← Book details Dream Girl Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 52

Sashe 31

Dream Girl Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Fadawa nayi kan gado, na cigaba da kukana, wayyo ni ameerah , wannan wane irin aure na saka kaina? A wurina aure nayi amma a wurin mijina kuma is jst like a game, it wil b over in no tym, yunwa ta tasomin har jikina ya fara rawa kan yunwa, na jawo ledojin da ya ajiyemin, kajine da lemo naci nasha nayi qat sannan na samu nutsuwa, toilet na shiga na hado alwala nayi nafila raka'a biyu ta godiya ga Allah, da addu'an Allah ya dorani akan mijina ya samana albarka, na shafa na rufe dakina nayi addu'oin kwanciya na kwanta.
[12/2, 9:14 AM] Deejah Abdul💗💖: Dream girl na deejah abdul
1⃣0⃣4⃣ khaleed ne kwance a dakinsa wai yau shi aka daurawa aure amma bada DREAM GIRL dinshi ba, waya ya dauka ya kira salmah, ta daga shine zaka cemun yarinyar da zaka aura ba sonta kake ba? Yace toh meh kika ganine? Wannan pictures da aka turomin duk wanda ya kallesu yasan happy marriage kayi, qawayena sai dariya sukemin wai an kasani, ni kuwa kasan ba macen da ta isa tayi takara dani, barema kai da nake ganin na mallaka tintini, duk cikin masifa take masa wannan maganar, yace haba sweatheart just calm down mana, ni naki ne tintini har yau har gobe, tsawa ta dakamasa , karka isheni da wannan dadin bakin naka, yace shima cikin masifa salmah ya kikemin tsawa kamar wani yaronki? Yau fa aka kawomin amarya amma yanzu gashi ina waya dake, idan amaryar tawa ta wani dameni yanda kike tinani, a daren yau har zan iya kiranki? Shiru tayi 4 sometimes toh shikenan, inanan dawowa nan bada dadewa ba, nd dat sooner dan you think, kuma idan nadawo take nakeso ka saki yarinyar nan, daz d only way da zaka tabbatar min da cewa dagaske ni kakeso kuma ba wani damuwa da ita kayi ba, yace shikenan ni ko gobe ne kidawo a shirye nike da rabuwa da ita, dama ae yarjejeniya mukayi na gayamiki.

Kashe wayar tayi tana murmushin mugunta i'm sorry khaleed, ni aure baya gabana yanzu, amma dole ne na nunawa qawayena ba namijin da ya isa ya latsani, kuma ba macen da ta isa tamin qwace kamar yanda suke tinani, dama iyayena sun dameni akan na dawo, zan dawo gida just 4 d mean time, idan nayi auren na tabbatar musu da ni na kai mace later na dawo germany na cigaba da harkokina.

Tohfah kunji salmah zata auri khaleed just 4 showup, dan kawai ta nunawa qawayenta ta isa, niko deejah ga khaleed ina kallo sai murna yameyi salmarsa zata dawo soon, nidai idone nawa naga yanda zasu kwashe.

Waya ya daga ya kira saeed shikam har yayi bacci, wane banzan ne yake kirana yanzu? Jin muryar khaleed tasa ya miqe zaune, lfy angon ameerah? Ko wani abune yasameta yanzu? Khaleed yace relax my man good news na samu shiyasa nakasa barin har gari ya waye, saeed yace wow ashe komai ya kammala ka samu amaryarka yanda kakeso congrat my man, kasamu ruwa da dettol ka gasata kafin inzo, khaleed yace kai banson iskanci fa, ina gabas kana yamma, meh kake tunanin zai shiga tsakanina da wannan yarinyar? ko ka manta kan yarjejeniyar da mukayi aure ne?

Saeed yace toh uban meh zaisa ka tadani yanzu? Khaleed yace Salmah ta wil b bak soon, saeed ya saki baki, dama shiyasa ka tadani wlh Allah ma ya isa, toh ubanme kakeso na maka? Toh meh za'ayi dan ta dawo? Khaleed yace aurenmu mana, saeed yace ameerar fa? Toh meh ya dameni dama ae yarjejeniya mukayi, saeed yace toh ae yarjejeniyarku ta shekara daya ce, khaleed yace nifa i don't care salmah na dawowa aurenta zanyi, ita kuma ta kama gabanta, saeed yace lallai kacika butulu khaleed ya Kashe wayarsa, saeed yace dole nayi wani abu kan lokaci ya quremin, amma khaleed bazan barka wannan salmar ta ruguza maka rayuwa ba.
[9/14, 7:21 PM] ‪+234 706 332 8523‬: [12/2, 9:14 AM] Deejah Abdul💗💖: Dream girl na deejah abdul
1⃣0⃣5⃣ Assubah nayi alarm ya tada ameerah, tayi sallah ta jawo qur'aninta da azkar ta shiga karantawa, tagama ta duqufa da addu'oi, sai da gari yayi haske, sai kuma ta kasa bacci, fitowa tayi tana zaga ko ina tana kallon yanda aka tsara mata gidanta, sai mamaki take dan ita ko a mafarki bata ta6a tinanin ta samu wannan daular ba, sai zagawa take tana bude ko'ina tana leqawa, har takai dakin khaleed ba tareda ta sani ba, turawa tayi qofar a bude, shiko ya fito wanka yana goge jikinsa, dagashi sai towel, ya juyo haka towel dinsa ya kwance daidai ameerah ta shigo dakin, ido hudu sukayi ta buga ihu ta fita da gudu, cikin hanzari yabj bayanta, bai tsaya ko ina ba sai dakinta, tunkararta yayi kuma still yana dagashi sai towel din, ta daka tsalle sai saman gado, ya biyota duk ta takure a bango, jikinta sai qyarma yakeyi, zuwa yayi ya matseta ya kafeta da ido, har sunajin bugun zuciyar junansu, ubanmeh kikajeyi dakina? Nidai kayi haquri wlh Allah bansn dakinka bane, ta fara hawaye ohhh toh meh kikaje nema har kika fada dakina? Ya qara matseta ita kuma sai qyarma takeyi, kayi haquri nace bazan qara ba Allah kuwa, 😭 dariya taso ta su6uce masa ya lura duk jikinta 6ari yake, kura ga tsoro ga ban tsoro, wurgata yayi a gado karki sake koda wasa kije dakina, if not zaki samu abinda kikaje nema, ya miqe ya ficewarsa itako tana kwance inda ya barta tana sauke ajiyar zuciya, wannan khaleed din akwai mugu ji yanda ya tsoratani. Ameerah bata qara fitowa daki ba har wuraren qarfe goma sha biyu ga yunwa ta addabeta amma takasa fita.

