← Book details Insaaf Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 53

Sashe 23

Insaaf Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wallahi idan tana nanma yimata zanyi, muyi wasa tare, muyi fira tare, mu shirya muyi kwalliya muje unguwa mudawo, idan tahadu da saurayi injirata tagama tazo mutafi, mudawo gida in sata agaba muyi bacci, nifa kaga Asim iyayena basu tsananta minba, Nima bazan matsawa yata ba, wani matsin Idan yayiwa Yaro yawa masifa yake janyowa, Saikaga qawayenta suna hure mata kunne daga gefe, a lalata ma tarbiyar daka Dade kana dora yaronka akai, bansan me zatai a bayan Idona ba, Gara najata a jikina tazama qawata, zatafi sakewa dani ta dinga sanar dani damuwar ta fiyeda qawayenta"
"zaki sata agaba ki kwanta tare da'ita, toshi kuma mijin naki fa?"
"shima ban Hana shi ba Asim, yazo mu kwanta wallahi"
Kansa ya Girgiza "Lalle Ishraqa soyaiyar taki kuma tazama tafitar haiyaci, idan kun fita saurayi yatareta zaki tsaya agefe kijirata, kundawo gidan ma bazaki bar yarinya tasake tahuta ba, saurayinta ya kirata awaya suyi waya, bazaki Bata Damar hakan ba Shima kina tare da'ita, no, kibar yarinya tasake mana "
" eh lalle Asim na lura idan Insaaf tana nanma Kaine zaka dinga hure mata kunne takula Samari
Koda yake ai babu damuwa ma tunda Kaine saurayin "
Annurin fuskarsa ne ya sauya lokaci daya, Dan qaramin tsaki yaja ya miqe tsaye zai tafi, wayar sa ce tafara qara yad'auka "Amjad"
Daga dayan bangaren Amjad yace "na'am Yaya, Yaya akwai matsala fa, baqin nan dazasu zo daga Singapore sunyo waya, kuma idan sukazo zasu tafi da wannan takardar dakukai zama dasu Akan ta ne, Allah yasa de kayi printing dinta"
Kansa ne yasara, Ahankali yasamu gefen gadon yazauna, Ishraqa na ganin haka itama ta zauna tana fuskantar sa, cikin tsananin damuwa yace "wallahi Amjad takardar nan Bata nan, bancireta daga cikin computer ba"
Amjad yace "yasalam, yanzu Yaya ya zamuyi?"
"wallahi bansaniba Amjad" Yana fadar haka ya kashe wayar Yana furta kalmar innalillahi wa Inna ilaihirraji'un
"meyake faruwa Asim?"
"Ishraqa abubuwa sunyi min yawa,bansan... bansan...

Yaya zanyi ba" ya qarasa maganar ararrabe cikin damuwa
Wani irin tausayinsa ya kama Ishraqa, jikinta yayi sanyi tace "meyake faruwa ne?"
"akwai mutanan dazasu zo daga Singapore ne, zasu karbi takarda awajan Amjad, zasuyi sign, to tana cikin computer nan data 6ata"
Cikin nutsuwa tace "Asim"
Kasa amsawa yayi,kawai juyo wa yayi ya kalleta batare dayace komai ba, cikin sanyin murya tace "Insha Allah, Allah Yana tare dakai, ka kwantar da hankalinka, muyi Addu'ah komai zaizo cikin sauqi insha Allah"
Daga kansa yayi cike da damuwa yace "nagode" daga nan ya tashi yafi ce cikin tashin hankali
Tsawon kwana biyu Asim ya dauka Yana cikin tashin hankali, yarasa wazai fadawa, jiyake dazai tariyo baya da yayi, jiyake inama ace bai tafi da wannan computer ba, inama ace yabi shawarar Amjad bai dora komai akai ba, tashin hankalin dayake ciki ne yasa ya manta da maganar makarantar Amina, abinci ma baya'iyaci sosai, idan yazauna saide yayi Shiru Yana tunani, babu wanda yayi tunanin Yana cikin damuwa ne saboda dama haka yake ba magana yake ba,acan 6angaren Amjad ma Yana can Yana nasa tunanin yanda za'ai su samu mafita
Zaune suke adaki Amrah tana koya mata daurin dankwali, bayan sun Gama tace "nikam Minal Yaya maganar school dinki ne?"
"har yanzu Yaya bece komai ba Anty Amrah"
"toke meyasa bazaki masa magana ba?

