← Book details Insaaf Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 53

Sashe 46

Insaaf Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A a, ba muga ta zama ba, Asim dauke ta mukoma asbitin nan"
Babu musu yace "to mamy"
Kayanta ya sauya mata, suka koma asbiti, wannan Karon likitan Yana ganinsu yace kawai ta'iyo fitsari a kawo masa, Asim ya sata tayi fitsari yakai musu, wani qarin ruwan suka saka mata, kafin Gari ya waye saida Tasha Leda hudu, daga nan fa Asim yakoma abin tausayi, gaba daya yashiga damuwa musanman idan ya kalleta yaga tasake yin wani irin fari, shi dama tun jiya dayaga yanayin ta yasan ba kalau take ba, amma saitace masa ita lafiyarta kalau, yanzu gashi daga jiya zuwa yau Tasha ledar ruwa har Tara, mamy ta kalleshi taji yabata tausayi, gakuma yarinya a kwance itama ba tasan inda kanta yake ba
Likitan ne yadawo zai dubata Asim yace "doctor result din bai futo bane?"
Kallansa yayi yace "yafuto, zamuyi mata scanning yanzu, sannan batada jini a jikinta, dole za'a qara mata"
"toku duba nawa idan yayi saiku saka mata"
"a a, akwai a asbitin ma, zamu saka mata yanzu, karku damu Yallabai" ya qarasa maganar murmushi Akan fuskarsa
Asim ya kalleshi wani irin haushi ya kamashi, su suna wannan halin amma dubi yanda doctor yake musu murmushi
Wata nurse ce tazo taturata sukaje akayi mata scanning, sannan suka dawo da ita suka daura mata qarin jini, idanun Asim yayi jajir damuwa tataru tayi masa yawa, Ajima ya kalleta yasake kallanta, gaba daya tausayin yarinyar yagama kamashi, ko menene yake damunta haka?

Likitan daya shigo dazu ne yadawo d'akin ya kalli Asim, ya miqa masa results din txt din yace "congratulations Yallabai, madam tana dauke da juna biyu na tsawon wata biyu, munyi mata scanning mungano 'yan biyu ne, shiyasa take wannan wahalar, but saide kuyi hakuri da wannan laulayin insha Allah Ahankali zata dinga Jin sauqi"
Zaro Idonsa yayi
yace "yan biyu doctor"
Cikin murmushi likita yace "to, abinda muka gani kenan, bamu saniba mata ne ko maza ne, akwai magungunan cin abinci damuka rubuta mata dashi zata rage yawan amai tanacin abinci ko yaya ne, amma rashin lafiya saide Ahankali shine zata warke"
Mamy ta lumshe idonta tana yiwa Allah godia, cikin farin ciki tace "Alhamdulillahi, Asim kaga ikon Allah ko?

Nida nake yan biyu ban haifi yan biyun ba, amma gashi kai Allah yabaka"
Wani irin farin-ciki yake ji sosai, ya kalli mahaifiyar tasa yace "mamy yan biyu fa" Sai hawaye
Murmushi tayi tace "godia zaka yiwa Allah Asim ba kuka ba, shine yabaka su alokacin daka rasa yarka qwaya daya jal, amfanin yarda da qaddara kenan"
Hawayen Idonsa yagoge ya kalli Insaaf datake kwance Ana mata qarin jini, cikin ransa yace I luv you so much Insaaf
Mamy ta kalli likita tace "doctor ai wannan albishir dole zan aikoma da goronsa"
Murmushi yayi yace "to hajiya godia nake" daga nan yafice daga d'akin
Mamy tace "To Asim, Bari inje gida na aiko muku da abinci, sannan in fadawa Ishraqa abinda yake faruwa, ga kuma Amrah anjima za'a kaita, ka zauna ka kula da'ita"
"to mamy, Allah yakiyaye"
Mamy na fita yakoma kan gadon ya rungume ta Yana kissing dinta ta ko'ina
Mamy tana zuwa gida taga Ishraqa ta tsaya Akan komai, komai Yana tafiya yanda ya kamata, lokacin data fada mata Insaaf tasamu ciki Sai tayi murmushi kawai, tana yiwa Allah godia, alokacin tayi gefe ta Kira El Hameed ta sanar dashi, cikin farin ciki yace "Alhamdulillahi, Habibty saiki shirya muje shopping a fara siyo mata kayaiyakin baby"
Ishraqa tace "Habiby mene?cikin wata biyu zamu fara yiwa siyaiyar kaya?"
Fada yafara yi mata "to zama zamuyi Sai haihuwar tazo sannan zamu siya?

