← Book details Dream Girl Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 52

Sashe 20

Dream Girl Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Mom tace salim ga ameerah how i wish kadawo kunsan juna kan haka ta faru, gashi kace jibi zaka koma, murmushi yayi mom she is preety, dukda hakan take i know zata kula da yaya khaleed sosai, kuma mom kinsan daurin auren broda kawai yasa na dawo if not sai next session, salim yace ina yaron da kikace zamu tafi tare? Mom tace kaga ni nama sha'afa wannan tashin hankali banma gayawa aliyun ya shirya, angama masa komai ba, tafiya kawai ta rage, mama ta ta6o aliyu da ya shiga wani yanayi, firgigit ya motsa, tace aliyu ga salim ku gaisa shine zaku tafi egypt din tare, hannu ya bashi suka gaisa, salim yace i'm happy nima zansamu danuwa a chan, sai kafara shiri dan jibi zamu wuce bayan andaura aure gobe.
Aliyu ya kalli mama har suna hada baki daurin aure kuma, mom tace eh maman ameerah, ae dan yarinya ta samu hatsari bazaisa ace za'a fasa daura aure ba, za'a daura auren a gobe idan yaso biki a daga har ta samu sauki, mama tace haj kina ganin haka zaiyi kuwa? Mom tace ba wata matsala wlh, ko da abunda kike tunani ne? Mama tace ba komai amma dole a sanarwa da kawunta mom tace bakomai alhj zaimasa bayani da kansa, mama tace toh Allah yasa hakan shine alkhairi akace amin.

Salim ne ya miqe toh ni zanwuce mom sai na dawo, hannu ya bawa aliyu danuwa kagama shiri fa kan jibin tayi, Aliyu ne yace nifa ba inda zani, salim dawowa yayi ya zauna, meyasa dan uwa? Komai fa angama karkamin haka mana, aliyu yace taya za'ayi natafi nabar er uwata a haka? Yasa kuka, mama tace cikin fada, da yake zaman da zakiyi shi zai hanata mutuwa idan Allah ya tashi kar6ar ranta, ko kuma shi zaisa ta warke, mom tace kima daina fadan haka ba abunda zai samu 'yata, kubarshi kawai idan bai amince ba, yaje next session, mama tace zuwa kam yagama zuwa saidai idan bana raye, baza' ayi kashe kudin banza ba, kuma itama er uwar tashi bazataso yafasa karatu saboda ita ba, dan haka katashi ka fice kafara shiri, Aliyu ya fita a fusace salim ya bishi ya lallasheshi hakan yayi daidai da shigowar kawu da iyalansa.
[11/23, 4:33 PM] Deejah Abdul💗💖: Dream girl na deejah Abdul
7⃣7⃣ Bayan su kawu sun zauna ne, angama gaisawa budar bakin saratu mom nikuma anya wannan ba gawa muke tareda ita ba? hjy asabe tace nima fa haka nagani, mutum kwance haka baya ko numfashi ace yana raye, da ma suncire mata wanna qarafunan a binneta kawai.
Kausar da ka zaune raku6e gefe tinda suka zo batace kanzil ba abun duniya ya isheta, ta miqe a fusace ke ki iya bakinki fa, ni er uwata da ranta ba abunda ya sameta, kunfi likitocin iya aikine da basusan ko tanada rai ko ta mutu ba? Mom tace kausar ya isa, amma hjy bai kamata ku furta haka ba, hjy asabe tace Allah ya baku haquri.
Mom tace alhj gwanda da kukazo dan koma baka zoba alhj zai sameka a gida, zancen daurin aure ne nikeson gayamaka, hjy asabe tayi saurin katseta ai munsan dole kuce kun fasa, mutum a haka munsan ko bata mutu ba dole ta nakasa, toh meh za'ayi da nakasashshe dama? Mom cikin 6acin rai tace wai ke wace irin macece ne? Bakinki bazai fadi alkhairi ba ne kam? Toh ni ameerah ko ta nakasa ba qafa ba hannu bazaisa mu gujeta ba, bare kuma doctor ya tabbatar mana ba wani nakasa a jikinta, akai ne ta bugu shiyasa har yanzu bata farko ba, saratu tace hauka zatayi kenan? Kawu ya daka mata tsawa, saratu kifita kibar dakinnan kan ranki ya 6aci, tafita tana kukan shagwa6a, mom tace alhj zancen daurin aure gobe yana nan bai chanjaba, alhj yayi jim sannan yace toh aini har na sanarwa mutanena anfasa, mom tace lokaci bai qure ba, kasake gayamusu daurin aure yananan, hjy asabe taja tsaki idan kuma yarinyar ta mutu bayan andaura auren fa? Mom tace wannan ba matsalarki bace, ko mutuwa ameerah tayi a gobe bayan andaura aure, zamuyi farinciki ta rasu tareda auren dana khaleed, barema da izinin Allah ba abunda zai samu ameerah, haj asabe baqinciki taga zai kasheta ta fice daga dakin.
Bayan tafita ne alhj yace hjy kuyi haquri, haka nike fama dasu, zantafi yanzu na sanarwa da mutane Allah dai ya tashi kafadunki ameerah ya matse qwallan munafunci ya fice.
[9/14, 1:58 PM] ‪+234 706 332 8523‬: [11/23, 4:53 PM] Deejah Abdul💗💖: Dream girl na deejah Abdul
7⃣8⃣ Bayan fitar kawu mom tace wai wannan wace irin macece, da ita da 'yarta? Mama tayi murmushin takaici, kinsan haka Allah yake halittr bayinsa, wasu mutane basason suga alkhairi gun wasu sai kansu, mom tace Allah ya sauwaqa, sallamar da akayi ta katsesu matar deputy governor ce ta shigo, sai shigowa ake da carton carton na lemuka da ruwa, tashigo ta tambiye mai jiki, akace mata da sauqi, mama tace saidai hjy kiyi haquri ban wayeki ba, hjy ta matse qwalla ta girgiza kai, ina baqincikin da ba alkhairi ne ya hadamu ba, nice uwa marar sa'a da 'yarta tayi yunqurin kashe' yarki sai ta fashe da kuka, dan Allah hjy kuyi haquri ta sauka ta riqe qafafun mama, mama ta share qwalla bakomai qaddara ce bata wuce ranarta, saidai muce Allah ya kiyaye gaba, check ta ciro ta miqawa mama na 2 million, duk da nasan wannan bazai siyowa 'yarki lfy ba, kiyi hakuri ki kar6a dan Allah ba danni ba, mama tace kibarshi wlh bakomai, bama buqatar komai, hjy tace idan baki kar6a ba zandauka baki yafemin bane kuma wannan laifi bazai ta6a barina na zauna lfy ba, idan na tuna abunda' yata tayi kuma ni banyi komai akai ba, mama ta kar6a tayi godiya sannan suka fice.

