← Book details Dream Girl Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 52

Sashe 26

Dream Girl Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Khaleed ma yayi landing saidai traffic hold up ya tsayar dashi a hanya. Muna zaune a garden muna hutawa dan ni wurin yayimin, wata nurse tazo tace its time 4 my medcine, natashi muka koma dakin da aka maidani, dan tinda na farfado anyi shifting dina daga ICU, Mom suka iso sukayi inquiry aka basu number dakina suka nufi dakin.
Ina zaune ina cin lunch sai ganin su mom nayi, da saurina na miqe har ina qoqarin faduwa, dan haryanzu jikina ba qwari na nufi wurinsu, kausar dariya tayi sister inlaw wlh kiyi a hankali kar jinya ta dawo sabuwa akayi dariya, mum ta riqoni ta rungumeni m so happy to see u my daughter nace me too mom, mundade a tsaye a haka sannan ta sakeni naje na fadawa mama, janyeni tayi kinga ni karki karyani, lura nayi tana share qwalla, na tayata mama kukan dadi kike ko? Karki damu bazan mutu da wuri na barki ba, kema sai kinga jikokinki, nayi sauri na rufe baki alamun jin kunya, dan qaramin duka ta kaimin nasa qara, tace mara kunya ashe har yanzu wannan bakin bai mutu ba, dariya akayi mom ta jawoni ta zaunar dani, nidai karki jimata ciwo daga zuwanki, mama tayi dariya ae kunfi kusa yanzu ni gwanda ma da kika daukemun ita, nace mama idan na tafi sai kinyi missing dina fa, Mom tace ina mijin naki na buda baki zanyi magana sai gashi ya fado kamar daga sama, sallamah yayi aka amsa jikinsa duk yayi sanyi ganin su mom da yayi, mom tasha mur daga ina kake, yarasa meh zaice mata, tunaninsa mun gayamata tin jiya bayanan, sosa qeya yayi mom neman wani doctor na tafi a germany, kausar ta kallan na kalleta, mama tace germany dannan wato duk likitocin da ke india basuyi maka bane? Mom tace toh ina likitan yake? Yace bayan na tafi ne kausar ta kirani ta gayamin ameerah ta farfado kuma ta samu sauqi shiyasa Ban daukoshi ba, kausar ta koma kallona nayi mata inkiya tayi shiru, harara ta watsomin ta kauda kanta, mom tace kenan ko hotel baku sauka ba? Tinda kai tin jiya bakanan kausar kuwa nasan a asibiti ta kwana, to kuzo muje hotel dinda muka sauka ku samu daki.

Cewa nayi mom plz kice doctor ya sallameni nima karku barni anan, Allah na warke, doctor ne ya shigo, ya duba hannuna yamin allura, mom tace doctor za'a iya sallamarta kuwa? Yace no saidai zuwa gobe idan sun kwance hannun idan aikin yayi, zasu iya tafiya dani zan iya dinga zuwa kullum na kar6i allura 4 3days.

