Sashe 15
Insaaf Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kinga momy Bata zuwa munayin wasa da baby ta, shikuma Daddy na kullum kullum baya dawowa da wuri"
Amrah tace "Widad I will slap you idan kika sake cewa Amina, Anty Minal sunan ta"
"to uwar 'yan tsari, sarkin azar6a6i, taso mutafi dan uban ki" suka tsinci muryar Lubna tana zagin widad, tana qarasowa kuwa ta fizgi hannun widad tare da makawa Amina harara, suka tafi, Amrah tabi bayan Lubna da kallo tare da girgiza kanta ta tashi takoma cikin daki
Jikin Amina yayi sanyi, amma haka ta daure taci gaba da zaman dole Afalon, tanaso taga gudun ruwan Anty Lubna
Har gab da magrib tana Zaune Afalon, bataga Anty Lubna tashiga kitchen ba, kuma tun shigar su daki da widad har yanzu Bata futo ba, Sai da aka fara Kiran sallar magrib sannan tafuto ita kadai ko lura da Amina datake falon batayi ba, Sai sauri take tana gyara gefen zaninta
Ahankali Amina ta tashi tabi bayan ta, a bayan labule ta 6uya, tsaf tagama Kallan Anty Lubna data tsugunna a bayan d'akin Asim tana tone qasar wajan, Sai waige waige take Dan Kar a ganta, Amina tana ganin wajan tasaki labule n data 6uya aciki , tajuya cikin daki da sauri tana tabbatar da hasashen ta
Tunda tashiga d'akin Bata sake futowa ba, ba tasan wainar da suke toyaba, abincin dare ma Kasa fita ci tayi, dama batason Zaman dinning dinnan, duk Bata sakewa
Lokaci yanaja, ta kwanta amma idonta biyu batayi bacci ba, tana jin Anty Amrah ta shigo d'akin amma Sai tayi Shiru kamar me bacci, itama Amrah batayi mata magana ba ta kwanta tafara bacci, tayi tunanin tana bacci
Amina dai Sai juyi take ita kadai, har dare ya tsala, Agogon d'akin ta kalla taga karfe biyu da rabi, Ahankali tatashi tabude kofar d'akin ahankali tafuto, falon ta kalla taga duhu duk an kashe komai ankwanta, babu alamun tsoro ko kadan a ranta, haka tabude kofar falon tafuto, Gari yayi Shiru musamman ma unguwar su daba kowa ne yake zama a cikin taba, bakajin motsin kowa, Shima mai gadi ya kashe wutar d'akin sa, babu qaran komai saina gyare, wajanda Anty Lubna tabinne Laya can ta nufa, Ahankali tafara tonewa saboda Kar tayi qwaqwqwaran motsi Asim yajiyo ta saboda bayan d'akin sa ne, duk wanda zaiyi abinda Amina tayi to tabbas saiyaji tsoro, amma ita abun mamakin ko kadan babu tsoro atare da'ita, hankalinta kwance tacire duka abinda Anty Lubna ta binne, sannan ta daddage ta wullashi bayan katangar gidan, sannan tarufe wajan kamar yanda yake, Takoma cikin falon, kofar falon tarufe ta jingina a jiki tasaki wata irin Ajiyar zuciya tare da lumshe idonta
Wani irin haske ne ya baiyana a cikin falon, duk da idonta a lumshe suke saida taga hasken, Ahankali tafara Bude idonta harta budesu gaba daya, dashi tayi tozali yafuto daga d'akin sa hannunsa dauke da ruwan gora, daga shi Sai gajeren Wando, murdaddan jikinsa ya sake futowa sosai, ga gashi ya kwanta Akan qirjinsa, Bata taba ganin qirar namiji a baiyane hakaba, shiyasa tana ganinsa haka ya tsorata ta sosai, gabanta yafara dukan Tara-Tara, cikin ranta tace Yaya Asim... dama haka jikinsa yake?
Kuma yafuto falo babu komai a jikinsa dagashi Sai gajeren Wando?
Sunkuyar dakanta tayi, tafara tafiya sum sum zata shige dakinsu
Takun da yaji ne yasa yajuya da sauri, yayi mamakin ganin ta, metake yi afalo a'irin wannan yanayin?