Wacce irin magana kike yi hakane?

Yarinya zata haifi yan biyu idan Allah yabata dama, a a, jikokina ne fa nafarko, saina tsaya jira Sai ciki ya tsufa sannan zan siyo musu kaya?

Toke idan bazaki ba, nikam zanje nasiyo musu "
Ishraqa tayi murmushi tace"to maida wuqar Yallabai, shikkenan Allah ya sauketa lafiya"
Da daddare su mamy suka hadu, aka yiwa Amrah fada tare da nasiha, Ishraqa takama hannunta suka shiga Mota Sai gidan Amjad, gidan ma babu Nisa sosai, acan suka Barta tare da qawayenta, bayan qawaye sun tafi, Amjad yashigo d'akin da sallama, Ahankali ta amsa masa, zama yayi agefenta tare da cire babbar rigarsa ya ajiye
Kallanta yayi yaga tayi wani mugun kyau, jikinta yayi wani irin fresh, qirjinta ya kalla yaga masha Allah komai acike, Ajiyar zuciya yayi yace "Anty Amrah kinyi kyau sosai"
Ahankali tace "thank you"
Tashi yayi yace "ki tashi muyi Sallah mana ko, saikici abinci ki kwanta ki huta"
Kallansa tayi, itade tasan cewa wannan aure dama yarjejeniya sukai, menene yakawo zancen sallah kuma?

Ba amaren da sukai auren gaskiya ne suke wannan abun ba?, wata zuciyar tace to ai ba neman ki yayi ba, ibada ce zakuyi, Ahankali tasauko daga gadon, yanda ta sunkuya wajan saukowar shiya Bawa Amjad Damar ganin qirjinta sosai, wani irin murmushi yayi wanda ake Kira zaki raina kanki yarinya
Bayan sun idar da sallar saita ga Yana kokarin cire mata hijabi, tace "bari mana Amjad, zan cire idan zan kwanta"
Ledar kazar daya shigo da'ita ya dauko yace "to kici kazarki saiki kwanta ki huta, kinsan akwai gajiya"
Cikin sauri tace "ka zata kuma?"
"emana, ta kice, siyo miki nayi, saboda nasan kina sonta"
Jikinta ne yayi sanyi, cikin ranta tace Allah sarki Amjad, yayi kokari, to Amma kuma menene abin siyo mata wata kaza?

Kaza ai ta amare ce kuma duk amaryar dataci saita biya
afili saitace "a a, Kaci abarka kawai, meyakaini cin wata kaza nida ba za mane yakawo ni ba?"
"a a, kici wallahi, menene aciki?"
Qinci tayi, duk da ranta yanason kazar, shi kuwa saiya dauko guda daya yabata a baki, babu musu tabude bakin tafara Ci, wasa wasa saida sukaci sosai shida ita, kayan wajan ya dauke bayan sun Gama, yadawo yazauna agefenta yazauna, cikin shagwaba yace" Anty Amrah.... tah "
Kallansa tayi ta kawar da kanta, jikinta ya matso yacire mata hijabin, batayi aune ba taji ya kwanta agadon bayan ta, yazubo hannunsa saman qirjinta ya matse ta a jikinsa, hancinsa yafara gogawa a saman wuyanta, cikin muryar rada yace" Antyyynaaaah......

"
Wani irin abu taji yafara yawo a jikinta,Amjad kuwa hannunsa daya dora aqirjinta yafara yawo dashi Sai qamshin datake ne yake sake fizgar jikinsa
Wani irin haushi ya kamata, cikin sauri takwace jikinta tatashi tsaye tace"Amjad pls tashi kafita"
"tayaya zan barki ke kadai Anty Amrah"
Hannunta ta hade waje daya
tace "pls, Dan Allah katashi kafi ce kabar min d'akin nan"
Yace "Ok" yafuto yaja mata kofar d'akin, compound din gidan yaje ya tsaya yakira wayar Yaya Asim
Bayan ya a dauka yace "Yaya"
Asim yace "ya akayi Amjad?"
Muryarsa ce take rawa kamar zaiyi kuka yace "Yaya Anty Amrah ce, kaga yanzu ma daga d'akin ta koroni"
Asim yayi Shiru, takaici yataru yayi masa yawa, yanzu dare ne, idan yace zaizo gidan nasu zai Iya kwakwkwada mata mari ne, tayaya zata bar masa dan'uwa a waje ita tazauna adakin?

