Sashe 28
Insaaf Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ko akwai abinda ya faru?"
"akwai Alhaji, babba ma kuwa, Asim ne yayiwa yarinyar maganar auren, saitake fada masa ai tun kafin suzo nan akwai Malamin daya daura musu aure"
Cikin sauri ya kalleta yace "tanan ta 6ullo kenan"
"bangane ba Alhaji kamar Yaya tanan ta 6ullo?"
Gyara zamansa yayi yace "Hajiya, kifita daga sabgar yarinyar nan, nagama lura da'ita kawai kwadayin kudi da son abun duniya ne yakawo ta gidan nan, da zata auri Amjad, tadawo tace Asim mijinta ne bayan tagama gane sirrin gidan tagano Asim ne me kudi, toni ban yarda da wannan batu ba, tayaya babu sheda babu komai haka kawai zan dauki Yarona inbata?
Taje ta kawo min mutumin daya daura auren, idan naji daga bakinsa zan iya yarda, idan hakan ne zansa Asim din yasaketa ta tattara kayanta tabar mana gida "
Mamy ta kalleshi cikin damuwa tace"Alhaji kayi hakuri mana, nifa na yarda da maganar Minal, alhaji ba zatayi qarya ba, tanada hankali"
"Mezai Hana kice haka tunda kece kika haifeta?
Nace mezai Hana kice haka?
Tunda itada Amrah duk daya kike ganinsu, Toni nagama magana, tashi kifice kibar min nan"
Babu musu mamy tatashi tafuto, falo ta zauna tarasa yanda zatayi, tayaya Alhaji zaice araba aure?
Asim yanason yarinyar nan, ita uwa ce tanason farin cikin danta, tasan cewa Minal itace farin cikin Asim, agaba zasuji Dadin zama da juna bayan soyaiya tagama wanzuwa atsakanin su,
Kanta ne ya kulle, takira Aminiyarta, tafada mata komai, nan da nan qawarta tabata shawara takira Babban abokin Daddy tasanar dashi, insha Allah zaisashi ya janye wannan maganar
Suna kashe waya mamy takira Alhaji Umar babban abokin Daddy, Alhaji Umar ransa yabaci sosai, yace taje ta kaiwa Daddy wayar, zaiyi magana dashi, idan yaqi karba kuma tarabu dashi zaizo gidan da kansa anjima
Mamy tayi masa godia ta kashe wayar, sannan ta nufi d'akin Daddy
Kasancewar abude tabar kofar lokacin da zata futo baiji alamun shigowarta ba, Yana tsaye yajuya bayansa, yabawa kofar baya, yayinda yake kallon window din d'akin
Magana yake yi cikin fishi, gaba daya Idonsa yarufe, cike da tsananin bacin rai yake fadin "Zan koreta yanzu yanzun nan, ni yarinyar nan tun lokacin dana ganta naji na tsaneta, kuzama cikin shiri zan koreta daga gidana yanzu tana futowa ku kashe ta
, duk itace Sanadin lalacewar komai, karka manta itace Sanadin barin Lubna daga cikin gidan nan, tayaya nida nakeso dukiyar sa data Insaaf duk sudawo hannu na zatazo ta hargitsa min komai?Akan kudi zan iya yin komai, sauran dukiyar gadonsu ina sane nahanasu,Dan haka sauran wadda take hannunsa ma zanyi kokari na qwace ta, Yaron ne akwai shegiyar basira shiyasa abin ya gagara, shikuma Amjad ta riga ta shanye shi bare nahada baki dashi, saboda haka ku kula, tana futowa agama da'ita, Shima Asim din Yana dawowa babu abinda zan jira, zan kashe shi.....
Yauwa saboda.....
"
Bata iya tsayawa tagama jin komai ba, jiri yafara daukan ta, haka tafara ganinsa bibbiyu, daga nan komaai na d'akin yafara rabewa a'idonta Yana zama guda biyu
Daqyar ta'iya daga qafarta tafuto daga cikin d'akin batare daya lura da'itaba
Ikon Allah ne kawai ya kaita dakinta lafiya, tana zuwa kuwa duhu ya mamaye idonta, tafadi a qasan tiles din d'akin
Amrah datake zaune tana kallo a system dinta cikin sauri ta diro daga kan gadon ta cicimeta tana kiran sunan ta "mamy...., mamy meyake faruwa?"
