← Book details Insaaf Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 53

Sashe 30

Insaaf Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Takawarku lafiya masoyan Insaaf, sharhi please
Amnah
[2/20, 10:32 PM] El~Yaqoub: INSAAF
Writing by:Amnah El~Yaqoub
31&32
Like my page on Facebook
https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493
Ina qara Bawa masoyan wannan littafi hakuri sakamakon Jina Shiru da sukayi kwana biyu
Banajin dadi ne wallahi, Mura ce take damuna dakuma ciwon kai sosai
, amma Alhamdulillahi yanzu dad'an sauqi, wanda suka sanni abaya nasan zasumin uzuri saboda inde nafara littafi kullum sainayi update, wanda suka kirani sukamin yajiki nagode sosai, Allah yasaka da Alkhairi yabar zumunci, nagode
________
Sai alokacin Amjad yagane abinda yasa mamy tayi masa haka, cikin kuka yafice daga gidan, yabi bayansu Daddy
Ishraqa kuwa Cikin sauri tafuto daga d'akin tana dube dube, amma inaaa!
babu ko alamar Amina, da gudu tadawo wajan El Hameed, Shima gaba daya ya rikice, cikin tashin hankali yace "ina take?"
Hawaye sha6e-sha6e Akan fuskarta tace "bangantaba Hameed, nashiga uku na, Hameed Insaaf ta gudu wallahi, Bata sona"
Cikin mamaki Mamy tace "Insaaf kuma?, me kike nufi Ishraqa?"
Wajansu ta nufa cike da tashin hankali tace "Mamy wallahi itace, 'yatace Insaaf, mamy Minal itace Insaaf d'ina, nashiga uku na Yarinya ta nake Kora daga gidanan"
gaban gogan namu yayi wata irin faduwa, Minal itace Insaaf?

Tayaya?

Meyake shirin faruwa ne yau?Wai Ishraqa Tana nufin 'yarta ya aura?

Innalillah.... wannan abun kunya dame yayi kama?

Shikkenan kuma, girmansa yariga yafadi, Ishraqa tayi nasara akansa
Ahankali yasa ka hannayensa biyu ya dafe kansa
Mamy tace "yau munga ta kanmu, Ishraqa maganar dakike fada kuwa da gaske ne?"
Ishraqa tayi Shiru tana kuka Bata Bawa mamy Amsa ba, El-Hameed ne yagoge hawayen Idonsa yace "Ba sunan ta Minal ba Hajiya, sunan ta Insaaf, shine sunan dana saka mata da kaina, sunan mahaifiyata taci"
Mamy tace "amma Yaya akai kuka ganeta?

Tsawon lokacin tana tare damu amma Baku ganeta ba"
Kai tsaye yace "ta kayanta hajiya, wanda yake jikinta lokacin da muka rabu da'ita, dakuma zoben dana siya mata da kaina"
Duk wannan Bayanin da ake Asim bai dago kansa ba
Abin duniya yataru yayi masa yawa, kwata kwata yaqi kallon su, amma Yana jinsu Sarai
Ishraqa ce tataso takama hannunsa, cikin kuka tace "Asim katashi muje ka nemomin yarinya ta,Insaaf tayi fishi dani tabarni, Dan Allah Asim katashi" taqarasa maganar Tana kuka sosai
Dago kansa yayi ya kalleta, yakai dubansa zuwa hannunta, duk ta kamashi ta rirriqe kamar tana tsoron a qwace shi,inda ace Dane, babu abinda zai Hana ya riqeta suje, saboda amintarsu tazama 'yan'uwan taka, amma yanzu, bazai iyuba, matsayin ta ya sauya da yanda ya santa abaya, Ahankali yazare hannunsa daga cikin nata
Kuma har lokacin bece da'ita uffan ba
Amrah kam mamaki yagama kashe ta, ashe duk abin nan dayake faruwa da dukiyar Minal suke taqama?

Ashe kudinta ne yarufa musu asiri?

Mamy ta kalleshi tace "Asim ai bamu gata zama ba, tashi zakayi mubi bayan yarinyar nan, duk abinda ya faru ai acikin rashin sanine"
"wanne irin rashin sani Mamy?

