← Book details Insaaf Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 53

Sashe 41

Insaaf Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bakisan akwai wanda ya fishi sonki ba?"
Cikin mamaki tace "waye?"
Kai tsaye yace "gani, I luv you so much Insaaf, kifada wa Mamanki tayi nasara akaina, wannan manyan idanun naki, da wannan dogon gashin naki, sunsa nafada cikin soyaiyarki, wadda ban shirya mata ba"
Yaqarasa maganar Yana shafa saman idonta, wani irin dadi taji ya ratsa cikin zuciyarta, ahankli ta lumshe idonta, hakanne yabashi Damar cigaba da shafa saman fuskarta, daga qarshe yadora bakinsa Akan nata
Yayi mamakin yanda ta bashi hadin kai wajan kissing dinta, cikin nutsuwa yake aiwatar da komai
Itama anata bangaren tanajin Dadin yanda yake kissing din nata Ahankali, ba tasan lokacin data ruqo kansa ba, hakan data masa yayi masa dadi sosai, hannunsa ne yafara yawo a jikinta, al'amarin daya dauke su kusan minti talatin suna abu daya, awannan lokacin da gashi har ita, sunyi sallama da kayan jikinsu, shine yayi kokarin jan blanket ya rufesu dashi, cikin bargon yasaka kansa Yana yi mata wani irin wasa mai wuyar fassarawa, lokaci daya yaji kansa yasara, irin ciwon kan da yaji rannan shine yanzunma yasake ji, Abin yabashi mamaki sosai, amma saiya fara Addu'ah acikin zuciyarsa
Bakinsa yadora Akan boobs dinta yanasha, yayinda Hankalinsa yayi gaba, tunanin sa yabar jikinsa, baya fata da burin samun komai Sai Raya sunnar ma'aiki tare da matarsa, acikin wannan halin yafara neman hanya, amma abinda yabashi mamaki Sai yaji kofa arufe, salati yafara yi acikinsa ransa, dama Insaaf budurwa ce kome?

Yanaso ya tabbatar, yanaso yau yasan komai dangane da yarinyar, wani irin qarfi yaji yazo masa, babu alamun tausayi yasake cigaba da neman hanya, lokaci daya yaji anyi wani irin wulli dashi har saida yaje qarshan gadon
Gabansa yayi wata irin faduwa, amma bai saka tsoro acikin ransa ba, ya kalleta yaga de tabbas ita kadai ce, cikin karfin hali yasake fuzgota jikinsa, wannan Karon tun kafin yafara neman hanya yaji an shaqe masa wuyansa, tuni yasake ta yasaka hannunsa duka biyun Akan wuyansa, Yana daga kansa Sama yaga d'akin nasu Yana wani irin Juyawa, daqyar yasamu numfashinsa yadawo daidai, lokaci daya yafara Tari, numfashinsa Yana Sama Sama kamar wanda yayi tseren gudu
Haqiqa yau yasake tabbatar wa Insaaf tanada aljannu, domin kuwa wannan abun da yaji, yafi qarfin ace karfin mace ne
Saida yagama Tari, sannan yafara ambaton sunayen Allah, tana ganin halin dayake ciki tatashi ta dauki bargon kan gadon tarufe masa jikinsa dashi, Ahankali yasaka hannunsa ya janyota jikinsa ya rungume ta, hawaye ne ya silalo daga idanuwanta, cikin kuka tace "Yaya kaima anyima abinda akewa sauran wanda na aura ko?