Saichan taji sallamar kausar har ta miqe sai ta tunada wulaqancin da ta mata jiya ta koma ta kwanta, kausar tayi sallamah ta kar6a mata a daqile batareda ta waigota ba, tace amaryarmu fa, ameerah tayi banza da ita ta miqe toh tinda fishi kike bari inkoma ta juya zata fita, da hanzari ameerah ta riqota ta rungumeta tana kuka, shine kika gudu kika barni da mugun yayanki, kausar cikin zumudi tace meh ya miki? Ko sai munyi gashi ne? Tureta tayi dalla ba abunda ya faru, kausar tace toh meh yamiki na mugunta? Ameerah ta gayamata ta fara yimata dariya, toh ae ke kikace kinji kingani, ameerah tace wannan qatuwar jakar fa? Kausar tace kudinku ne na biki da gifts sauran ma sai mom tazo tukunna, zare ido nayi, tace kije ki kaiwa mijinki kusan yanda zakuyi, a tsorace nace kije dai ke, tace keda mijinki kuma? Cewa tayi 1st dai sai kin tsala ado tukunna, nace kausar yunwa tace ga breakfast dinku chan parlour kan dining kije ki tsala ado tukunna, ta turani toilet ta dawo ta zauna tana jiran na fito.
[12/2, 9:14 AM] Deejah Abdul💗💖: Dream girl na deejah abdul
1⃣0⃣6⃣ koda nafito kausar ta fitomin da wani hadadden sari wai shi zansaka nace mata kinga mutane zasuzo gidannan bazan saka saree ba, tace shikenan wasu kayan india ta daukomin irin dogon rigannan da pencil trouser da mayafinsu masu shegen kyau, kausar ta taqarqare ta tsaramin kwalliya ta fesheni da tiraruka, ta sakamin wata sarqa indian design take na dauki sheqi, tafara daukana pics wai wannan dole nasakashi Dp, turani tayi naje dakin khaleed na kirashi na kama hanya na tafi, saida na tura qofar muka hada ido na tuna da abunda yace, duk na qara zuwa dakinsa sai nasamu abunda naje nema, ae ba shiri na saki qofar na dawo daki da gudu kamar watche aka koro, kausar har tsoro taji lfy? Meh ya faru? Wa ya koroki? Kan na bata amsa sai gashi ya fado dakin, murmushin mugunta tayi, sumui sumui ta miqe ta fita, dama shi ita yake kallo dan baisan tana gidan ba, tinkaroni yayi nafara matsawa baya, meh ya kaiki dakina? Sai ja da baya nike shiko yana matsowa, dama dama yace dama meh? Take hawaye suka zubomin nace toh ka tsaya daga chan na gayamaka mana ina share qwalla, bai tsayan ba niko banfasa ja baya ba, ban ankara ba najini a qasa jakar da kausar tazo da itace ta kadani, matsowa yayi ya miqomin hannunsa alamun na riqa ya tadani, na bashi hannun fozgoni yayi da qarfi na fado masa, matsemin hannu yayi nayi qara inajinki meh kikajeyi dakina? Duk na dabirce na rasa meh zance masa, ok kinason ganina ne? Na girgiza masa kai toh menene? Sai lokacin na kalli jakar da ke gabanmu nafara nuna masa ita da hannu, kallonta yayi miye a ciki? Sai lokacin ya sakeni naja baya da sauri, bude jakar yayi kudine fal a cikinta dollars da nera da wasu gifts anyi wrapping, yace na menene wannan? Nace mom ce tace kausar ta kawo mana, wai namune da aka tara, ta6e baki yayi toh ni meh zan dashi? Cikin mamaki na kallo shi kudi ne fa, yace and so? Ki dauka kawai ni ba abunda zanyi dashi, nace mata toh ni meh zanyi dashi yace ki watsar, har ya juya ya fita, kuma ya juyo dama shikadai na ya kaiki dakina? Kai na girgiza masa, ya fara matsowa toh menene? Da gudu na wuce nayi hanyar fita ya riqoni, ya quramin ido nafara qoqarin qwacewa, da hannu daya ya riqeni amma nakasa qwacewa, kayi hakuri dan Allah yunwa nikeji, toh a gida ba'a koyamiki girki bane? Nima nan yunwar nakeji nace abinci na kan dining mom ta aiko shine dama zangayamaka, ya sakemin hannu na fita da gudu.

Dariya khaleed yayi, wai meh yasa nakeson tsorata yarinyar nan ne? Wata zuciyar tace dan kaga tana tsoronka ne, wata zuciyar tace birgeka takeyi, ya girgiza kai no dat can't be but kawai nasan its fun to watch her getting scared, dariya yayi sannan ya fito dakin.
Chapter 31 · 0% Book details