← Book details Insaaf Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 53

Sashe 25

Insaaf Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nagode...

Nagode... ta dalilin ki....

Yauma na rayu...., akaro na biyu"
Kukan yaci gaba dayi sosai, kansa Yana kan Boobs dinta, yayinda hawayen Idonsa suke silalowa zuwa cikin rigarta suna sauka a saman breast dinta
Numfashin tane yake wani irin gudu, gaba daya ya d'aure mata kai, babba dashi Yana kuka, saita ji ta nemi nata hawayen tarasa
Ahankali tadora hannunta akansa, tanaso ta janye masa kansa dake kan qirjinta, amma yaqi Bata Damar hakan, domin kuwa sake riqeta yayi Yana kuka kamar Dan qaramin Yaro
Batada zabin daya wuce taqara bashi hakuri kozai daina wannan kukan, Ahankali tace "Dan Allah kayi hakuri"
Saida yasha kukansa, sannan yayi Shiru, amma kansa Yana nan inda yake
Turo kofar d'akin akayi aka shigo, cikin sauri takai kallonta ga wajan, gabanta ne yafadi ganin Muhsin abokin sa ya shigo, cikin sauri tafara qwace jikinta daga nasa, Saide kuma ta makara, domin kuwa Muhsin yariga ya gansu
Asim kuwa ko a jikinsa, Ahankali ya d'aga, ta cikin sauri kuwa tafice daga d'akin hijabin ta a hannu
Muhsin ne yazauna tare dashi har can dare, sannan yatafi gida, Yana tafiya kuwa Daddy da mamy suka shigo d'akin nasa, alokacin harya sauya kaya zuwa jallabiya zai kwanta, adakin nasa suka zauna gefen gado, shikuma yazauna kansa aqasa, Daddy yace "Asim Iyayen Lubna sunzo sun sameni sunata bani hakuri, meyake faruwa ne kayi mana Bayani"
Be 6oye musu komai ba yafada musu abinda Amina tafada masa, da kuma shawarar da Ishraqa ta bashi, da yanda tasa masa maganin har Widad taci, sannan yaqara da cewa "Daddy saide kuyi hakuri, amma dole zankai Lubna wajan hukuma, dole zatayi musu Bayanin wanda ya sata yin wannan aikin"
Mamy tace "innalillahi wa Inna ilaihirraji'un.... wannan masifa dame tayi kama?bazan hanaka ba Asim, may be ma dasa hannunta acikin mutanan da suke bibiyar rayuwarka, tunda zata iya Sama guba a abinci ai zata hada baki dasu, kakaita koma inane, nayarde maka"
Daddy yace "gaskiya Lubna ta aikata babban kuskure, amma ni a ganina idan aka kaita wajan hukuma ma kamar zubarwa kanmu mutunci ne, ai abun kunya ne ace Asamu irinta acikin zuri'armu, abarta da Allah kawai, zataga yanda makomarta zai kasance, gashi yanzu tayi niyyar kashemin dana, amma al'amarin yajuye yakoma kan 'yarta, kayi hakuri my son, insha Allah zaka samu Yara masu albarka, wanda zasu futo daga tsatson uwa tagari "
Mamy tace"Eto kuma hakane gaskiya, to kayi hakuri Asim"
Shide Asim yarasa gane wanne irin hakuri ne da Daddy, duk lokacin da abu ya sameshi saiyace zai kula da bangaren, kuma daga baya saide abashi hakuri, yanzu wannan dinma gashinan yace yayi hakuri
Daga musu kai yayi kawai, yace "zan kwanta"
Basu qara ce masa komai ba,mamy takashe masa wutar d'akin suka futo
Haka gidan sukaci gaba da zama Shiru, har akai sadakar ukun Widad
Alokacin ne kuma masu buqatar takardar nan turawan Singapore sukai waya zasu zo washe Gari, tashin hankalin da Asim ya shiga, yawuce misali, haka Shima Amjad, Amina da Amrah suna d'akin mamy suna gyara mata,Sai lailaye gadon nan suke, mamy tana kan sallaya tana waya da Daddy daya fita unguwa, Amjad ne yashigo, duk ya Rame yayi wani iri, kwanciya yayi agefen gadon, Amrah ta daka masa wata uwar harara, ta tsani tana gyaran gado azo a kwanta wallahi
Mamy ta Gama wayar ta kalleshi, "Autan mamy, jeka kiramin yayanka"
"magana kuma mamy?"
"Eh jeka turomin shi"
"mamy, yayafa baya cikin nutsuwar sa yanzu, Nima daga wajansa nake, ko magana ma bayason yi, kibari Hankalinsa yad'an dawo saikuyi maganar cikin nutsuwa, may be danyarabu da matarsa ne shiyasa, kuma taqi dawowa, Aida yanzu andawo da'ita, ni dama nagaji da jarabar kishin ta wallahi
, Gara daya saketa, idan besaketa Bama wataran saide kiji na saketa "
Amrah tace"to sannu Daddy"
Mamy ta jinjina kanta "meyasameshi yanzun?"
"mamy akwai wata takarda da mukai missed, kuma mutanan da suke buqatar takardar zasuzo su karba ne, bamu San abinda zamu ce musu ba"
Mamy tace "wacce irin takarda ce wannan?

