← Book details Dream Girl Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 52

Sashe 41

Dream Girl Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Falon salmah ya nufa yana huci kamar wani zaki, tsaye kawai sukaga mutum akansu yana huci, ku da iyayenku meh kukayiwa matata? A tsorace suka waigoshi ganin yanayinshi yasa cikin su ya duri ruwa, salmah tunaninta kardai ameerah ta gayamasa kuma har ya yarda.
[12/17, 9:14 AM] Deejah Abdul: Dream girl na deejah abdul
1⃣6⃣2⃣ Wata tsawar ya daka musu ba magana nike muku ba? Wata figaggiyar ta fara magana haba angon salmah mu meh zamu yiwa matsiyaciyar matarka? Komai ta gaya maka karya take, take ya kifa mata wani wawan mari saida taga stars, dayar zatayi magana haba khaleed......... Bata karasa ba taji saukar nata marin, tuni salmah ta fara tsorata, a fusace ya fara magana duk er iskar da ta kara shigomin gida bare har tayi tinanin taba ameerah wlh sai ta raina kanta, nuna salmah yayi da yatsa wato dan kince na saki ameerah naki, mahaifiyata ta gayamiki bazata saku ba, shiyasa kika fito da wata hanyar dan ki tsoratata tabar gidan? Toh bari kiji ingayamiki bazan saketa ba, yanzu ma nafara zama da ita aurenki ba karani da komai ba sai bakinciki, keda baki damu dani ba, 'yan iskan kawayenki ma sufini daraja miye naki na kishi? So i' m giving you a last warning karki sake kikara zuwa inda matata take, ku kuma ku ficemin daga gida, kar er iskar da ta kara shigomin gida, cikin tsawa yace musu ku wuce nace da gudu suka fita, yaja jikinsa fuu yayi part din ameerah.

Salmah ta sauke ajiyar zuciya, ohh abunda ta gayamishi kenan? Murmushin mugunta tayi, khaleed i'm so sorry fushinka bai dameni ba, nafi bukatar matarka a kanka, zuwa kusa da ita yanzu ma na fara, ta wuce dakinta.

Shiko zuwa yayi yafara trying keys din yana kokarin bude kofa, jin haka ya kara firgita ameerah kukanta ya tsananta, tanajin anbude kofar ta kurma wani uban ihu ta dafe kanta, khaleed da ya firgita ya rasa meh sukayi mata ko suka gayamata da ta tsorata haka, zuwa yayi ya tabata khadijah jin ankirata da khadijah yasa ta daure ta bude idonta da sukayi jajir dan kuka da tashin hankali, da gudu ta afka jikinsa shiko ya rungumeta, tsayuwa ta gagaresu ya zauna da ita kan gado yana bubbuga bayanta, tayi shiru sai sauke ajiyar zuciya take, dagota yayi meh sukayi miki? Komawa tayi ta kwanta a kirjinsa tayi lamo, tana tuna maganar salmah ko ta gayamasa gaskiya bazai yarda ba, jin tayi yana cewa ba abunda zasu yimiki bazasu kara dawowa gidannan ba, da mamaki ta kalloshi ya gyada mata kai, tacd toh kome suka gayamasa oho, cewa yayi ameerah jikinki yayi zafi, tace yunwa nakeji banci komai ba tin safe, take ta bashi tausayi ya mike ina zuwa, da gudu ta bishi ta makaleshi karka barni anan please, tsoro nakeji cewa yayi toh dauko hijabinki da sauri ta jawo ta saka ta koma ta mannemasa a jiki shiko ya riketa tamau kamar mai gudun a kwace masa ita.

Mota suka shiga suka fita, tsirai ya fara siya mata da naman kebab da youghurt tafara ci tin a mota tsabar yunwar da takeji, sukaje oasis bakery suka kwaso snacks da lemuna, aka dawo kusha shagalinku Junction suka kwashi kilishi da dambun nama kamar masu tsaraba, saida taci tayi kat sannan ta fara dawowa hayyacinta, cewa yayi toh nifa baza'a sammin ba? A baki ta dinga bashi yana karba, da haka har suka isa gida, suka kwashi kayansu suka nufi sashin ameerah duk a idon salmah.

Bayan sunkoma daki ma hanashi fita tayi, saida ya jira tayi sallar isha'i, yace zaije dakinsa binshi tayi itafa bazai barta ita kadai ba yau tsoro takeji, sukaje yayi wanka ya fito, tana ganinsa ba riga ta dukunkune kanta, shidai murmushi yayi, yagama yasa sleeping dress dinsa yazo ya kwanta dan nesa da ita, a haka ameerah ta dinga jan jaki saida taji ta manna jikinta da na khaleed sannan taji ta nutsu, shiko yanajin haka ya kara jawota ya manne a kirjinsa yasa hannuwansa ya zagayeta, tare suka sauke wata ajiyar zuciya, da haka wani bacci mai dadi ya kwashesu.

Jarababbiyar kuwa har cikin dare saida ta tashi taje sashen ameerah taji kofa gam, ta window taje tana lekawa tayi sa'a a bude, wayam taga dakin ba kowa, wani haushi taji wato khaleed dakinsa yaje da ameerah? Wani kishinsa taji yana shigarta ta juya taje dakinta, ranar dakyar ta samu bacci ya dauketa.

TOH ALLAH UBANGIJI YA SHIRYARDA MASU HALI IRIN NA SALMAH, YAKARE EN UWANMU MATA DA AFKAWA IRIN WANNAN BALA'I AMIN.

