← Book details Insaaf Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 53

Sashe 33

Insaaf Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"
Kallanta yayi yace"mekike buqata?"
"ni babu abinda nake buqata, buqata ta daya sune iyaye na, kuma na gansu, Kai nake tambaya bansan dame zan saka maba"
Kallanta yasake yi,cikin ransa yace "your lips"
Afili kuwa saiya daga kafadunsa biyu, yace "kisaki jikinki da Iyayen ki, bakida kamar su a rayuwa"
Mamy tafuto daga dakinta ta gansu azaune awajan har yanzu, tayi murmushi ta nufi hanyar d'akin Amjad.

Sallama suka doko atare duk su biyun, Ishraqa da El-Hameed, Asim yayi Shiru yayi Suman zaune, ya kalli Minal yaga kujerar datake zaune tana fuskantar tasa kujerar, idanunsa ya runtse
Karfa Ishraqa tayi tunanin wani abu, gaba daya Sai kunya ta kamashi, Abin yabashi mamaki Wai shine dajin kunyar Ishraqa, wannan al'amari dame yayi kama?

Ishraqa kuwa wajan mamy ta nufa suka fara gaisawa harda El Hameed din, Kallon El Hameed tayi, sannan tayi masa sign da idonta zuwa wajan su Asim da Amina
Asim yayi Shiru kamar baiji shigowar Suba, yanaji mamy tace "Ishraqa ku zauna mana, Bari indubo Amjad nadawo"
Cikin sauri Shima ya tashi, yad'an hade fuskarsa saboda Karma Ishraqa taga fuska tayi masa magana
Bayan mamy yabi, aikuwa tana ganin tasowarsa tace "Asim, baka ganmu bane?"
Amina tayi murmushi itama tataso ahankali ta nufi wajan Iyayen nata, atare kuwa suka sauke Ajiyar zuciya ganin ta saukko daga fishin nata
El-Hameed ya tashi ya ruqo hannunta yazaunar da'ita a tsakiyar su
Asim kuwa bai saki fuskarsa ba yadawo da baya yamiqawa El Hameed hannu suka gaisa, yasake yin hanyar d'akin Amjad
Ishraqa tayi murmushi tace "Asim jiya baka shigo minba bayan mun tafi gida, yauma nayi tunanin zaka shigo amma banganka ba"
Batare daya kalleta ba yace "Eh wallahi"
Yana fadar haka yayi d'akin Amjad
Fashewa tayi da dariya,El Hameed yace "Habibty Sirikinki nefa"
Tace "ka qyale Asim Habiby, borin kunya kawai yake, kasan kafin muga Insaaf nafada masa zan bashi auren ta, amma Asim saiya nunamin kwata kwata shifa bazai auri yarinya taba, harda cewa Wai tayaya zai auri yarsa ta cikin sa, kajifa wani rikici, shiyasa yanzu nakeso na tuna masa maganar amma kaga yaqi tsaya wa awajena "
Minal tayi murmushi, tatuna lokacin da Ishraqa take cewa karta miqe kafa agidan Asim, ta riga tayi masa mata, ashe ma itace matar
*** ****** ***
Tana zaune agefen gadon sa, ta ajiye abincin a qasan d'akin, shi kuwa Yana kwance Akan gadon yakifa kansa acikin fillo
Cikin shagwaba yace "Anty Amrah Niki qyaleni, nace miki banjin Dadin bakina bazan iyacin komai ba"
"to inkoma in fada mata kace bazakaci abincin ba?"
Dago kansa yayi daga cikin fillo ya kalleta yace "wacece?"
"mamy ce ta turo ni"
Bata fuskarsa yayi
"auke bazaki iya zuwa a matsayin ki na yar'uwata kibani kulawa ba Sai mamy tasaki?"
Amrah ta kalleshi ta girgiza kanta, "me hali de baya fasa halinsa, Amjad Wai meyasa ka rainani ne Dan Allah?

Kokuma saboda kaga kanmu daya?"
Cikin sauri yace "kanki daya dawa?