Ishraqa yarinya ce? kina gani tana yimata fada Nima da kaina nayi mata magana, amma taqi saurare na, yanzu ne hakan ya janyo?"
Cikin kuka itama tace "Allah katashi ka nemomin yarinyata"
Kallanta yayi, shi Sai yanzu nema yake ganin wasu abubuwa wanda Minal takeyi kamar Ishraqa, komai kuka, abu kadan kuka, yanzu duba yanda take kuka saikace wanda aka yankata
Ajiyar zuciya yayi, ya tashi, gaba dayansu suka dunguma suka bar gidan
*** ****** ***
Ko kallon gabanta batayi, haka take tafiya tana share hawaye, ba tasan inda zataba, ba tasan ina ta nufa ba, ko'ina ma jefa kafarta takeyi, saida tayi tafiya me Nisa sannan tanemi waje ta zauna, ta kifa kanta Akan cin yarta tana kuka mai cin rai, haqiqa rashin iyaye bashida dadi, amma ayau kam ta haqura danata Iyayen, Gara tatafi wata duniyar daban ta shimfida sabuwar rayuwa, to Amma ina zata?

Su Inna sun koreta, maigari yace suma subar masa garinsa, idan Takoma Garin ma, haka zata zama kamar wata mujiya acikinsu, dole tabar Garin nan Takoma wani Garin inda ba'asanta ba, ba'asan wacece itaba, to Amma akwai auren Asim a kanta, Yaya zatayi dashi, lokaci daya zuciyarta ta ambata mata sunan kotu
Cikin sauri tatashi tsaye ta goge hawayen idonta, afili tace "Gara inje kotu ta rabani da wannan auren"
Hannunta ta kalla batada kudi ko sisi, kayanta da suke hannunta taduba ko zataga kudin sadakinta data ajiye, nanma taga bayanan, kenan ta barshi agidan, to Yaya zatayi?

Dan qaramin zoben gold dinta ta kalla, kode shi zataje ta siyar tayi kudin Mota?

Girgiza kanta tayi,tasake kallon zoben, afili ta furta "to amfanin me zakamin?

Suma wanda suka sakamin zoben sun rabu dani, tayaya Nikuma zanci gaba da zama dakai" tana fadar haka tayi jifa da zoben, rigar ma ta wullar da'ita
Tundaga nesa yake hangota tana jifa da kaya, mamaki ya kamashi, kamar Minal yake hangowa, to meyake faruwa ya ganta anan?

Ita daya kamata ya ganta agida yadauke ta su tafi makaranta?

Gudun motarsa yaqara, Yana zuwa dede inda take ya tsaya, yafuto da sauri ya qarasa wajan ta yace "Minal, mekike anan?"
Kallansa tayi tace "Yaya Muhsin"
"na'am Minal, ina zakije?

Asim Yamin waya dasafe inzo na daukeki zan kaiki makaranta"
Girgiza kanta tayi tace "babu komai Yaya Muhsin, ka kaini kotu Dan Allah"
"kotu kuma?

Meza kiyi a kotu?"
"Yaya Muhsin inaso alqali yaraba aurena da Yaya Asim"
Kallan mamaki yake jifanta dashi, yarinyar nan kuwa tasan yanda Asim yake kishinta?

Saboda me zatace Araba musu aure?

Anya kuwa babu abinda yake faruwa?, Ajiyar zuciya yayi sannan yace "Kinga shigo Mota mu tafi"
Babu musu tashiga motar, shikuma ya tattara mata kayan data zubar awajan, suka dauki hanyar zuwa gidansa
*** ****** ***
Duk gaba dayansu kowa Hankalinsa atashe yake, musanman Ishraqa da El-Hameed, Dan kwalin abayar datayi rolling dashi tuni gefensa yajiqe da hawaye
El-Hameed dinne ma me dauria, Asim kuwa abu ne yataru yazame masa goma da a shirin, ga 6atan wannan yarinyar, ga kuma Amjad, duk Hankalinsa ya tashi,gashi wajan ba wajene dazaka dinga ganin mutane sosai ba bare ka tambayesu kosun ganta
Wayar sace tayi qara, amma be kula ta ba bare yadauka, Sai a Karo na biyu ne yad'auka tare da fadin "Muhsin"
Daga daya bangaren Muhsin yace "Abokina meyake faruwa ne?

Naga matarka a hanya tana watsi da kaya"
"tana ina Muhsin?

Ne manta mukeyi"
"tana gidana, suna tare da Nabila"
"Okey, gamu nan zuwa"
Yana kashe waya Ishraqa tazuba masa ido tana jira taji abinda zai fada musu, mamy tace "ya'akayi ne Asim?"
Cikeda aji yace "tana gidan Muhsin"
El-Hameed yace "Alhamdulillahi, Allah abin godia Bari nakira Hammudi"
Ishraqa kuwa murmushi take, yayinda wani hawayen farin ciki yake zubo mata, juyawa sukai suka koma daya layin, inda gidan Muhsin yake, El-Hameed Sai dariya yake, yakira Hammudi.

