← Book details Insaaf Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 53

Sashe 10

Insaaf Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yaya makomar auren Asim da Amina?
ta wacce hanya zata fada masa wadda zai fahimceta cikin sauqi?

Wanda suke tambayar wacece Insaaf ina fatan yanzu kun samu amsar tambayar ku?
sharhi
Amnah El~Yaqoub
[2/6, 11:16 PM] El~Yaqoub: INSAAF
Writing By:Amnah El~Yaqoub
9&10
Like my page on Facebook
https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493
Dedicated to *FAUZIYA* *S* *MADAKI* My Admin sarkin gyara,
ina alfahari dake akoda yaushe
Sai a lokacin mamy ta lura da Amina, takai kallonta wajan Asim ko zataji yabawa Amjad amsar tambayar sa, amma saitaji baice dashi komai ba, asalima tafiya yafara yi, Ahankali mamy takai hannunta wajan Amina, takamota tace "taho baiwar Allah"
Amina ta dauki bakkon kayanta suka tafi, mamy takama dantsen Asim tariqe gam kamar za'a sake qwace mata shi, Amjad Kuwa hannunsa yariqe Yana tambayarsa "Yaya babu abinda yasameka ko?Allah nagode ma dabasu kashe min kaiba"
Mamy ta kallesu tayi murmushi, cikin ranta tana qara jinjina tsananin shaquwar datake tsakanin Asim da Amjad
Duk mutanan dasuka ganshi inde dama sun sanshi to saisun tayashi murnar dawowarsa, idon Amina yayi tsilli-tsilli yau gata a Airport, saida suka kammala komai sannan sukahau jirgin dazai tashi zuwa Lagos
Acan ma suna sauka motoci guda biyu suka gani na gidan sunzo suna juransu, already mamy tayi magana suzo tun kafin sutaho, rarraba idanunsa yake kozaiga daya daga cikin direbobin dasuka rakasu Yola, amma babu ko mutum daya daga cikin su, hakan yana nufin dama can sun shirya barin gidan kenan shiyasa aka hada baki dasu domin aga bayansa, to waye awaje dayake son ganin bayansa?

Waye shi?

Yasan cewa a cikin gidansu de babu, suna zaune lafiya cikin qaunar juna dukansu, family ne da suke da hadin kai sosai, to Amma tayaya wani a waje zaizo yahada baki da mutanan gidan domin a dauki ransa?

Wannan tunanin da yayi ne yasa shi ciwon kai,lumshe Idonsa yayi tareda dafe kansa, mamy da Amjad har rige rigen tambayar sa suke "lafiya kuwa?"
Bece dasu komai ba, kawai de ya d'aga musu kansa alamin babu komai
tun kafin su qara so wajan motar duka drivers din suka zo suna masa sannu da zuwa cikin farin ciki ganin yadawo gida, Allah ya baiyana shi
Awannan lokacin kam Amina tazama yar kallo, daga ganin yanda mamy take nan-nan dashi tasan cewa ba qaramin so suke masaba
Suna zuwa unguwar kuwa tasake zama yar qauye tuburan, domin kuwa saida aka tantancesuma suka shiga, hakan yana nufin unguwar akwai tsaro, Karon farko data fara tunani Akan abinda yasamu Asim, abinda yafara zuwa ranta shine unguwa irin wannan me cike da matakan tsaro tayaya wani daban zai shigo har inda kake ya cutar dakai batare da an kamashi ba?harbi fa ba qaramin abu bane, idan abun yazo da qarar kwana shikkenan mutum yamutu, amma a harbeka ajefaka cikin ruwa wacce irin tsanace wannan?

