← Book details Dream Girl Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 52

Sashe 27

Dream Girl Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Tsaye yayi kamar ya wuche abunshi, ya juyo dai ya kalloni muka hada ido, ya dawo ya zauna, spoon ya dauka ya debo abincin ya zunguromin batareda ya kalla ba, jiyayi anqi kar6a ko da ya lura a hanci yake qoqarin turamin abincin, da sauri ya sauke spoon m sorry plz yace, na fashe da dariya, shima da ya kalli painting da yamin a hanci ya fara dariya, muka riqa dariya kamar zautacci, mom suka shigo, son lallai duniya tayi dadi kace dama, wuri kakeso mubaku da matarka ku kyakyata, nidai duqar da kai nayi alamun kunya, shikuma har yanzu bai rufe baki ba, duk ya kalle fuskata sai tabashi dariya, kamar wani cartoon na koma, tissue yasa ya gogemin hancin, doctor ya shigo ya kwance hannun, ya tura a wani machine ya cire, ya daga sama ya sauke, yace do u feel any pain? Na girgiza masa kai, hannun yaja da qarfi saida nayi er qara, yace very good ur hand is ok now, saidai karkiyi aiki mai wahala dashi ko ki dauki abu mai nauyi sai nan da 1week, na gyada masa kai, allura ya ciro zaimun ya lura banyi breakfast ba, ya ajiye eat your food first, idan kungama akirani namiki alluran den u can go.
Mom ta kallemu wato abincin kuka aje kuna shan soyayya ko? Duqar da kai mukayi tace oya kabata abincin da sauri karku batawa doctor time, spoon ya dauka ya fara bani ina kar6a, saida na qoshi na nunamasa ya isa, ya gogemun baki ya bani magani ya fita kiran doctor.
[9/14, 4:47 PM] ‪+234 706 332 8523‬: [12/2, 9:14 AM] Deejah Abdul💗💖: Dream girl na deejah Abdul
9⃣5⃣ Da assubah ma bayan munfarka nayi 'yan karance-karancena da nasaba nagama, kuma nidai nagaji da kwanciya tashi nayi, na kama hanyar fita ya bini da ido kawai, dakin kausar naje na riqa buga mata qofa, tataso tana tsaki ta bude, koda ta bude na ingejeta na shige ciki, mitsitstsike ido tayi, au amaryar broda ya haka tin da safe? Sai kuma tafara dariya, harara na watsa mata, toh ni meh nayimiki kuma? Nace tambayata ma kike? Dariya ta saka toh miye laifi dan mata ta tafi gun mijinta? Nace nidai karki qaramin haka, cewa tayi sister do u want to get close to broda or not? Nace inaso mana tace toh kina nisanta kanki dashi taya zaki samu kusanci dashi? Nace sis nifa Allah tsoronsa nike somtimes, tace gwandama ki daina, danni yanxu ma nafara, duk wata hanya da zata sa kusamu kusanchi sai na ingizaki kinbita, cewa tayi ki tashi ki koma ni
bacci zankoma, gado taga na haye na kwanta murmushi tayi ta rufe dakin ta dawo itama ta kwanta.

Da safe bayan kowa ya tashi munfito, muka gaida su mom, restsurant dinda ke hotel din muka sauka, mukayi breakfast, sannan muka fito yawon buda ido.

Munje amusement parks kala-kala, da ordinary parks ma irinsu, cross maiden, horniman circle gardens, joseph baptista garden da sauransu.

Muna chan mom ta tuna da zuwa asibiti tace muje da khaleed, bayan anyomin allura ne, horniman garden din yace amaidamu, zuwa yayi ya samu wuri yayi zamansa, nima haka sai kallon mutane da nike, khaleed harda beach saida yasa aka kaimu, shiga ruwa yayi yanata wasa nikam ina nesa akwaini da tsoron ruwa.
Bamu muka koma ba sai yamma kausar sai tsiya take mana, wai dama neman hanyar guduwa mukeyi, shine daga zuwa asibiti mukaje shaqatawa, mom tace kada ki samusu ido, mutum da matarsa, idan angama biki ma ae dole suje honeymoon, a raina nace honey wahala dai, wannan idan na yarda mukaje honeymoon guduwa germany zaiyi ya barni, ina kwance bana motsi ya tafi bare ina qalau.

