← Book details Insaaf Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 53

Sashe 42

Insaaf Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ina nufin muharraminta"
Mamy ta nuna Asim da El-Hameed tace "wannan shine mijinta, wannan kuma mahaifinta ne"
Yace "Okey, ku dauko min ita"
Asim ya tashi yanufeta, Shima El Hameed ya qaraso, hannu Asim yasa zai kamo ta ta watsa masa wata irin harara, manyan idanunta har wani komawa gefe daya suke saboda masifa tace "karka tabani"
Lokaci daya annurin fuskarsa ya dauke, wannan ba Insaaf dinsa bace, Insaaf dinsa tanada tarbiya, bazata aikata haka ba, yasan cewa kawai aljannu ne, cikin bacin rai ya damqo hannunta, Shima El Hameed ya kama daya hannun nata, suka fara kokarin dagata, amma tana yin wata irin Girgiza takusa watsar dasu awajan
Amjad dake gefe azaune Ahankali ya matsa kusa da mamy ya kama hannunta yariqe
Malamin Yana ganin yanda ake kokawa da'ita ya tashi ya dauko wani ruwa acikin gora, yabude shi ya tuttula mata a jikinta, lokaci daya jikinta yasaki, tazube a tsakiyar falon, wani irin kuka tafashe dashi irin me gunjin nan, ga wani irin numfashi datake yi kai bazakace macece take wannan numfashin ba, kamar muryar gardi
Ishraqa ta dora kanta Akan qafafunta tafashe da kuka, kuka take sosai harda shashsheka, Amrah ta matsa jikinta tana Bata hakuri da muryarta datayi rauni alamun itama tana gab da Fashewa da kukan
Malamin Yana daga tsaye ya kalli Insaaf dake kwance tana wani irin gunji marar Dadin ji, yace "ba zakuyi magana ba?"
Tayi Shiru ta qyaleshi, yajuya ya kalli ya ransa yace "kufara"
Matasan yaran kusan su biyar suka matso kusa da ita suka fara karatun alqur'ani, Kowa da inda yake karanta wa,sunkusa minti talatin suna karatu amma Insaaf ko uhm batace ba, tana kwance tana wannan gunjin kukan
Ran Malamin ya6aci, cikin fishi ya tashi ya dauko wannan ruwan daya zuba mata dazu, ya kwara mata shi a fuska, wani irin qara tasaki wanda yasa mutanan falon suka fara toshe kunnuwansu
Har zuwa wannan lokacin Ishraqa taqi dago kanta ta kalli Insaaf, kuka kawai take tana tausayin yar Tata
Cikin tsananin azaba ta daga hannunta, cikin wata irin murya me girma tace "zan fada...., karka sake qonani, zan fadaaaa!...."
Amjad ya zaro Idonsa waje
, yasaki hannun mamy yakamo dantsen hannunta yariqe sosai
mamy tana jin yanda jikinsa yake rawa, haka tayi fuska ta qyaleshi
Malam yace "mezaku fada?

Suwaye ku?"
Cikin gunjin kuka tace "Auranta nayiiiii...., nine mijinta manub....

Nine nake kashe duk wanda ta aura, nine nashiga jikin mutanen dasuka Santa nasanya musu tsoron ta acikin zuciyar su, banaso kowa ya ra6eta, matata ce"
Gaba daya falon Sai suka fara salati, Asim yayi Shiru Yana kallon ikon Allah, shida matarsa wani shege agefe Shima Yana iqirari matarsa ce
Malam yace "to Manub danme zaka aure ta?bayan kasan babu aure atsakanin mu?

Meyasa kake cutar da ita kana daukan ran mutane wanda basujiba basu gani ba?"
Shiru tayi batayi magana ba, ruwan hannunsa yasake watsa mata cikin sauri tace "tun tana qara ma na aure ta, meyasa saida ta girma zasu aure ta bayan nadade da auren ta, lokacin da motar su tayi hatsari a gefen gidanmu ita kadai ce tafuto tana kuka, ni kuma tundaga nan naji ina sonta na aure ta, na dauke ta daga Garin na kaita tsakanin kano da Adamawa na ajiye ta,tundaga nan nake bibiyar rayuwar ta, suma wanda suka tsinceta sukaci amanata suka aura mata dansu Ammar, Shima na kashe shi sannan nashiga jikin uwar Yaron nasaka mata tsanar Insaaf acikin ranta har saida suka koreta daga gare su "
Asim ya tuna irin rashin mutuncin da Inna tayiwa Insaaf ranar dasuka koreta, dama abin yayi yawa, ashe ba'ita kadai bace da sharrin aljannu
Malam ma yayi Shiru yanajin wannan rashin Imani, yace" yanzu zaka rabu da'ita kokuma saina konaka?

