashin hankali ba, wani bangare da zuciyarsa yace masa laptop dinka, itace dalilin dawowarka, yatuna yanda su Inna suka iya rufe Idonsu suka ciwa wannan yarinyar mutunci tayaya zai Iya tambyarsu wata laptop bayan radadin dasukeji na rashin dansu?

Yasan cewa laptop kam yariga yarasata, yarasa komai, bai kuma san Yaya zai fuskanci Ishraqa da wannan maganar ba (Tofa!

Akan bakkon kayan nata tazube tana gunjin kuka, yanzu su Inna dama ba iyayenta bane? to suwaye iyayenta?

Menene sunan ta?

Babu wanda yasan amsar duka tambyoyinta Sai Allah
Dago kanta tayi, can ta hangeshi Yana tafiya har yayi Nisa, awannan halin batada wani zabi bayan tabishi, idan tabarshi yatafi ma ina zata?

Ina ta nufa?

Wata ke dashi a duniya bayan Allah?
Chapter 7 · 0% Book details