Haka ake musu Yaya shikkenan daga nan Bana sanin komai saide Naga sun mutu, Dan Allah karka tafi kabarni, Yaya Asim ina sonka, please karka barni kaima"
Ahankali yasaka hannunsa Yana shafa gadon bayan ta, haduwar fatar jikinsu babu kaya ba qaramin tada masa hankali take ba, yanda boobs dinta suke mintsininsa jiyake kamar yayi wasa dasu, amma daya tuna irin shaqar da akayi masa awuya, Sai yasa hannu yashafi wuyan nasa
Kenan yarinyar nan budurwa ce, idan miji Sai sadu da itane ake samun wannan matsalar, cikin muryar datasha wahala yace "suma irin haka ake musu suna mutuwa kafin su shiga ciki?"
Kanta Yana kan qirjinsa ta gyada masa kai, wata irin Ajiyar zuciya yayi mai sanyi
Yasake rungume ta sosai a jikinsa, wata zuciyar tace dashi to qila saura kai, babu makawa kaima zaka iya mutuwa yanzu, tunda gashi tafada da bakinta suma sauran hakan ce take faruwa dasu, Sai yanzu wani irin tsoro ya kamashi
Amma daya tuna da Allah, saiya yi qarfin hali yace mata "kiyi Shiru, insha Allah babu abinda zai faru, ina tare dake akoda yaushe"
Yanzunma daga masa kai tayi, Ahankali ya tashi yashige toilet yayi wanka a gurguje, sannan yazo yatada kabbarar sallah, sosai ya kaiwa Allah kukansa dangane da wannan matsalar, bayan ya idar ya dauki alqur'ani yafara karanta wa
Itama hakan tayi, tazo gefensa suna karatun tare, saida yamma liss sannan sukai Addu'ah suka shafa, har lokacin gaban Asim bai daina faduwa ba, amma idan ya tuna yariqe Allah da manzonsa Sai yaji nutsuwa ta shigeki
Tare suka futo daga d'akin shida ita, yasaka hannu yarufe kofar harda saka key, ta kalleshi tace "Yaya ina zamuje Naga kana rufewa?"
Girgiza kansa yayi yace "bazamu sake kwana adakin nanba, Sai mun nemi mafita"
Cikin sauri tace "to adakin Anty Amrah zan dinga kwana?

Kai kuma d'akin Yaya Amjad?"
Shiru yayi Yana kallonta, Sai can yace "kuma fa hakane, Kinga babu inda zaki tafi kibarni, insha Allah ayau zansan abinyi, kije d'akin Amrah, zanje wajan mamy yanzu"
Tace "to" sannan tawuce d'akin Amrah, shi kuwa Yana zuwa d'akin mamy yazauna akusa da ita
Ta kalleshi tace "Asim lafiya ko?"
"lafiya, amma ba kalau ba mami, ina zan samu manya manyan masu Ruqiyya ne yanzu?"
Cikin mamaki tace "Ruqiyya?

Waza'ayiwa Ruqiyya?"
Sharhi
Mrs Usman ce
[2/28, 8:40 AM] El~Yaqoub: INSAAF
Writing by:Amnah El yaqoub
45&46
https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493
Dole na jinjina muku saboda yanda kuke qoqarin bin wannan labari, koda yaushe sharhin ku Yana birgeni
, banda bakin da zanyi muku godia, Amnah tana tare daku akoda yaushe, ina qaunarku har cikin raina
Alkhairin Allah yakai gareku :
Ayusher
Zeee jhn
Fatyn Kaihaf
Ayusher Abdallah
Fidos Yar mama
Alhusna Mrs Idris
Zainab S muhd
ZeeMusty
Na sadaukar da wannan page agareku, Amnah tana yinku sosai wallahi
_____
Shiru yayi yakasa Bata amsa, mamy tace "Asim, maganar ruqiyya kake, nace waza'ayiwa Ruqiyya?"
Kansa aqasa yace "Insaaf"
"innalillahi...

Wani abunne yasake faruwa kuma?

Ko Aljannun tane suka tashi?"
Asim ya kalli mamy yayi Shiru, to yanzu ta ina zai fara yimata Bayani?

Tayaya zai kalli idon mahaifiyar sa yace neman haqqinsa yaje yi yaji an shaqe masa wuya?

