← Book details Insaaf Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 53

Sashe 19

Insaaf Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"
" A a Habibiy, dama saramin naji yanayi, yanzu yadena "
"Habibty, ya kamata ki rage sa damuwa aranki, kina yawan tinani idan Bana nan ko?"
"dole ce tasa hakan, Asim ne yazo, shine nabashi labarin Insaaf, I think wannan ne dalili"
"nahadu dashi a waje, yanzu de ki tashi muje asbiti ko?"
"A a Habibiy, naji sauqi fa, saide muje wajan doctor din damukai magana dashi zai dubamu"
"to shikkenan, kibari gobe saimu tafi, but are you sure kinji sauqi dangane da ciwon kan?"
Ahankali ta lumshe masa idonta tabude, murmushi yayi, sannan yayi kissing goshinta, daganan suka futo daga d'akin
*** ****** ***
Washe Gari dasafe bayan sun Gama break fast zama sukai afalo itada Amrah, Amrah ta qarewa kayan jikinta kallo taga duk sun mutu, kuma koda wasa Bata taba nuna musu komai ba a haka take saka abinta, shikuma Yaya Asim irin yad'an dauke ta suje shopping dinnan ma beyi ba, wani lokacin har Gara Amjad ma zai dan kai mutum shan Ice cream(
Amma Yaya Asim, idan kudin tambayeshi ma yanzu zai fara jero ma tambaya mezakai da kudi, taqarqari yabaka dubu hamsin kaje ka qarata,kokuma yahau fada shi bayason almubazzaran Ci da kudi saboda bakasan zafin nema ba (
yanzu ta wacce hanya ya kamata tayi masa magana Akan suna so Yabasu kudi suje shopping?

Minal batada komai, kamata yayi Yabasu ko dubu dari ne, asiyo mata komai da komai tafuto gari ta dinga shiga mai kyau, wata zuciyar tace mata to kode mamy zata fadawa?

To ai kuma mamy ma idan taji cewa zatayi Asim din baqonsu ne da bazasu fada masa ba? (
To'ita yanzu Wai ya yazasu yine?

Amjad har code din Atm dinsa tasani saboda tsabar yanda yake Bata kudi komai Baja Baja, amma Yaya Asim, hmm inajin ma saudaya tataba ganin nasa Atm card din, Shima ganine daga nesa (
Shi Ala dole Yana tattalin dukiyar insaaf, kuma dacan Bahaka yakeba, tunda aka dauki wannan kudi na insaaf aka bashi, Tofa daganan komai ya canja
Sake Kallan Amina tayi, tayi gyaran murya tace "Am...Minal, ko zaki fadawa Yaya Asim yabamu kudi mutafi shopping ?

Tunda Kinga babu abinda mukeyi yanzu, ni wallahi Kinga har fargabar magana nake masa"
Cikin mamaki ta kalli Amrah "to Anty Amrah kema kina fargabar yimasa magana ni kuma dayake bani tsoro mezan iya fada masa?"
Amrah tazaro ido waje tace "tsoro kuma?

Tsoron sa kikeyi dama?"
"ni wallahi tsoro yake bani Anty Amrah, tayaya zan'iya tambayar sa kudi?

