Sashe 1
Insaaf Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Root Entry
WordDocument
0Table
Data
Normal
[2/3, 1:06 PM] El~Yaqoub: INSAAF
Writing by:Amnah El~Yaqoub
MARUBUCIYAR :
*DANA SANI*
*BURINAH*
*WAZAN ZABA?*
*SHALELAN BABA*
*NI DAKE*
*DANGI DAYA*
*INSAAF*
Like my page on Facebook
https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493
*Page Din farko nakane dan'uwa na,PRINCE ABBA BAKARYA, ubangiji Allah yabar zumunci, Amnah tana yinka sosai
Dasunan Allah mai rahma mai jin qai, ya Allah yanda nafara wannan littafin lafiya, Allah kabani ikon gamawa lafiya, kuskuren da zan rubuta wanda nasani, da wanda bansaniba, Allah yayafe min, Allah ka haneni rubuta abinda zaiyi Sanadin tashin hankalin wani ko wata.
Dan girman Allah, masu doramin littafi a channel dinsu su daina, wallahi tallahi tunda nafara rubuta littafi, bantaba shan wahala irin yanda Nasha wajan rubuta labarin DANGI DAYA ba, amma abin baqin ciki ina gamawa kuka sacemin kuka doramin a channel dinku, FARAR SAQA TV wallahi idan kuka sake doramin littafi a YouTube zanyi reporting dinku a lalata channel Din, kuntara views din banza
, banyi littafin kudi ba banga dalilin dazaisa kunemi kudi da littafi naba, inada Damar dazan siyar dashi amma ban siyar ba,Bana saka number ta a littafi, amma acikin littafin littafin DANGI DAYA nasaka number brother na, idan kunyi masa magana zai sanar dani, yanzu de na roqeku kudaina, nagaba kuwa bazan roqeku ba.
To wannan Karon alqalamina yatafi Lagos, kuyi hakuri wannan littafin zakuci Karo da kuka,
dakuma emogi d'an kadan
Bazan ziga littafina ba, kakaranta kaji yanda yake da kanka
*A taqaice*
Labarin INSAAF labari ne da taurarin ciki suke fuskantar qalubale iri-iri, tauraron dakuma tauraruwar, kowa da irin nasa qalubalen, wanda daga qarshe zan warware muku komai insha Allah
__________
Manyan motoci ne guda biyar suke sharara gudu a babban titin dazai kaika mubi local government, Cikin jihar Adamawa, sosai suke gudu kamar sun samu titin gidansu, duka motocin guda hudu farare ne, kuma kowacce daga cikin su number motor tana dauke da sunan INSAAF, guda dayace baqar qirar Range rover take dauke da number LSR Lagos Surulere, daya daga cikin local government dake Lagos state, sosai suke gudu Bana wasaba, motocin farare biyu agaba, biyu abaya, Sai kuma baqar motar datake tsakiyarsu
Su biyu ne azaune a bayan motar shida yayansa, gaba dayansu suna sanye cikin suit wadda tayi bala'in yimusu kyau
Babban Hankalinsa Yana kan computer dake kan cinyar sa Yana typing cikin sauri, computer na qarewa kallo launin brown, amma maimakon aga sunan company computer daya qerata sainaci Karo da sunan INSAAF
Agogon dake daure a tsintsinyar hannunsa qirar Gucci ya kalla yasaki wani gajeren tsaki, sannan ya maida Hankalinsa kan abinda yake
matashin saurayin dake gefensa kyakkyawan gaske, suna mutuqar kama da juna, saide shi bekai shi shekaru ba, window dake gefensa yagama kalla bayan sunzo wucewa ta wani qauye dake kusa da Mubi, sannan ya juyo ya fuskanci dayan yace "Yaya, kasan wannan qauyen fa mukazo nida Mamy last year munraba musu zakkah, wallahi Yaya nide qauyen Yamin
, Shiru babu hayaniya, gashi lafiya muka Gama abinda yakawo mu muka tafi"
Shiru yayi Yana jiran yayan nasa yabashi amsa, amma Shiru kamar da dutse yake magana, kawai typing dinsa yake
Bata fuska yayi kalar shagwaba ya kalleshi sosai "Yaya magana fa nakema"
Batare daya kalli qauyen ba Hankalinsa Yana kan abinda yake yace masa "naji"
Shima da yaji irin amsar daya samu Sai yayi Shiru bai sake magana ba, ya rungume hannunsa a qirjinsa Yana Kallan window tare da tunanin Mamynsa, Yana fatan inama ace ta biyosu
*** ***** ***
"AMINA!"
