← Book details Insaaf Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 53

Sashe 4

Insaaf Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

In an'isa shege nake, wallahi tallahi bazai iyuba, banga gawar danaba danhaka dana bai mutu ba"
Dan sandan ya kalli magidancin mutumin yace "Alhaji hakuri zakayi, har yanzu munakan bincike ne, dole abinda bincike ya nuna dashi zamuyi amfani" Yana Gama fadar haka yajuya ya maida kallansa ga Amjad da'akayi wa aiki a goshinsa saboda bugewa da yayi, sakamakon kadeshi da Mota tayi, idanunsa yayi jajir kasancewar sa fari, har yanzu hawaye sunqi tsayawa a'idonsa
ya kalleshi da kyau yace "kayi hakuri kadena kuka, kaci gaba dayi mana Bayanin yanda abin ya faru"
Cikin kuka yace "sun kashe shi fa..., agabana suka harbeshi yafadi"
Gaba dayansu mutanan falon suka fashe da kuka, mamy tana zaune agefe tana Jan carbi, idanunta sun kumbura da alama Tasha kuka taqoshi, Amjad Yana jikin ta kamar Yaron goye, Sai kuma wata mata agefenta kana ganin ta kasan ba bahaushiya bace, balarabiya ce
Magidancin nan yanajin furucin Amjad yafara Baza babbar rigarsa Yana fadin "shikkenan, innalillahi wa Inna ilaihirraji'un...

Shikkenan Asim, wayyo niya Allah na" Sai jagwab yazauna aqasa
Gaba daya yabawa 'yan sandan da suke tsaye tausayi, duk ya susuce kamar ma baya cikin haiyacinsa
Miqewa Dan sandan yayi yadubesu "kuyi hakuri hajiya, muna nan munakan bincike har yanzu, saboda awajan da abin ya faru kwata kwata babu alamar gawar sa, saita driver kawai awajan, shikuma Amjad yace agabansa suka harbeshi, hakan yana nufin cewa kode be mutu ba yagudu da kansa, kokuma wanda suka harbeshi sun tafi dashi, amma insha Allah zamu tsaurara bincike Akan hakan, sannan Commissioner da kansa yabada cigiyar photonsa agidajen television's dakuma gidan redio duk wanda yaganshi yatemaka yasanar a police station din dake kusa dashi, insha Allah za'a bashi kyauta mai tsoka"
Yajuya yabawa mutumin daya Kad'e Amjad da Mota hannu, yace"godia muke Yallabai, Haqiqah zuwansa yaqara taimaka mana wajan bincikenmu"
Mutumin yace "babu damuwa"
Kallansa yamai da ga Amjad yace"ko zaka iya binmu zuwa office domin sake amsa wasu tambayoyin?

"
Amjad yanajin haka ya sake shigewa jikin mamy ya rungume ta, hakan dayayi shiya sake nunawa d'an sandan cewa babu inda zashi, gaba daya tsoron mutane ma yake yanzu, ko nanda bakin gate bayajin zai Iya fita batare da mamynsa tana kusa dashi ba
Dan sandan yayi murmushi kawai daga nan suka fita gaba dayansu
*** ***** ***
Amina da Inna suna zaune atsakar gida, Inna tana gyara daurin tsintsiyarta daya kunce, ita kuwa Amina tunanin wannan mutumin dasuka tsinta na cikin ruwa take, koya warke oho, amma gsky yanada kyau kam kamar bature, tarasa wazata Bawa labari ko zataji dadi
(kunsan idan gulma tanacin mutum
Kamar an mintsineta ta tashi tace "inna zanje gidansu lubabatu yanzu zan dawo"
"saikin dawo, Karki Dade akwai inda zamuje"
Tace "to Inna"
Tana zuwa gidansu lubabatu taga ancika falon nasu danqam dayara da manya anata kallo, saboda duk qauyen daga gidansu lubabatu Sai gidan maigari nan ne kawai suke da kayan kallo
Yara yan kallo suna ganin shigowar Amina daya bayan daya suka watse, har bige juna suke wajan fita, jikinta ne yayi sanyi, duk saitaji ta muzanta, ita kuwa lubabatu da murmushi tatareta, tasa hannu zata janyota jikinta goggo ta daka mata wata uwar tsawa "ke Luba, koma daki kokuma yanzu inci mutuncin ki, sakara kawai wadda batasan ciwon kanta ba"
Lubabatu sum sum tashige cikin daki ganin ran goggon nata yabaci yanda Bata taba zato ba
Goggo tadubi Amina tace "kifita daga harkar 'yata Luba, ko'itama so kike ki lashe mata kurwa tabi sauran mazajen ki?

To aniyarki tabiki, tsabar masifar naci irin naki yanzu Samari ko wajan Luba sun daina zuwa saboda Ana ganinku tare, to aniyarki ta kiyayi ramata...."
Dagudu Amina tajuya tafice daga gidan, cikin kuka tafado gidansu ko sallama babu, Inna ta kalleta takasa binta tabata hakuri, tasan wannan kukan nata baya rasa nasaba da qaddarar rayuwarta, toya zasuyi?

