Sashe 52
Dream Girl Part 2 Complete Hausa Novel · about 9 min read
Ranar muna zaune a gida saeed ya kira khaleed aunty fareedah na asibiti tana labour, muka dunguma mukayi asibiti, kusan awa 4 amma shuru hankalin kowa ya tashi, sai daga baya doctors suka fito da sukayi mata aiki, ta haihu ta haifi 'ya mace, saidai muyi hakuri Allah yayi mata rasuwa tsabar kaduwa take nakuda ta tasomin akayi labour room dani.
Yaya saeed kuwa anan wurin ya zube a some, kausar ma bleeding ta farayi aka dauketa itama, khaleed ya zauce ya rasa inama zaisa kanshi, wannan tashin hankali.
Operation akayimin aka ciremin 'ya' yana duk 3 maza, akasakasu a incubator dan wata bakwai ne basu gama kwari ba, bani na farfado ba sai bayan kwana 3, da tashina kuma da zancen aunty fareedah na farka, kowa wurin kuka yakeyi. Barin ma khaleed da yayi uwar rama cikin kwanakinnan 3, ni ba ko ta cikina nake ba dan kwata-kwata banma lura da babu cikin ba.
Sai a lokacin nasan kausar miscarriage tayi akan kaduwa, saeed kuwa haukane kawai baiyi ba, saidai fa kawai muyi hakuri aunty fareedah ta tafi saidai ayimata addu'a Allah ya gafarta mata munyi rashi.
Gida na koma mama taci gaba da kula dani da yarana 3 maza, da sukaci sunan Umar faruk, Abubakar siddik, da kuma Aliyu. Akan yanda haihuwar tazo ba wani shagali da akayi saidai fatan Allah ya raya, kausar kuwa ita ta karbi jaririyar da aunty fareedah da ta haifa, ta dinga shayar da ita.
Khaleed kuwa kullum yana gida makale dani da yaransa, mama kuwa gyara takemin na musamman ta matsu na cika arba'in, ta gangamani na koma gidana, dan khaleed ko kunyarta bayaji dan agabanta zai iya rungumeni ba abunda ya masa zafi.
[12/25, 9:01 AM] Deejah Abdul💗💖: Dream girl na deejah abdul
1⃣9⃣6⃣ Bayan na koma gidana kuwa sabon amarci muka bude, duk sai rama nike ga rigimar yara 3 ga ta ubansu danshi wai kullum sabuwa yake jina bana taba isarsa.
Kausar kuwa saida tayi dagaske kan tasamu saeed ya dan dawo normal, ta zama uwar 'ya'ya 3 kuma duk diyan aunty fareedah, kai bakace ba ita ta haifesu ba.
Bayan shekara daya, suhaila tayi candy muka shiga bikinta itada yaya musty, yarana sunyi bul bul gwanin sha' awa, kowa son daukarsu yake, bare mom da dad yanda sukeji da yarannan kamar su hadiyesu, ko yaushe suna gidan mom, nima nafison ta daukesu dan nadan sarara shegiyar barna ce da su, amma da ubansu ya dawo zai kwasosu waishifa baya jin dadin zaman gidan idan ba sojojinsa.
A wurin bikin suhailat ne, mom ta gayyato matar deputy governor, ana mukejin labarin husnah, wai tana prison a america, ankamata da laifin drug trafficking, sunyi mata life imprisonment, kuka take kowa saida ta bashi tausayi, gashi deputy governor ya sake aurensa har matarsa ta haihu ita kuwa, shikenan dan ya juyar mata da mahaifa bazata kara haihuwa ba, husnah kawai ta mallaka ga abunda ya faru da ita, kowa wurin ya tausayamata, saidai fatan Allah ya kiyaye gaba.
Mungama bikin suhailat muka kaita abuja da yake yaya musty ya samu aiki a chan, saidai fatar Allah ya basu zama lafiya, kausar kuwa na dauke da karamin cikinta gashi ita ke kula da little fareedah dan sunan uwarta taci shiyasa suke ji da ita sosai gashi yarinyar sak uwarta batabar komai nata ba kamar antsaga kara.
🍇🍇🍇 Bayan shekara biyar🍎🍎🍎
Ameerah ce da khaleed, da kuma yaransu 3 keta aikin buga ball, kausar da saeed sukayi sallamah suka shigo, tareda 'ya'yansu 4, uku na aunty fareedah maza biyu da kuma little fareedah, sai danda kausar ta haifa Muhammad ana kiransa ameer, gata kuma dauke da wanin cikin, yaran suka dunguma suka fada foot ball field din suka fara wasa da junansu, saeed yace ai sai kufito ku barwa yara wurin suyi wasarsu tinda ku bakwa girmah.
