Sashe 3
Dream Girl Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
sukuma mahaifansa sunqi su amince da haka, saidai ya kawo wacce yakeso sunbashi one week time, shikuma idan ba salmah ba he promised bazai zauna da kowacce mace ba, take hawaye suka cikamun ido na juya gefe na share kar saeed ya lura, yace so kinji matsalar abokina gashi sati dayan da aka bashi gobe ne zata cika daz y kika ganshi ba annuri, na jinjina kaina lallai yana cikin matsala, toh yanzu ya zaiyi, how i wish nasan amsar tambayarki nima da na samowa abokina solution, anyway ni zantafi en mata sai wani ganin ya juya ya tafi abunshi ya barni nan zaune bana ko motsi kamar wata statue. [9/14, 12:55 PM] +234 706 332 8523: [11/10, 2:39 PM] Deejah Abdul💗💖: Dream girl na deejah Abdul 1⃣5⃣ zaune nake nayi jungum hawaye sai korar juna suke, har hijabina ya fara jiqewa idona har sunyi red kamar wadda uwarta ta rasu, duhu ne naga yafara sauka wurin sannan na tashi na kama hanyar gida, tafiya nake kamar wachche qwai ya fashewa a ciki, gabadaya hankalina baya jikina, ina isa qofar gida naji ana kiran sunana, ko waiwayawa banyi ba bare mai kiran sunan yasa ran zan saurareshi, haba ameerah magana fa naketsa miki tindazu nazo nan ina jiranki akacemin ba kyanan, a fusace na juyo malam na aikamaka da invitation nace kazo ne? Ko anaso dole ne wlh mustafa kafita hanyata dan nagane take_takenka dan ka kuskura ka gayawa mama cewa wai sona kake wlh sai kayi danasani a rayuwarka, baki ya saki yana kallona dan ko a mafarki baita6a tsammani na iya tsiwa haka ba, tsaki naja na shigewata a gida, Aliyu ne yazo wurinshi ashe dama yana tsaye yana kallonmu, yace danuwa kayi haquri my sis ba haka take ba inaga dai da abunda yake damunta, jst go i'll talk to her later, sannan ya tafi. Mustafa cousin dinane dan wan mahaifiyata, yaro ne mai natsuwa kuma shima din ya hadu dai_dai misali, lura nayi da en kwanakinnan yana yawan zuwa gidanmu, kuma duk yazo sai yace a kirani mu gaisa, harda en gifts yake kawomin da mama, shiyasa nagane inda ya dosa, nasan kuwa idan har ya gayawa mama zancen yana sona na kade dan nasan tsaf yadda zatayi dan yaron yanada kirki, shiyasa nikeson intaka masa birki, dan nariga nayi nisa a son maso wani banajin kira. Fusace na fada gida nayi sa'a ba kowa a tsakar gida dakina na wuce direct na kullo qofa na fada kan katifata, da yake ina hutun sallah shiyasa banma bi ta tinanin sallah ba. [11/10, 2:55 PM] Deejah Abdul💗💖: Dream girl na deejah Abdul 1⃣6⃣ Aliyu ne ya banko qofar dagani ransa a 6ace yake, haba sis haba sis ae wannan bai kamaceki ba, yanzu miye laifin mustafa da zaki wulaqantashi, ko bakomai ai dan uwanki ne, hannu na daga masa ya isa aliyu kaga kaina kemun ciwo dan Allah kafita kabarni na huta, amma dai koma miye yaha musty bai chanchanchi hakan ba, mamace ta shigo tana kallon aliyu wanne mustafan tayiwa wulaqanci, cikin sauri nace mama wani yaro ne a chan layin ya dameni bayan ni nagayamasa bana sonsa, mama tace to wai ke ubanwa ma kikeso ni nagaji da halinnan naki duk wanda yazo gidannan da sunan yana sonki zakice ba kya sonsa, ko a haka zanta zama dake a gidannan muna gwada tsayi? Aliyu ne yace yo mama dama wa zataso bayan ta dorawa kanta........ Alamar magiya nayiwa aliyu alamun kar ya fada dan Allah, sai ya fakaice yace bayan ta dorawa kanta wani ustazanci kamar wata waliyiya, mama tace yo waya gayamata su ustazan basu son maza, dariyace taso ta su6ucemin, nace mama nidai kiyi haquri zan gyara, tace karma ki gyara yarinya kisha mamaki dan duk wanda naga dama zanbashi ke inhuta, shigowar saudah ne yasa mama da aliyu suka fita suka bar dakin. [11/10, 5:44 PM] Deejah Abdul💗💖: Dream girl na deejah Abdul 1⃣7⃣ juyawa saudah baya nayi nace meh kin qara zuwa da wani sabon wulaqancin ne, dariya tayi wai ke har yanzu fushi kike? Haba qawata ki haqura mana Allah tsokanarki kawai nakeyi, ns basar toh miye labarin da kikace zaki bani, bayan kin shareni kuma wane labarin zanbaki, toh shikenan riqe abunki nayi kwanciyata na qyalete. Duka saudah ta kaimin wlh ni badan nasaba da halinki ba, da tuni mun raba hanya shegen mishkilancin tsiya kamar wata er sarkin misira, dariya nasa na kaimata duka aini namafi er sarkin misra, gimbiya ameerah kenan na dagamata gira, muka tafe muka qyalqyale da dariya, amma wannan da ake dakon son sai yayi haquri dake, nace ba wannan ne sunanshi ba sunanshi KHALEED, kwantawa saudah tayi itama, ke qawas ashe love story yaci gaba ambarni abaya, toh ya akayi kika samo sunan keda kikace bakisan sunan ba, na kwashe duk yanda akayi bayan barina gidansu har zuwa yau da nasamo wannan bad news din na gayamata. Saudah ta sauke ajiyar zuciya tace ina ke ina jayayya da er governor da er germany ai ni a ganina gwanda ki haqura kawai wannan battle yafi qarfinki, zumbur nayi natashi zaune in haqura fa kikace saudah ai kuwa wlh kiji sai inda qarfina ya qare, ni kisani wannan er deputy governor batama dameni ba dan nasan bata gabanshi, wannan salmar ce dai ta tsayamin a heart dan ita yakeso nafara hawaye, saudah tace qawas gwanda kawai ki manta da wannan khaleed din dan yafi qarfinki, hannu na dagamata qawas ya isa haka indai bazaki fadi alkhairi ba gwanda kiyi shiru kawai, in yafi qarfina baifi qarfin Allah ba, danni dakice na haqura da khaleed gwanda ki fallamin mari. Baki qawas ta riqe miyayi zafi Allah ya ba mai rabo sa'a nace ameen. Kinga kafin ki fara fushin bari na gayamiki abunda ya kawoni, gobe za'a kawo lefena, washe baki nayi dama kinada wannan good news din kiqaki gayamin da wuri saida kika 6atamin rai? Saudah tayi dariya tace ai yanzu na gyara ran ko, dariya nayi nima nace shine baki gayamin da wuri ba ina matsayin babbar qawa, tayi dariya ina naganki bare nagayamiki kina fushi dani, gashi duk sanda nazo kinfita ashe ke gun zuwa kika samu, saudah ta miqe ni zantafi kishigo da wuri gobe akwai aiki nace toh na rakata waje, sannan nadawo na kwanta ina saqa abunda zanyi dan inga na taimaki rabin raina kuma yanda za'ayi na sameshi. [9/14, 12:55 PM] +234 706 332 8523: [11/12, 3:22 PM] Deejah Abdul💗💖: Dream girl na deejah Abdul 1⃣8⃣ ranar dai rabin dare haka ya qaremin ina saqa da warwarar abunda zanyi, sai kusan asubah nasamu bacci ya daukeni, asubar ma makara nayi saida mama taga ban tashi ba tazo ta tadani, ina gama sallah kuwa da qyar nayi azkar dina nakoma