Kije ki sameshi yayi miki lesson dinki, idan kun Gama saikiyi masa maganar karatun"
Littafin ta tadauka tace "tona tafi"
Wannan Karon babu alamun tsoro a tattare da'ita tanufi falonsa, Addu'arta daya Allah yasa baya tare da wannan jarababbiyar matar tasa
Tana budewa kuwa ta ganshi azaune a falon yariqe kansa da hannayensa duka biyu kamar me ciwon kai
Shikuwa Asim tunani yake sosai, baisanma ta shigo falonba, tunani yake kode zaibi jirgi ne yakoma qauyensu Minal ya tambayi su baba ko sunga computer dinsa?

Wata zuciyar tace masa to ai kuma suma sun bar Garin, maigari ya koresu
"Innalillahi wa inna ilaihirraji'un" , ya maimaita hakan a ransa
Ahankali ta qaraso wajansa ta tsugunna, tace "Yaya"
Amma bai dago ba,hannunta ta daga ahankali zata ta6ashi,
a Karo na biyu tasake cewa "bakada lafiya ne?"
Cikin sauri ya dago kansa sukai ido biyu, ganin hannunta yayi dab dashi kamar tanason tabashi, yabi hannun nata da kallo Yana mamakin meyasa Bata tsoron ta6ashi wani lokacin?

Sai kuma yayi tunanin cewa ai yarinya ce, sannan Kuma babu wanda yake kusa da'ita a gidan Sama dashi, may be tana ganinsa ne kamar yayanta
Itace tafara dauke idonta daga cikin nasa, tace "Yaya lesson nazo"
Girgiza kansa yayi, cikin damuwa yace " ba yanzu ba,kitashi kitafi"
Furucinsa ne ya tabbatar mata da Yana cikin damuwa, kokuma ba kalau yake ba, duk da dama amsar tasa haka take ba yawa ba dadi
Gabanta ne yafara faduwa ahankali tace "bakada lafiya ne?"
Bebata amsa ba, kansa kawai ya Girgiza mata,kallonsa tayi tasake cewa "kayi hakuri" sannan ta tashi tafice, bayan ta yabi da kallo, saida yaga fitar ta sannan ya maida kansa cikin tafukan hannunsa
Batafi minti goma da fitaba Lubna ta shigo falon nasa da wata takarda a hannunta, akan hannunta kujerar dayake zaune ta zauna, fuskarta fal take da kwalliya, tace "Daddyn Widad inaso zanyi oder wasu kayan kwalliya ne daga Dubai, shine nakesan dubu dari biyu"
Dago kansa yayi ya kalleta, tunda safe yake cikin wannan halin amma Bata tambayeshi menene yake damunsa ba, yarinya qarama yanzu ta tashi daga wajan amma saida tayi masa wannan tambayar, Anya kuwa har yanzu Lubna tana sonsa kamar da?

To kode gaskiyar Minal dinne da tace Lubna tanaso ta kashe shi?

Kai tsaye yace mata "Bandashi"
Bude baki tayi cike da mamaki "bakada shifa kace?

Kawai de kace bakada niyyar bani, amma bawai bakada shi ba"
Cikin bacin rai yace "Wai Lubna meyake damunki ne?

Meyasa bakida hankali da tunani wani lokacin?"
"dakata Asim, Dan nazo wajanka neman kudi ba shine zai baka Damar dazaka dinga cimin mutunci ba"
"OK, haka kikace?

Yanzu ke bakiga halinda nake ciki ba zakizo haka ko ladabi babu kimin maganar kudi?"
"kawai kace Lubna banda niyyar baki kudi, bazan bayarba, amma ba maganar wani hali dakake ciki ba, ni bakaga halin danake ciki ba?"
"fice kibarmin falon nan please"
"basai ka fadaba" tana fadin haka tafice daga falon, Kai tsaye dakinta tashige tana cizon yatsa,bacin rai fal ranta, magana tafara afili, "ni Asim zaiwa haka akan dubu dari biyu?

