Sashe 50
Insaaf Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Menene yake faruwa ne?"
Su Ishraqa ne suka qaraso wajan,tare dasu mamy
Sai alokacin Inna ta kalli Insaaf tace "kiyi hakuri Amina, Dan Allah ki yafe mana, saida na aikata miki wannan butulci nagane nayi kuskure, nasoki kamar yata taci kina, bansan wacce irin zuciya gareni ba dana aikata hakan, kiyi hakuri kiyafemin Amina"
Hawaye ne yazubo mata, tasa hannu ta share, tace "Inna nayafe muku, dama ban riqeku ba, kun riqeni kamar yarku, Baku qyamace niba, kun dauki danku kunbani Inna duk da kunsan larurar datake tare dani, babu komai Inna,baba, kudena neman yafi yata, nayafe muku wallahi"
Asim ya sunkuyar da kansa Yana shafa goshinsa, yayinda hannunsa daya yake cikin aljihun Wandon jeans dinsa
Wani irin kallo yayiwa Insaaf, ko menene nacewa sun dauki dansu sun Bata?
Menene ma natada maganar auren?
Tun kafin tasake cewa ta auri maza shida Gara subar wajan, dan zuciyarsa zafi take masa yanzu haka datayi maganar ta auri wani
Ya kallesu yaqaqalo wani murmushi yace "mu qarasa gida mana ko"
Su Inna suka kalleshi, Malam yace "ikon Allah, bawan Allah Kaine?"
Asim yayi murmushi, El-Hameed Hameed yace "Insaaf, muje gida su huta"
Inna tace "Insaaf kuma?
Bawan Allah kasan Amina ne?"
Murmushi sukai, mamy da Ishraqa suka jasu zuwa Mota, Asim kam budewa Insaaf gaban motarsa yayi, Amrah tashiga baya tarufo Dasauri danma Kar Amjad yabiyota
Ishraqa tayi murmushi tasa Amjad ya dauki su Inna, sannan suka wuce gida.
Suna tafiya a hanya taga gyada dafaffiya, tace "Yaya kasiya min gyada"
Parking yayi yace "to Baby"
Amrah tayi fari da idonta cikin ranta tace tab inaga Yaya Asim ya manta ina cikin motar
Gyadar yasiyo mata, yabata, budewa tayi zata fara Ci, yace "kibari muje Gida saina 6are miki"
Insaaf tayi murmushi tace "to Yaya"
Kai tsaye gidan mamy suka je, gaba dayansu zama sukai afalo, Ishraqa da mamy suka gabatar musu da abinci da kuma abin Sha, Inna da baba de Sai kallon falon suke yanda aka tsara shi, duniya kamar baza'a mutu ba
Asim Yana kusa da Insaaf Yana 6are mata gyada tanaci
Mamy ta zauna tace "sannunku bayin Allah, mungode sosai, ai Insaaf tabamu labarin ku, kuma munji Dadin irin ruqon da kuka yi mata"
Baba yace "hajiya Amina ce kike Kira Insaaf kokuma watace?"