Gaskiya dole ya shiga cikin damuwa,tunanin ta yayi Nisa har suka qara so cikin gidan, gida ne tsararre daya amsa sunansa,bazakace a cikin Nigeria yake ba,ga motoci Kala Kala da suke adane agefe,Bude musu motar a kayi, sannan suka shiga cikin gidan, mutum uku ne a zaune cikin nashahurin falon nasu, mata biyu matasa dakuma yar qaramar yarinya, mamy tana yin sallama suka maida kallansu bakin kofar, Gaba dayansu suka miqe tsaye cike da mamaki, da gudu Lubna tataho ta rungumeshi, lokaci daya tasaki kuka tana shafa kansa, itama dayar tana qarasawa tahada dashi da Lubna ta rungume su tana kukan itama, yar qaramar yarinyar cede tataho ahankali, hankalinta a kwance tana wasa da teddy ta tsaya awajan, mamy kuwa murmushi take amma hawaye ne yake zuba daga idonta
Amjad yayi Shiru yana kallon su, duk Sai kuka suke sun rungume shi, gyaran murya yayi sannan yace "to.., to to, Anty Amrah kukan ya'isa haka saiki cikashi"
Wadda yakira da Amrah tadago ta watsa masa harara, kallanta nasake yi sosai, kana ganinta kaga yar qwalisa kuma zakayi tunanin Amjad din ya girmeta, amma kuma gashi yakira ta da Anty Amrah
Shima dauke kansa yayi daga wajan ta Yana yatsina fuska, da alama basa shiri da juna (
Amrah ta kwantar da kanta akafadar mamy cikin shagwaba tace "mamy..."
Mamy tashafa kanta,sannan tasa hannu tagoge mata hawayen idonta, takasa cemata komai
Amjad ya sake kallon Anty Lubna data maqalqale Yaya Asim ko kunyar mamy bataji yace "to Laila majnun, ai gaisuwar ta'isa haka"
Gaba dayansu sukasa dariya, sannan Lubna tacikashi, yar qaramar yarinyar ce ta kalli yaya Asim tace "Uncle ni nayi fishi dakai, shine katafi America kaqi dawowa ka manta Dani"
Kallansa yakaai wajan yarinyar yayi murmushi, sannan yasa ka hannu yadagata Sama, hannu tasa taja hancinsa tace "Daddy kakawo min tsaraba?

Mamy tace katafi America kuma zaka dawo, zaka tahomin da jirgin Sama mai tashi"
Murmushi yayi yace "Am sorry my daughter...Daddy yayi laifi, gashi bankawo miki jirgin samah ba, amma zamu shiga jirgi muyi yawo, ki kalli ko'ina saimu dawo gida ko?"
"eh Uncle, I miss you" tafadi haka sannan tayi kissing din kumatunsa, daganan suka qarasa cikin falon
Amina de kallonsu kawai take, jikinta duk yayi sanyi, saida suka zauna sannan Anty Lubna ta lura da Amina, dammm!!!

Gabanta yayi wata mummunar faduwa, haka kawai taji yarinyar Bata kwanta mata ba, wacece ita?

Menene yahadata da mijinta har suka taho tare?

Itafa Bata fatan kowacce mace ta ra6i mijinta, zata iya yin komai Akan mijinta, sosai take mutuwar sonsa, tsanar yarinyar ta darsu a cikin ranta, ta yatsina fuska tare dayin qaramin tsaki ta dauke kanta
Amrah datake zaune kusa dashi tadubeshi tace "Yaya, yakamata kayi wanka kahuta, zanshiga kitchen da kaina in hadama girki me dadi, yau ranarmu ce, Bata Anty Lubna ba" taqarasa maganar tana kallon Anty Lubna, ahankli Lubna tayi mata dariyar yaqe kamar zata fashe da kuka (
Ajiye yarinyar datake hannunsa yayi, yashafa sukarta tace "My Widad, daddy zaiyi wanka OK?"
Tace "eh Kayi wanka kazo kabani labarin America"
Murmushi yayi ganin yarinyar da gaske ta yarda da maganar da Mamy ta shirya mata, sannan ya kalli Amrah yayi mata nuni da Amina "Amrah, kikaita d'akin ki tayi wanka, kiyi mata abinda ya dace"
Yana fadar haka yafara tafiya zuwa dakinsa, Luban ta Mara masa baya, Amjad ya d'aga murya yace "Yaya baka fada mana Sunan taba"
Cak yaja ya tsaya batare daya juyo ba
Mamy ma ta kalli Amina da murmushi dauke a saman fuskar ta tace "Yata Yaya sunan ki?"
Wasa take da yatsun hannunta, Ahankali tadago daradaran idanunta tace "Am..