Tanaso tace ita yarinya ce ba tasan me ake nufi da aure ba?

To yanzu bazaije gidan ba, idan yaje a kanta zai huce dama akusa yake matarsa babu lafiya
Ajiyar zuciya yayi yace "
"Kora kuma?

Kai kuma shine kafuto kabar mata d'akin?

Amjad kana Jina ko?

Babu wata Anty Amrah, Amrah zaka ce, itace aqasanka yanzu, kadena mata shagwaba kafuto mata a namiji, karka sake tsaya wa ta rainaka kana Jina ko?"
Shima Amjad din Ajiyar zuciya yayi yace"nagane, angama yaya"
Daga nan yakashe wayar yajuya cikin gida
Washe Gari dasafe likita ya sallamesu, jikin nata dadan dama dama, tana zaune a gaban motar Asim Yana ja, tafiya kadan Saiya kalleta yace "baby babu komai de ko?"
Tace "babu komai Yaya"
Sunci gaba da tafiya taga wata mata a gefen hanya tana saida dambu, cikin sauri tace "tsaya Yaya, tsaya tsaya kasiya min dambu, yaban sha'awa"
Kallanta yayi cikin mamaki yace "dambu kuma baby?"
Batare data kalleshi ba tace "Eh, shi nake so"
Kansa ya Girgiza yace "yanzu baby kirasa abinda zakici Sai abincin bakin hanya? kan titi?"
Cikin shagwaba ta daga masa kanta alamun eh
Jinjina kansa yayi, yafita yasiyo mata, yabata sannan yaja motar suka tafi, suna zuwa gida tabaje a falon tasa dambu agaba tana Ci, sosai take wata irin Loma kamar mayunwaciya, Asim yayi Shiru Yana kallanta
Mamy kuwa da tasan halin mace mai ciki murmushi kawai tayi
Saida taci dayawa sannan tafara jin amai, cikin gudu tayi daki tashige toilet tana amai, Dasauri ya tashi zai bita mamy tace "ina zaka?"
"mamy Kinga gudu takefa, kuma likita yace ta dinga tafiya ma Ahankali, saboda lafiyar abinda yake cikinta"
Mamy tace "oh ni Hussaina, Dan Allah Asim ka sararawa ranka"
Dawowa yayi yazauna badan yaso ba, itama Insaaf din Bata Dade ba tafuto tana goge bakinta, ta kalli mamy tace "mamy zo6o nakeso Nasha"
Mamy tace "to Insaaf, zauna ki huta zan hada miki shi yanzu yanzu"
Tace "to mamy" sannan ta maida kan TV
Acikin TV din ne aka nuno wata mata tana cin alale da manja, lokaci daya taji a duniya babu abinda takeso inba alale ba, Asim Yana kallonta qasa-qasa, Yana jira yaji me kuma zata tace tanaso
itama Juyawa tayi ta kalleshi tace "Yaya"
Cikin sauri ya kawar da kansa Yana Addu'ah Allah yasa ba alalen siyarwa zata sake cewa tanaso ba
Mamy ta kalleshi taga yanda yake kawar da kai, dariya ta kamata, ta zuba musu ido tana kallon ikon Allah, Insaaf tasake juyowa ta kalleshi da kyau tace" Yaya kaje ka samomin Alale irin wannan, shi nakeso naci"
Amnah El yaqoub
[3/3, 11:02 PM] El~Yaqoub: INSAAF
Writing by:Amnah El yaqoub
51&52
Like my page on Facebook
https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493
Sarai yaji abinda tace, amma saiya sake kallanta yace "mekikace?

Mekikeso kici?"
Cikin shagwaba tace "Bana fadama ba"
Qeyarsa ya Sosa ya tashi yace "to bari naje na nemo miki"
Mamy tace "A a, kayi zamanka, Bari naje nayi mata saina hado mata zo6on ma"
Komawa yayi yazauna Yana Kallan Insaaf, tosu masu cikin dama haka suke? daga wannan abu Sai wannan?
Chapter 46 · 0% Book details