← Book details Dream Girl Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 52

Sashe 42

Dream Girl Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Salmah taja iyayenta da bakinsu ya mutu, dad mutafi wani wawan mari ya sakar mata, ya tureta ta fadi salmah kin cucemu kin lalata rayuwarki, na turaki karatu ashe ke abunda kikajeyi kenan, wlh sai Allah ya saka mana, kije duk inda kikeso kiyi abunda kika ga dama, bani bake, tashi tayi dad nima bani na dorawa kaina ba Allah ne, uwarta tace karkiyiwa Allah karya wallahi ba haka Allah ya yiki ba, nima ba haka na haifoki ba chan kikaje kika koyo wannan muguwar dabi'a kuma mu ba'a gidanmu ba, cewa tayi shikenan tinda kukace haka nayimuku alkawarin bazaku kara ganina ba, zankoma chan inda akafi bukatata, dad kar ka manta sanda ka samomin admission a germany saidai naca banaso kace sai na tafi, so just don't blame me, kar Wanda ya sake yaje nemana kuma, daga yau ku dauka bakuda 'ya mai suna salmah ta ficewarta.

Dadyn salmah yaja matarsa suna kuka sunkai bakin kofa ta silale kasa ta fadi, daidai shigowar doctors aka kwasheta aka dora kan gado su saeed sukayi kanta, wasu doctors sukayi kan khaleed.
[9/15, 2:43 PM] ‪+234 706 332 8523‬: [12/19, 6:36 PM] Deejah Abdul💗💖: Dream girl na deejah abdul
1⃣7⃣1⃣ Doctors sunyi iya kokarinsu suka samo khaleed amma saida aka lika masa oxygen, doctor yayi ta fada yace a guje bata masa rai, duk wani abu da zai bata masa rai a nisanceshi.

Mahaifiyar salmah kuwa jininta ne yayi mugun hawa, doctors sunyi iya kokarin su ganin sun saukar da hawan jini amma ina, take aka rasa ta ta rasu, dad din salmah yayi kuka kamar ransa zaifita, salmah kuwa tasha tsinuwa ba adadi, dad ne yaketa bashi baki aka dauki gawarta aka fita da ita aje ayimata sutura akaita makwancinta.

Jikin kowa yayi sanyi, wannan tashin hankali har ina, fatar dai kawai Allah ya tsayar anan. Ameerah kuwa zaune take gadon khaleed sai mom tayi fada sannan take dagawa ko abinci sai anyi fada takeci, mama ma tazo asibitin mom tayi mata bayanin abunda ya faru, tayi mana Allah ya kyauta ta tafi.

Kwanan khaleed biyu sannan aka cire masa oxygen ya dan farfado, abinci yanaci amma sai ruwa-ruwa, amma dai baya cewa kowa kala, fuskar nan a murtuke ba annuri.

Satinmu daya aka sallamemu dan ya wartsake, saidai haryanzu baya fira saidai karamar magana, haka muka koma gida mom tasa anrufe part din salmah bayan sun kwashe kayan su, dan khaleed yama daina kula wurin da ta zauna bare ransa ya baci.

Tinda muka dawo gida a kullum yana dakinsa zaune, baya ko fitowa saini da nike shiga ina kaimasa abinci kuma ba laifi yanaci, bayan haka ba abunda ke hadani dashi amma yau nayi kudurin nafara kokarin mantar dashi salma ya koma rayuwarsa.