Ami...."
Kafin ta qarasa taji muryar Asim cikin kwanciyar hankali yace "MINAL"
Amjad yace "gaskiya sunan Yamin dadi" yafadi hakan yana Dora hannunsa Akan setin zuciyar sa (
Asim ya kalleshi yayi cikin dakinsa, itama Lubna tashiga sannan tarufo mana kofar (
Amrah ta kalli Amina tace "Minal taso muje"
Bakkon kayanta ta dauka tabi bayan Amrah, ita kuma mamy ta dauki wayarta domin Kiran Daddy
suna zuwa d'akin taji waani qamshi ya dake ta,saida ta nuna mata komai sannan tafuto tabarta a d'akin
Tana futowa daga wanka tasaka doguwar riga ta atamfa daya daga cikin kayanta
Babu abinda tashafa ko mai babu bare powder, I fuskarta tayi fayau, sallah tafara ramawa sannan tazauna adakin tayi Shiru tana tunanin rayuwarta, har yau takasa Bude ledar da Inna ta Bata, wacece ita?

Bata saniba, menene sunan ta?

Bata saniba, Ahankali tabude jakar tafuto da ledar, sannan tafara kunce qullin dayake jikin ledar, gabanta yafara tsananta faduwa, hannunta ya dauki wata irin rawa, tana Gama kuncewa taci Karo da wata tsaleliyar riga ta Yara fara tas, doguwar riga ce amma taji adon net, hawaye ne suka fara tsiyaya daga idonta, muryarta narawa tafara girgiza kanta tana cewa "A a...

A a...

Bahaka bane, niba yar tsuntuwa bace, kune Iyayena Inna"
Haka take kuka tana magana ita kadai kamar ta fita daga haiyacin ta, rigar ta daga ta rungume ta afuskarta tana matsanancin kuka cikin kuka tace "ya Allah ka baiyana min iyayena" qaran wani abu taji yafado daga qasan rigar, Ahankali tabude idonta takai kallanta gareshi Dan qaramin zobe ne na gold amma nayara, hannunta har rawa yake ta dauki zoben tana kallonsa, yayinda idanuwanta suke zubar da hawaye, zoben ta kalla sosai a yanzu kam yayi mata kadan ta sakashi a hannunta, bazai shiga ba, kwalliyar zoben ta kalla taga anyiwa harafin { i } wata irin kwalliya, idonta Akan wajan tace " i ?" tome yake nufi?

Iman?

Inaya?

Intisar?

Kokuma iklima?

Girgiza kanta tayi ta hada rigar da zoben ta rungume taci gaba da kuka, adede lokacin Amrah tashigo d'akin taganta, jikinta ne yayi sanyi, Ahankali ta qaraso ta ajiye abinci agabanta tace "Minal meyafaru kike kuka?

Ko wani abun aka miki?"
Hannu tasa ta share hawayen sannan ta girgizawa Amrah kai
Batare data yardaba tace "to kiyi hakuri, ga abincinki nakawo miki, idan kingama ki kwanta ki huta"
Nanma Batayi mata magana ba kawai de tasake girgiza mata kai alamun to
Amrah tatashi tafuta daga d'akin har tana waiwayenta
Tana ganin fitar Amrah tamaida rigar da zoben cikin Jakarta, sannan tashige toilet ta wanke fuskarta, tadawo taci abincin Dan kadan, sannan tafara istigfari da yatsun hannunta, ahaka bacci yayi gaba da'ita a zaune
*** ***** ***
Da daddare suna zaune shida Mamy da Daddy afalon Daddy, kansa aqasa, ya sauya kaya zuwa qananu baqin jeans dakuma riga milk color, yayi masifar yin kyau, sumar kansa sai sheqi take, Daddy yace "Kaci gaba da Addu'ah my son, insha Allah nayima alqawarin Nima zan tsaya tsayin daka Inga an nemo wadannan mutanan da suke son ganin bayanka, ka kwantar da hankalin ka kaji, ai kunyi magana da commissioner of police ko?"
Ahankali kansa aqasa yace "eh"
Mamy ta kalleshi tana jiran taji qarin Bayani, saita ji Shiru, wannan hali na Asim Yana Bata mamaki, ace iyayenka ma suna ma magana amsa saide ta kasance ataqaice?

Dago kansa yayi suna hada ido da'ita ya sunkuyar da kansa, Dan yasan zai samu Rabon harara ne kawai, to Yaya zaiyi?
Chapter 10 · 0% Book details