Like
[9/15, 2:42 PM] ‪+234 706 332 8523‬: [12/19, 7:06 AM] Deejah Abdul💗💖: Dream girl na deejah abdul 1⃣6⃣9⃣ Shafa fuskarsa hawayenta na diga a wuyansa, haka yasa khaleed ya fara motsawa, ameerah ta rike hannunsa gam, sai kuwa gashi ya bude idonsa, tar sai a fuskar ameerah murmushi tayi masa shima ya maida mata yasa dago hannunsa ya goge mata hawayen yaga drip a hannunsa, cewa yayi why are you crying? Meh ya faru waige-waige ya fara ya ganshi a asibiti, dubawar da zaiyi sai ya hango salmah a kwance a dayan gadon, take ya fara tuna abunda ya faru dazu, aikuwa ba shiri ya ture ameerah mom dake kusa ta riketa, ya fizge drip dinda ke hannunsa yayi kan salmah.

Kausar ta fita da gudu tayi waje takira dad da saeed da gudu suma suka shigo, khaleed kuwa har ya cakume wuyan salmah, hakan yasa ta bude ido a firgice ta fara wutsil-wutsil, saeed da dad sukayi kansa dakyar suka banbareshi ta mike cikin hanzari jikinta na bari, haka yayi daidai da shigowar iyayen salmah.

Da gudu ta afka jikin mahaifinta tana kyarma khaleed kuwa sai zillewa yakeyi shi abarshi sai ya kasheta, dad ne ya wanka masa mari sannan ya dan nutsu, sai ya rungume dad yana kuka mai tsuma zuciya dad salmah ta cuceni, dad kuce ta jaye daganan banason ganinta, dad wlh na saketa saki uku take mahaifiyar salmah tasa kalima ai shikenan, dannan ba zaka ko tsaya ayi bahasi ba kayimata saki har 3? Amma yaron nan ka cucemu, yarinyar nan dakyar muka samu ta yarda zata aureka hakan yasa mukasan sosai take sonks, amma shine dan rashin mutunci zaka saketa a gabanmu?

Mom tace hajiya ya kamata kafin kifara masifa kisan meh er ki tayi har aka saketan, dadyn salmah yace meh tayimishi da zafi haka? Mom a fusace tace toh mata takebi mijin nata bayada bambanci da fanko a wurinta, mom din salmah tace toh da maza kukeso ta rika bi? Ai nidai nasan salmah da yawan tara kawaye mata kuma nima inayimata fada akan haka, idan har tana biyar abokan ta bata kula mijinta ai wannan baici yamata saki 3 ba, kamata yayi ya gayamana sai muyi mata fada.

Haushi ya ishi mom kamar ta kai mata duka, tace ace diyarki tana neman mata en uwanta har kice ba'a yimata adalci ba? Toh tinda sai anmiki gwari-gwari madigo takeyi, mata ke biyamata bukatarta itama auren bayada muhimmanci a gunta dan tafijin dadin mace akan mijinta.

Mom din salmah ta fara girgiza kai tana kuka, sam wannan ba gaskiya bane, sam wannan kazafi kukayuwa 'yata, dama munsan bakwa kaunarta kun hada da kishiyarta kunyi mata kazafi dan ya saketa, toh ya saketa ku zuba ruwa kasa kusha, kuma wlh Allah sai ya sakamana mu kuncucemu.
[12/19, 7:43 AM] Deejah Abdul💗💖: Dream girl na deejah abdul
1⃣7⃣0⃣ Dadyn salmah ya fara masifa shima na yarda da abinda matata tace wannan kazafi ne, alhj khalipha kaban mamaki, taya za'ayi haka ta faru kana sane baka dauki mataki ba, dad ya daka masa tsawa alhj usman ya isa haka, ka dubi yanayin yarona ji yanda ya fita hayyacinsa, ji yanda yake kuka kamar mace sannan kace sharri aka yimata.

Da idonsa ya ganta bawai gayamasa akayi ba, ga er takunan ta kartata idan karya akayi mata, dadyn salmah ya tambiyeta er Dady fadamin gaskia abunda suka fada gaskiya ne? Girgiza kai ta dingayi dad karya sukemin sharrin ameerah ne da kausar su suka shiryamin, khaleed ya zabura yayi kanta zai chakumota, dad da saeed na rikeshi dad kubari na kasheta kawai har tanada bakinda zata karyata da idona fa na kamata.

Salmah tace dad mom kuzo mubar wurinnan tinda ya riga ya sakeni miye amfanin bada hakuri, sukace hakane kuwuce mutafi, kausar tace ku dakata, zuwa tayi gaban salmah ta tsaya kince karya muka miki ko? Toh ni inada prove din abinda kikayi.

Salmah ta kara tsorata, tace mom dad kuzo mutafi karku saurareta karya takeyi, mom din salmah ta tsaya tace tanada prove ko? Inaso nagani da idona dan na tabbatarmusu da 'yata kazafi akayi mata, kausar ta zuge jakarta ta jawo wayarta video da ta dauka, ta kunna ta mika mata, take mom din salmah tayi suman tsaye, mijinta ya karbi wayar yana kallo take ya runtse idonsa wasu zazzafan hawaye na zuba, dad ya karbi wayar yakasa kallo ya runtse ido, mom ta ansa ta kalla itama tana Girgiza kai, saeed ya karba ya kalla cike da takaici, khaleed ya kwace wayar ya duba hawaye nata tsiyaya wata kara ya saka ya daga wayar sama ya watseta a kasa, saida kowa ya tsorata nan ya sake zubewa kasa, ameerah ta buga ihu tayi kansa tana Girgizashi, tana kuka mai tsuma zuciya, khaleed dan Allah ka tashi wlh idan ka mutu nima mutuwa zanyi, i can't live without you wake up please.
Chapter 41 · 0% Book details