Ita kanta abar abawa hakuri ce yanzu bare kuma ita kanta Aminan(
Tashi tayi zata fara shara goggon lubabatu tashigo gidan, Inna tace "sannu da zuwa goggon Luba"
Cikin fishi goggo tace "ba wannan ne yakawo niba, zuwa nayi inyi miki kashedi da gargadi Akan yarki Amina, tarabumin da yata, babu ita babu Luba, kowa yayi harkarsa, idan bahakaba kuwa wallahi hukuma ce zata rabamu"
Tana fadar haka tajuya fuuuu tafice daga gidan, Inna tazauna Akan kujera da sauri tana ambaton sunan Allah, Sai yanzu ne tasan dalilin shigowar Amina tana kuka
Amnah El~Yaqoub
[2/4, 11:52 PM] El~Yaqoub: INSAAF
Writing by :Amnah El~Yaqoub
Dedicated to :Itz Sadeek, Alkhairin Allah yakai gareka
Like my page on Facebook
https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493
Toyaya zasuyi da rayuwar su?

Qaddara ce Allah yariga daya dorawa Amina, su kansu basusan takamaimai abinda yake damunta ba, kuma Malam Yana karbo mata rubutu awajan Malam liman tanasha duk lokacin da abin ya faru
Babu me'iya sauya Qaddara face Allah
Ajiyar zuciya tasaki, tayi wulli da tsintsinyar hannunta sannan tafara hada abinci awani kwanon silva mai Dan kyau, shinkafa da wake ce amma duk ta caku6e,(
Dakin Amina ta nufa
, tana daga labulen taganta a kwance tayi kukanta harta qoshi
"taso mutafi, wannan koke-koken babu inda zai kaiki, ki kaiwa Allah kukanki yafi miki wannan asarar hawayen"
Ahankali ta tashi suka tafi, ko wanke fuska batayi ba, suna cikin tafiya sukazo wucewa ta majalissar su isyaku yayan Lubabatu , Ada isyaku Yana ganin Inna duk abinda yake zai Bari yazo ya gaisheta saboda qawancen dake tsakanin Amina da Luba, amma yanzu yana ganinsu yadauke kai kamar bai sansu ba, qarshe ma suna hada ido da Amina yasakar mata wata uwar harara, Inna tana ganinsa, Sukuwa sauran yan majalissar duk suka watse
Abin yayiwa Inna ciwo sosai, ashe har yanzu haka Amina tana fuskantar wannan matsalar?

Ashe har yanzu mutanan Garin basu saduda sunyi hakuri ba?

Amma ahakan har take iya futowa aduk lokacin dataso?

Inna Bata Gama tunanin taba suka hadu dawasu Yara sun dawo daga makarantar Allo, mutum daya daga cikin yaran tana ganin Amina tadaga murya tace "la'ila wallahi ga Amina nan"
Atake yaran suka fara watsewa, kowa Yana gudu
Inna batasan lokacin da hawaye suka zubo mata ba, Ahankali take share hawaye tana kuka, Amina tajuyo ta kalleta zatayi mata magana kawai Sai taga tana kuka, cikin sanyin murya tace "Inna meyasa kike kuka...?

Bata Gama magana ba itama taji wani qullulun abu yatsaya mata awuya, lokaci daya tafashe da kuka itama, haka suke kuka itada Inna babu wanda yabawa kowa hakuri, har suka qarasa bakin titi suka shiga motar da zata kaisu Yola, anan Amina tasan inda zasuje
Daqyar suka kawo kansu asbitin itada Inna, dasuka shiga ciki ne basusha wahala ba Allah ya nuna musu su baba Azaune a wata bishiya, bayan sun gaisa baba yace "Larai aida bakusha wahala kunzo da abinci ba"
"yanzu Malam muda mukazo dubiya tayaya zamu taho haka hannu babu komai"
Yace "Ai Ammar Yana siyo mana biredi, kuma akwai kayan shayi aciki" yadubi Amina yace "yanaga idonki sil haka ko kwalli babu 'yar baba? , kamar ma kinyi kuka"
Inna tace "munyi kuka de baban Amina, al'amarin Amina yafara bani tsoro Malam, Anya kuwa ba zamuyi qaura mubar Garin nan ba?"
Ammar dake tsaye yace "Inna Garin iyaye da kakanni idan muka barshi ina zamu?

Duk suyi su Gama gulmarsu ai WATA RANA SAI LABARI {littafin takwarata miss suwara
} yaci gaba da cewa "wanda zai baka labarin ma wata Rana bazaka sameshi ba"
Inna tana jinsa tayi Shiru,taga alama Ammar bashida hankali, Dan baiga abinda tagani bane yau shiyasa yake fadar haka, Inna ta kalleshi tace "kuje da'ita tadubashi, Nima gamu nan nida Malam"
Ammar yadubi Amina yace "muje qanwata"
Inna naganin tafiyarsu tadubi Malam tace "Malam al'amarin Amina fa yayi tsamari, yanzu futowar mu daga gida duk wanda yaganmu gudu yake, wallahi Malam bansan lokacin da nafara yiwa yarinyar nan hawaye ba, nikam Malam mezai hana muhada Ammar da Amina aure?inyaso daga nan mutattara yanamu yanamu mubar Garin?
Chapter 4 · 0% Book details