Kuka tafara tana jijjigata, ganin kamar mamy ta suma ne yasa tatashi Dasauri ta kawo ruwa ta yayyafa mata, cikin ikon Allah kuwa tafarka, tana Bude idonta tace "Amrah, tashi kikira Minal ku hada mana kayan mu, zamu bar gidan nan"
Gaban Amrah yafadi,kuka ne ya qwace mata, koma menene tasan cewa akwai damuwa mai girma, tace "mamy meyake faruwa?
Meya sameki Dan Allah, kifadamin"
Jikinta ne ya dauki rawa, tace "nace ki tashi kikirata"
Amrah tatashi tayi dakinsu cikin sauri domin kiran Amina, mamy tana ganin fitar Amrah tafashe dawani irin kuka mai cin rai, sosai take kuka banda kanta dake mata wani irin ciwo, afili tafara furta kalmar "innalillahi wa Inna ilaihirraji'un"
Wayarta ta dauka takirashi, bugun farko ya amsa yace "Mamy nah"
Cikin dauriya Dan kada ya gane halin datake ciki tace "Asim kana ina?"
"ina Airport mamy, mungama komai, Ana sanarwa ma a shiga ciki"
Kasa riqe kukanta tayi, cikin gunjin kuka tace "Asim kadawo...."
"innalillahi..., mamy kuka kuma?
Meya sameki?
Meyasa kike kuka kifadamin waye ya6ata miki rai?"
Tausayinsa ya kama mamy, cikin kuka tace "Asim nacema kadawo gida yanzu yanzu, akwai matsala"
Sharhi
Sharhi
Sharhi
Amnah El yaqoub
[2/17, 10:45 PM] El~Yaqoub: INSAAF
Writing by:Amnah El~Yaqoub
29&30
Like my page on Facebook
https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493
Wayar yakashe cike da tashin hankali, direban daya kawo shi Airport din yayiwa magana kawai suka juya
Gaba daya hankalin sa ya tashi, menene zaisa mamy kuka?
Tabbas akwai abinda yake faruwa agida, koma menene ya tabbatar ba qaramin abu bane, tunda har ta'iya cewa yafasa wannan tafiyar yadawo gida.
Suna hanyar komawa gidan yadubi direban yace "kayi sauri mana"
Cikeda ladabi yace "to Yallabai"
Gudu yaqara amma Asim Sai yake ganin kamar ma basa tafiya, wayar sa yad'auka yakira Amjad, bugun farko yad'auka tare da sallama
"Amjad kaje gida yanzu yanzu, ina tunanin akwai abinda yake damun mamy"
Cikin mamaki yace "Mamy kuma?
Naga lafiya muka Barta agida, meyasa meta?"
"nacema kaje gida, Nima gani nan zuwa"
Yana fada masa haka yakashe wayar yanajan qaramin tsaki
Sun kusa zuwa gidan kenan, Ishraqa ta ki rashi "Asim baku tashi bane har yanzu?"
"bamu tashi ba Ishraqa, Aina fasa ma nadawo gida, zanyi waya office sutura wani ya wakilceni"
"Meyake faruwa kadawo, lafiya kake deko?"
"no, Ishraqa mamy ta kirani tana kuka tace nadawo gida bansan menene yake faruwa ba, bansani ba ko wani abun ne ya faru da Minal ko Amrah"
"kagani ko, aikaga abinda nake fad'ama ko, Asim nafadama kakori yarinyar nan daga gidan ka, zata rusa muku gida, na tabbatar yanzu ma itace Sanadin komai, idan an tabaka kace ai tausayinta kake, to akwai lokacin da za'azo Kaine zaka zama abin tausayi ba'ita ba, tayaya zaka dauko yarinyar da zata zo ta rusa muku farin cikinku...?"
Dan qaramin tsaki kawai taja, takashe wayar Tata Cikeda bacin rai
El-Hameed yadubeta yace"meyake faruwa ne Habibty?"
"Nida Asim ne, Wai yafasa tafiya malesia, mamy takirashi tana kuka Wai yadawo gida akwai matsala"
El-Hameed yace "subhanallah kuka kuma?
