← Book details Insaaf Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 53

Sashe 8

Insaaf Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Dasauri ta dauki kayanta tadora aka tabishi (
Yanajin tafiyarta a bayansa amma ko kallon inda take Baiyi ba, suna tafiya babu wanda yake magana Sai kukanta da yake barazanar rabe masa kansa gida biyu wanda yake masa matsanancin ciwo, ita kuwa kuka take kamar hauka, barinma idan tatuna maganar su Inna, ita yar tsuntuwa ce, haka suka dinga tafiya har sukai nisa sosai daga qauyen suna shirin shiga wani qauyen nagaba
Yagaji sosai da wannan tafiya, shikansa baima San ina sukeyi ba, ga zazzabi daya rufeshi, sanyi yakeji a jikinsa kamar Ana zuba masa ruwan qanqara, ya kamata subar tafiyar haka su qarasa titi su nemi Mota
Har zuwa wannan lokacin Amina kuka take, har mamakin kukanta yake kwata kwata Bata gajiya, adede wata bishiya ya tsaya batare da tunanin komai ba yazube awajan tare da riqe kansa da yake masa mugun ciwo
Tana ganin haka kukanta ya qaru, bakkonta dake kanta tasauke qasa, sannan ta tsugunna akusa dashi har jikinta Yana gogar nasa, cikin muryar kuka tace "meyake damunka?, kaima mutuwa zakayi ka barni ko?, nikam nashiga ukuna..." ta qarasa maganar cikin matsanancin kuka tana Dora hannunta a kanta (
Jinta akusa dashi,dakuma sanyin dayakeji yasa yafuzgota jikinsa kozaiji dama dama, al'amarin yabawa Amina tsoro, harta zaro manyan idonta tana kallansa ganin yanda ya rungume ta hartanajin yanda Boobs dinta suka kwanta Akan faffad'an qirjinsa, shi kansa ya karbi saqon yanda ya kamata dukda Yana cikin yanayin zazzabi (
Rawar sanyi da taga yanayi anan tagane nufinsa, Ahankali tasa hannu tacire babban dankwalin atamfar da yake kanta, iskar bishiyar da suke zaune takad'a dogon gashinta zuwa fuskar Asim, idanunsa a lumshe suke, amma Sarai yaji saukar gashin nata, hannunta tasa tajanye gashinta sannan tarufe masa jikinsa da d'ankwalin
*** ***** ***
A bangaren isyaku kuwa, Yana zuwa police station jikinsa har rawa yake yace Yana so ahadashi da d.p.o
kofur Shamsu yakalleshi "lafiya kake neman sa?

Idan qara kakawo muzaka yiwa bayani"
"Yallabai ba qara nakawo ba, abinda nakawo ai ya girmi qara Yallabai,"
Yayi qasa-qasa da muryarsa yace "kuma zaku samu naku kason, zanbaku wani abu daga ciki"
Sunajin furucin isyaku suka fara washe baki, nan da nan suka kaishi har office din d.p.o, isyaku ya kalleshi da kyau yace "Yallabai ina mutumin nan da kwamishinan 'yan sanda yabada cigiyar sa?

"
D.p.o ya kalleshi da kyau yace "eh inajin ka meyafaru"
Saida ya kalli gefe da gefensa kamar Yana tsoro Kar wani yaji shi (
sannan yace "to yanzu haka Yana nan a cikin qauyenmu, inaso kabani yansanda Mota guda, muje ataho dashi" (
D.p.o ya kalli isyaku da kyau yace "ka tabbata abinda kake fadamin gaskiya ne?"
Isyaku yasa ka hannunsa dede fuskarsa yanuna idanunsa duka biyun yace "ganin Idona naganshi Yallabai" (
D.p.o yasake kallansa da kyau yanaso ya Gano gaskiyar abinda isyaku yake fada masa,Anya kuwa gaskiya ne?

Tayaya mutum babba kamar Asim zai Iya zama a cikin wannan qauyen?

Anya ba qarya Yaron nan yake musu ba?
cikin zaquwa isyaku ya
ce "haba Yallabai, me muke jirane?