Haba Amrah, kema kinsan Aina fiki wallahi"
Dan qaramin tsaki taja, tatashi tsaye tace "ga abincinka nan, idan kayi niyya saika dauka Kac...."
Bata rufe bakinta ba yawani fusgota ta'iyo baya Sai ganinta tayi azaune kan cinyar sa
Ranta yayi masifar 6aci, ta kalleshi zata fara zazzaga masa masifa taga Shima Hakan take, domin kuwa idanun Sama sun rufe saboda 6acin rai, nunata yayi da hannunsa yace "Karki sake min tsaki Amrah"
Haushi yasake kamata, ta kalli yanda tazauna a jikinsa kamar wani muharramin ta, tace "Amjad, cikani kokuma na wanka ma Mari yanzu nan"
"bazan sakeki ba Amrah kiyi abinda zakiyi, kinfara isata Amrah, ina dalili koda yaushe bakida wanda zaki raina acikin gidannan saini, wallahi idan naqara jin kinmin tsaki da gani harke Sai ran kowa yabaci a gidannan"
Muryarta ce tafara rawa alamun tana gab da sakin kuka tace "anyi Tsakin, Kai waye da bazan ma tsaki ma,?"
"Mtsww!"
Tasake yin wani tsakin,kallanta yayi cike da mamaki, babu shakka saiya yi maganin Amrah sannan zata fara ki yaye bacin ransa
batayi aune ba taji lips dinsa Akan nata
Iya hakan yaso ya tsaya, danya tsoratar da'ita, amma yanayin da yaji yafara fisgarsa ne yasa da zafi-zafi yafara tsotsar bakinta, hannunta duka biyun tasa tafara dukansa, wani irin hawayen baqin ciki yafara silalowa daga idanuwanta
Cike da mugunta yagama kissing dinta sannan Dan kansa yasaketa, cikin sauri tatashi tafashe da kuka, ta dauki flate din data rufe masa abinci ta kwad'a masa, cikin sauri yasa hannu ya tare, tasake daukar fillon gefensa ta doka masa.

Mamy ce taturo kofar tashigo taga abinda suke, Asim ma Yana bayan ta, cikin kuka tace "Azzalumi"
Mamy tace "Waiku yaushe zaku San kun girma ne?

Ku kenan koda yaushe kullum cikin fada?

Yanzu abin naku har ya wuce cacar baki yakoma doke-doke?"
Amrah ta share hawayen idonta tawuce su mamy batare data tanka ba, Asim yabita da kallo
Mamy tanemi waje ta zauna ta kalli Amjad"menene yasamu idonka haka?"
"babu komai mamy, kawai de bansamu bacci bane"
Kanta ta jinjina tace "katashi Kaci abinci"
Cikin sanyin jiki yace "to mamy"
Daga nan tajuya tafice daga d'akin
Asim yasaki Ajiyar zuciya yazauna Shima a gadon batare dayace masa komai ba, Amjad dinne ya kalleshi yace "Yaya kayi hakuri Akan abinda Daddy na yayima, Dan Allah kayi hakuri Yaya" ya qarasa maganar Idonsa na kawo ruwa
Asim ya kalleshi yace "Daddynka ne kai kadai kenan?"
Fadawa yayi jikin Asim yasaki kuka, Asim ya Girgiza kansa yace "Wai kai Yaro ne?"
Girgiza kansa yayi yace "kayi hakuri Dan Allah Yaya"
"naji, nahaqura ni, katashi Kaci abinci mukoma police station, insha Allah komai yazo qarshe"
Daga masa kai yayi sannan ya tashi daga jikin Asim din, yasakko qasa zaici abincin yaji mararsa ta riqe, cikin sauri ya dafe cikin sa yace "Wayyo Allah na Yaya"
Asim yace "miye kuma?"
"Yaya cikina ciwo"
Kallansa Asim yayi, yayi Kasa da murya yace "kai, meka yiwa yarinyar can?"
"to Yaya kullum saita dinga min fada, ita mamy ce da zata sani agaba tana min fada?

Yaya cewafa tayi zata mareni, ni kuma na koya mata hankali"
"yayi kyau, ai yanzu itama ta koya ma hankalin ko?"
Kallansa yayi kamar zaiyi kuka, yace "Yaya wai dama haka akeji?"
Asim ya girgiza kansa ya tashi yafice daga d'akin batare dayace masa komai ba
Yana futowa falon yagansu Sai Fara'ah suke, besan Akan me suke tattaunawa ba, kawai ganinta yayi Sai dariya take, tsananin mamaki ya kamashi, dama yarinyar nan tana dariya amma shine batayi?