Gaba daya Sai kunya ta kamashi, karfa yarinyar nan ta raina shi, ya sunkuya ya kalli jikinsa cikin sauri yahade qafafunsa waje daya (
Yana dagowa ya ganta zata shige daki, nan take ya daure fuskarsa yace "ke zonan"
gabanta ne ya tsananta faduwa ahankali ta juyo tazo gabansa ta taugunna batare data kalleshi ba, tace "gani Yaya"
Duk da yaji Dadin muryarta dakuma yanda takirashi da sunan hakan bai Hana shi daure fuska ba, bayason tagama kallansa ta raina shi
"me kikeyi afalo bakiyi bacci ba?"
Tambayar tashi tazo mata a bazata, tarasa wacce amsa zata bashi, cikin inda inda tace "dama... dama... am kallo nazo zanyi....
Shine naleqa waje nadawo"
Zuba mata ido yayi Yana kallanta batare da yayi magana ba, dataji Shiru saita dago kanta ta kalleshi karaf idonta yasauka a cikin nasa, cikin sauri ta maida kanta qasa, Shima kallanta yayi ya sake tsuke qafafunsa Yana hadesu waje daya (
Sannan yace "kawomin cup a kitchen"
Cikin sauri tatashi tayi kitchen din dama Zaman ya gundureta, tana kawo masa cup din tasake taugunna wa tabashi, karba yayi ya ajiye shi aqasa sannan yabude gorar ruwan yafara zubawa a cup din, saida yazuba sannan yasa hannu zai dauka cup din ya qwace daga hannunsa zai Fadi awajan, cikin sauri tasa hannunta zata tare cup din Shima yasa ka nasa hannun, hannunsa bai sauka ko'ina ba Sai Akan nata hannun, dago kanta tayi tana kallonsa Shima yazuba mata ido Yana Kallan manyan idanuwanta batare da sun janye hannayensu ba
Adede lokacin Lubna tabude kofar d'akin nasu tafuto taana zuba hamma, (
tashafa wajan baccinsa taji baya nan, kuma ta duba toilet ma baya nan, bakin data Bude tana hamma saita Kasa rufe shi tazub
a ido tana kallon su baki bude(
Lokaci daya ta nemi baccin dayake idonta tarasa, huci tafara yi kamar zakanya ta nufesu, batayi wata wataba ta hankade Amina daga kusa dashi tafadi can gefe
Har hakan yayi sanadiyar faduwar cup din qasa, cikin fishi tace "annamimiya, uban me kikeyi anan Keda mijina?
Ki tashi kibar nan wajan tun kafin nazama ajalinki"
Ahankali ta miqe tsaye tace "Anty Lubna bafa komai nake...."
"banason jin komai kibace kibar nan wajan nafada miki"
Girgiza kanta tayi tajuya tayi cikin dakinsu, Lubna ta juya ta kalli Asim daya zuba mata ido Yana kallonta Idonsa yayi jajir, tasan idan tayi magana tsaf zai Iya wanka mata Mari, Dan haka batace masa komai ba tashige daki tana sakin tsaki, sake kallonta yayi Yana jinjina rashin taarbiya irinna Lubna, yanzu shi takewa tsaki?
Haqiqa tafara kawo shi wuya, Idan ya tashi yimata hukunci ba zataji dadi ba, in banda shirme metake tunani zai aikata da wannan yarinyar dayasan cewa idan yayi aure da wuri zai haifi kamarta?
Amina kuwa bataji Dadin abinda Lubna tayi mata ba, to Naga itama din mijinta ne, meyasa zatake mata haka?
Cikin ranta tace wallahi Allah saiya saka min, kuma niba annamimiya bace, saide ke
Washe Gari da safe weekend ne kowa Yana gida, Amina Bata tashi da wuri ba kasancewar ta Dade batayi bacci ba, Sai wajan karfe goma tafarka, azabure tatashi kasancewar tatuna da maganar Lubna, idanunta tahau murtsikawa ta diro daga kan gadon tashiga toilet ta wanke bakinta da idonta tafuto falon, duk mutanan gidan suna nan banda Daddy
Anty Amrah tashige daki tana amsa wayar Amjad
"kakusa zuwa ne?
