← Book details Dream Girl Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 52

Sashe 16

Dream Girl Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haj asabe tace waima ni alhj bangane maka ba, taya za'ayi ka wani lalla6asu harda basu haquri bayan wannan cin fuskar da sukayi mana, a gabanka sun wulaqanta mana 'ya, alhj yayi murmushin mugunta, ai haj wannan yaron da kike gani yafi qarfin wulaqanci a wurina, sai miye dan yace bayason kodaddoyar yarki? Ai amirar ma' yata ce kuma ni naga hanyar cin arziki, dan haka tsayawa zanyi na kashe kudi nayiwa ameerah duk abunda uba zeyiwa 'yarsa, ta haka zansamo kan yaron, dandama akwai wasu kwangiloli da na dade ina nema bansamu ba, amma yanzu ta hanyar yaron nan nasan komai zaizo da sauqi, kema ki saki jiki ayi komai dake kija yarinyar a jiki duk abunda ake buqata kiyi mata, ta haka zamu samu kansu, haj da alhj suka sheqe da dariya harda tafawa, dadina dakai shehu wlh akwai kwanya.
Saratu ce ta fara kukan shagwa6a, hjy tace ya akayi ne sara baby, ta ture baki kamar uwarta, ni mom Allah na lura bakwa sona, wannan guy fa dani ya dace ba watchen matsiyaciyar ba, alhj yace toh ai kema ki saki jiki ki daidaita da ita ko bayan auren ne kya qwaceshi tinda dai ba uwarku daya ko ubanku daya da ita ba, zaki iya aurenshi, ai na lura er kissar nan da kwarkwasa ta mata duk kin iya, ko dazun ma na lura sai satar kallonki yake😳 dandai kawai yana gaban ameerar ne yake fadar haka, saratu ta washe watsatstsun haqoranta Allah ko dad? Yace gaskia nike fadamiki.
Saratu tace nifa dama ina mamakin yanda wannan hadadden guy zai so watchen matsiyaciyar, haj tace ai ba mamaki sungaji da talaucin ne suka masa asiri, saratu kuwa tace ae asiri yazo qarshe kuwa dan yanzu khaleed sai saratu, suka sheqe da dariya.
Nidai deejah nace shedanu ina jira inga yanda khaleed zai fatattaka ku.
[9/14, 1:24 PM] ‪+234 706 332 8523‬: [11/21, 8:16 PM] Deejah Abdul💗💖: Dream girl na deejah Abdul
6⃣6⃣ tafiya muke a mota amma ba wanda yayi magana kowa da abunda kemasa yawo a zuciya, saida muka isa gida saeed ke cewa niko ameerah, dagaske wannan kawunki ne? Murmushin takaici nayi ai bakuma ga komai ba, kunci sa'a haj ta dauka gun saratu kukazo, da bansan da wanne ido zan kalleku ba, ba yanda zanyi shine madaurin aurena, tinda ni banida uba yanzun amma da ba abunda zaisa mama tace kuje gunsa, kuyi hakuri da abunda ya faru, saeed yace ae ke zamu bawa haquri dan ke sukafi ciwa zarafi, anyway zamu wuce ameerah, saeed yace buddy bari inbarku kuyi magana ka sameni a mota, tsayuwa mukayi ta kusan 5minute ba wanda yayi magana sai ni da nike satar kallonshi, dago kai yayi muka hada ido nayi sauri na kawar da kaina, sai cewa yayi now what is next? Nace nima bansaniba, yace shikenan i'll tell mom ita tasan meh za'ayi, sauri nayi nace plz karka gayawa mom abunda ya faru, cewa yayi what do u take me as? Ke kika dauki abunda ya faru wani abu da har kike tinanin akwai abun fada a ciki, anyway gud night ya juya suka tafi, niko na shige gida.
Sallamah nayi dakin mama, ta kar6a ta lura nayi wani suku-suku, tace meh ya faru ameerah? Na kwashe duk abunda ya faru na gayamata, tsaki tayi ni nama dauka kawun naki, yaqi amincewa ne da na ganki haka, nace mama kinyarda da abunda kawu yace na zaiyi komai? Tace ba abun mamaki bane dan ya lura yaron dan masu hali ne, toh zaiyi tunanin ya samu wani abun so ko dan haka zaiyi, tace mubar zancen su kiramin maman khaleed muyi magana, wayata na dauka nasawa mama number mummy ta kira, inaji tana gaya mata zasu iya turawa ayi magana a saka rana, suka gama plan dinsu sukayi Sallamah, mama tace wai lfy ameerah kike haka ba wani kuzari? Nace mama may b gajiyace kawai bari inje daki, tace kodai zullumin auren ne kika fara? Toh gwanda ko ki saki ranki dan aure anyi angama tinda kikace kina so, ban tankata ba nayi daki dan nima bansan meh ke damuna ba.
[11/21, 8:37 PM] Deejah Abdul💗💖: Dream girl na deejah Abdul
6⃣7⃣ khaleed ma da ya isa gida gun mom ya wuce, ya gayamata sunje sungaida kawun ameerah, kuma yace ko gobe ma za'a iya turawa, mom tace ai yanzu na gama waya da maman ameerar, kuma namayi magana da dadynka, yace gobe zai tura mutane ayi magana, khaleed yace dady kuma mom? Tace ae na gayamaka dama fushi ne kawai kuma ya sauko yanzun, nd above all deputy governor yace ya fasa bada 'yarsa, yanzu ba komai tsakaninsu sai business, alhandulillah khaleed yace, mom tace khaleed bakasan farincikin da nike tare dashi ba, Allah dai ya nunamin ranar da za' a kai ameerah gidanka son, miqewa yayi yace zanshiga daki mom a gajiye nake, tace shikenan ya tafi, mom kuwa har ta fara plans din abubuwan da za'ayi a biki.
Khaleed ya koma daki yayi zugum, shi da yasan ma husnah zata haqura da baiyi kaudin amincewa da ameerah ba, wata zuciyar tace masa da badan ameerar ba kuma ae da yanzu, shirye-shiryen aurenka da husnah akeyi, tsaki yaja aidai yanzu its too late to cry, ni wannan ameerah Bansan wane irin farin jini ne da ita ba, dangi kowa zancenta yake, wai nayi sa'ar mata above all ga mom, ni nasan ranar da game dinmu zaiyi over, zamuyi rigima da mom akan ameerah, amma kuma ae dole mom tayi haquri tinda itama ameerar da wanda takeso.
Musqutawa yayi bari na kira salmah na gaya mata, amma kuma miye ma na gayamata tinda aure ba lasting zaiyi ba, bari na kirata dai musha fira i'm missing her alot, kiran wayarta yake amma busy ya gaji yaje ya kunna tv yana kallon news, txt yayi mata, saida ya manta da yayi txt sannan reply yazo, karanta txt din yake yafi a qirga yana aikin murmushi, daga bisani bacci yayi gaba dashi.
[9/14, 1:25 PM] ‪+234 706 332 8523‬: [11/21, 11:12 PM] Deejah Abdul💗💖: Dream girl na deejah Abdul
6⃣8⃣ lokaci nata tafiya, anyi tambaya ansaka rana nan da 3weeks, abu kamar wasa, anbiya sadaki dubu 100, daura aure kawai ya rage, sai lefe da za'a kawo gobe.
Ni kuwa abubuwa summin yawa gashi muna shan bikin saudah, inajin haushin rabuwa da qawata, dan a bauchi za'a kaita gidan angonta usman, kuma mama ta hanani zuwa bauchin wai amarya tsautsayi ne da ita, ga karatu lectures muke ba kama hannun yaro, ga zullumin aure duk nayi rama, amma kuma nayi haske da yake har anfara yimin gyaran amare.
Abun mamaki duk abunnan da ake tareda haj asabe da saratu akeyi, haj asabe itace, kawo wanchan jiqon bada wannan sassaqen wai duk abani nasha, nikuwa idan na fakaici idonta na zubar, abubuwanda na yarda dasu kawai nike ci, da yake akwai qawar mama da take hadamin tsimi, da wasu abubuwan a gyara kuwa harda maman saudah ba'abarta a baya ba, ni ameerah abubuwanda ake dirkamin har banason shiga gida idan na fita, na safe daban na yamma daban wai duk gyara ne, kawu kuwa duk abunda ake buqata bayarwa yake.