Mamy tayi murmushi tace "itace, Aminanku dakuka sani mu anan itace Insaaf"
Ta nuna Ishraqa da El-Hameed da Asim tace "wannan shine mahaifinta, ga maman ta, wannan kuma dana ne Asim, wanda kuka taimaka wa daga baya ya aureta"
Inna tace "Allahu akbar, Allah mai iko, Amina ashe kinsamu Iyayen ki"
Insaaf tayi murmushi cikeda jin dadi, har yanzu gani take kamar Inna ce namanta, suntashi tare, sunyi rayuwa tare, ka wayi Gari bakasan kowa ba saisu, sune kake gani a matsayin iyayenka
Mamy tace "hakane, dama haka Allah yake ikonsa, tahadu dasu ne bayan sunzo Lagos itada Asim......" daga nan mamy ta basu labarin komai
Jikinsu yayi sanyi gaba dayansu, ashe attajira suke riqewa basu saniba,sun koreta gashi ita ta gansu amma Bata gujesu ba, Ishraqa tadubesu cikeda kulawa tace" Inna ya kamata kubamu labarin yanda akai kuka samu insaaf"
Baba yace "lokacin akwai Yaya na dayake zaune akano, munkai masa ziyara a hanyar mu ta tafiya gida motar mu ta lalace, Sai muka fara tattaki, anan muka ganta azaune a wata bishiya, mu kayi mata magana amma kwata kwata saimukaga Bata fahimtar yaren damuke mata, larai tasa hannu ta dauke ta, muka shiga cikin garuruwan da suke a hanya mukai cigiyar ta, amma babu wanda ya nuna ya santa, haka muka tafi da'ita garinmu, bayan munje gida yin duniya larai tayi da ita tana tambayarta Yaya sunan ta, amma saide kallo, bamuyi dabarar gwada mata kowanne yare ba kamar fillanci ko zamuji ta amsa, haka muka hakura muke kiranta da suna Amina, saida ta girma tayi hankali muka aurar da'ita daga nan muka Gano cewa tanada matsala duk wanda ta aura Yana mutuwa, haka naje wajan limamin garinmu nake karbo mata rubutu, daga qarshe de har muka aura mata danmu Ammar,Shima Allah yayi masa cikawa "
Kuka ne ya kamashi, yasa hannu ya goge hawayen Idonsa sannan yaci gaba da cewa "daga nan ne mai Gari ya koremu, larai tarasa nutsuwarta har saida ta kori Amina saboda mutuwar Ammar, mu kuma muka tafi gombe, nafara neman kudi ina ciyar damu, daga baya komai nawa yaqare, wani bawan Allah a gombe yabamu shawara mu tafi Lagos mu nemi kudi, ance Garin ba'a zama haka, Ana neman kudi sosai, shine muka taho nan muka fara Bara "
Babu wanda bai tausaya musu ba, Insaaf de tun dazu take goge qwalla, El Hameed yace" kayi hakuri baba, kadena kuka, Baku aikata abinda zakuyi kuka ga, bakomai ne yake kashe mazajen da Insaaf ta aura ba Sai aljani, kuma shine yashiga jikin matarka yasa ta kori Insaaf, kuyi hakuri muma mun Fahimci komai, Allah yayafe mana baki daya, kuma Insha Allah kunzo gida, babu inda zaku tafi, zaku zauna agidana tare dani, mungode Allah yasaka da Alkhairi "
Asim yadago kansa ya kalli El-Hameed yace"sai baba yafara zuwa company, akwai aikin dazan do rashi akai, sannan nayi masa alqawarin gida insha Allah, saisu zabi inda suke so su zauna "
Amrah tayi murmushi tace "shikkenan Insaaf tazama me gida biyu, ga gidan Anty ga gidan inna"
Dariya suka yi gaba dayansu, Ahankali tatashi tashige dakinta nada, Sai runtse idonta take sabd yanda take Fama wajan
Amjad ya yunqura zai bita suka hada ido da mamy, wannan shine Karon farko da yaji kunyar mamy, kuma yasan kowa ya kalli tafiyar Amrah dole zai gane abinda ya wakana a tsakanin su, Ahankali ya tashi yafice daga falon
Har dare duk suna zaune afalon sunata fira, babu wanda yakai Insaaf farin-ciki, Sai wajan qarfe Tara Amjad yashigo gidan kansa aqasa, ya kalli mamy yace "mamy zamu tafi"
Mamy ta kalleshi taga Sai sunkuyar dakai yake
tayi murmushi ta kalli Ishraqa tace "maman Insaaf turo masa Amrah su wuce, dare yayi"
Ishraqa tasan dalilin dayasa mamy tayi mata magana, babu musu kuwa tabi bayan Amrah, tana zuwa ta ganta a kwance adakin, zama tayi akusa da'ita tace "Amrah, kitashi Amjad yazo, zaku wuce gida"
"Anty nifa babu inda zani, kawai kifada masa yatafi shi kadai"
"Amrah, kunzo tare tayaya zakice yatafi shi kadai?"
Wani irin kuka ne yazo mata tace "Anty wallahi Dan nakoma kashe ni zaiyi, Amjad bashida tausayi, ni ko kallansa nayi gabana faduwa yake, dan Allah kice masa yatafi kawai"
"haba Amrah, kamar qaramar yarinya?