Sashe 31
Insaaf Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Auren da Allah ne yahad'a abinsa?"
Muhsin yasaki dariya yace "to abokina me amfanin auren da babu kulawa, may be abinda tagani kenan, babu kulawa, gashi bataso kaima baka so"
"kaga Muhsin, Dan Allah kadena wannan maganar kotu kotun, tayaya zan saki yarinyar Ishraqa?
Da wanne idon zan kalleta?inajin tausayin yarinyar, Gara na tausaya mata mu zauna ahaka"
Muhsin yace "tab!
Tausayi manya, yanzu Yaya maganar Daddy?"
"bansani ba Muhsin, yanzu nakeso Nabi bayansu"
Muhsin yace "eh ya kamata muje, amma mu shiga gidan mu fadawa mamy, saimu wuce"
Asim yace "OK,no problem"
Daga nan suka shiga cikin gidan.
Suna shiga falon suka zauna, har lokacin Amina tana wajan mamy,Ishraqa jitake kamar taje ta janyota jikinta su dauwama ahaka, amma tasan ta6a tawa yarinyar rai, dole hakan zai Iya faruwa, Asim ya kalli mamy yace "Mamy kiyi hakuri, inaso naje wajan Amjad, Yana cikin damuwa mamy"
Amrah ma tace "eh mamy Dan Allah, kinji mamy, Nima zan bisu, Dan Allah mamy karmu tafi mubarshi"
"Dan Allah kudena min wannan maganar haba!"
Muhsin yace "Mamy kiyi hakuri, amma idan kuka tashi daga nan muma ba zamuji dadi ba"
Ishraqa ma da idanunta sukai jajir tace "kiyi hakuri mamy, tunda Allah bai bashi nasara ba, Allah ma gafurun rahimu ne"
Kanta ta sunkuyar qasa tace "Hakane, to shikkenan, zamu zauna insha Allah"
Turo kofar falon akayi, gaba dayansu suka kai dubansu zuwa ga kofar, Amjad ne yashigo duk Hankalinsa atashe, kana ganin idanunsa zaka san yasha kuka Bana wasa ba, mamy tana ganinsa tatashi tashige dakinta, Asim ya Girgiza kansa cike da damuwa yamiqe zaibi bayan ta
Ahankali yace "Yaya"
Asim ya tsaya cak awajan
Ahankali yataka zuwa wajansa yace "karka bita Yaya, na cancanci fiye da haka Yaya, kakoma ka zauna zan bita da kaina"
Yana fadar haka yasa ka kansa zuwa d'akin nata, batare daya jira amsar Asim dinba
Ajiyar zuciya Asim yasaki yadawo falon yazauna kusa da Muhsin, ya kalli Amina suna hada ido ta sunkuyar da kanta tana wasa da yatsun hannunta
Yasake daga kai ya kalli Ishraqa suka hada ido,take maganganun datake fada masa Akan auren yarta yafara dawo masa, cikin sauri ya sunkuyar da kansa qasa
Cikin ransa Yana fadin shikkenan burin Ishraqa yacika,girma nade yariga yafadi
Mrs Usman ce
[2/21, 10:14 PM] El~Yaqoub: INSAAF
Writing by:Amnah El yaqoub
33&34
Ina qara miqa saqon ta'aziyya ta ga dan'uwana Wato Its Saddik, Allah yaji qanta, Allah yayi mata rahma, Allah yasa tahuta
Idan Tamu tazo ya Allah Kasa mucika da Imani
Like my page on Facebook
https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493
_________
Tabbas idan yaci gaba da zama awajan, babu abinda zai hana Ishraqa tayi masa wankin babban Bargo
Danhaka yayi qasa da muryarsa yace "Muhsin, ya kamata mubar wajan nan"
Cikin mamaki Muhsin yace "saboda me?"
Da idanunsa yayi masa nuni da 6angaren da Ishraqa take
Nan take Muhsin ya fahimta, yayi murmushi sannan yace "muje"
Ko inda Ishraqa take bai iya kalla ba suka fice daga falon, suna compound din gidan Muhsin yasaki dariya yace "wai saboda kaga Ishraqa a falon ga kuma Minal shine kace mu futo?"
"Muhsin idan ganine Aida sauqi, kawai yanda nagama cikawa Ishraqa baki bazan auri yarta ba, shi nake tunawa, kuma nasan bazatayi fuska ta share ba"
Muhsin ya kwashe da dariya yace "lalle Asim, toba Gara ka tsaya ba, ayi wacce za'ayi?, yanzu dakasa muka futo ina zamuje?"