Kabasu umarni kawai mu tafi, ha'ah"
Yaqarasa maganar tasa cikin gundura (
D.p.o yayi Ajiyar zuciya yace "tunda hakane, ainima banga ta zamaba, dani za'aje, tashi mutafi" (
Murna ta kama isyaku, nan da nan kuwa aka cika Mota da yansanda kamar yanda isyaku ya buqata, saide suna zuwa kofar gidan Malam Buba sukaga babu Asim babu dalilinsa,(
Sai sauran mutane dasuka Gama watsewa daga jana'izar Yaya Ammar, dakuma Inna da baba dasuka kwashi kayansu a amalanke da alama Garin zasu Bari
Idanun isyaku yayi wiqi-wiqi ya raina fata (
D.p.o ya kalleshi cikin bacin rai yace "ina yake?"
Isyaku yayi Shiru kamar andoka masa sanda yakasa d'ago kansa yakalli d.p.o bare su hada ido dashi (
D.p.o Yana ganin alamar qarya isyaku ya shimfida musu nan take ya kalli yaransa yace "ku saukeshi a motar nan kuyi masa dukan kawo wuqa"
Isyaku yanajin haka yadora hannunsa aka (
) yace "nashiga uku ni isyaku namutu na lalace, Yallabai shi dukan dama harda na kawo wuqa?"
D.p.o yace "zaka ganshi yanzu-yanzu" yaqare maganar Yana Kallan yaransa
Nan da nan kuwa suka gane ma'anar kallon nasa, suka jefo isyaku waje daga cikin motar suka hau dukansa kamar Allah ya aikosu, Sai ribd'arsa suke Yana ihun neman agaji (
Basubar isyaku ba saida suka nuna masa jiki, nan take zazzabin wahala ya rufeshi
*** ***** ***
Tun dazu yake hangosu daga gonar sa, yaga alama kamar matafiya ne, gashi har yamma tayi yanaso Shima yatafi gida, dama gewaya yazoyi gonar tasa
"bayin Allah lafiya kuwa kuke zaune awajan nan tun dazu?"
Ahankali ta dago kanta ta kalleshi, babban mutum ne daya manyanta sosai, kansa Yana dauke da rawani irinna malamai, cikin sanyin murya tace "tafiya muke, bashida lafiya ne"
Mutumin ya kalleta yaga idonta duk hawaye sun bushe, ya kalli Asim daya riqe Amina a jikinsa yaga bacci yake, yace "Ashsha, Aida kin nemi temako yarinya, ku taso mu qarasa gidana yasha magani,tasoshi"
Duniyar tunani tafada, to ita dabatasan sunan saba tayaya zata kirashi harya tashi?

Daga wa mutumin kai tayi alamun amsawa, Ahankali tafara zare jikinta daga nasa, cikin baccinsa yaji zatabar jikinsa yasaka hannu ya sake rungume ta
Mutumin ya kallesu yayi murmushi da alama de ma'aurata ne, ya kalleta yace "tashi mijin naki mana"
(miji) kalmar tadaki dodon kunnanta, Allah yakiyaye tasake yin waani auren a yanzu, idan tayi aure ma ai batayi wa kanta adalci ba, tunda tasan haqqin wanda ta aura zai rataya awuyanta ne idan ya mutu
Hannunta takai kan muscles
dinsa tafara tashinsa, Ahankali ya dago kansa tare da Bude lumsassun idanunsa da sukai ja saboda tsabar zazzabi ya kalleta, tace "Katashi mutafi"
Mutumin dake tsaye ma yace "kuyi hakuri na tasheku, kuzo muje gidana ku huta gashinan babu Nisa"
Ahankali yamiqe tsaye Yana runtse Idonsa, yadora hannunsa Akan goshinsa daya Sara masa kasancewar ya tashi tsaye,jiyayi kansa Yana juyawa yatafi luuu zai Fadi, cikin sauri Amina tatareshi yazube ajikinta, kansa ya sauka adede qirjinta, gabanta yayi mugun faduwa,meta aikata haka?