bacci ba, bani na farka ba sai qarfe goma, da yake weekend ne su suhaila na gida inaga shiyasa mama bata tadoni ba, nayi aiki, a gurguje na fito na dibi dumame naci na fada wanka, nafito na shirya, na saka hijabina nayo waje, mama ce tace sai ina kuma, dan na lura kwanan nan qafar kare kikaci, shiyasa kullum sai kinfita wai ina ma kike zuwa, karfa kiga na sake miki kizo kiwuce gona da iri, haba mamata ai kema kinsan er da kika haifa bazatayi shashanci ba, gidansu saudah fa nike zuwa da yake bikinta ya kusa, kuma yau za'a kawo lefe shiyasa ma zanje da wuri yau, mama ta saki fuska to ai ba laifi adawo lfy, kigaida hajiya asabe sai nazo taya murna nacd toh na zura takalmina zanfita. Khairi ne yace shishta(sister) kizo mana da alala da sho6o (zo6o) dariya muka sa nace qanen shishta don't worry zakaci alala da sho6o na fice. Gidansu saudah na nufa, nashiga sunata faman aiki na cire hijabina nima na shiga akayi dani, bayan mungama ne nace bare inje gida inyi wanka, kan masu kawo lefen suzo, mamarsu saudah ce ta debomin alale da zo6o, abinci da ma wasu kayan soye-soye da akayi na tarar baqi, nayi godiya na fice gida, da shigata khairi ne ya taso da gudu ya tareni ya kar6i wasu kayan da nazo dasu, dariya nayi nace khairi baban kwadayi ga alale da sho6o nan ayita fama, mama tace har ankawo lefen, nace a'ah nadaizo in watsa ruwane kan suzo, na debi ruwa na fada makewayi. [11/12, 3:23 PM] Deejah Abdul💗💖: Dream girl na deejah Abdul 1⃣9⃣ nafito wanka na bude akwatina na za6o sababbin kayana, na sheqa kwalliya, wata atamfa nasa mai kallar ja da black, dinki atamfar ya kar6eni gashi dama red nd black color sunamin kyau, red hijab dina na dauko nasaka saidai yau ban dauko mai kaimin har qasa ba yadai rufemun hands kawai, black shoes nasaka na riqe red nd black purse dina, ina fitowa suhaila tace su sis yau ansha kyau kamar wadda zataje beuty contest, murmushi kawai nayi nacewa mama natafi, koda na isa gidan har sunzo, lefe yayi kyau ba laifi daidai gwargwado, cikin raina sai fata nike Allah ya nunamin nima khaleed ya kawomin nawa. Daki na wuce wurin saudah da yake ita bata fito ba, tambayana take qawas ya kikaga kayan, dariya nayi nace gulmammiya ai da sai kifita kigani tinda kinkasa haquri, nace sadiq din naki gaskia bai iya za6en kaya ba ba abunda yayi kyau, qirji saudah ta dafe nashiga 3, na kece da dariya kewai har kin yarda wlh komai perfect kamar ke, duka ta kaimin na goce ni har kin tsoratani tace, fira muke da saudah amma ni duk rabin hankalina yana gun dream man dina na matsu time yayi na wuce inda ya zamemin ibada kullum, da qyar naga anyi la'asar sallah kawai na sallamah na miqe tsaye, saudah na fadin ina zuwa qawas, ban waiwayota ba nace sai na dawo qawas, murmushi tayi a ranta tace Allah ya raba rai da wahala. [11/12, 3:25 PM] Deejah Abdul💗💖: Dream girl na deejah Abdul 2⃣0⃣ tafe nake ina sauri dan naga na dan makara, kar nayi missing ganin abun qaunata, shigata wurin keda wuya nafara waige-waige ta bayana naji kamar ana magana, najuya na nufi gun sa'id ne na hango yanata zuba dukda bansan meh yake fada ba, raina yamin fes dan duk na hango sa'id nasan my dream man is there