← Book details Insaaf Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 53

Sashe 37

Insaaf Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kinyi wani fresh,Wai Yaya Asim ya ganki kuwa?"
"A a baidawo ba"
Amrah ta riqe ha6arta tace "Tabdi, injin bazai ganeki ba"
Murmushi tayi maimakon tabata amsa saitace "tunda yamma fa nazo, ashe ke bakya gidanma Sai mamy ce take fadamin"
Zama tayi akusa da'ita tacire mayafin kanta tace "Eh wallahi naje Agege suna, wata qawata ce ta haihu"
Tace "To Allah yaraya"
"Amin Minal, Bari inyi sallah"
Tafadi haka tare da shigewa toilet
Da daddare mamy ce tarakata d'akin Asim din, sannan tayi mata sallama tafuto
Haka ta zauna shiru ita kadai, Bata taba shiga cikin dakinsa ba Sai yau, koda yaushe iyakarta falon sa,amma tsarin d'akin nasa yayi mata sosai, babu tarkace dayawa, kayan furnitures din brown ne and milk color, mayafin jikinta tacire tashiga toilet tayi alwala tazo tayi sallar Ishsha'i, harta idar baidawo ba
Ta kalli agogo taga bakwai da kwata, afili tace "bari intashi inyi wanka na kwanta"
Kayan jikinta tafara ragewa, saida tacire komai ta zubasu Akan gadon, daga ita Sai d'an qaramin pant yaturo kofar d'akin yashigo
Gabansa ne yayi mugun faduwa saboda ganin abinda bai taba zato ba, qyam yaqame akofar d'akin Yana kare mata kallo, shi Yana tunanin yarinya ce qarama ashe Bahaka bane?

Lokaci daya yaji yanayin sa Yana sauyawa, Addu'ah yafara yi a ransa Allah yasa karta juyo ta ganshi, ta tsaya ahakan yayita kallonta
Hannu tasa zata janye pant din amma saitaji a jikinta kamar Ana kallonta
Juyawar da zatayi kuwa Sai ganin Asim tayi yazuba mata ido Yana kare mata kallo
Wani irin ihu tasa tashige cikin toilet din d'akin da gudu
Sai a sannan yayi wata irin Ajiyar zuciya, sannan yashigo d'akin yazauna a bakin gado, yaushe tadawo ne?

Amma mamy Bata fada masa ba
Murmushi yayi ya kalli kofar toilet din, cikin ransa yace matsoraciya, ji yanda ta tsorata kamar Bata taba aure ba
Lumshe Idonsa yayi Yana shafa sumar kansa
Tun dazu tagama wankan, amma ba tasan Yaya za'ai tafuto a haka ba, idonta ne ya sauka Akan towel dinsa na wanka, tadauka tadaura sannan tafuto, Sai Jan towel din take qasa
Yanajin alamun futowar ta yabude lumsassun idanunsa yazubasu a kanta, fatarta Sai qyalli take tana wani irin sheqi, jiyake kamar ya fuzgota jikinsa amma kuma hakan bazai iyuba dole saita saki jikinta dashi
Juyawa tayi ka kalleshi cikin sauri yadauke kansa, itama idonta ta dauke tana tuno yanda yaganta babu komai dazu, itakam wannan mutumi Yana samun nasara a kanta
Wajan mayukansa tanufa duk saita rasa abinda zatayi, kayan mayukanta dasu turaruka wanda aka hado mata Asudan duk suna cikin Jakarta
Yana daga kwancen yace mata "baki iya sannu da zuwa ba Sai ihu ko?"
Kanta ta sunkuyar qasa tace "sannu da zuwa Yaya"
"yawwa, bakiga man shafawar bane nazo na dauko miki?"
Mamaki ya kamata, Yaya Asim ne mai cewa zai dauko abu?
girgiza masa kai tayi tace "a a"
Ahankali yataso daga kan gadon yaqara so wajan ta, tsoro ya kamata, gaban ta yafara faduwa, tasake yin qasa da kanta taqi kallonsa, shi kuwa mansa dayake shafawa ya dauka ya zauna a qasan kujerar datake zaune, sannan ya lakuto man a hannunsa, ya dauki kafarta yadora Akan cinyar sa yafara shafa mata
Lokaci daya taji wani irin yanayi Yana shigar ta, shi kansa laushin da yaji fatar jikinta nayi shiyasa yaci gaba da shafa mata man, Yana shafawa Ahankali baisan lokacin dayazo cinyar ta ba, Sai alokacin ya kalleta, cikin sigar rad'a yace "Sannu da zuwa"
Daga masa kai tayi, mamakin sa duk ya cikata
Yasake yin qasa da murya yace "meyasa baki fadamin zaki dawo yau ba?"
Hannunsa dayake murza mata cinya tafara janyewa, maimakon yajanye hannunsa, saiya hada hannun nata yariqeshi cikin nasa
Ahankali tace "babu komai"
"saboda bakya missing Dina ko?"
Ya jefo mata wannan tambayar
Kallansa tayi cikin sauri, murmushi yasakar mata, dimple dinsa ya lotsa, saita ga yaqara yin kyau, kuma ya birgeta kamar ta dora hannunta awajan
"kishirya zanje wajan Mamy"
Wata irin Ajiyar zuciya tasaki lokacin da yafita daga d'akin
Kai tsaye d'akin mamy yashiga, tace "Ashe kadawo?"
"nadawo mamy, ashe Minal tadawo"
"Ishraqa ta rakota da yamma, nayi tunanin zaka dawo da wuri ma"
"wallahi mamy aiki ne ya tsaida ni, kuma... kuma bansan... bansan cewa zata dawo ba" ya qarasa maganar a rarrabe
Mamy tayi murmushi tace "to saura lefe dakuma tare wa ko?"
Kallanta yayi yace "lefe?"
"au kama manta da lefe kenan ko?