"
"bazan Barta ba, matata ce ita "
Malam yanajin haka yayiwa yaransa alama suci gaba da karatu, suna farawa tafara ihu tana cewa"zan fita, wallahi zan fita"
Malam yace "ta'ina zaku fita?"
"tabaki, wallahi zan Barta har abada"
Malam yace "Bata baki zaku fita ba, ta hanci zaku tafi, sann
an muddin kasake dawowa jikinta saina qonaka gaba daya"
"zan tafi, zan tafi, wallahi natuba bazan dawo ba" Yana fadar haka Insaaf tafara jera atishawa, saida tayi guda uku qwarara sannan wani irin bacci mai nauyi yayi awon gaba da'ita
Malam ya tashi ya hada musu magungunan da zatayi amfani dashi, ya basu sannan yace "insha Allah tabarsu kenan, bazasu dawo ba, ni Nasha ganin irin wannan case din dayawa, yanzu wannan maganin zatana amfani dashi kullum, daya mai ne ta dinga shafe jikinta dashi idan zata kwanta, sauran kuma Nasha ne, dana turare"
El-Hameed yace "mungode Malam, Allah yasaka da Alkhairi, yanzu Malam menene abin sadakar?"
Murmushi yayi "dubu arba'in ne, amma kukawo abinda yasamu"
Asim yayi gyaran murya yace "Mungode Malam, insha Allah zan aikoma da check na nera million daya, kuma dan Allah Kaci gaba da saka matata acikin Addu'ah Allah yaqara kare min ita"
Muhsin yayi murmushi ya jinjina kansa
Ishraqa tadago kanta tace "mungode Malam, Allah yasaka da Alkhairi,haqiqa ka ceci rayuwar yata, bamuda bakin da zamu gode ma, ka shirya next week dakai za'ai Umara insha Allah"
El-Hameed ma yace "sannan idan Malam yadawo daga Umara akwai sabuwar Mota tasa ce halak Malak"
Yaran Malam suna jin haka suka saki kabbara, dama ko ba'a fada maba kana ganin yarinyar kasan yar gata ce ta gaske, yanda suka taho yuya guda haka duk Akan mutum daya,
Malam yace "haba bayin Allah, ya zaku min haka?, ai wahalar tayi yawa"
Mamy tace "babu komai Malam, qalubale dakuma halin kadaici da tsananin tashin hankali da yarinyar nan ta fuskanta Sanadin wannan matsalar bazai fadu ba, mune da godia wallahi"
Malam yace "to hajiya, nagode, Allah yabata lafiya, sannan insha Allah zan dinga aiko mata da magungunan dazaran sun qare, saitaci gaba da amfani dasu"
Gaba dayansu suka sake yimasa godia, Asim yasaka hannu ya dauki Insaaf, Sai yaji ta shafal, ba kamar dazu ba, har lokacin tana bacci ba tasan abinda yake faruwa ba
Muhsin ne yayi driving dinsu suka koma gida, Amjad kuwa Kasa driving din yayi, Sai El Hameed ne yamai dasu gida
Gaba dayansu gidan mamy suka wuce, Amjad saida ya ganshi azaune a falon gidan, sannan yasaki wata irin Ajiyar zuciya
Mamy ta kalleshi tayi murmushi
Kai tsaye Asim yawuce da'ita dakinsu, Akan gadon ya kwantar da'ita Shima ya kwanta, sannan ya janyota jikinsa ya rungume tsam Akan qirjinsa Yana shafa dogon gashin kanta.

Su kuwa gaba dayansu a falon mamy suka zauna aka sake jajantawa juna,Ishraqa de fata take Allah yasake hada fuskarta da mutanan da suka riqe Insaaf tsawon rayuwar su, sun san cewa ita ba yarsu bace amma suka riqeta ruqo na gaskiya.
har aka Kira la'sar Asim bai futo ba, mamy taji Shiru ta kalli Amrah tace "ke jeki Gano ko tatashi, naji su Shiru"
Ishraqa tace "a a mamy, barsu su huta, anjima da daddare Sai mu dawo"
Mamy tace "a a, muje ku ganta kafin kutafi Ishraqa"
Amrah ce tatafi d'akin nasu, tayi nocking taji Shiru, Ahankali tatura kofar tashiga, anan ta gansu kwance Akan gadon ya rungume ta a jikinsa kamar zai mai data ciki, Bude kofar da yaji anyi ne yasa yabude Idonsa dake cikeda bacci ya kalli kofar, Yana ganin Amrah yace "ke lafiya?"
Kansa ta sunkuyar tace "Yaya waisu Anty Ishraqa ne zasu tafi gida, shine zasu ganta"
"kice su shigo"
abinda yace kenan, ya maida kansa kan fillo
Dawowa falon tayi tafada musu, gaba dayansu suka shiga d'akin, alokacin ya tashi yashiga toilet Yana alwala, saida yafuto ya gansu duk sun kewaye ta, itama tana zaune a tsakiyar su kamar ba'ita ba, cikin mamaki yasake kallonta, Agogon hannunsa yake daurawa ya qaraso gaban gadon yace "babu abinda yake damunki ko?"
Tace "babu komai Yaya, Wai yanaga duk jikinku yayi sanyi?

Menene yake faruwa?"
Mamy tace "babu komai Insaaf, tunda kina jinki lafiya to Alhamdulillahi , Allah ne yarabaki da masifar datake damunki, insha Allah saide atada labari, aljannu ne ajikin ki kuma an cire miki su"
Tace "aljannu?"
Duniyar tunani tatafi....

Sai alokacin tatuna ashefa ance ta shirya zasu tafi wajan ruqiyya, to ai daga nan ba tasan ma menene yasake faruwa ba
Asim ya matsa yariqe hannunta yace "zanje masallaci, ko akwai abinda kike buqata?"
Kanta ta girgiza tace "babu komai Yaya, Allah yadawo dakai lafiya"
Kansa ya d'aga mata kawai, daga nan yafice daga d'akin
Suma su Ishraqa sunaji an idar da Salla a masallaci suka tafi, saboda sunsan Asim din zai Iya dawowa
Ana idar da sallah kuwa yadawo, mamy Yagani zaune afalon,itada Amrah da Amjad, Shima zama yayi Yana duba saqonni acikin wayar sa
Har dare suna zaune afalo kadan kadan suna fira, amma Asim kam Hankalinsa Yana wajan Insaaf, dama kawai yake nema yagudu wajan ta
Mamy tatashi tashige d'akin tana fadin "bari naje nayi wanka nahuta"
Cikin sauri kuwa Shima ya tashi yashige cikin d'akin nasu.
Chapter 42 · 0% Book details