Sport wears na saka er body hug da mini skirt jajaye, naje kaimasa breakfast, na zauna har ya kare ci na kwashe kayan nafita yabini da kallo, koda na dawo yana kishingide yana karanta jarida, jaridar na kwace hannunsa ya kalloni da mamaki, ke miye haka nace nima zan karanta ne, cewa yayi bani kayana kinji, na mike tsaye na juya zan wuce yace ameerah kibani abuna nace, waigowa nayi ok zo karbi gashi, tsaki yaja ya taso zai kwace na dagata sama, hannun yabi zai karba na sake janyeta ina masa dariya, cewa yayi ina wasa dake ne? Daga masa gira nayi sai mu fara daga yau, matseni yayi zai kwata da karfi na wurgata waje ta window, hararata yayi ya juya zai koma ya kwanta, nace ashe ma matsoraci ne kai bansani ba, waigowa yayi ni kike cewa matsoraci? Gwalo nayi masa ya taso ya biyoni na sheka da gudu kuwa, gudu muke muna dariya muna zagaye gida najashi mukayi hanyar garden saida nakai karshe naja na tsaya ba wurin gudu kuma dan ya tare hanya sai matsowa yakeyi ina matsawa har na cimma gina, hannu yasa yayimin rumfa wa kike cewa matsoraci? Nayi shiru ina Girgiza kaina kawai, ya kuramin ido, baki yasa ya cizamin lebe nasa kara ke kin iya surutu ko, nace toh kaine kwana biyu kadaina magana kamar ina tare da kurma a gida ni kuwa kadaici ya dameni, daga kai yayi really nace eh mana, nima na cizar masa lebe, rike bakin yayi nayi sauri na tureshi, na sheka da gudu saida nayi nisa na juyo na masa gwalo, nima na rama girgiza kai kawai yayi yana dariya bai biyoni ba, ni ko na wuce dakina na fada gado ina mayarda numfashi.
[12/19, 7:22 PM] Deejah Abdul💗💖: Dream girl na deejah abdul 1⃣7⃣2⃣ inanan kwance har baci ya daukeni bani na farka ba sai karfe goma 12 agurguje naje kitchen na dora girki na gama na fito nashiga wanka na hado da alwala, kwalliya na tsaya na tsantsara, nikaina nasan nayi kyau nagama nayi sallah, sannan na fito naje dakin khaleed nakaimasa lunch, naga dakin wayam, na buda har toilet bayanan, naje falonsa da main falo duk bayanan, a dan tsorace naje waje ina dubawa motocinsa duk suna nan, garden nashiga na hango shi chan a rakube zaune, nace wato tinda nabar khaleed a wurinnan yananan kenan, zuwa nayi ina lababe, naje ta bayansa na rufe masa ido, ajiyar zuciya yayi khadijah kin rainani ko? Zagayowa nayi ina dariya, ya akayi kasan nice nadan turbune fuska, jawoni yayi na fado jikinsa, ke bakyaji ko? Ya shake kamshin jikina ya lumshe ido, na sakalo wuyansa ina murmushi, tinda nabarka anan kananan kenan? Girgiza min kai yayi tareda lakacemin hanci yanzu nazo daga masallaci na fito, nace oya tashi muje kayi lunch ya langabemin kai, bana iyaci banida karfi, dariya na kyalkyale kaganka kuwa? Kamar baby murmushi yayi kamanke dai, ke kika koyamin nace tashi mutafi, Girgiza min kai yayi bana iya tashi.

Mikewa nayi tsaye, oya tashi in goyaka, mikewa yayi yace oya duka toh, na duka kuwa shiko ya dane baya aikuwa ragajab muka zube kasa, nasa kukan shagwaba shiko meh zaiyi idan ba dariya ba, dariya yake saida yakai kasa yana nunani, raguwa kawai na turbune fuska na fara bubbuga kafa ina kukan shagwaba, ni Allah sai na rama shiko dariya yaketayi, tashi nayi ina zumbure baki na kama hanyar wucewa ni namayi fushi dakai, janyoni yayi ta baya ya rungume i'm sorry, ya waigoni ya rike kunnensa yaje kasa ya taso i'm sorry nace, cewa nayi ni sai ka goyani, ba musu ya bani baya, na tattare skirt dina na dane ina dariya, jira nake naga ya fadi naga shiru, dukan bayansa nayi banga ka fadi ba, ya fashe da dariya waye kedince zaki kadani? Ni ko gudu ma sai inyi dake, shekawa yayi kuwa niko duk na tsorata na rikeshi gam na runtse ido ina ihu, ka tsaya karmu fadi muji ciwo fa.