Kawu kowa da suka fita masifa ya dinga yiwa haj asabe da saratu waisu bakinsu bazai iya shiru ba? Sai sun bata masa plan susa yakasa samun komai, hjy asabe kuka tasa wai ita wlh tasan asiri aka masa dan yanzu baya qaunarta da ita har 'yarta, shidai girgiza kai kawai yayi, a ransa yana danasanin auren mace mai qwaqwalwar kifi irinta, gashi ta haifa masa ' ya irinta, kansu baya ja, da haka suka isa gida.

Khaleed kuwa ana wurin rabon invitation card batareda yasan nashi ake rabawa ba, dan saeed yace masa na abokin aikinsu ne, bayajin dadi shiyasa yace ya taimaka masa, duk inda sukaje saeed shikadai yake zuwa, yabar khaleed a mota, wannan kenan.
[11/23, 5:39 PM] Deejah Abdul💗💖: Dream girl na deejah Abdul
7⃣9⃣ Yau takama ranar juma'a ranar da za'a daura auren khaleed da ameerah, shiga da fice a gida ana shirye-shiryen daura aure, amma khaleed baimada lbr shi ya ajiye tinda ameerah na asibiti ba wani zancen daura aure, Allah dai ya bata lfy ya warware mata wannan fake auren, shima ko zai samo natsuwarsa.

Salim ne yafito yaci uban ado kamar wani dan sarki ya sauko parlour, kausar ta fara shewa wannan wankan yayi bro dole kabani poster tazo suka dauki hotona, sai ga mom da dad sun sauko suma sunci uban ado, kausar ta sheqa ta rungumosu, akayita daukar pictures, salim yace dad uban gayyarfa bai fito ba kar ya 6atamana lokaci, bari naje na fito dashi mom tace kaje ka fito dashi, ya fito ya nufi side din khaleed, qwanqwasa qofa yake, amma khaleed na kwance a daki har wata fever yakeji, masifa yafara yiwa salim ya daina qwanqwasa masa qofa, haka yayi daidai da zuwan saeed wurin, da kuma fitowar su dad, saeed yace salim kaje ku tafi da su dad kawai zanzo da khaleed din, suka shiga motocinsu suka wuce.
Qofa ya fara duka buddy kazo ka bude qofar mana, khaleed haka ya taso ya bude qofar ya koma ya kwanta, saeed yaje ya ta6ashi yaji zafi gau a jikinsa, tashi yayi ya koma mota, ya bude jakaraa ta aiki allura ya dauko da wasu tabs, khaleed na kwance ba zato ba tsammani, Allura kawai yaji an soka masa, saida ya riqe gado da qarfi, 😂 yace aboki wlh ka cika dan iska, da kajimin ciwo fa? Saeed yayi dariya ai nasan kai jarumi ne, tadhi kasha tabs dinnan ka tashi mutafi, khaleed ya kar6a yasha yace, bt ni ba inda zani dan bakada tausayi bakaga yanayin da nike ciki ba ne?
Saeed yace idan ma nabarka a haka ba sauqi zakaji ba, nasan ba aikin da zakayi sai tunanin salmah, dan haka ba wani dogon excuse ka tashi kawai ka watsa ruwa, mutafi ka rakani daurin aure, khaleed yace auren wa kuma, saeed yace mai katin da muka raba jiya, ae yaune daurin auren, buddy katafi kawai bazan iya zuwa ba, miqeshi saeed yayi ya tura toilet, na baka 15 minute kafito, ba barin da zammaka naje nadawo nasamu kayi mushe a daki.
Chapter 20 · 0% Book details