Idan naganshi agabana tsoro yake bani"
Amrah ba tasan lokacin data kwashe da dariya ba, ta kalleta "to ai danaga ke har fira kukeyi Keda shi, shiyasa nafadi haka, amma Bari yafuto Sai na gwada, amma tare zamuje dake"
Ahankali tace "to"
Basu Dade da Gama magana ba yafuto daga dakinsa cikin shirin tafiya wajan aiki,yau shigar manyan Kaya yayi, harda babbar riga,yadine me mutuqar tsada launin Light blue, hular daya Dora akansa tayi masa mutuqar kyau, sajen daya zagaye masa bakinsa yaqara futowa, Hankalinsa Yana kan waya yayi hanyar fita daga falon
Cikin sauri Amrah tace "Yaya ina kwana"
Kallo daya yayi musu yadauke kansa "lafiya"
abinda yafada kenan, daga nan bai qara sauraron suba yafita daga falon
Amrah ta kalli Amina tace "Kinga mutumin damuke jira yayi gaba yabarmu"
Tace "Tomu hakura kawai Anty Amrah idan yadawo kokuma wata Rana...."
"wacce irin wata Rana?, Toni in banda wajan cin abinci ma bakoda yaushe nake ganinsa ba, kullum Yana aiki kamar computer, tashi mu bishi"
Cikin sanyin jiki tace "to"
Suna fita compound din gidan suka hangeshi yana danna waya kusa motarsa, ga driver nan Yana qarasa goge motar, Sai sheqi take tana daukan ido
Dago kansa yayi ya hangesu suna qarasowa wajansa, shigar jikin Amina ya kalla yaga wannan de atamfar tatace datasa ranar aurenta,daurin dankwalin kanta ya kalla anan ya hango tulun gashin kanta daga gefe, duk yayi wani iri saboda babu gyara, tsaki yasaki cikin ransa, yarinyar nan batason gyara gashin ta, kuma gashin nata yanada tsawo sosai, may be ma tsawon nasa ne yasa yayi mata yawa wajan gyara, yarinya qanqanuwa da wannan uban gashi dama tayaya zata iya gyarawa? dududu batafi a zaunar da'ita ayi mata kwalliya ba
Qarasowa wajan sukayi itade ta sunkuyar da kanta qasa taqi dagowa su hada ido
Driver ya dubeshi yace "Yallabai zamu iya tafiya, nagama"
Amrah tayi sauri tace "Yaya..., Dan Allah Yaya ko zaka bamu kudi munaso muje shopping nida Minal"
Qura mata ido yayi Yana kallonta, Yana jira tagama magana
Amrah kuwa tana ganin haka cikin ranta tace shikkenan, dama nasani, yanzu haka dubu hamsin din daya saba zai wullo mana mutafi, danya qara musu wani abun saita cigaba da cewa "kuma Yaya kaga Bata da abubuwa dayawa, duk muna so musiyo, dasu takalma da jaka"
Asim ya sake kallanta yaga Sai abubuwa take jerowa, itama dataga haka saita sake cewa "dasu mayafai, da riga da Wando"
Dauke kansa yayi daga kallonta, yaga alama bazata Dena yimasa lissafi ba, ya maida kallonsa ga Minal yaga kanta Yana qasa tana Jan yatsun hannunta, itada ake maganar saboda ita amma takasa cewa komai, yanzu haka Yana sata yin magana zata fashe masa da wannan shegen kukan nata
Hannunsa yasa ka cikin aljihun wandonsa, Amrah tayi tunanin kudin zai basu harta fara Addu'ah Allah yasa yadebo dayawa (
Saitaga ya miqo mata ATM card dinsa yace
"gashinan,7788 ne cord din, kuciri yanda zai isheku"
Amrah ta hangame baki hannunta riqe da atm card, lokaci daya ta Lula duniyar tunani, eh lalle Sai yau taqara tabbatar wa Yaya Asim Yana ciki (
Shikuma Yana Bata card din yashige Mota, driver Yaja suka tafi, sun danyi tafiya kadan yasa driver ya tsaya, sannan ya sauke glass din motar qasa ya qwala mata Kira "Amrah!!"
Sai alokacin tayi firgigit tadawo daga duniyar tunanin data tafi, cikin sauri ta kalleshi "Na'am Yaya"
"please kubiya ta saloon awanke mata kanta"
Cikin sauri Amrah tace "to Yaya, zamuje ko'ina"
Tajuyo ta kalli Amina "muje mu shirya mutafi Minal, ba zamuje da motar gidaba, taxi zamu hau tunda ba waje daya zamuje ba, idan mukaje da Mota itama kaya zata zame mana"
Tace "to Anty Amrah"
Ko awaya daya basu qara agida ba, suka tafi, Kai tsaye Barack sukaje, suka shiga ERENA, Amrah kawai kwasar kaya take tana miqa ATM
ta lodo mata riga da Wando masu masifar kyau, banda dogayen riguna masu mutuqar kyau da tsada, takalma, jaka, Dan kunne, sarqa, kayan kwalliya, dakuma less daban daban Kala Kala masu kyau da shadda, atamfa ce batada yawa, itade Amina kallonta kawai take, kayan sunyi yawa kamar wanda za'a hada wa wata lefe, ita tsoro ma kasuwar tabata da farko, yanda taga jirgin sama Yana yawo a saman kasuwar
Daga nan sukaje wajan saloon, tsananin mamaki ya kama Amrah dataga yawan gashin da Minal take dashi, tana ganin gashin babu wanda yafado a ranta Sai Anty Ishraqa, har so take wataran tazo gidansu idan zatayi sallah tabude kanta taita kallon gashin
Harta Bude baki zatace amma Minal kede ba bahaushiya bace kawai kuma Sai tayi Shiru, saita ga idan tayi mata maganar kamar cin fuska nema agareta tunda kowa yasan cewa ita din batasan asalinta ba
Harda wankin qafa saida akayi mata, lokaci daya kuwa tafuto fess, Wai ahakan ma Bata fara amfani da mayukan dasuka siya ba
Saida suka kai kayan daya kamata adinka wajan dinqi, sannan suka bashi kudinsa, suka dauki taxi suka tafi gida
Amrah Sai daria take a ranta, kawai hango Yaya Asim take a office yanajin alert, Suda daukan kudi shida karbar alert
*** ****** ***
"kamar de yanda bincikenmu ya nuna Alhaji, kaida Hajiya bakuda wata matsala dangane da rashin haihuwa, lafiyarku kalau, kawai Allah ne bai kawo samun Rabon ba, may be Sai zuwa nan gaba, saide kuci gaba da Addu'ah Allah yakawo masu albarka"
El Hameed yamiqawa doctor din hannu tare da yimasa godia, yakai kallonsa ga Ishraqa yaga har idanuwanta sun kawo ruwa
Yace "Habibty tashi muje"
Bata'iya ce masa komai ba ta tashi tafuto daga office din, motar yabude mata ta shige, tana zama kuwa takifa kanta acinyarta tafashe da kuka
Shima zagayawa yayi ya shiga Yaja motar suka dau hanyar gida, kallanta yayi ya maida dubansa kan titi "yanzu Habibty ashe bazaki godewa Allah Akan kyautar da yayi mana abaya ba?, lokacin daya bamu Insaaf roqarsa mukayi?