Kinga tashi, tashi kishirya muje gidan, ai bekamata mu zauna ba"
Tashi tayi tashige dakinta domin shiryawa, baqar abaya ta sanya, Sai dankwalin abayar data Yafa , saita koma kamar wata yar shekara talatin
*** ****** ***
Tana gama waya da Asim tanemi 'yan sanda, cikin tsananin damuwa tace su hanzarta suzo gidan
Nan da nan kuwa 'yan sanda suka shigo Mota suka nufo gidan
Direban Yana tsayawa a compound yabude motar yafuto, ko rufe motar beyiba yashiga cikin gidan dad'an saurin sa
Kai tsaye dakinta yashiga yaga tana janyo kayanta daga cikin wardrobe tana lodasu Akan gado
Har zuwa lokacin kuka take saide bame qara ba, kawai share hawaye take kamar ba'ita ba
Yanda ya banko kofar ya shigo d'akin ko sallama babu hakan ne zai nunama cewa Hankalinsa atashe yake
Wajanta ya nufa yariqe kafadunta, cike da tashin hankali yace "Mamy..., meyake faruwa ne?menene yasamu yaran?
Ko kece akayi miki wani abu, mamy kifadamin mana"
Kukanta ne ya tsananta, sosai take kuka harda shashsheka, tasa tafukan hannunta biyu ta rufe fuskarta, hannunsa yasa ya janye nata hannun, gabansa Yana faduwa sosai, yanzu kam ya tabbatar wanine yamutu kawai, jikinsa ne yayi sanyi yace "Mamy...."
Dago kanta tayi ta kalleshi, tsananin tausayinsa ya kamata,tsawon wannan shekarun Yana Fama da tashin hankali, kullum Yana cikin fargabar fita, idan yayi tafiya me Nisa Sai ansan yanda akai aka shirya masa wata maqarqashiyar, ashe Daddy ne, wacce irin rayuwa ce wannan ace qanin ubanka uwa daya uba daya shine yake nema ya kasheka da hannunsa saboda son abin duniya?
Ahankali tasa hannunta tarike fuskar sa dashi, Allah abin godia, Allah yaqara Kare mata danta
jikinsa tafada tana cigaba da kuka,bayan ta yafara bubbugawa yace "kiyi Shiru mamy"
Ahankali tasa hannu ta share hawayen nata, sannan ta janye jikinta daga nasa Tana cewa "kadawo?"
Bebata amsa ba Sa
i wata tambayar daya sake jefo mata "meyake faruwa mamy, waye yamutu?"
"babu komai Asim, kaje ka hada kayanka gidannan zamu Bari"
Cikin sauri yace "barin gida kuma mamy?
Meyake faruwa ne Wai?"
"nacema kaje ka hada kayanka, bazamu Ci gaba da zama anan ba, inason rayuwarka, inaso ka rayu tare dani"
Zama yayi a gefen gadon Yana cewa "hasbunallahu wa ni'imal wakeel
Amjad ne yashigo d'akin cike da damuwa, Yana zuwa ko kula Asim beyi ba yanufeta,gabansa banda faduwa babu abinda yake, tsawon rayuwar sa da mamy shide ze'iya cewa betaba ganinta tana kuka ba, saide in suna Yara, amma da hankalin su de betaba ganiba, hannunta ya kama yariqe yace "mamy meyake damunki?
Yaya yacemin kina kuka, mamy waye yasaki kuka?"
Hannunta ta fizge daga cikin nasa, tayi banza da qyaleshi, be daddara ba yasake kamo hannunta, kafin yayi mata magana ta daka masa wata irin tsawa "banason nacin banza da wofi ka qyaleni dallah!!!"
Cikin sauri Asim dayake zaune agefe gado ya kalleta
Meyake damun mamy ne?
Yau mamy ce takewa Amjad tsawa?
Yaron da ko kadan batason ganin damuwar sa?
Ahankali yafara ja da baya haryazo jikin bangon Dakin ya tsaya Yana kallonta cike da mamaki, zuciyarsa banda bugawa babu abinda take, gaba daya jikinsa yayi sanyi, me yayiwa mamy tayi masa irin wannan tsawar?
Kode shine yabata mata ranta?
Qwalla ce takawo cikin idanunsa, Ahankali yasa ka hannu ya share, Yana kallonta, amma kwata kwata mamy taqi ta kalli inda yake ma
Asim yatashi ya qarasa wajansa zai lallasheshi, cikin sauri tace "Asim idan kaje wajan Yaron nan sai ranka yabaci"
Gaban Asim yayi mugun faduwa, idanunsa harya fara sauya kala cikin tsananin damuwa yace "mamy Wai meyake faruwa ne?