Zaiga abinda zai biyo baya kuwa"
Tana fadar haka tatashi ta dauko maganin datace tafasa saka masa a abinci, ta kalli maganin tace "Gara ayita ta qare, inma ka kwanta jinyar zan iya qarawa gaba, Lubnan da kasani Bata yanzu ba"
kitchen tashiga tahada masa jallop din taliya, girkin ya tsaru, yaji nama manya manya aciki, saida tazuba maganin aciki, sannan tajuya tasake Juyawa yanda zai hade jikin abincin, ta dauko flet mai kyau, tajuye abinci duka aciki, sannan tawuce tafuto falo, anan taci Karo dashi da mamy azaune a falon, da alama akwai maganar dayake mata,falonsa takai abincin sannan tadawo wajan su, tsugunnawa tayi aqasa, cikin ladabi tayi masa magana "Daddyn Widad na kaima abinci, nasan kana jin yunwa"
Kallanta yayi, yaga kamar ba'ita ce tagama yimasa rashin kunya ba, amma yanzu harda tsugunnawa a gabansa, yace "no, kibarshi"
Mamy tace "a a, haba Asim, yazatasha wahala tayi ma girki kaqi Ci?

Kaje Kaci, Nima zanje daki nayi wanka"
Daga kansa yayi, sannan ya nufi dakinsa, Lubna tasaki wani matsiyacin murmushi tawuce nata d'akin
Yana shiga falon ya kalli abincin, gaba daya shaf ya manta da maganar Amina, uwa uba abokiyar shawarar sa Ishraqa tabashi shawara cewa Minal qarya take, hakan yasa ya shiga dakinsa zai wanke hannunsa
Yana shiga d'akin widad tafado cikin falon tana qwala masa Kira, "Daddy yau ni a wajanka zan zauna muyi wasa"
Ko sauraren amsar sa bayiba, tasaka hannu acikin jallop din taliyar nan tafara Ci
Sosai takecin abincin,tashi tayi ta kunna kayan kallon falon, tadawo ta zauna tanaci tana kallo, yatsina fuska tayi, saboda yanda taji cikinta ya murda, lokaci daya ta qwalla qarar dayaja hankalin 'yan gidan gaba daya, aguje Asim yafuto daga cikin d'akin, Yana zuwa falon yaga Widad a kwance wani irin kumfa Yana fita daga bakinta
Gabansa ne yayi mugun faduwa,lokaci daya maganar Amina ta Fado masa ((Dan Allah Yaya karka sakecin abincin da Anty Lubna zata baka, wannan shine abinda nakeso nafadama, amma fa Amana))
Amrah da Amina gaba daya jikinsu rawa yake, tuni hawaye ya wankewa Amina fuska
Cikin sauri yayi kanta Yana jijjigata, kamar wani zararre haka yakoma "Widad!

Widad!!"
Dayqar tabude bakinta tace "Da... ddy..."
Lubna ce ta shigo d'akin da gudu, tana ganin halinda Widad take ciki, ta yanke jiki ta Fadi sumanmiya
Mamy ce kawai mai qarfin halin Kiran driver, cikin sauri kuwa Asim yashiga suka nufi asbiti, Amrah da Amina kuma suka kinkimo Anty Lubna suma suka bisu abaya
Gaba dayansu atsaye suke sunyi cirko cirko suna jiraan futowar likitocin da suke duba Widad, tsawon minti talatin aka dauka, suna tunanin zasu futo amma shiru, har Anty Lubna ta farfado anyi mata qarin ruwa ta fixgeshi tafuto, Sai kuka take kamar ranta zai fita
Mamy tana gefe daya atsaye tana salati, Amina da Amrah kuwa kowa hawaye yake, Asim kuwa ko kallon inda Lubna take baiyi ba
Kusan awarsu daya da wani abu suka futo, doctor ya kallesu yace "saide kuyi hakuri Yallabai, munyi iya bakin kokarin mu, amma hakan Bata samu ba, Allah yayi mata rasuwa"
Wani irin sarawa kansa yayi kamar an Doka masa guduma, lokaci daya ya sulale yazauna awajan Yana ambaton kalmar "innalillahi wa inna ilaihirraji'un"
Amina da Amrah suka saki wani irin kuka, kowa Sai Kiran sunan yarinyar suke, mamy ma hawaye ne yake zubo mata, tasa hannu tana sharewa, me Widad taci?

Anty Lubna tadora hannu aka
"nashiga uku na, nide 'yata Bata mutu ba, nashiga uku widad Karki tafi ki barni, karkimin haka widad, Asim ka kashe min yata, meyasa zaka Barta taci?"
Cikin tsananin bacin rai ya nufeta ya sharara mata wani kyakkyawan Mari, su mamy sukai kansa, amma kafin su riqeshi ma yadamqi wuyan Lubna ya shaqeta," Mena miki?

Meyasa kikeson kasheni?

Kifadamin waye yasaki?
Chapter 23 · 0% Book details