← Book details Dream Girl Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 52

Sashe 43

Dream Girl Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shidai ameerah ta birgeshi duk shigar da tayi indai fita zatayi zakaga hijabi zata saka, gashi ko batayi kwalliya ba kyau take, naturally beutiful, cewa yayi breakfast fa? Siyayyar da mukayi jiya na kwaso nace meh zakaci? Snacks naga ya kwasa nace kai baka gajiya da cin snacks ne? Yace ya na iya tinda matana basu iya girki ba, harararsa nayi ni Allah na iya girki, yace ke matatace? Wani kallo nayimai mai wuyar fassara muka hada baki tare yana kwaikwayon muryata mukace haka naji ana cewa, duka na kai masa ya goce yana dariya, muka fita na rufe kofa.

Koda muka fita salmah na game field ko ta dauka zanjene oho, mota taga munwuce munshiga khaleed yaja muka fita, kwallon da ke hannunta tayi wurgi da ita cikin jin haushi, khaleed fa naso ya shiga gonarta, yana nufin bayan ya kwana da ita a dakinsa da safe ma bazai barta ba da ita zai dinga fita? I have to do something.

Office dinsa mukaje kowa sai kawo gaisuwa yake, abunda ya farantamun rai duk wanda ya tambaya is she your madam? Yes yake cewa, haka mukayi ta zama a office dinsa, bini-bini ya kalloni, da nayi dogon motsi sai ya tambiyeni abunda nike bukata duk ya kasa tabuka wani abun kirki, karfe goma sha biyu nace masa zanje inda mom, tasowa yayi yace muje ya saukeni, koda ya kaini yace yaushe zanje gida? Nace ya barshi kawai kausar zata maidani idan na tashi, gyadamin kai yayi ya tafi niko na wuce ciki.
[12/17, 7:54 PM] Deejah Abdul: Dream girl na deejah abdul
1⃣6⃣4⃣ koda naje kausar ce zaune a falo tana ganina ta taso da gudunta oyoyo ta rungumeni, nace ba wani nan bayan kin manta dani yanzu sai yaya saeed kike yayi, ta marairaice Allah ba haka bane kiyi hakuri, natsani ganin wannan kishiyar takine, i hate naga broda yana kulata shiyasa na rage zuwa.
Muka zauna tacemin ya kishiyar taki? Take taga nasha jinin jikina, nace mon fa? Tace batanan nikadai ce siyama na skul, ya naga kinyi wani zuru-zuru haka? Harda wani kodewa kikayi nace kausar ni bansan ma ta ina zanfara ba, tace fara ma ko daga ina I'm getting restless, nace mata kausar salmah is lesbian, kulalo ido tayi a tsorace, meh kikace? Taya akayi kika sani? Na kwashe duk abunda ya faru jiya na gayamata.

Mikewa tayi tsaye tafara yawo a tsakiyat falo taje ta dawo, tasake dubana are you sure? Murmushin takaici nayi toh da karya zanmiki? Cewa tayi perfect daz great, nace miye wani perfect? Tazo ta jawoni tashi muje gidan, yau karshen zamanta da broda yazo, yau sai tabar gidannan, dakatar da ita nayi meh kike tinani? Kinaga idan kingayawa khaleed gaskiya zai yarda ne? Tace a'ah nasan bazai yarda ba, zai yarda ne kawai idan ya kamata red handed, just trust me kizo mutafi i have a perfect plan.

Hijabinta ta dauko tasa ta jawo hannuna, muka kama hanyar waje sai naga ta jani zamu fita gate, nace ba ga motarki chan ba? Tace no bazamu tafi a motata ba, adaidaita sahu zamu shiga, binta kawai nayi batareda nasan meh take shiryawa ba, haka akayi kuwa adaidaita sahu muka shiga har kofar gida ya saukemu.

Kausar ta leka gate, bakowa tajani muna lababe kamar barayi muka shiga, cemata nayi ke dalla sakeni tinda ba sata mukazo ba, cewa tayi banason salmah ta ganni ne bare tasan ina gidan, nace toh ma ai batanan ta fita duba kiga ba motarta ma, sannan ta sakeni muka taka muka shige part dina.

Muna zaune a daki mukaji mota ta shigo gate, muka leka salmah ce kuwa, ta dawo ita kadai kuma, kausar tace perfect cewa tayi ina kayan da na siyomiki ranar? Nace mata suna wall drop, taje ta kwaso ta zube akan gado, wata ficiciyar riga ta zabo shara-shara da mini trouser ta mikomin, kisaka wannan yanzu, nace mata kausar have you gone mad? Ya zancemiki mace tana bibiyata kamar mayya, kice na saka wannan kuma? Ai dama wannan tsinannun kayan ne suka jamin masifa, instead of na jawo hankalin mijina sai na jawo wannan jakar.