Karki manta wasu mutanan dayawa neman guda d'ayan ma suke amma basu samu ba"
Cikin kuka tace "tomu damuka samu d'in ina take?

Ina 'yata take?" tasake rushewa da kuka
Kansa ya Girgiza yace "Ishraqa bake kadai fa kike son Insaaf ba, Nima Ina qaunarta, inaso kisani banida kowa a duniyar nan saiku, bayan ke banida kamarta, muyi Addu'ah idan tana Raye, Allah ya baiyana mana ita, idan kuma Bata Raye Allah yabamu hakurin rashin ta"
"nide 'yata Bata mutu ba, karka sake cemin 'yata ta mutu, zata dawo wajena" (
Shiru yayi bece da'ita komai ba ganin sun qaraso gida, Hon yayi Yana jira megadi yabude musu get amma Shiru da alama baya kusa ne
Adede wannan lokacin aka kawo mutanan kasuwa, d'an taxi ya saukesu da kayansu niqi niqi a hannu
Ishraqa acikin Mota tana kuka taga maigadi bashida niyyar budewa kawai saita Bude murfin motar tafuto, idanunta sunyi jajir kasancewar ta farar balarabiya
Amina tana ganinta tasaki ledar hannunta qasa, faduwar abun da Ishraqa taji ne yasa tajuya ta kalli wajan, idanunta yahadu dana Amina, lokaci daya faduwar gaba ta ziyarcesu
Junansu suka zubawa ido suna Kallan kallo amma babu wanda yayiwa wani magana acikinsu, jikin Ishraqa yayi sanyi, kallon yarinyar take sosai tanaso tasan meyasa gabanta yake faduwa kawai daga haduwar su?

Amina hamdala kawai take a ranta, batasan meyasa ba haka nan taji Allah ya d'ora mata son matar, komai nata birgeta yake, musanman yanda take kwalliya,Anya bazata koyi irin kwalliyar matar nan ba?
Chapter 19 · 0% Book details