Bai direni ba sai dakinsa ya saukeni kan gado, ya juyo ya dubeni idona rufe gam, ji nayi ya cijemin lebe na bude ido ina sauke ajiyar zuciya, lakacemin hanci yayi matsoraciya, kece da tsoro kike cewa wani matsoraci, nace bawani nadauka zaka kadamu ne, hannunsa yaja ya tada muscle kinga ni mai karfi ne, hannu nasa na taba, nima na bude nawa hannun zan tada nawa amma banga komai ba, meh zaiyi inba dariya ba ke ko? Kin iya ba mutum dariya.

Cewa nayi oya abincin ka, cewa yayi ok bari na watsa ruwa, ko zaki tayani? Kulalo ido nayi yayi dariya ok matsoraciya jirani inzo ya shige wanka abinsa.
[9/15, 2:43 PM] ‪+234 706 332 8523‬: [12/17, 7:22 PM] Deejah Abdul: Dream girl na deejah abdul
1⃣6⃣3⃣ Kiran sallar asubah ya tadani na farka na ganni a kirjin khaleed, na tsaya ina kallon kyakkyawar fuskarsa, shima ya bude idonsa ya kalloni ya lakacemin hanci matsoraciya, ni dagani kiga kan a tada sallah, ko har masallacin zaki bini ne, narai narai nayi da ido zanyi kuka, ya janyeni gefe ya shiga toilet ya fito nima na shiga, fitowar da nayi instead of naga bayanan sai naganshi tsaye yana jirana, cewa yayi zo muyi jam'in kan ki taramin jama'a da ihu, bansan sanda na fara dariya ba shiko ya tsaya yana kallona yana murmushi, nazo nasaka hijabina mukayi sallah, bayan mungama azkar na jawo qur'an kan bed side drawer ina karantawa but a silent mode, khaleed yace read louder inaso naji nima gyadamasa kai nayi nafara rera karatuna shiko yana saurare da haka har gari yayi haske na ajiye kur'anin, yace zaki koma bacci ne? Nidai zanshiga wanka dan yau kafin 8 nikeso naje office, cemasa nima Allah bazan zauna ba, yace office din zakibini kenan? Nace eh dariya yayi shikenan bari na shiga wankan kije daki ki shirya kan nafito, gyada masa kai kawai nayi ya shige, fitowa nayi ina lababe zanje part dina kamar barauniya, da sanda na wuce wai duk dan kar aji takuna, nakai bakin kofa hannu na rawa na bude kofa na shige da sauri na rufo na mayarda key nacire key din na ajiye, na fada toilet shima nasa masa key, nayi wanka nafito daure da towel, naji ana bubbuga kofa, natsaya nayi jim aka sake bugawa cikin sarkewar murya nace waye, khaleed yace nine sarauniyar matsorata murmushi nayi na bude masa na janyoshi ciki na rufe kofa, cewa yayi wa kike especting ya shigo yanzu?

Nace bakowa, kallona yafarayi sama har kasa, niko na juya ina goge jikina nafara shafa mai, zuwa yayi ya shafamin biya kamar yanda salmah tayimin jiya, na daka tsalle na kurma ihu na dane gado, a tsorace ya kalloni meh yafaru kuma? Ko tabanki da nayi ne? I'm really sorry i don't mean to scared you, bazan kara ba zo ki saka kayanki mutafi.

Shi duk abun ya daure masa kai, dan na tabata ne tayi haka? Amma kuma ai a jikina ta kwana yau, meh mutanen nan suka mata ne da takasa natsuwa har yanzu? Kafin ya gama tinaninsa na saka riga doguwa ta atamfa dikin yayimin das a jiki, shidai sai bina yake da kallo, na feshe jikina da turaruka body spray na saka hijabina da takalmi kalar pattern din atamfana nace mutafi.
Chapter 42 · 0% Book details