To kuyi wata mana, da a'ina kuka Barta harta Fadi?"
"mamy wanda yafara rubutawa baya qasar, kuma da tawadar qasaar Germany akayi rubutun, idan muka sauya da namu zasu gane, takardar yaboyeta tare da sauran document dinsa acikin laptop dinsa, kuma yace computer ta 6ata"
Gaban Amina nane ya yanke yafadi, cikin tashin hankali tace "innalillahi..."
Daga nan tafice daga d'akin cikin sauri, gaba dayansu suka bita da kallo
Afalo ta wuce Asim daya shigo gidan yazauna cikin damuwa
Da gudu tashiga dakinsu, a haukace tabude kayanta ta dauko masa computer sa, innalillah kawai take maimaitawa cikin ranta, da yanzu ta cucesu, bayin Allah ashe neman computer suke Bata sani ba
Tana futowa daga d'akin ta ganshi afalon azaune, cikin sauri ta qarasa wajansa tace "Yaya..."
Yana dago kansa, ta miqa masa laptop din, mamaki, faduwar gaba, tsananin murna suka kama Asim, cikin sauri ya karba dawani irin farin ciki Akan fuskar sa yace "Minal... a'ina kika ganta?"
Itama murmushi
tayi masa, tace "kayi hakuri Yaya, dama tana wajena, na manta ne ban bakaba, Sai yanzu naji Yaya Amjad yace ita kuke nema"
Shiru yayi Yana kallonta, murmushin yayi mata kyau sosai, zai Iya cewa wannan ne Karo na biyu dayaga murmushi Akan fuskarta,amma dariya kam bai taba ganin Amina tayi dariya ba, amma farin cikin data sashi yau, Shima yayi alqawarin zaisa ta, saiya nemo mata iyayenta, sannan dole zai ware mata Rana guda yakai ta wajan wasan Yara tayi abinda ranta yakeso
Afili yace "kiramin shi, jeki turomin Amjad din"
Juyawa tayi, ta koma d'akin mamy tana basu labari, ai suna jin abinda take fada musu duk suka dawo falon gaba dayansu, Rabon da mamy taga Asim yadanyi walwala tun mutuwar Widad, amma yau gashi Minal tasa shi, lalle taqara yarda minaal itace farin cikin Asim
Kunna computer yayi, ta kawo komai Yana nan yanda yake kawai keyboard dinta ne suka lalace, Amjad yabawa, yace yaje yadauke musu duk wani abu dayake kanta, yadena ajiye komai da komai Akan computer daga yau
Saide In abun yazama dole
*** ****** ***
Washe Gari Amjad yahau jirgi yakoma Yola,aranar kuwa baqin sukazo suka karbi takarda, hankalin kowa ya kwanta
Asatin
Amjad yadawo Lagos, yayiwa mamy maganar auren sa da Minal, tace masa kawai yaje yaci gaba da shirin biki, aikuwa nan da nan gida ya rikice, Sai siyaiyar kaya mamy take dan'autanta zaiyi aure
*** ****** ***
Muhsin ne ya shigo falon nasa, ganinsa da computer agaba yasa ya jinjina kansa "sannu da aiki abokina"
Saudaya ya kalleshi "sannu da zuwa Muhsin, Bari nasa a kawo ma ruwa"
"a a barshi, gani ga fridge din idan zansha zan dauka"
Asim yace "OK"
Muhsin yayi Shiru Yana saurarensa, yayi tunanin zai ajiye abinda yake yabashi lokaci sudanyi fira ko kadan ce, amma Sai yaga babu alamar hakan
Ajiyar zuciya yayi "amma Asim duk matar da zata aureka Sai tayi hakuri dakai, kullum aiki, Kai baka gajiya da wannan aikin ne?