Wannan mutumin gaba daya yagama jin komai na jikinta yau, Sai bayan ta riqeshi ne take tambayar kanta mema yakaita tareshi batabarshi yafadi ba?

"subhanallah..." cewar wannan mutumin, yaci gaba da fadin "kamashi muje, sannu bawan Allah"
Haka Amina tariqeshi ajikinta, Shima mutumin yariqe masa hannu suka tafi, basu yi wata tafiya mai nisaba suka qara so kofar gidansa da yake cikeda almajirai sunata karatun Allo
Kai tsaye gidansa yakaisu, matarsa tayi musu tarba mai kyau, takaisu wani daki atsakar gidan dake gyare tsaf, harda shimfida, mutumin yadubi Asim yace "kwanta anan Yaro" ya sake Kallan matarsa yace "kawo musu abinci da ruwa, zanje nasiyo masa maganin zazzabi"
Matar ta Amsa masa sannan tafuta daga d'akin, Amina ta dubeshi tace "ga katifa nan ka kwanta"
Daga mata kai yayi alamun amsawa, sannan ya fara shirin kwanciya Akan katifar, tsugunnawa tayi asetin kansa tasaka hannu tana gyara masa fillon daya Dora kansa akai
Yasaba duk lokacin dabayajin dadi Mamy ce take zama atare dashi, musanman idan Yana ciwon kai ta dinga yimasa massage akansa kenan harsai yadanji dama dama, Amina kuwa tana gyara masa fillon tafara kokarin miqewa ahankali yasaka hannunsa da yayi zafi sosai yariqeta, bin hannun nasa tayi da kallo fari tas dashi, hannunta tafara zarewa ya sake damqe hannun nata cikin nasa, babu yanda ta'iya haka tadawo wajan tazauna tayi Shiru tana kallon ikon Allah, shikuwa bargon dake kan shimfidar yaja yarufa dashi har kansa
Sai gab da magrib maigidan yadawo, har lokacin tana nan zaune a d'akin tayi tagumi,saide ta qwace hannunta daga cikin nasa dataga yayi bacci, abincin da matar ta kawo musu ma cokali daya tayi tarufe abincin, maganin ya ajiye yace "tasheshi yaci abincin yasha magani"
Fillon nasa tafara bugawa, daqyar ya tashi, maigidan yabashi abincin, daqyar yaci kadan, Ahankali yace "ya'isa" kallansa tayi cikin sauri, tun taho warsu daga qauyensus Sai yanzu taji yayi magana, ga fuskarsa a daure, mamaki ya kamata tsawon wannan lokacin suna tafiya Amma beyi mata magana ba
Maganin yabashi,Asim ya kalli maganin ya yatsina fuska, sannan yace "banson magani" murmushi mutumin yayi, yace "haba dana Sai kace ba namiji ba kace bakason magani?

Kokuma saboda baku sanni bane shiyasa?

To sunana malam Ibrahim mai Allo, ni limamin Garin nan ne, ga mata ta can, nakawo ku gidanane kuhuta idan kaji sauqi bayan kwana biyu saiku tafi, bazan cutar daku ba Yaro"
Murmushin qarfin hali Asim yayi jin wannan dogon Bayani da yayi musu, Ahankali kamar me koyon magana yace "A a... ni.. dama can banso"
Malamin yayi murmushi ya ballo maganin yabawa Amina yace "toke yata karbi kibashi, wata qila ke kikasan Yanda kike bashi" (
Cikin inda inda tace "a a Nima fa bansan..."
Ganin zata tona musu asiri yasa Asim cikin sauri yabawa liman hannu, liman yabashi maganin, yaqyar ya'iya hadiye maganin har wani girgiza kansa yake kamar me iskokai (
Sannan yatashi yafuto domin yin alwala, Shima liman yafuto Yana tambayar sa menene sunan sune, basu fada masa ba, itade Amina bataji amsar daya bashi ba
Wajan karfe Tara na dare ta futo daga d'akin tazauna a tsakar gidan, liman yashigo gidan ya ganta azaune yace"yata meyasa baki kwanta ba har yanzu?
Chapter 8 · 0% Book details