Girgiza kansa yayi yace
"akwai de matsala mamy"
"to Asim cemin kake akwai matsala akwai matsala, kuma kaqi sanar dani komai"
Wayarta ta dauka takira Insaaf, bugu daya ta dauka, mamy tace "kizo inasan ganinki"
Tana zuwa d'akin taga Asim azaune, tanemi waje tazauna agefensa
Mamy ta kallesu tace "ku fadamin menene yake faruwa har ake nema Akira masu ruqiyya?"
Cikin sauri ta daga kanta ta kalleshi tace "Yaya masu ruqiyya za'a Kira?"
Cikin damuwa yadaga kansa yace "abinda nake tunani kenan, sannan daga baya Sai a hada har gidan ayi karatun Qur'ani"
Shiru tayi tana nazari Akan maganar sa, tarasa meyasa ake mata kallon me aljannu, ita Bata taba tashin aljannu ba, babu wata wadda ta taba cewa tanada aljannu, amma zataga gudun ruwan su, Ahankali tace "to akirasun"
Mamy ta kallesu tace "toku tashi kuje, tunda kungama yanke shawarar komai"
Insaaf ta kalli mamy tace "mamy dazu nefa...."
"Bari muje mamy, zamu dawo anjima"
Asim ya katse Insaaf din cikin sauri
Mamy tayi Ajiyar zuciya tace "to Allah yakaimu"
Suna futowa daga d'akin nata, yace zaije wajan Muhsin, zasu dawo anjima, tayi masa fatan Allah yakiyaye sannan Takoma d'akin Amrah tana fatan ace matsalar ta tazo qarshe
*** ****** ***
Zaune suke a gaban wani malami da Muhsin yayi musu jagora zuwa wajansa
Malamin yayi Ajiyar zuciya bayan yagama jin duk abinda yake tafe dasu
yace "subhanallah...., dagaji ta hadu da mugayen aljannu ne, Bari nakira wani abokina, saina hadaku dashi, kuyi hakuri insha Allah, zaku samu mafita"
Wayar sa ya dauko yakira wani Malamin daban yayi masa Bayanin komai, Malamin yace ataho masa da yarinyar, yanaso yaganta
Sallama sukai, ya dubi su Asim yace "munyi magana dashi, amma dole saikun tafi da yarinyar, yanaso yaganta"
Muhsin yace "Okey, to shikkenan Malam, mungode, zamuje insha Allah"
Malamin yace "babu damuwa, kuje waje, zanturo muku wanda zai muku jagora zuwa wajansa"
Godia suka sake yimasa, sannan suka futo daga falon nasa
Kai tsaye gida suka wuce duka su ukun, a lokacin duk suna zaune afalo, Amjad yajuya Sai kallon Amrah yake, tana dago idon ta saita ga sun hada ido dashi, harara take sakar masa taci gaba da kallo
Insaaf da mamy kuwa kallo suke, basusan abinda yake wakana atsakanin su Amrah ba
Asim ne yashigo falon, gaba dayansu sukai masa sannu da zuwa,Insaaf ta miqe zuwa kitchen ta kawo masa ruwa ta ajiye agabansa, sannan ta zuba masa a cup tabashi, Takoma kusa da mamy itama ta zauna
Da wani irin kallon soyayya yabita, kwata kwata ya manta su mamy na wajan
mamy ta kalleshi tasaki gyaran murya tace "ya akayi Asim?"
Cikin sauri yajuyo ya kalleta, sumar kansa ya shafa yace "Mamy mun dawo, but yanzu zamu juya, Malamin yace muzo mu tafi da'ita"
"ku tafi da'ita ina?

Ai bazata biku ita kadai ba, Gara mutafi gaba dayanmu"
Tajuya ta kalli Amjad taga yatusa Amrah agaba Yana aikin kallo, ta Girgiza kanta, wanna yaran kuwa lafiyar su kalau?

Gaba daya Yara sun susuce Akan mata?

Daga murya tayi tace "Auta kutashi mutafi, Amrah jeki kiramin Ishraqa kice tazo akwai inda zamuje" tasake duban Insaaf tace "dauko hijabin ki mutafi"
Babu musu tashiga daki ta dauko hijab dinta suka futo daga gidan gaba daya, a compound suka hadu da Ishraqa da El-Hameed, mamy tasake yimusu Bayanin komai, El Hameed yace "to hajiya ko zamuje wajan Malamin daya Bata magungunan nan ne?"
Mamy tace "A a Hameed, muje wajan wannan din de agani, Fatanmu de Allah yasa mudace"
Gaba dayansu suka amsa da Amin, sannan Amjad ya dauko wata motar suka tafi gaba dayansu
Bayan sunje gidan Malamin sosai ya karbesu hannu bibbiyu, acikin babban falon sa suke azaune gaba dayansu, kowa yayi Shiru Yana jiran Malam
Saida yagama sallamar wasu mutanan sannan yadawo kansu, yasake basu hakuri suka sake gaisawa ya kalli Asim yace "ina yarinyar take?"
Asim ya kalli Insaaf ya nuna ta, Malamin ya kalleta yace "taso nan yata"
Wani irin d'an iskan kallo tayi masa tasaki wani irin tsaki mai qarfi
Lokaci daya su mamy suka saki baki suna kallonta cike da mamaki, Malamin yayi murmushi yasake kallonta yace "bazaki zo ba?"
Kai tsaye tace "bazan zoba, duk abinda kakeji dashi Nima inaji dashi"
Wannan Karon kam, tabawa kowa mamaki, shide Malamin baice da'ita komai ba, yayi wata irin dariya yace
"to bari mugwada muga abinda kikeji dashi din"
yajuya ya kalli su Asim yace "Waye yayanta anan?
Chapter 41 · 0% Book details