Mama tace ae dama ambar zancen bikinnan tinda abun yazo haka, muna komawa ta wuce gidanta kawai, tinda angama gyara komai, mom tace wai hakan yayi ameerah? Gyada kai kawai nayi, khaleed yace ae ama daina zancen wani biki.
Kausar tace broda meh kake yiwa sauri ne? Ko munyi bikin ae dole akai maka matarka, harara ya watsa mata ta basar, mom nifa Allah gwanda ayi bikin komai fa munshirya, kuma kinsan kowa cemasa muke biki sai sister inlaw ta warke, mom tace nima dai haka nagani, gobema shopping zamu dan har indian night sai anyi, kausar tafara ihun murna, mama tace itadai tagaji zata shige, mom ma ta miqe, kausar ma ta tashi, jawo hannunta nayi, nace miye naki na wani dagewa sai anyi biki? Jawoni gefe tayi sis we need dis, qawayen salmah nakeso na turawa hotinan biki, nasan dole su tura mata, idan taji haushi may b tace ma ta haqura dariya mukayi muka tafe, khaleed daki shima ya wuce, niko nabi kausar saida muka kai bakin qofa ta shige da sauri ta turo qofa, ta barni waje turus, dole na miqe na wuce dakin khaleed, qwanqwasawa nayj, yace waye? Haushi naji kamar ince ubanka ne, nadai daure nace nice, ya taso ya bude cewa yayi ae na doka a dakin kausar zaki kwana dan naga dazun ma chan kikaje, murmushi nayi a raina wato saida ya biyoni yaga inda naje kenan, yau ma gado ya barmin ya kwana a sofa.
[12/2, 9:14 AM] Deejah Abdul💗💖: Dream girl na deejah abdul

9⃣6⃣ cikin en kwanakinnan biyu da suka rage mana mun zagaya ko'na munbuda ido, munje cinema kala-kala munyi kallon sababbin films masu fitowa, Biggest shopping mall da ke mumbai kusan duk saida muka zagasu, irinsu , high street phoenix dake lower parel mumbai, Inorbit mall dake malad, infinity mall dake new link road mumbai, Oberoi mall dake goregan east, Artria mall dake worli, Mun jibgo kaya kamar zamu buda shop, su suhaila dake gida ma duk mun za6a musu.

Yauma itace last day dinmu a india, wasu shagon jewelries mukaje da designer saries, india akwai designer jewelries both passion jewelries and gold, mom duk sarqoqin da ta zubamin a lefe, saida ta kwasarmin wasu designer gold, wai wa 'yannan na biki ne, tanaso nayi looking like a princess, mama tayita hanata mom tace itada ' yarta, mama taja bakinta tayi shiru tana mamakin irin wannan soyayya da mom keyimin, itama kausar ko kishi batayi sai za6amun take.

Kausar ce ta jawo hannuna ta hade da na khaleed wani shock naji har tsakiyar kaina, ba shiri na janye, tsakiyarmu ta shiga ta jamu sai gefen saries, gasunan masu shegen kyau, wai mu za6a irin na celebrities ne, chan ta jawo wani, sis Allah wannan zaiyi masifar yimiki kyau, kinga wannan irinshi ne naga priyanka chopra tasa a wani award night da akayi last year, dariya nayi toh priyanka kikace ni miye hadina da ita, tace ae sis kinfita kyau da diri saidai ta gwadamiki hasken fata, nace Allah kausar idan mutum ya dauki zugarki sai yafara girman kai, nace ae sai ki gwadamin yanda zansaka saree din, wata mata data gani a shop din taje ta taho da ita, wai dan Allah ta nunamana yanda ake saka saree, itako da murnarta ta amince wani daki da ake chanja kaya ta shiga damu, muka cire na jikinmu, muka saka er qaramar rigar saree din, amma munbar dogon wandonmu da yake ciki, ita ko ta laulaya mana ta liqe, kausar ta walwalemin gashin da ke bayana ya zubo, harda fita ta dauko bindiya wannan da aka maqalawa a goshi ta doramin, ts jani mukaje gaban mirror, nikaina saida na kasa gane kaina, saree din ba qaramin kyau yayi mana ba, idan kaganmu kamar indiyawan barin ma kausar da take fara tas sai ta sade dasu, nima din namafi wasu indiyawan haske, dan suma da baqar fata a cikin su, jawo hannuna kausar tayi muka fito, kowa ya kallemu sai kaji yace wow u ar looking very beutiful muko muce thanks, khaleed taje ta jawo sai qaremata kallo yake, tace broda look there, sannan ya kalloni, quramin ido yayi 4 quite sometimes, kausar sai kallo take tana dariya, shi baimasan tanayi ba, saida ta kirashi broda, broda, ya kaga matar taka? Basarwa yayi, wannan wane haukane maza kuje ku chanja kayan, kausar ta ja hannuna zo muje wurinsu mom, gabanmu ya tare ba cewa nayi kuje ku cire kayan ba? Su mom suka iso wurinmu, khaleed ina su ameeran ne? Nuna mata mu yayi, dariya mom tayi wai en matanane bangane ba, wow wlh kummafi indiyawan kyau, mukayi dariya, er qaramar camera da muketa daukar pics da ita duk inda mukaje ta fiddo, ta fara daukarmu hotuna, taba khaleed taja hannun mama suka shiga cikinmu aka dauka, khaleed mom ta tura akayi mana mu 3, kausar ta jaye akafara daukarmu mu 2, kausar sai wani zuwa take tana maqalemu tana bamu style mom na dauka, mom sai cewa take muyi smile, khaleed dole tasa yakeyi har aka gama, kausar ta kar6a tana dubawa, wow mum wlh munsamu na sourveniers sunyi kyau sosai, mom tace ku wuce mutafi hakannan dare ya fara yi, kuma morning flight zamu dauka zuwa 9ja, muka wuce muka koma hotel kowa ya gaji dakinsa ya wuce direct.
Chapter 27 · 0% Book details