Mom tace toh mu mungaji munso mu huta, ameerah ki haqura sai goben kawai, suka juya zasu tafi, kausar ma ta dau jakarta, mom tace ina kuma zaki? Tace mom nima inaso na huta ga mijinta nan ya tsaya da ita 4 tonight, mama tace gaskiyarki fa zo muje, haushi harda hawayena, kausar ta kalloni tayimin gwalo, suka hada ido da khaleed ta watsa mai harara ta fita. Mom ta radawa khaleed a kunne son is your chance today to spent time wit your wife, dan idan ankoma biki zamu shiga so bazaka samu chance irin wannan kusa ba, ta fice ta barshi a sandare kamar photo, niko sai share hawaye nake.
[9/14, 4:43 PM] ‪+234 706 332 8523‬: [12/2, 9:14 AM] Deejah Abdul💗💖: Dream girl na deejah Abdul
9⃣1⃣ khaleed ya dade anan tsaye sannan ya shigo dakin waige-waige ya fara, ya hango ledar snacks da drinks dinda kausar ta bari yazo ya diba, ya fara turawa kamar mayunwaci, nidai kallonsa kawai nike, a raina nace ita salmar ta kasa baka abinci ne ko kuma ba abinci a germany? Yanda yake tura bread yana kora lemo ni har abun dariya ya bani, na rufe bakina kar ya lura dariya nike masa, karaf muka hada ido yace abincin germany ba dadine, murmushi nayi ae kuwa naga ka kwaso yunwa na india da dadi kuwa, ya jikin yace min nace da sauqi, sai kuma shiru ne ya biyo baya, sai chan nace masa ya salmah din? Ya wani washe haqora dariyar da baita6amin ba, lafiyanta qalau wlh, i missed dat girl da inada chance da nayi ko 2weeks a germany, bamu wani samu time sosai ba, idan kika ganta yanzu ta samu hutu ta qara kyau, kamar na daukota na taho da ita, haushi ya kamani wai dama wannan ya iya surutu? Meyasa ma na tambiyeshj ita? Cewa nayi cikin fushi a raina, toh meh yahana ka sakota jaka kazo da ita? Ashe maganata ta fito fili, dariya naga yanayi na qura masa ido, kinga ni banyi tinanin haka ba fa, amma da na sakota bag din kuwa, da yanzu sai na cire abata na riqa kallo, ya sake dariya, taisayin kaina nafara ji wato shi ko zancen salmah akayi masa nishadi yake shiga, wayyo ni ameerah, take qwalla ta cikamin ido, na juya kai na share kar ya lura.
Sauri nayi nace masa yaya saeed fa? Waya ya zaro ya kirashi miqomin wayar yayi, ya daga nace hello yaya saeed, cikin farinciki yace princess, Allah mungodemaka inanan inata zullumi ashe ke kin warke? Fira mukasha dashi, yabani aunty fareedah itama, tace qawata akwai special tanadi da nayimiki fa, sai kundawo Allah ya baki lfy, nace ameen mukayi sallamah na bashi wayarshi. Shuru ne ya biyo baya a dakin, har nurse ta shigo ta bani dinner da magani nasha, fita yayi ya dade a waje saida dare ya tsala sannan ya shigo, icecream naga ya miqomin na kar6a na fara sha, shikuma ya koma gefe yana shan coffee, duk sanda zan dago kai na kalleshi sai naga yana smiling, nasan kuwa duk akan salmah ne, haushi ya isheni kamar na tsala ihu amma ba dama, a haka har bacci yayi gaba dani.
[12/2, 9:14 AM] Deejah Abdul💗💖: Dream girl na deejah Abdul
9⃣2⃣ da assubah alarm din khaleed ne ya tadamu, tashi mukayi sallah, azkar dina nayi na shafa addu'oi, sannan na dauko qur'an da kausar ta barmin na fara karantawa, cikin er qaramar muryata da qira'a ta mai dadin saurare.
Khaleed shima ya kammala tashi sallar yayi kasake yana sauraren karatun ameerah, har wata nutsuwa ta saukar masa, saida gari yayi haske, na rufe qur' an na aje, toilet na shiga da kayan da kausar ta barmin, brush nayi nayo wanka na chanja kaya, wata 3quater riga ce da pencil trouser da mayafi, samfurin kayan india ne, kayan sunmin kyau ba laifi na fito, na kwanta a gado na, khaleed kuwa ya bini da ido aransa yace itadai komai nata a nutse takeyinsa, tsaki yayi kuma y do i even care. Karaf muka hada ido dashi murmushi na mai sanyi na masa, nace good morning, ya kawar da kansa gefe sannan yace morning ya jikin nace masa da sauqi, ear piece nasa na kunna qira'a ina saurare, kwanciya nayi na rufe ido alamun bacci, yadan jima yana kallona sannan shima ya shiga toilet ko da yafito, ya chanja kaya, baqar shirt yasa da wando ya fito fes dashi sai sheqi yake, nidai satar kallonsa kawai nike duk inda yayi ina binsa da ido kamar munafuka, wanda bai lura ba zaice bacci nake, snacks din jiya naga ya sake kwasa yaci yasha lemo, da ya gama ya miqe zaifita kuma sai ya juyo ya kalleni, doso wurina yayi niko na qara rufe ido, zuciyata sai harbawa take da sauri, duqowa yayi ya ciremin ear piece dinda ke kunnena, shi a tunanin sa nayi bacci, ya aje wayar a gefen gadona ya juya ya fita, sai lokacin na bude idona ina murmushi, my khaleed you ar not dat bad na qara murmushi, na rufe ido bacci ya daukeni.

Cikin bacci naji ana ta6ani buda ido nayi, kausar ce gira ta dagamun, amarya how was your first night? Naga sai wani sheqi kike, bacci kike amma kowa ya kalleki, yasan kina tareda farinciki coz u r smiling while sleeping, duka na kaimata ke bakida kunya ko? Ina ruwanki da sirrin ma'aurata mukasa dariya, mom da mama suka shigo tareda khaleed, mom tace en matana meh kukewa dariya? Kausar tace mom abun sirri ne, tace kudai kuka sani idan tayi tsami zamuji, nurse ta shigo ta kawomin breakfast da magani, kausar ta kar6a har ta fara bani, sai kuma ta aje, brother kazo ka ciyar da matarka ni nagaji da bata, kaga hannunta na dama a sangale, yi yayi kamar baijita ba, mom tace bakaji meh qanwarka tace bane? Mama tace kibarshi may b kunyarmu yake, mom tace toh wa zai cigaba da kulamasa da ita dama? Ae gwanda ya saba, muje muga doctor yazo ya duba hannun if possibl ya bata sallamah suka fita, kausar ta miqe nima zanbiku ta wuce abunta.
Chapter 26 · 0% Book details