Dariya kausar tayi, just relax ai yanzu munriga munsan weak point dinta, dan haka ko yanzu zuwa zakiyi ki tsokano mana ita, nace wlh kausar bakida hankali, ni kinsan yanda nake tsoronta ma, jiya fa a dakin khaleed na kwana dan zama dakina ma gagarata yayi, dariya ta sake tace ai kin more kuwa yanzu dai karbi ki saka, nace saidai ke ki saka wolla, tace ai ke take kwadayi ba niba, indai har kinaso ta fita rayuwarku keda broda you have to trust me and wear dis, na karbi kayan naje toilet na chanja na fito, kausar tace wow kinganki kuwa so hot, harara na watsa mata, race the count down begins now.
[9/15, 2:43 PM] ‪+234 706 332 8523‬: [12/18, 7:29 AM] Deejah Abdul: Dream girl na deejah abdul
1⃣6⃣5⃣ Kausar tace oya kije ki tsokanota nasan ai bazata rasa zama main parlour ba, kuma ko part dintane sai kije nace kausar you must be kidding me naja na zauna, tace sister inlaw joke apart Allah dagaske nake, nace kausar wai meh kike tinani ne? Nifa kar plan dinki ya ruftadani wlh i can't stand dat woman there, meh kikeso inyi na barta ta tabani ko meh? Kausar cikin fushi tace kefa Allah kincika tsoro nasan abunda nake, kije kawai ni bance ki bari ta tabaki ba, so kawai nake ta ganki a haka, nasan tinda ta kwallafa rai a kanki tana ganinki a haka hankalinta zai tashi, ki daure ki tafi kawai fatana kawai ta fada tarko, kina zuwa idan ta ganki ki dawo daki nasan zata biyoki idan tazo ta tarar dani ba abunda zata yimiki, nace ba kuma kince bakison ta ganki ba? Kausar tace eh banason tasan na shigo ne kawai but inaso tayimin ganin surprise just ki adana tambayoyinki kije kawai, girgiza kai nayi nace ni bansan inda kika dosa ba nafita na kama hanyar main falo fatana kawai tana ciki, dan bana fatar abinda zai kaini part dinta.

Kamar da gaske na shiga main falo tana ciki kuwa, wani shedanin film take kallo irin nasu, da gudu na dawo dakina ina sheshsheka kamar watche aka biyo alhali ko ganina batayi ba, kausar ta mike da murnarta ta ganki ne? Na girgiza mata kai alamar a'ah tsaki taja ta dauki jakarta ni zantafi tinda kin gagara kiyi abunda na saki zamana anan bayada wani amfani

Da sauri na sha gabanta kiyi hakuri wlh Allah zanje tace oya ki wuce toh, tsayawa tayi niko na wuce gabana na faduwa duk na waigo sai naga kausar ta tsare ni da ido, da haka har nakai kofar shiga na sake waigowa tayimin inkiya just go inside, wata ajiyar zuciya naja na sauke, sannan na dauki kasada na wuce ciki, ga dukannin alama tayi nisa da kallon abunda take kallo dan har yanayunta ya sauya kuma bataji ma shigowata ba, karfin hali nayi na wuce ta gabanta nayi gaban t.v zumbur ta mike tsaye zuwa nayi na dan duka kamar ina neman wani abu, muryarta naji daga bayana sweetie meh kike nema ne bari nazo na tayaki, da sauri na mike tsaye zuciyata kamar ta balle kirjina ta fito tsabar harbawar da take da sauri, innayi wasa fa zansamu heart attack take, amma dakewa nayi nace mata no wani movie nake nema bayanan ma inaga ba anan na ajiye ba, kallonta nayi wani fitinanne kalo takemin da wannan kattan idanun nata, sama da kasa take kallona tana hade yawu, ni ko na daskare wuri daya, cewa tayi naga fitarku da khaleed amma bansan kin dawo ba are you here for me?

Wasu wahalallun yawu na hadiye, na daure na sakarmata wani murmushi, hakan ya kara mata karfin guiwa, wani murmushi tayi na cin nasara ta marairaicemin kai, Allah ina bukatarki ameerah, rashinki yasa nike kallon wannan ko zai ragemin abunda nikeji, amma abun sai dada karuwa yake, ke kadaice maganina ware hannunta tayi come to me please i will make you forget all your problems.

Wani fitsari naji yana neman kuccemin, matsowa naga tanayi, sai da kama hanyar part dina ina ja da baya, just wait there please, girgiza mata kai nayi nace not here please, just follow me sai bina takeyi tana murmushi niko inaja da baya, da haka har nakai bakin kofar dakina naja na tsaya, tayi haka ta sakalo wuyana ta hango kausar a daki, sai naga taja ta tsaya, cewa nayi meyafaru? Bakya bukatana ne? Don't you want me anymore? Da ido ta dinga nunamin alamar induba bayana kamar tayi kuka, kausar nagani zaune tana ware ido, nace ohh kausar yaushe kika shigo? Tasowa tayi meh kikeyi tare da wannan? Nace oh salmah kike nufi? Mutum da abokin zamansa bazamuyi fira ba? Tabe baki tayi ku kuka sani, ni kinga zo inada magana, juyawa nayi wurin salmah i'm sorry nace mata can we chat later? Gyadamin kai kawai tayi amma fuskar nan tata tayi bakinkirin kamar ta kurma ihu, juyawa tayi kamar wadda kwai ya fashewa a ciki, kausar kuwa rufe baki kawai take dan takasa controling dariyarta.
[12/18, 8:12 AM] Deejah Abdul: Dream girl na deejah abdul
1⃣6⃣6⃣ tana shigewa falo kausar ta turo kofa ta fashe da dariya, kinga fuskar mutuniyarki kamar watche aka gayawa duk iyayenta sun mutu, tsalle taga na daka na sheka da gudu tace ke lfy nace ina zuwa toilet naje nayi fitsarin da ke kokarin fitomin tin dazu.

Ina fitowa kausar ta taso miye? Nace fitsari kadan na saki fitsari a gaban salmah aradu, kausar ta kwashe da dariya matsoraciya kawai, ya kukayi ne? Na kwashe yanda akayi na gayamata dariya kamar cikinta zai fashe lallai za'a baki award kin iya acting, nace ai dole nayi acting kin turani gun wannan mayyar Allah da kin kwaso gawata dan da ta rikani inajin zuciyata ce zata buga, dan a tsorace nake daurewa kawai nayi, saida na kawo bakin kofar nan nadan samu nutsuwa shiyasa acting din ya kara kyau, nace ni namayi mamaki da ta kasa ganin yanayin tsoro a tare dani.
Chapter 43 · 0% Book details