Kai tsaye yace "Wajan Daddy"
"Wajan Daddy kuma?
Kasan abinda kake fada kuwa Asim?"
"nasani Muhsin, Saboda Amjad, muje"
Muhsin ya kalleshi ya Girgiza kansa, besan wacce irin zuciya abokin nasa yake dashi ba, koma menene yasan cewa haqiqa Minal tayi sa'ar miji, bece dashi komai ba suka tafi
*** ****** ***
Bayan tashiga d'akin Kasa jurewa tayi tafashe da kuka, Ahankali yaturo kofar d'akin nata yashigo jikinsa a sanyaye
Kallanta yayi yaga tabawa kofar baya, hakan yana nufin koma waye yashigo batason ganinsa kenan, gwiwo yinsa yazube aqasa, yace "mamy..."
Tana jinsa tayi Shiru, hawaye take amma takasa juyowa ta kalleshi
Yace "mamy Ashe zaki iya yin fishi dani?, zaki iyayin fishi da Amjad dinki?
Autanki?"
Wannan maganar daya fada saita sa jikinta yayi sanyi, kukan ta ya tsananta
Shima ganin tana kuka Sai hakan ya sashi zubda hawaye yace "Mamy uwa Bata fishi da yaranta, tunda na tashi bansan kowa ba, bansan mahaifiyata ba kena sani a maimakon ta Mamy, kuma kin hadani da yaranki kinyi kana tarbiyar da kowacce uwa tagari take yiwa yaranta, mamy bantaba sanin wani abu waishi zalunci ba bare nayi, kuma Narasa wanda zan zalunta Sai Yaya Asim...., mamy meyasa laifin mahaifina zai shafeni?
Kiyi hakuri Dan Allah na roqeki "
Yaqarasa maganar Yana hade hannunsa waje daya
kuka yake sosai, kuma har lokacin Bata juyo ta kalleshi ba, cikin kuka yace" Mamy tun muna Yara kece kike fada mana mu daina ruqo, mu dinga hakuri da juna, ubangijin daya haliccemu ma muna aikata masa laifi kuma yayafe mana, meyasa ba zakiyi hakuri kiyafewa mahaifina ba?
"
Hannu tasa ta share hawayen idonta, bazata iya fishi da Amjad ba, tana kaunar Yaron acikin ranta, amma mahaifinsa ya yaudaresu, kudi da Rudin duniya sun Gama dibansa.
Ahankali ya tashi zai futo daga d'akin, saboda mamy de ko kallansa taqi yi.
Tanajin alamun tashinsa ta juyo tace "toda katashin inane zakaje?"
Cikin sauri ya juyo ya kalleta, amma Yana tsoro yakasa qarasa wa wajan ta, Sai tausayin sa ya kamata, tace "kaje kanemi abinci Kaci"
"banajin yunwa mamy...."
Batace masa komai ba tanemi gefen gadonta tazauna, Ahankali yatako wajan ta, tare da riqe hannunta yace "mamy ki yafe mana nida Daddy please"
"Amjad me mahaifinka Yamin dazaka ce nayafe Mas....."
Bata qarasa ba taji wani irin taqaici ya kamata, har yanzu idan tatuna abinda alhaji yayi jitake ta tsaneshi, wani irin sabon kuka yazo mata, Bata Hana kanta ba, haka tafara hawaye tana sharewa, Shima kukan yasaka mata, tana ganin haka tajashi jikinta ta rungume shi, kowa kuka yake acikinsu, ita kuka shi kuka babu wanda yabawa dan'uwansa hakuri, da kansu suka gaji suka daina
Tashi tayi takamo hannunsa tace "muje nabaka abinci"
Haka suka futo falon inda suka Bawa kowa mamaki, ta kalli Ishraqa da ido ya kumbura saboda kuka, ta kalli El-Hameed shikuma yazubawa Amina ido Yana kallonta, takai kallonta wajan Aminan taga tana nan zaune inda ta Barta, amma ta lumshe idonta kamar me bacci
Murmushi tasaki, saboda Iyayen da yarinyar duk sun Bata dariya, kuda yarku amma kuna tsoron tunkararta?
Haqiqa yau Minal tazama boss, kuma da alama Sai daya Actor din yazo sannan ne zasu daidaita
Zama tayi, sannan tazaunar da Amjad agefenta, ta kalli Amrah tace "Amrah kawowa Amjad abinci"
Amrah tatashi tayi kitchen tana mamakin wannan shaquwa ta Amjad da mamy, kome yafada mata harta sauko cikin sauri haka?
