← Book details Dream Girl Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 52

Sashe 15

Dream Girl Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

A waje mama ta sameni raku6e tace sai kizo mutafi aini na dauka kinkai gida, nace mama taya zan barki tareda wa 'yanchan mara mutuncin, jira kawai nake naji 6ur nashiga na watse su, mama tayi dariya waini ameerah ina kika koyo masifa ne? Nace mama gunki mana kema ai bakya daukar raini, tace um lallai kuwa amma dai yanzu nema muke a wurinsu dole mubi a sannu.
[9/14, 1:19 PM] ‪+234 706 332 8523‬: [11/20, 6:01 PM] Deejah Abdul💗💖: Dream girl na deejah Abdul
6⃣2⃣ kamar yanda kausar tacemin zatazo haka kuwa akayi qarfe goma tana gidanmu, dama na shirya shigowa tayi ta gaida mama muka kama hanyar skul a motarta bamu wani sha wahala ba da yake inkanada kudi komai yana zomaka da sauqi, kausar tayimana registration har da course registration duka angama anyi signing departments, mamaki kawai nike abunda zan dauki kusan 3 weeks inayi yau gashi angamamun within 3 hours, qarfe daya muka bar school instead of kausar ta ajiyeni a gida, sai ta shiga yawon dangi dani, ko'ina sai nunani take ga matar yaya khaleed har gidajen qawayenta saida ta kaini, shiyasa kwata-kwata na sha'afa da zuwan da zamuyi gidan kawu shehu da su khaleed, Wuraren qarfe biyar sai ga kiran mama tafaramin masifa gidan ubanwa naje tindazu su khaleed sukazo suna jirana, amma tasa aliyu ya tafi dasu yanzu duk inda nake maza da aikin sauri na wuce chan na sameshu, gabana ne ya dinga faduwa bansan irin tarbar da za'ayi musu a gidan ba, cikin sauri nace kausar ta kaini bado quaters gidan kawuna, ta juya muka nufi chan.