Haba Asim, ai yanda akewa kowacce yarinya itama ya kamata ayi mata, Sai kuma kutashi daga nan kukoma naku gidan"
"Za'ayi mata mamy, amma maganar tashi mamy ina zamuje mu barki?"
"A a,Lubna ma Dan dole ne shiyasa nayarda kuka zauna anan, saboda koda yaushe neman ganin bayan ka ake, amma yanzu Alhamdulillahi babu wannan matsalar, kaga saiku tashi"
"A a mamy, zamu zauna anan din tare daku, nasan itama zataso hakan"
"to shikkenan, Allah yasanya Alkhairi, Allah yabaku Zaman lafiya, Dan Allah kadinga Jan yarinyar nan a jiki Asim, kadinga Bata kulawa ko zata saki jiki dakai, Kaine zaka koya mata Yanda zata Soka"
Sumar kansa ya shafa yace "insha Allah Mamy"
Daga nan yayi mata sallama yatafi dakinsa
Yana zuwa yaga harta kashe wuta ta kwanta, murmushi yayi yawuce toilet ya watsa ruwa, sannan yasha coffee yayi shirin bacci
Kwanciya yayi a gadon, yasaka hannu ya janyota jikinsa, Ahankali tabude idonta dake cike da bacci ta kalleshi, iska ya hura mata a'idon yace "Daga yau inde ina nan Karki sake kwanciya ke kadai"
Kallansa take kwata kwata Bata Fahimci abinda yake nufi ba, Shima kamar yasan Bata ganeba, cimak ya dauke ta yadora ta a jikinsa Sannan yace "Nan ne wajan baccinki"
Ahankali ta daga masa kanta, hular kanta yacire yafara shafa dogon gashin ta, Sai cusa hannunsa yake ciki, hakanne yasa ta lumshe idonta tayi luf Akan faffadan qirjinsa
Batasan lokacin da bacci ya dauke ta ba, hannunsa yasa ya rungume ta sosai a jikinsa, yanajin yanda albarkatun qirjinta suke ta6ashi, amma beyi mata komai ba, ya Dade Yana zuba murmushi shi kadai, sannan Shima yasamu bacci ya dauke shi
Asuba tagari
Mrs.Usman ce
[2/26, 2:01 PM] El~Yaqoub: INSAAF
Writing by:Amnah El yaqoub
41&42
Like my page on Facebook
https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493
Shine yafara tashi da asuba, har zuwa lokacin tana jikinsa a kwance, Ahankali yasaka hannunsa ya janye gashin kanta, sannan yayi kissing wuyanta yashiga toilet.

