Sashe 5
Insaaf Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"
"wacce irin magana kike wannan Larai, Amina fa ta dauki Ammar ne a matsayin yayanta"
"hakane Malam, amma tasan cewa akwai aure atsakanin su, tunda munfada mata cewa shidin kamar d'an ruqo ne awajan mu"
Saida baba yayi jimmm sannan yace "eto hakanma shawara ce mai kyau, saboda a cikin Garin nan namu de babu wanda zai qara futowa yace zai auri Amina, kuma Amina bazataci gaba da zama haka agabanmu babu aure ba, dole zata tafi Dakin mijinta, idan a kayi auren kawai saina saida gidanmu mubar Garin, Larai kin kawo shawara mai kyau, hakan za'ayi "
Suna shiga Dakin tayi tozali da kyakkyawar fuskarsa data sake yin haske sosai, Yana kwance Yana bacci, ansaka masa robar qarin ruwa, zama tayi Akan kujera ta dubi yayan nata tace"Yaya ai kamar ma bacci yake "
" bacci yake qanwata, tunda muka kawo shi sau daya yafarka, daga Naan kuma baisake farkawa ba, amma sunce zai Iya tashi daga nan zuwa Gobe ko jibi "
Batace masa komai ba illa idanu data zuba masa, idan ta kalli farar fatarsa saita kalli Tata fatar, bakomai ne yake Bata mamaki akansa ba Sai gashin idonsa kamar na mace, haka taita kallansa ita kad'ai tana mamakin baiwar kyau da ubangiji yayi masa
Su Inna ne suka shigo itada baba, kana ganin fuskar su zaka hango tsantsar farin cikin da suke ciki, Inna ma tadubashi tayi masa Addu'ah sannan sukai shirin tafiya gida
Saida suka qara sati biyu a asbiti sannan aka sallamesu, ahakan ma shine ya matsa saboda yasan cewa tabbas 'yan gida suna nemansa, especially Mamy
Amina tana share tsakar gidansu suka shigo shida baba da Yaya Ammar, Ammar ne yake riqe dashi duk da Yana d'an daurewa Akan sauran ciwon da wajan yake masa saida ya gaza, yadawo Yana rintse idonsa
Tsintsiyar hannunta tayar tataresu da gudu tana musu sannu da zuwa, kallo daya ta yiwa baqon nasu, Yana sanye cikin suit dinsa wadda suka tsinceshi da'ita, amma jacket din nasa tana hannun Yaya Ammar , Sai ta cikin kawai white color tadubeshi cikin zazzakar muryarta tace "sannu"
Batare daya kalleta ba ya daga mata kansa kawai, Sai runtse ido yake, daga wannan Bata sake yimasa magana ba tajuya, cikin ranta tana fadin wannan daga gani bashida juriya (
Inna tace "Ammar qarasa dashi dakinka, akawo muku abinci"
Yace "to Inna" ya kama hannun Asim yace "muje abokina"
Ahankali yajuyo domin ganin mamallakiyar wannan zazza
kar muryar,Yana juyawa kuwa yayi tozali da dogon gashin kanta, tsananin mamaki ya kama shi, wannan qanqanuwar yarinyar ce harta mallaki wannan uban gashin?
To Amma shi fuskarta yaso gani, dagowa tayi zata zubar da sharar data Gama, cikin sauri ya janye fuskar sa daga kallanta
Suna shiga Dakin Ammar yanuna masa kan katifarsa yace "abokina ga wajan zama"
Daga masa kai yayi batare da yayi magana ba, Ammar ya dauki buta ya futo zai shiga bandaki, cikin ransa Yana mamakin wannan bawan Allah, ace mutum babu magana saide Shiru haka da d'aga kai kamar qadangare (
Fillo yad'auka yakarashi ajikin bangon Dakin sannan yazauna ya jingina ahankali Yana qarewa d'akin kallo,Ahankali ya lumshe Idonsa Yana tunanin mahafiyarsa, ko a wanne hali take yanzu?