Kaga niba wani kitchen dazan shiga, Kai inde baka takurani ba bakajin dadi kwata kwata rayuwarka" (
hamdala Amina tayi dataga Asim baya nan, qila baici abinci Bama kwata kwata
Qamshin girki taji Yana tashi a kitchen, tadan leqa saita hango Anty Lubna tana girki, haka nan taji zuciyarta takasa samun nutsuwa da wannan abincin, Bata saniba ko acikinsa tazubawa Asim maganin, idaanma tazuba idan ma Bata zubaba insha Allah bazata Bari yaci abincin Nan ba
Zama tayi akujera tana tunanin dabara, agabanta Anty Lubna tagama jera abincin akan tire, ta qwalawa Amrah Kira
"Amrah!, nagama ki futo kikai sauran kan dinning, gana yayanku nazuba masa nasa daban zan kai masa daki"
Tazo wucewa tagaban Amina ta kalleta ta watsa mata harara, Amina ta yunqura ta tashi kamar zatayi cikin d'akin su da niyya tabangaje Anty Lubna, aikuwa abinci ya 6are (
Tana ganin abincin ya zube tayi hamdala a ranta
Anty Lubna kuwa baqin ciki ne ya kamata kamar ta mutu, maganin da suka dauki tsawon lokaci suna so su sakawa Asim a abinci yau tasamu tasaka masa shine wannan yarinyar zata zubar da abincin?
Ta daga kai ta kalli Amina, tasaka yatsanta abakinta Tama rasa me zata mata taji sanyi, Amina ta sunkuya tahada mata kayan daya zube ta dago tace "Anty Lubna Dan Allah kiyi haku...." Bata qarasa ba Lubna ta zabge ta da wani irin gigitaccen Mari (
Akan Idonsa yaga Marin da Lubna ta zabga mata, ya tsaya a bakin kofar falon nasu yanaso yaga gudun ruwan ta
Ihun kukan datasa ne yasa Amrah futowa daga d'akin su da gudu, tana ganin Yaya Asim a bakin kofar falon ransa a mutuqar 6ace, Sai tayi Shiru
Anty Lubna tasake kallon Amina cikin haushi, saboda tayi mata wannan Dan Marin ne yasa tabude baki take mata wannan uban ihun?
Aidama haushinta takeji, da baqin cikinta ta kwanta cikin dare saboda ta ganta da mijinta, cikin bacin rai tace "Dan uban ki Nasha wahala na yi girkin zaki zubar min dashi?
Tsugunna ki tas ki debeshi"
Tana kokarin tsugunna wa tasake dauke ta da wani Marin wanda ya gagata Amina, cikin tsawa yace "Lubna!!!"
Atare suka kai kallonsu wajan kofar, Amina tashige cikin dakinsu da gudu tana kuka, cikin falon ya qara so cikin fishi yace "waike Lubna wacce irin mahaukaciya ce ne?"
Amrah tana ganin haka tayi d'akin mamy tadugu zata sanar mata, saboda Bata taba ganin ran yayan nata yabaci haka ba
Cikin bacin rai itama tace "nikake cewa mahaukaciya saboda wannan yarinyar marar asali?, kasan wahalar danasha wajan wannan girkin zatazo tazubar min dashi?"
Nunata yayi da hannu yace "to waye zaiyi abinda kikayi yanzu inba mahaukaci ba?
Yarinyar dabatafi ki zaneta da tsinken tsintsinya ba shine zaki kamata kina duka kamar Kin samu baiwa?
Dududu nawa yarinyar take dazaki mata irin wannan dukan?
Kokuma bakya tunanin irin wannan dukan zaisata ta kangare?
Duka lalata Yaro yake, idan kika kuskura kika sake dukanta wallahi Sai ranki yabaci "
Yana fadar haka yabi bayan Amina cikin d'akin su
Mamaki, taraddadi, dakuma faduwar gaba duk suka taru sukayiwa Lubna yawa, Anya kuwa Asim bai fara samun matsala Akan yarinyar nan ba?
Kode ba kalau tabarshi ba?
Yanzu wannan yarinyar zai Dubi idonta yace mata tadaketa da tsinken tsintsiya?
Saikace Widad?