Hammudi Yana dauka yace "Wajadnaha ya Hammudi, Wajadnaha allailah, kuntu masrur wallahi"
Daga daya bangaren Hammudi yake tambayar sa "wa suka samu?"
Ishraqa ta qwace wayar tace "Insaaf"
Haka suka dinga waya da Hammudi har suka qaraso gidan Muhsin, su mamy da Asim de kawai kallonsu suke
Yanda suke farin-ciki abin tausayi
Har rige-rigen shiga falon Muhsin suke, Suna shiga kuwa suka ganta azaune itada Nabila matar Muhsin, duk yanda Muhsin yake Bata labarin amaryar Asim yarinya ce batayi tunanin takai hakaba, a ganinta tsaf Minal din zata iya dauke Asim
El-Hameed Yana qarasawa cikin falon Dasauri yaje ya rungume ta, Ishraqa kuwa tana zuwa Sai tayi turus jikinta duk yayi sanyi, amma haka ta zauna tana kallonsu itada El Hameed tana murmushi, yayinda hawayen farin-ciki yake zubo mata
Mamaki ne ya kama Amina, takai kallonta zuwa ga mamy taga itama Sai Fara'ah take, hakama Amrah, sai alokacin yashigo falon shida Muhsin, hannunsa Yana zube cikin aljihun Wandon Suit din dake jikinsa, saide babu jacket din yacire ta, kana iya ganin yanda murdaddan hannunsa yake ta cikin rigar, kallo daya sukai wa juna kowa ya dauke kansa, Muhsin Yana kallonsu gaba dayansu
Mamy ta kalli Amina tace "Minal 'yata, kigodewa Allah, yau Allah ya baiyana miki Iyayen ki"
Dasauri tatashi tsaye tana yiwa mamy wani irin kallo, mamy tasake jinjina mata kanta tace "hakane Minal, Ishraqa da El-Hameed sune Iyayen ki, yau Allah ya karbi Addu'ar ki"
Girgiza kanta tayi, idanunta qamas babu kuka, tace "mamy aini banida wasu iyaye, niba iyayena bane, suje su nemi 'yarsu"
Gaba daya falon babu wanda Bata Bawa mamaki ba, jikin El-Hameed yayi sanyi, ya kalli Ishraqa, itama kallansa tayi, wani irin kuka me ciwo yazo mata
Takai hannunta takamo na Minal sannan tace "Insaaf...

Karki min haka 'yata, nice mahaifiyar ki, Kinga mahaifin ki Insaaf"
Taqarasa maganar tana nuna mata El-Hameed, fizge hannunta tayi daga cikin na Ishraqa, tafada jikin mamy tana kuka sosai
Dasauri Ishraqa da El-Hameed suka taso zasuzo wajan ta, mamy ta daga musu hannu batare datace komai ba, sannan takama hannun Minal din suka futo daga gidan
Har sukazo harabar gidan mamy Bata saketa ba, daga Ishraqa har El-Hameed jikinsu yayi bala'in yin sanyi
Saida suka shiga gidan Asim ya kalli Muhsin yace "yarinyar nan tanada damuwa wallahi, duk Sai wahalar damu take, Sai shagwaba takewa mutane sukuma su mamy suna biye mata"
Muhsin yace "a a Asim, ya kamata kuyi mata uzuri, damuwar datake ciki ai tanada yawa, kuma gashi kaima kace ba sonta kake ba, aikuwa kaga ni banga laifin taba" ya qarasa maganar yanaso yaga yanayin Asim din
Shikuma Asim kafadarsa ya d'aga yace "tokai yanzu kana ganin ya dace ace na auri 'yar Ishraqa?

Da girmana da komai Sai a tambayeni wanake aure ince 'yar qawata,
Abin da kunya Muhsin, ita kanta yarinyar ba tafi karfin in raineta ba"
Muhsin yayi wani qaramin murmushi yace "Asim bafa haram bane, ni banga abin damuwa Akan haka ba, koda yake, ai itama yarinyar baso take ba, shikkenan saika sauwaqe mata ta auri wanda ra'ayinsu yazo daya, saboda kaga dazu ma Dana hadu da'ita roqona take yi Dan Allah nakaita kotu Araba aurenka danata "
Cikin sauri ya kalli Muhsin tare da zaro manyan idanuwansa yace"kotu fa kace Muhsin"
Dariya takama Muhsin, amma saiya danne yace "Of course, abinda tafadamin kenan, shine nace tayi hakuri muje gida"
"yanzu ita har tasan a kaita kotu Araba aure?
Chapter 30 · 0% Book details