Saida yayi wanka sannan yayi alwala ya shirya cikin jallabiya,kan gadon yazauna ya sunkuya daidai fuskarta, yadora lips dinsa Akan idonta yayi kissing, Ahankali tabude idonta Sai ganinsa tayi kamar zai hade fuskar tasu waje daya,hannunsa yadora Akan lips dinta ya shafa, sannan yace "ki tashi lokacin sallah yayi"
Batace dashi komai ba tafara kokarin tashi, yace "natafi masallaci"
Wani irin juyi tayi, tasaki hamma, tafara salati, cikin sauri yafice daga d'akin, idan baiyi da gaske ba Insaaf zata iya karya masa alwala
Har Gari yayi haske baidawo ba, itama tana idarwa tagudu d'akin Amrah, ta kwanta anan taci gaba da baccinta,
Ita Amrah tana bacci batasan ma tashigo ba
Sosai su kasha bacci itada Amrah, Sai wajan karfe goma suka tashi, Amrah ce tafara farkawa tana ganin Minal abayanta mamaki ya kamata, dukanta tayi abayanta tace "Insaaf...

Yana ganki adakina?

Ina kika bar mijin naki?"
Cikin muryar bacci tace "miji...?"
Zaro ido tayi
data tuna da Yaya Asim...

Tace "kaiiii, qarfe nawa yanzu?"
Amrah ta kalli agogo tace "Karfe goma, meyasa kika taho nan?"
"toshi mafa baya nan, masallaci yatafi"
"kuma memakon ki zauna acan harya dawo idan akwai abinda zaki masa kiyi masa shine kika gudo d'akin nan?"
Kallan Amrah tayi tace "yanzu yatafi ne?"
"a a nikam Ina zan sani?

Amma baya kaiwa goma agida kema kin sani"
Tashi tayi tafuto daga d'akin, tana zuwa falo taci Karo da Ishraqa da wasu kayaiyakin nata data biyota dasu
Tsananin mamaki ya kamata, waje tanema ta zauna,tana kallon Minal din, mamy ce tafuto daga dakinta ta kalli Minal tace "Insaaf har an tashi ne?"
"mun tashi mamy ina kwana?"
"lafiya kalau, jeki hadowa Umman naki abinci"
Cikin sauri Ishraqa tace "a a mamy, aqoshe nake, sauran kayanta ne nabiyota dashi yanzu zan koma gida Nima"
Kallan ta yayi, cikin shagwaba tace "Anty Naga ko zama bakiyi ba"
"bagani azaune kinganni ba, kwanciya kikeso nayi kuma?"
Mamy tace "Insaaf dauki kayan kuje d'akin, Bari naduba Amrah"
Tana fadar haka tashige d'akin Amrah, dama tayi hakane danta basu waje ko akwai abinda zasu tattauna, tsakanin 'Yada uwa
Mamy tana tafiya Ishraqa ta kalli Minal tace"dauki kayan muje"
Babu musu ta dauki kayaiyakin tayi cikin d'akin Asim, itama Ishraqa tabi bayan ta
Suna shiga Ishraqa ta qarewa d'akin nasa kallo, tanemi waje ta zauna a gefen gadon, itama Insaaf din zama tayi agefenta tana sakin hamma
Ishraqa takama kunnanta tariqe tace "ke!"
Cikin sauri tasa hannunta awajan tace "Anty akwai zafi Allah"
Bata saki kunnan nataba tace "inake ina bacci mijin ki yana fita aiki sassafe?"
"Anty wallahi nadena"
Sakin kunnan tayi ta kalleta tace "Haba Insaaf, kirufamin asiri mana Karki bani kunya awajan Asim, nagama cika masa baki zai samu kulawa awajan ki amma gashi tun ba'aje ko'inaba Harkin fara rabuwa dashi, to Asim daban yake da sauran mazajen ki, da ilminsa, kuma kullum fita yake Yana haduwa da wasu matan, in kuma kofa kika budewa kishiyar ki to....

"
Cikin sauri ta katse ta tace"Anty wacce irin kishiya kuma?"
"Insaaf kishiya de dakika sani, bakya son kishiya zaki kwanta kina bacci?, haba Insaaf, ina abubuwan dana fada miki?

To inzaki ware ki ware, kinji nafada miki"
"to Anty inde share share ne zanyi"
"ba share share kadai ba Insaaf, kidinga Jan mijin ki ajikin ki, kina bashi kulawa, ta hakane zai manta da kowacce mace ai"
"nifa kunyar sa nakeji Anty, yanamin kwarjini, kuma harga Allah banaso yamutu, Allah idan yamutu bansan Yaya zanyi ba"
Hannunta taruqo tace "Insaaf...., ai mungama da wannan matsalar insha Allah, menene amfanin magungunan da baban ki yakarbo miki?
Chapter 37 · 0% Book details