Amjad....
Sunan Yana Fado masa ya runtse Idonsa saboda tuno yanda suka rabu da Yaron, koshi ma sun kashe shi?
Dole yatafi gida, akwai matsala idan yaci gaba da zama anan, to Amma kuma Anya ba zaiyi hakuri yazauna anan garinba?
Saboda mutanan da suke bibiyar rayuwar sa bazasu qyaleshi ba muddin su kasan yana Raye, to Amma Mamy fa?
A wanne hali take ciki...?waye yake son ganin bayan sa?
Waye?
Waye shi?
Babbar damuwar Sama itace laptop dinsa dabai san inda takeba, haqiqa Amjad yayi gaskiya dayace akwai kuskure wajan Dora komai a cikin wannan laptop din
"Salamu Alaikum"
Zazzaqar muryarta tadaki dodon kunnansa, batare daya Bude Idonsa ba, ya amsa mata, kallon ta takai gareshi taga Idonsa a lumshe, Sai gashin Idonsa dasuka kwanta wanda ya sake qawata masa kyakkyawar fuskarsa
Ahankali ta dauke kanta daga gareshi tabude kwanon abincin data kawu musu tafara zubawa, taliya ce jalop, amma ta hausa, d'ago kanta tayi tanaso tace masa ga abinci amma kuma lokaci daya yayi mata kwarjini, shidin daga ganinsa kasan cewa babban mutum ne, sallama ma bata samu matsayin daya Bude ido ya amsa mata ba inaga maganar abinci?
Duk yanda akai da alama Yana cikin dumbin damuwa, ashe a duniya akwai mutane masu damuwa kamar ita?
Matsalarta babbar matsala ce, damuwar ta babbar damuwa ce da har tasa take ganin kamar tafi kowa shiga cikin damuwa
"ga Abinci inji Inna" maganar ta tasake fadowa cikin kunnansa, Ahankali yake Bude Idonsa harya budesu fes a kanta, bece mata uffan ba yafara kokarin tashi zaune, Garin gyara zama yadan bige kafadarsa me ciwo da jikin bangon Dakin, cikin sauri yace "Washh"
Kallansa tayi da sauri takai hannu zata taroshi Sai kuma tafasa ta tsaya cak, ta tashi ta sauri tafuto daga Dakin tana Kiran Inna
Inna ta qaraso taga Yana runtse ido tace "Meyake faruwa ne bawan Allah ko jikinne?"
Tana daga bayan Inna tace "Inna Fama ciwonsa yayi"
Inna ta kalleshi cike da tausayi tace masa "sannu"
Ahankali yace mata "yauwa" sannan yazauna ya dauki spoon zai fara cin abincin
Inna ta karbi cokalin tace "kawo nabaka bawan Allah, idan Ammar bashida lafiya ninake bashi abinci dakaina"
Beyi mata musu ba yasakar mata cokalin tafara bashi, Amina tana tsaye ta rungume hannun ta aqirji, tana kallonsu, bakinsa ta kalla d'an qarami kuma ja, gashi cokalin nasu irin me nauyin nan ne wani kwafd'ed'e me fad'i (
Abincin datake bashi kadai shine yatuno masa da mahafiyarsa, Allah sarki mamy...., yasan cewa duk inda hankalin ta yake a yanzu yakai maqura wajan tashi
Baba ne ya qwalawa Inna Kira, ta amsa masa sannan ta kalli Amina tace "zoki bashi abinci Amina, kiyi ahankali"
"to Inna" cewar Amina data matso wajan ta zauna
Inna tafita daga Dakin, Shima ya dauki ruwa yasha Yana mamakin wannan jaririyar da'akace tabashi abinci (
Ita kuwa zuciyarta d'aya tadebo abincin zata bashi, amma saiya daga mata hannu, (
itama batace masa komai ba tamaida spoon din cikin kwanon, sannan tarufe abincin tatashi tafuto daga Dakin