cikin sauri tafuto daga cikin dakinta tana daura dankwali a kanta, sanye take cikin atamfa wata kod'ad'd'iya, duk da ta daura dankwali hakan bai Hana gashin kanta mai tsawo da santsi futowa ba,Allah yayi mata baiwar gashi sosai me matuqar tsawo da sheqi,wani sillallan takalmi tasaka tace "Inna gani"
"yauwa Aminatuwa 'yar albarka dauki tulun nan kisamo mana ruwa mudora abinci, Kinga yayanki baya nan, kuma wajan akwai Nisa, Dan Allah Karki tsaya shirme a hanya kinji ko"
Ahankali cikin sanyinta tace "to Inna"
Sannan ta dauki tulun tafice daga gidan batare data saka ko mayafi ba
Tana cikin tafiya tana yar waqarsu ta dandali ta hangi wata majalissa duk maza ne sunata fira suna daria,Sai masu shan rake suma sunata nishadi, mutum daya ne daga cikinsu ya hango tahowarta ya fadawa sauran, lokaci daya majalissar ta watse, tuni wajan yakoma kamar ba'a halicci mutane, mamaki ya kamata, kawai saita girgiza kanta tawuce
gidan qawarta lubabatu tashiga bakinta dauke da sallama,ta tarar dasu zaune a tsakar gida suna hira itada goggonta, lubabatu tana ganinta tace "Amina sannu da zuwa, kamar kinsan yanzu nake shirin biya miki kozakije Debo ruwa"
Itama murmushi tayi, cikin sanyin muryarta mai zaqi tace "Tona hutar dake, tashi mutafi"
Tamaida Kallan ta wajan goggo zata gaisheta, amma kafin ma tayi magana goggo tace "Ai Amina saide kije ke kadai, lubabatu tanamin aiki"
Cikin tsananin mamaki ta kalli lubabatu taga azaune taganta babu abinda take, cikin sanyin jiki tace "to goggo" sannan tajuya zata fita daga gidan
Lubabatu ta tashi zata bita, cikin tsawa goggo tace "ke!!
Dawo ki zauna"
Kamar zatai kuka tace "goggo rakata zanyi kofar gida"
Cikin Kallan rashin mutunci goggo ta watsawa Amina harara, sannan tacewa lubabatu " Ai basai kin rakata Bama, da tare kuka shigo?
Ba'ita kadai tashigo ba?
To rakiyar ta'isa haka daga nan bakin kofa ma"
Amina tana ganin haka, tasake girgiza kanta Akaro na biyu, wani irin abu yatare mata maqoshi, kuka takeso tayi amma tahana kanta, saide manyan idanuwanta sun kada sunyi jajir, cikin sauri tafice daga gidan
Tafuto kenan daga gidan su lubabatu taga isyaku yayan lubabatu suna zaune shida abokansa kusan su biyar, isyaku Sai tsari yake, Sai zuba surutu yake suna dariya, kasancewar sa mutum mai yawan surutu, ta gabansu tazo ta wuce amma abin mamakin shine su basu guduba amma cikin sauri suka juya mata baya, ko kadan sunqi yarda su kalleta
Ahankali ta daga kanta taga yanda mutane suke gudunta, lokaci daya taji hawaye masu dumi sun silalo daga idanuwanta, wannan Karon batayi kokarin Hana kanta kuka ba, sosai take hawaye tana tafiya cikin sauri, tun tana yin kuka na hawaye harta dawo tanayinsa da sheshsheka, in banda tanada karfin hali da tuni tayi wurgi da tulun Takoma gida, amma ahakan ta daure tanufi hanyar Rafi ita kadai
*** ***** ***
Cike da qwarewa motocin suka tsaya awajan taron Bude daya daga cikin Babban Companynsu dake Mubi local government
An tsara sunan company asama mai taken....