Bayan yagama cin abincin Yana shirin tashi Asim yashigo, yayi mamaki dayaga har lokacin su Ishraqa suna gidan, yanayin Zaman nasu ya kalla yasan akwai sauran waani abun kuma, Allah Allah yake Kar Ishraqa ta kunya tashi a gaban Minal dakuma su mamy, shiyasa yaqi kallon inda take ma
Fuskarsa yad'an daure sannan ya zauna yakalli mamy yace "Munje wajan Daddy nida Muhsin, basu bamu damar ganinsa ba, sunce Sai kinje, Mamy kiyi hakuri Dan Allah"
Amjad dake zaune kansa ya Sara, Shima Hakan ce tafaru dashi bayan yabisu abaya, kwata kwata basu bashi Damar ganin Daddyn ba
Ahankali yamiqe ya kalleta yace "Mamy saida safe"
Daga nan yawuce dakinsa
Itama Amina kokuma nace Insaaf, tashi tayi ta nufi hanyar dakinsu, ciki-ciki tace musu "saida safe"
Asim ya kalli Amjad, yasake dawo da Idonsa ya kalli Minal, Ahankali yace "ikon Allah"
Yau kuma anta6o shagwa6a66e da wata shagwa6a66iyar babu Zaman lafiya
Amrah ce tatashi tabi bayan Amjad, saide tana kama handle din d'akin da nufin budewa taji shi a kulle, haka tadawo falon ta zauna jikinta a sanyaye
Ishraqa da sauqi tamiqe zatabi bayan Amina, mamy tayi sauri tace "karkije Ishraqa, kibata lokaci ta huce, zatafi saurareku"
Dawowa tayi ta zauna Akan kujerar tadafe kanta da hannunta
, idanunta nakawo ruwa
Kallanta Asim yayi yace "kuma wa zakiyi wa kukan?"
El-Hameed yayi murmushi, Amrah ma ta kalleshi tayi murmushi, mamy tace "Asim kabarta da abinda yake gabanta mana, idan bazaka lallashi Minal ba ai bazaka zo ka tunzura Ishraqa ba"
Shiru yayi bece komai ba, Ishraqa ta kalleshi takawar dakai batace dashi komai ba, besan cewa dama aciki take dashi ba, jira take tagama da matsalar gabanta sannan tadawo kansa
Amina kuwa tana shiga d'akin ta jingina ajikin kofar d'akin tana tunani, rayuwa kenan, yanzu ashe Anty Ishraqa itace mahaifiyar ta?
Qwalla ce ta cika idonta,tatuno lokacin da Ishraqa take zazzaga mata masifa harda cewa inde Asim ne to tayi masa mata, ko waye yace mata ita din sonsa take?
Harda cewa Wai karta miqe kafa, to mezatai dashi itama tunda shima ba sonta yake ba, hawaye ne yazubo mata tasa hannu ta share
Tana shirin barin jikin kofar tajiyo mamy tana cewa "Ishraqa, ya kamata kifada mana dalilin dayasa yarki ta6ace daga hannun ki, nide nasan kintaba cemin Insaaf yarki ce, kuma kinaso na dinga kiranki maman Insaaf, amma duk cikin mu nan babu wanda kuka taba fadawa dalilin dayasa kuka rabu Kuda yarku"
Hawaye ne yazubo mata, ta kalli El-Hameed tace "ka basu labari"
Shima kallanta yayi yace "A a kibasu labari Ishraqa"
Asim yayi murmushi,cikin ransa yace yau Habibty Takoma Ishraqa
Ahankali tafara basu labari tace "kamar yanda na fadawa Asim, Insaaf Bata wuce yar shekara biyu ba, muka nemeta muka rasa,kafin muyi Candy muka koma Sudan nida iyayena, bayan nayi Candy aka daura mana aure nida El Hameed, iyayensa suna da hali kamar yanda nawa suke dashi, shekarar aurenmu daya Allah ya azurtamu da samun Insaaf,Iyayen El Hameed sun nuna mata gata sosai, sunyi mata kyautuka masu yawa, haka Nima nawa Iyayen, lokaci daya mahaifiyar El Hameed tarasu, daga baya Shima mahaifinsa ya kwanta ciwo, anan ne ya mallakawa Insaaf kadarori masu yawa, kuma aka saka sunan ta Akan komai, daga baya Shima Allah yayi masa rasu.