Tsayawa yayi awajan Yana kallon su cike da birgewa, El Hameed Sai waya yake amsawa Yana Bata tana gaishe su, sauqinta daya suna jin English, da Dan wanda tasamu a qauye tayi amfani suka gaisa dasu
El-Hameed yace "yata, saiki shirya muje gida kiga kayaiyakin ki, da dakinki, photunanki nada wanda kike yarinya, bakyajin magana, amma dazaran mamanki tayi miki tsawa saiki fara kuka
idan ta lallashe ki kikaqi yin Shiru itama saita fara kuka, ko nono tabaki kikaqi karba yanzu zata shiga damuwa "
Ishraqa tayi masa wata harara ta masoya
Duk falon Sai suka sa dariya, amma banda Asim dayake tsaye
Ishraqa ta kalleta tace "Yaya a kai kuka rabu da mutanan dasuka riqeki Insaaf?

Yanzu suna ina muje muyi musu godia?"
Hannunta ta wara alamun Bata saniba, tace "Nima bansaniba, bansan inda suke ba"
"to meyasa kuka rabu?"
Asim yazuba mata ido Yana jiran amsar da zata basu, saiyaji tace
"megari ne ya koremu,su suka tafi, ni kuma sainabi Yaya"
Ishraqa ta daga kai ta kalli Asim, suna hada ido yadauke kansa
Takalli Minal, cike da tsokana tace "wanne Yaya?"
Bata San Yana tsaye a bayan su ba, Danhaka kai tsaye tace "Yaya Asim..."
Sai yaji muryar Tata taqara gyara masa sunan nasa, Bata taba kiran sunan saba, amma yau daya Sai yaji kamar tafi kowa iya ambaton sunan
Ishraqa tayi dariya tace "to ai bangane bane danaji kince Yaya, dakin cemin dasu Inna suka tafi nikuma sainabi mijina"
Nanma taqarasa maganar tana kallon Asim
El-Hameed yayi dariya ya girgiza kansa, Asim kuwa kawar da kansa yayi gefe, yaga alama Ishraqa nema take de saita Tona masa asiri hankalinta zai kwanta
Minal tayi murmushi, ita ba tasan duk wannan tambayoyin da Ishraqa take mata saboda Asim neba
Ahankali yatako yazauna a daya daga cikin kujerun falon, ya kalli cikin idon Ishraqa yace "toba shikkenan magana ta qare ba?"
Babu wanda bai Bawa dariya ba, sosai Amina take dariya, yadago kansa Yana satar kallonta, itama anata bangaren satar kallonsa tayi, aikuwa Idonsa yahadu dana juna, cikin ransa yace kai,ya Allah!

Ya kalli mamy yace "Mamy Yaya maganar Daddy?"
Daure fuska tayi tace "nayi waya dasu dazu, nace sutura case din zuwa court, acan Sai suyi masa hukuncin daya dace dashi"
"mamy kiyi hakuri, Nima dayake son yakashe ni nabarshi da mahaliccinsa"
"Asim bazan rabu dashi ba saiya yiwa kotu Bayanin duk abinda ya shuka, Sai yafadi mutanan daya hada baki dasu suke son kasheka, dukiyar ku kuma idan yabayar kansa, idan bai bakuba zai Baku ranar lahira, ranar da bashida kudin biya saide abiyaku da ladansa, Shima ladan idan babu Sai a rage naku zunubin aqara masa, saboda Amjad yasa na jinkirta maganar, saboda inajin nauyin Yaron, amma babu yanda zanyi, idan bai Fadi da wanda yake waya Akan akashe kaba, to koda shi anyi masa hukunci sauran suna nan, saboda haka dole yafada su waye, a yanke wa kowa hukuncin daya dace "
Duk falon Sai sukai Shiru suna sauraron mamy, gaskiya tafada, Daddy bai kyauta musu ba, Amina ta kalli Asim, saiya Bata tausayi, koda yake a yanzu kam shidin ba abin tausayi bane, itace abar tausayi tunda shide yagama da tasa matsalar, itace de duk lokacin data tuno mutuwar da mazajen ta sukeyi, Sai gabanta yayi mugun faduwa
Asim ya kalli mamy yace "hakane Mamy, amma Sai yaushe zamuje?

Amjad yana cikin damuwa"
"idan kungama abinda kuke anjima Sai muje"
Amjad ne yafuto daga dakinsa, yagama cin abinci yayi wanka ya sauya shiga zuwa manyan Kaya kamar yanda yayansa yasa ka, wani irin kyau yayi kamar baya tattare da damuwa
Su Ishraqa ya kalla yace "Anty ina kwanan ku"
Suka amsa masa cike da kulawa, ya kalli mamy yace "Mamy ina Anty Amrah?"
"Amrah tana daki, mekuma zakaje kayi mata?
Chapter 33 · 0% Book details