Acan Dakin baba kuwa su Inna sungama magana da Yaya Ammar Akan Akan zasu hadashi aure da qanwar sa, kasancewar yasan cewa akwai aure atsakanin su shiyasa koda wasa baiyi musu ba, ya amince da buqatar su
Ita kuwa Amina Batasan abinda ake ba kawai daga Dakin Yaya Ammar data futo kai tsaye dakinta tawuce, suma suna Gama tasu maganar suka wuce Dakin Ammar din gaba dayansu
Asim Yana ganin shigowarsu yaji dadi, bayan sun zauna baba yafara magana dashi "bawan Allah mude bamusan daga inda kakeba, kuma acan asbiti ma bamuyi wannan maganar dakai ba,nide sunana Abubakar amma Ana kirana da Buba awannan qauyen, wannan danane Ammar, dakuma matata larai, 'Yata Amina itace ta tsinceka a bakin Rafi taje Debo ruwa, tazo gida da gudu tasanar damu, d'ana Ammar shine yabani shawarar a kaika asbiti, kuma Alhamdulillahi yanzu kaji sauqi, muna so katashi muje gaban maigari kayi mana Bayanin daga inda kake "
Ajiyar zuciya yasauke bayan yagama jin Bayanin su,Ahankali yafara magana"Baba sunana Asim...."
Sai kuma yayi Shiru daga nan, su baba suka zuba masa ido suna kallansa, tabbas wannan daga ganinsa kasan Yana dauke da damuwa, to Amma babu Dadi bakasan mutum ba kawai kafara yimasa tambayar dabata daceba, danhaka baba yayi Shiru, Inna tace"muna jinka Hasim..." (
"bafa Hasim ba Inna, Asim,ake cewa"
cewar Ammar
Shide Yana jinsu bece dasu komai ba, Ahankali yaci gaba da cewa "Agarin Lagos nake, iyayena da 'yan'uwana duk suna can, Dan Allah baba kubar maganar zuwa wajan maigari, inaso kumin alfarma natafi gida gobe, nasan Hankalinsu atashe yake"
Baba yayi murmushi yace "To madallah, haka akeso, amma bazaka tafi Gobe ba, kabari Sai jibi, Gobe zanyi auren 'Yata Amina tareda Ammar"
Mamaki ya kama Asim, aure kuma?
Wannan qanqanuwar yarinyar zasuyi wa aure?
Bece da baba komai ba Sai "Allah yakaimu jibin"
Washe Gari da sassafe aka daurawa Amina aure da yayan nata, akofar gidan maigari, wannan qauye kuwa Shiru kakeji anyi tsit kowa Yana jiran mummunan labari a cikin wannan satin, ango Ammar kuwa yasa sabon kaya Sai qyalli yake Yana walwali, baba yakira Amina har daki yayi mata Bayanin komai, lokaci daya ta rushe musu da kuka tace Bata yardaba, Bata so tarasa yayanta, Bata so yamutu yabarta, amma haka su baba suka daddage sukai mata nasiha mai ratsa jiki, musanman Inna ta mafi baba dagewa Akan Amina tayi hakuri ta rungumi aurenta
Baba yace tatashi taje ta fitar da kayan dakinta za'a gyara musu shi su zauna aciki, kafin baqo yatafi su koma Dakin Ammar din
Haka tafuto idanunta jajir Tasha kuka, dama d'akin bawani kayan kirki ne aciki ba, daga katifa Sai bakkon kayan ta, dakuma wani kwando Dan qarami na kayan kwalliya.
Bakkon tafara dauka taji nauyi, sai tatuna da laptop din baqonsu datake ciki, tafitar da'ita tsakar gida, a lokacin Asim ya futo alwala tajuya ta kalleshi, Shima ya kalleta, idanunsu yahadu dana juna, cikin sauri kowa yadauke kansa, Yana alwala Yana d'an satar kallon ta, mamaki yake menene yasa ta kuka?
Sake satar kallonta yayi Yana tunanin ina wani girma awajan wannan yarinyar dazasu yimata aure?