Office aiki gida aiki, haba, ya kamata ka ragewa kanka wannan aikin"
Murmushi yayi "Muhsin kenan, wanne irin hakuri kuma?

Bagani azaune agida ba, tana ganina"
"to tana ganinka tana ganin photo, kaida photo ai duk daya Asim, yauwa Asim ina wannan yarinyar me manyan idanun nan?"ya qarasa maganar Yana kallon yanayin Asim
"wacce yarinya kenan?"
"wannan qanwar taka, kyakkyawan nan, Yama sunan ta....

Amina ko...

Yawwa Minal"
Annurin fuskarsa ne yadauke, tuni ya kawar da computer tasa gefe guda, ya kalleshi yace "tambayarta kake?"
Muhsin yace "yes, saboda ai Nima kamar qanwa tace, tunda kaima qanwar ka ce"
Jinjina kansa yayi, sannan yace "ta'ina?

Lalle Muhsin kanada kalan dangi dakuma cusa kai, ita Minal dinne harta zama qanwar ka?, to kashiga cikin gidan ka tambayesu, may be tana ciki"
Muhsin yayi murmushi ganin ya kunno abokin nasa, yace "tokai Asim menene na daukar zafi dannace qanwata?

Koka fara Santa ne dakake kishi"
"inrasa dawa zanyi kishi Sai Minal?

Karka manta bayan alaqar datasa na kawota gidannan, ina ganinta yarinya qarama, wadda inda ace nayi aure da wuri zan haifi kamarta"
Zaro ido Muhsin yayi, "yanzu Asim Minal din zaka Haifa?

Lalle bakada mutunci, kuma Kai qaramin Dan renin hankali ne, Malam dama na tambayeka ne domin na gwada ka Akaro na biyu Inga kana sonta ko baka sonta, kasan ita yarinya qarama ce wadda zaka haifi kamarta amma ahakan kake liqe mata, kana yiwa yarinyar mutane wayo kana jin dumin qirjinta,
Nan nazo nasameka d'ame d'ame Akan qirjinta kana wani kuka saikace qaramin Yaro, kagama jin tudun qirjin yarinya kazo kana huramin hanci kai baka sonta, to qinta kake?

"
Wani malalacin murmushi yayi" Muhsin kenan, wato kana bani mamaki wani lokacin, daka ganni Akan qirjin nata saime?

Dama de kawai kacemin zuwa kayi Kamin hayaniya saboda rannan kazo kaganmu a haka, todana kwanta Akan qirjin nata cemaka akai wani abu naji?

"
Muhsin ya Girgiza kansa" a a, ina zakaji wani abu kuwa, kaida kake waliyi, Nima bance kaji komai ba, amma ina baka shawara, ka gaggauta auren yarinyar nan, idan Bahaka ba duk lokacin da Amjad ya aureta wataran zaka aikata wa matar qaninka abun kunya "
Ransa ne yabaci sosai, ya saka hannu ya dafe kansa
" Muhsin waye yafada ma zan iya auren Minal?

Tayaya zankai kaina ga mutuwa?

Bayan rasuwar mahaifina banqara jin tsoron mutuwa ba Sai da widad tatafi, da hankali na da komai tayaya zankai kaina cikin rijiya?
Chapter 25 · 0% Book details