Kausar tace mutafi ciki mubarsu anan suyi wasa, dane bayan khaleed nayi nace ni goyani nagaji bazan iya tafiya ba, cewa yayi kefa kin kara nauyi yanzu ba kamar da ba ni bazan iya goyaki ba, gefe na koma ina bubbuga kafa da kukan shagwaba, saida yaje ya duka na hau bayan sannan muka wuce falo.
Saeed da kausar sai girgiza kai suke suna dariya, kukan dai ko a gaban yara ma bakwa girma, kausar tace ni kuwa sister inlawa yaushe zaki kara haihuwa ne? Ni kinga 'ya' yana 4 ga na biyar a cikina, akayi dariya sannu uwar biyar, tace i'm serious fa ko suhailat de haihuwarta biyu yanzu, cewa nayi ni 'yan 3 dina fa sun isheni.
Khaleed ya mike tsaye, ai wallahi baki isaba, ashe kuwa akwai zancen karo amarya ta haifamin yara, bari ma kiga na nemo tsohuwar matats salmah may b yanzu ta shiryu tinda dama ba sona kike ba.
Kwalalo ido nayi har idona sun ciko, da hawaye, khaleed kuwa ya basar yasa call, sai chan naji yana cewa toh shikenan nagode kwarai ya kashe wayar ya dawo ya zauna jiki a sabule yasha mur.
Zuwa nayi na duka gabansa khaleed wasa kakeyi ko? Ya kauda kai gefe wanne irin wasa ni dagaske nake bayan bakya sona, hawaye suka kwararomin wallahi Allah ina sonka, son da nake maka bantaba yiwa ko wanne namiji a rayuwata ba, kaine namijim da na fara so a rayuwata, cikin mamaki ya kalloni, tsohon saurayinki fa da ya rasu? Juyawa nayi wurin saeed da kausar nace ku gayamasa gaskiya please.
Suka fashe da dariya, wato yau zancen kishiya zaisa a tona tsohon sirri, saeed ya fara kora masa bayani ba wani saurayi fa da nayi duk karyace, shi nakeso tin asali nayi karyane kawai dan na aureshi, khaleed baki bude ido bude yake kallon saeed.
[9/15, 2:51 PM] +234 706 332 8523: [12/25, 9:31 AM] Deejah Abdul💗💖: Dream girl na deejah abdul
1⃣9⃣7⃣ muka fashe masa da dariya, yace lallai yarinyarnan kin iya acting sosai, kuma ku nan duk daku aka shirya min wannan ko? Shine kikayita wahalardani kina nunamin bakya sona? Nace ai soyayar taka sai da nayi dagaske nasamu, nima nasha wahala kai bakayi komai ba ma.
Kausar tace kaima yaya saeed fa kadaina yiwa yayana dariya dan, kaima bakasan cewa ni naganka inaso har mom ta ganeba, ta kiraka tace ta baka ni, da mamaki ya kallota, khaleed ya fashe da dariya shima yauwa kanwata kin ramamin, saeed yace lallai Matannan kun iya acting muka kyalkyale da dariya muka tafe, saeed yace khaleed nima na goyi da bayanka mu karo musu kishiya kawai, khaleed yace ni ae har nayi booking tsohuwar matata zan maida, tashi nayi da gudu na rikeshi ina kuka nidai ka dains banaso Allah yace ahaf ai sai nayi kuma, faduwa nayi kasa ina birgima da kuka ni wallahi banaso, zuwa yayi ya dagoni ya sharemin hawaye to kice kina sona inji, nace inasonka Allah, yace banji ba nace i love you, ya mike tsaye say it louder nadan bude murya nace i love you, yace ki kara fada, zuwa nayi daidai kunnensa na kwala masa ihu I LOVE YOU KHALEED ya dafe kunnensa zaki fasamin kunne, su kausar sai dariya suke.
Zuwa nayi naja hannunsa, ka fasa ko? Jawoni yayi ya zaunar, kwantar da hankali kinyi belin kanki, zancen babyn fa? Nace zan haifamaka dozin ma yace really? Na gyada kai, nace anjanye zancen salmar ko? Yadan bata fuska yace Allah ya kiyaye ameerana, ko mata sunkare a duniya meh zanyi da salmah? Ki kwantar da hankalinki salmah ma bata duniyar nan, nace kamar ya? Yace yanzu wayar da nayi aka gayamin achan germany abokan iskancinta suka kasheta, wai tana musu kwacen mata shine suka hadu suka kasheta, iyayenta ko gawarta basu samu ba dan konata sukayi, wai kankamesa nayi ina kuka, Allah yayi mana kyakkyawan karshe, masu hali irin na salmah Allah ya shiryar da su, dan ita dai karshenta baiyi kyau ba.
Wayata tayi kara, naga number mama, na dauka tace nazo gida wai saratu ce tazo, muka dunguma mukayi chan har yara, inkaganta abar tausayi tayi baki kirin dama farin na bleaching ne.