A gidan kawu shehu kuwa, hajiya asabe na ganin mota qirar range rover sabuwa fil ta shigo gate, ta zabura ta miqe koda taga kyawawan samari sunfito a mota batama lura da aliyu da suke tare ba, ta sheqa da gudu sai dakin saratu, sara baby ki tashi mana, itako sai wani mitsitstsike ido take, tafara kukan shagwa6a ita a dole an takurata, ruwa haj asabe ta debo ta watsa mata, firgigit ta miqe zaune, hajiya tace ke gantalalliya ki tashi inajin ga saurayinnan naki dan qasar masar da kikace zaizo nan yazo, miqewa saratu tayi da gudu ta leqa waje, hajiya asabe ta jawota ke mahaukaciya badai haka zaki fita ba fuska duk yawun bacci, kije ki tsala ado nikuma zanje nakaisu dakin baqi, tace ok mom tayi ciki da gudu, ita kuma hajiya ta zuri gyale tayi waje tana wanin takon qasaita, zuwa tayi ta samesu sai a lokacin ta lura da aliyu da suke tare, cewa tayi malam lfy dai kazo ka tsare mutane? Aliyu yace dama cewa akayi na kawosu haj tace toh ai ka kawosun sai ka sani inda dare ya maka, Aliyu sumui-sumui ya kama gabansa, sukuwa khaleed da saeed sai kallon juna suke, hajiya tace ku wuce kuka tsaya anan, falon baqi takaisu, aka fara jera musu lemo da snacks kala-kala da soyayyen kaji😋, fita tayi bari na kira muku alhajin kafin baby tazo, sudai basu gane meh take nufi ba sukace toh.
[11/20, 6:22 PM] Deejah Abdul💗💖: Dream girl na deejah Abdul
6⃣3⃣ Haj. Taje tacewa alhaji ya fito ga saurayin saratu nan yazo dan masar, alhj cikin washe baki ya nufi falon baqi, aka fara gaisawa alhj yace ko zansan ko kai dan gidan waye, khaleed yace sunana khaleed muhammad khalipha, dan gidan alhj M khalipha ne ni da ke sama road, haj da alhj suka kalli juna suka washe haqora, saeed yace alhj munzo neman auren 'yarka ne, muna fatar ba wata matsala? Alhj murya na qyarma yace ai ba wata matsala wlh haj tace haba wache matsala za' a samu kuwa? Aimu indan tamu ne ko gobe ku turo a daura aure, saeed yace to alhamdulillah idan munje gida zamu gaya musu sai suzo ayi magana.
Saratu ce ta shigo taci wani jeans da wata ficiciyar riga, tasa belt ta tsuke kunkuru ya matse wuri daya, kamar an daurawa akuya zani😂 tasha wani uban janbaki kamar wata dodanniya, wai ita a dole ga farar mace, aranta tana nasawa ita da ta gayawa saurayinnan adress dinta bata zata zaizo ba dan yaune farkon haduwarsu, wucewa tayi tana wata karairaya ga Saratu ba shape ko'ina a shafe ba sha'awar kallo, amma ita nan ganin take cikakkiyar macece, cewa su khaleed sannunku da zuwa ta zuba masu lemo a cups ta miqa musu, ya baku ta6a komai bane haka tana wane kashe murya kamar tsohuwar karuwa saeed ne yace bakomai mungode, khaleed kuwa ko kallo bata isheshi ba.
Daidai nan kausar ta ajiyeni a bakin gate nace ta wuce kawai tareda su khaleed zanwuce ta wuce abinta, koda nashiga sai naga takalmi a falon baqi, direct chan na wuce na shiga da sallamah ta.
[9/14, 1:21 PM] ‪+234 706 332 8523‬: [11/20, 6:51 PM] Deejah Abdul💗💖: Dream girl na deejah Abdul
6⃣4⃣ Saeed da alhaji ne suka kar6a saratu na ganina ta miqe tsaye, ta nunani da yatsa ke meh ya kawoki gidannan ko wani ya gayyatoki ne, kinji labarin saurayina yazo shine kika wanko qafa kikazo toh ki fice dan nan ba sa'arki, turus nayi ina kallon ikon Allah, khaleed da saeed kuwa sai kallon kallon suke, wai meh ke faruwane? Saeed ne ya miqe yace wai meh yake faruwa ne alhaji mufa zancen ameerah mukazo bamu fahimci meh ke faruwa anan ba, alhaji yace meh, amma haj tazo tacemin saurayin saratu ne yazo, khaleed sai a lokacin ya kalli saratun yace wannan abar ce zata zama budurwata? Haj cikin 6acin rai tace, meh kake nufi da wannan abar? Ita ba mace bace da meh wannan matsiyaciyar ta fita? Wlh Allah da nasan zancen wannan matsiyaciyar kukazo da ko ruwan gidannan ba zaku kur6a ba, khaleed zaiyi magana saeed ya riqeshi, amma dukda haka saida ya wurga mata bandir din dubu hamsin yace ga kudin ruwan da mukasha nan, idan sunfi haka ma sai ki fadi a qaro, mamaki ya kashe haj da saratu har alhj ma ya saki baki yana kallo.

Alhaji ne yayi ta maza yace kunga ba haka za'ayi ba, misunderstanding ne kawai aka samu dan itama saratu saurayinta zaizo daga masar yau, haj ta dauka kune, amma kuyi haquri dan Allah indai ameerah ce na baku, ku turo magabatanku ko gobe ne a saka rana, kuma zanyi komai da uba zaiyi dan naga na fidda 'yata ameerah kunya, na dai na dasqare wuri daya ina sauraren kawu na zuba qarya. Saeed ne yayi godiya yace zasu tafi, saida yazo kusa dani yace mutafi ameerah sannan na motsa, nace angode kawu su haj da saratu sukabini da harara muka fice.
[11/21, 7:55 PM] Deejah Abdul💗💖: Dream girl na deejah Abdul
6⃣5⃣ fitarmu keda waya alhaj da hajiya suka fara rige-rigen daukar bandir din kudin da khaleed ya jefowa hajiya, da yake alhj yafi qarfi ya ture asabe gefe ya dauke kudin😂 ture baki tayi uwa ungulu na cin kashi, alhj gaskia wannan zalunci ne, nifa aka jefowa kudin alhj yace ke asabe da a kayiwa wulaqanci aka wurgowa ai baima kamata ki kalli kudin ba, haj asabe tace Allah alhj ni kasan indai akan kudine gwanda mutuncin ya zube dama meh ya rage? Nidai ka yagomin kawai dubu goma ya ciro ya miqa mata, ta qare ture baki alhj gaskia raba daidai zamuyi, cewa yayi idan bakiso wlh ki kawo wannan dinma zanqara, dama wa yake cin kudin ba ku ba? Saratu ce tace dady nima dan yankomin mana, dubu 3 ya jefa mata shegiya da son kudi kamar uwarta, haj tace iyayenta dai ai kaima alhj gameda son kudi, ba kanwar lasa bane.
Chapter 15 · 0% Book details