Kamar yanda akace za'a kawo lefe hakan kuwa akayi, su mama sunyi nasu shiri daidai gwargwado na tarbon lefe, haka aka riqa jibge kaya kamar za'a buda boutique a gidanmu, mutanen sai tururuwa suke kallon kayan ameerah, ko sata akayi baza'a gane ba akan yawan kayan, dan haj da kausar dakansu sukayi visa, qasashe 3 sukaje hado kayan lefen. Hajiya da saratu ranar kasa 6oye baqincikinsu sukayi, suka rinqa masifa da mutane masu zuwa ganin kayan lefe, haj asabe tace akai kayan kawai a gidanta idan ba haka ba mutane zasu sace kayan mama bata sani ba, wata yayar mama da take nan, tasan halin haj asabe tas tache ba inda za'a tafi da kayan, tananan ita zata kula da kayan, cin mutunci sukayi tatas da ita da gorace-gorace, wai ai duk mijinta yake komai, haka dai suka bar gidan daga qarshe sukaje gida suna baqinciki, itadai saratu duk gold dinda aka zuba yafi tada mata hankali, cewa take da yanzu ita aka kawowa, amma duk da haka sai tasan yanda akayi suka zama nata.
[11/21, 11:44 PM] Deejah Abdul💗💖: Dream girl na deejah Abdul
6⃣9⃣ Sannu sannu bata hana zuwa akace, yau saura kwana 3 daurin auren khaleed da ameerah, 6angarori biyu kuwa ba abunda ake sai shirye-shirye, kawu shehu ya taqarqare yana kashe kudi, kayan dakin da aka siyowa ameerah dukda da haj asabe da kanta saida tayi mamaki, tace asiri mukayiwa mijinta yake kashe mana kudi haka, shikuwa yasan abunda ya shirya, mutane ya dauko dan kawai gyaran gidan khaleed da ameerah, anjera kaya anyi komai gida sai sheqi yake kamar a dubai, kowa yaje santin gidan yake, furnitures dinda aka saka a gidan sun dace da yanayin gidan, komai yayi tsaf-tsaf, nidai DEEJAH da na leqa gidan daqyar aka fito dani, nace zanyiwa ameerah wanke-wanke, amma haka haj asabe da saratu suka taso qeyata waje, wai kar na 6ata furnitures din, tun basu mori komai ba😢, mama harda kuka tayi tanayiwa alhj godiya dan ya fitar da ita kunya, duk da cewa a qasan zuciyarta tana shakkan abunda kawu shehu keyi dan tasan ruwa basa tsami banza.
Chapter 16 · 0% Book details