Labari ta shiga bamu tana kuka, wai tinda suka kwashe dukiyar kawu suka gudu, london suka tafi, achan ta hadu da wani saurayi shima dan nigeria, suka kulla soyayya har ta aureshi, ashe dan giyane, duk dare in yayo shansa sai ya hada itada hajiya asabe ya kwana dasu, haka ya maidasu matanshi su 2 ya kwanta dani ya kwanta da mom, daga karshe dai duk shi ya kwashe dukiyar ta koma hannunsa, da mukayi yunkurin guduwa, shi ya kamamu anan ya harbe mom ta mutu, ni kuma dakyar nasha, saida nayi yawon karuwanci a london sannan na samu kudin dawowa gida nigeria, yanzu haka ina dauke da cutar kanjamau ta fashe da kuka, kowa dai kuka ts nemi gafararmu muka yafe mata.
[12/25, 10:29 AM] Deejah Abdul💗💖: Dream girl na deejah abdul
1⃣9⃣8⃣
🍇🍇🍇THE END🍎🍎🍎
Kawu yayi gyaran murya yace ameerah kisa baki a maganar nan, tun shekarun baya nake biyar mamanki ta amince muyi aure taki, kuma wallahi Allah na chanja halayena, gidana ma ya dawo hannuna dan yanzu business dina yadan dawo all thanks to you and your husband da yake bani contracts, na kalli khaleed ya kannemin ido.
Gyaran murya nayi nace kawu karka damu ka turo magabatanka kawai ni na amince, mama ta dauko pillown kujera ta wurgomin ameerah yaushe kika zama uwata da ubana tashi tsaye nayi ina dariya toh mama ki amince mana, su umar suka fara tafi suna granny say yes please, kowa ya dinga cewa ta amince.
Tashi tayi tace toh shikenan iyayena na amince, gidan ya dauki sowa da tafi. Khaleed yazo ta bayana yana radamin a kunne, nima fa m eager to b a father again kizo muje gida, anan muka silale muka gudu gida, muka lula duniyar soyayya.
Aliyu da salim sunzama manyan mutane, suna aiki a sabon kamfanin da khaleed ya buda, sun shirya plan dinsu sai zuwa sukayi suka gayamana, aliyu zai auri siyama qanwar salim shi kuma salim zai auri fatima kanwar aliyu, kowa yayi farinciki da wannan plan din, sai biki muka fara shirye shirye bayan an daura auren mama da kawu shehu.
INA GAYYATAR DUK ILAHIRIN MASOYA WANNAN LITTAFI BIKIN SALIM DA FATIMA, ALIYU DA SIYAMA AMMA FA BANDA 'YAN WAWASO LOLZZZ.
alhamdulillahil lazi bini' imatihi ta timmussalihati, anan na dire wannan littafin nawa da na radawa dream girl, godiya ga Allah da yabani ikon farawa da kuma kammalawa, ina rokon Allah kuskuskuren da nayi a ciki Allah ya gafartamin, ladar da ke ciki kuma Allah ya bani, ina rokon duk wanda na batawa rai ta dalilin wannan littafi ya gafarceni banyi da niya ba.
JINJINA DA GODIYA GA MASOYA WANNAN LITTAFIN.
MY FACEBOOK GROUP DEEJAH ABDUL'S NOVELS THOUSANDS OF MEMBRS.
MY WATSAPP GROUP MEMBERS DEEJAH ABDUL'S NOVELS 1&2
FEENAT JA'AFAR GROUP MEMBERS
DAMARY GROUP MEMBERS
BEUTY RUSH MEMBRS
BE A LADY WITH CLASS MEMBRS
DA DUK WANI GROUP MEMBRS MASOYA WANNAN BOOK DIN DA BANSAKA BA, DA DUK WANI MASOYIN WANNAN LITTAFIN DA BANSAKABA A DUK INDA SUKE A FADIN DUNIYAR NAN INA MIKA GAISUWATA DA GODIYA A GAREKU.
GAISUWA TA MUSAMMAN A GAREKI MY ONE AND ONLY ELDER SIS NAFISA ABDULLAHI DUKAMAJE ALLAH YA RAYAMIKI YARANKI MINAL DA DADYNMU.
SADAUKARWA
Na sadaukar da wannan littafin ga mahaifina late Abdullahi Aliyu dukamaje, ina baran addu'a a wirinku duk wanda ya karanta wannan littafin yaji dadinsa, ya karu da kalma ko guda dayace a ciki, da ya tayani da addu'a Allah ya gafartawa mahaifina, da duk musulmin Allah da suka rigamu gidan gaskia.
ALHAMDULILLAH sai mun hadu a sabon littafina idan Allah ya bani iko mai kaunarku KHADIJAH ABDULLAHI ALIYU DUKAMAJE. (AKA DEEJAH ABDUL DREAM GIRL) NAGODE